Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 71 of 78
Wannan zuwa na Daddy ya tsayama Sulaiman a rai matuÆ™a. Zuciyarsa bata nema bugawa ba sai da aka cire camara É—in da Smart yace a gefen kunnensa. Wani irin raÉ—aÉ—i yake ji a ransa da mamakin ta ya akai camara a jikinsa bai sani ba, har tsawon wane lokaci yaran nan suka É—auka suna wasa da hankalinsa batare da ya taÉ“a farga ba. Sai yanzu ya gane Smart ne *_AMM_* da ya dinga turo masa saÆ™wanni. Tabbas yaron yayi gaskiya, ya É—aukesa a bakomai ba, amma gashi ya zame masa komai. Ya kaisa Æ™asa a lokacin da bai zato ko tsammani ba, ashe abinda suke zargin wani babban mai faÉ—a aji ke musu shine ke aikata musu shi. Yaron da basu taÉ“a kawowa a hasashen su ba. Shi baima taÉ“a kallonsa a jerin maÆ™iyan da zasu iya juya rayuwarsa haka ba. Ranar yaci kuka mai suna kuka da har sai da ya rasa hawaye. A rana ta uku aka É—aukesa da ga Kano gaba É—aya zuwa Lagos. A rayuwarsa bai taÉ“a sanin akwai azabar rayuwa irin wannan ba a duniya. Duk da yasan shi mugune, sun kuma kashe mutane da dama a dalilin harkar Æ™wayar da sukeyi idan suka bijire musu. Amma wannan É—in na musamman ne. Duk taurin zuciya da taurin kai irin na Alh. Sulaiman a wannan gaÉ“ar sai gashi yana hawaye, shi kansa yasan anzo dai-dai wajen kuma. A randa aka isa da shi Lagos wahalar da yaci bai ma san ya fara kiran sunan Dada da Baba Garko ba akan suzo su taimakesa ya tuba, har Hajiya Turai da Tajuddeen da sauran Æ´aÆ´ansu sai da suka sha kira. Wannan itace nadama mara amfani, domin kuwa bakin uwa shine ke tasiri akansa tare da haƙƙokin mutane dana Æ´aÆ´ansu da suka zama sanadin lalatama rayuwa ta hanyoyi da yawa, gashi nan a kwanaki uku kacal rayuwarsa ta sauya a yanda ko maÆ™iyinsa ya gansa dolene ya tausaya masa, dan a yau ma sai da suka sake masa karaya biyu a hannu É—aya. Bai san sanda azaba ta sakashi fara lissafo abokan huÉ—É—arsa ba. Wanda dama tunda aka kamashi hankulansu a tashe suke matuÆ™a suma, sau faman kai gwauro da mari sukeyi akan al'amarin shiyyasa ma aka É“oye Alh. Sulaiman É—in ashe..........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 6ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
......An cigaba da kame-kame a ƙasar mai ban tashin hankali. Inda harda sunan wani tsohon shugaban ƙasa, da wasu manyan ƴan siyasa a gwamnoni da ƴan majalisu ma dake ci a yanzu ya fito, sunayen manya-manyan ƴan kasuwar da ba'a taɓa zato da tsammani ba. Tare da manyan ma'aikatan gwamnati da tsabar yanda ake kallonsu iyayen ƙasa ake kiransu. Al'amari yakai intahar da mai gyarashi sai dai UBANGIJI. A cikin abinda baifi awanni a shirin da huɗu ba na cikar kwanakin Sulaiman a hannun hukuma sojoji suka sauke shugaban ƙasa tare da wasu gwamnoni. Hankalin mutane ya tashi matuƙa da tunanin ko juyin mulki ne, sai gashi bayan cikar wata a wa ashirin da huɗun an maye gurbin shuwagabannin da mataimakansu amma an maida shugaban ƙasar shima....
    _____★
 An wuce da Dada da Baba Garko zuwa Æ™etare domin duba lafiyarsu. Hakan yasa Lulu shiryawa itama ta koma wajen mijinta bisa umarnin su Daddy. Taso ganin Ummah itama amma hakan bai faru ba saboda kai-kawon da tayi duk bata jin daÉ—in jikinta. Smart da kansa yaje tarbarta airport shi da É—ansa. Ta rungumesu su duka cikin Æ™arfin hali da jin kewarsu duk da dudu kwananta tara ne kacal. Suna isa gida ta zube kwance a falo, hakan yasa kowa ya fahimci bata jin daÉ—in jikinta. Kiran Ammah da ya shigoma Smart da ke kallonta ne ya hanashi magana. Sai da ta katse ya kirata dan haka yake musu duk wanda ya kirashi koda a yaran gidansu ne. Bayan ya gaisheta da girmamawa take tambayar Æ´an tafiya sun iso lafiya. Cikin É—an damuwa yace, “Gata nan duk a galabaice muna shigowa ta zube a falo.â€
    “Ya salam, ai kuma dai kunyi ganganci ne. Dan ma ALLAH ya bata Æ™arfin hali ne kawai. Amma a halin da take ciki ai ba kowa zai iya É—aukar wannan kai-kawon ba da hayaniyar da aka sha. Sai kuyi Æ™oÆ™ari ku tafi asibiti dan a tabbatar da lafiyar abinda ke jikin nata da ita kantaâ€.
   Cike da mamaki Smart da ke kallon Lulu ya ce, “Ammah abinda ke cikinta kuma? Wani abu tace miki yana damunta?â€.
     Cikin murmushi mai sauti Ammah ta ce, “Aiba saita faÉ—amin ba Babana. Duk wanda ya kalli Mawaddat ai yasan akwai ciki a jikintaâ€.
    “Ciki fa Ammah?â€.
  “A'a kaini tsaya, wai ku baku san da cikin ba ne ko mi?â€.
 “Wlhy Ammah ni ban san tana da ciki ba. Itama kuma na tabbata bata san da shi É—in baâ€.
    “Kai nikam yau naga sakarkarun yara. Yanzu ita Bilkisun dake tare da ku ga wannan tsohuwar ace suma duk basu lura ba. Aiko wannan cikin in bai kai wata huÉ—u ba ma to gab yake da kaiwa. Dan da alama ma babu jimawa da zuwanta nan ALLAH ya bada shi. Sai kuyi Æ™oÆ™ari dai kuje asibiti toâ€.
   A sanyaye yace, “To Ammah insha ALLAHUâ€.
  Yana yanke wayar Lulu ta miÆ™e cikin Æ™arfin hali zuwa bedroom. Dan wanka kawai take sonyi. Da kallo suka bita su duka. Iya Tabawa ce ta katsesu da Æ´ar dariyar ta. A tare duk suka juyo suna kallonta. Tace, “Ai tun watan daya gabata na fahimci uwar É—akina nada shigar ciki. Nayi shiru ne dai kawai saboda dambarwar da naji anayiâ€.
    Dariya aunty Bilkisu tayi sosai tana kallon Smart daya rasa abin cewa. “Ka gani kunata faman fitina ashe ma ALLAH ya bada abinda ake ma rigimar. Nima sai gab da zata tafin nan na fahimta sai dai zuciyata bata tabbatar ba shiyyasa bance komai ba. Ashe Iya Tabawa ta mana na manya ne ma ita. ALLAH ya raba lafiya, ya bata lafiya ita kumaâ€.
   A hankali ya amsa da Amin yana sauke ajiyar zuciya. Sai kuma ya miÆ™e yabi bayanta zuwa bedroom É—in. Ya samu tana wanka, dan haka ya zauna a bakin gado yana zaman jiran fitowarta. Babu jimawa ko sai gata ta fito tana faman dafe kai. MiÆ™ewa yay ya riÆ™ota ganin kamar tana tangaÉ—i. Ƙasa-Æ™asa ya ce, “Miya faru kuma?â€.
  “Ina ganin jiri†ta bashi amsa a hankali. Kwantar da ita yay a saman gado ya rungumeta a jikinsa yana mai sauke tagwayen ajiyar zuciya. Idanunsa a lumshe yana shafa mata kai ya ce, “Dama kin san kina da ciki amma kika kasa sanar min?â€.
     Kanta ta girgiza masa a hankali da faÉ—in, “Wlhy ban sani ba. Duk da ina jin canji a jikina ba a yanda na saba ba na É—auka kawai yanayi ne dan lokacin cikin AA ma sai da ya kai wata kusan huÉ—un na sani bayan ma anyi yunÆ™urin zubar da shiâ€.
   Sake ƙanƙameta yay a jikinsa yana mai jin wani irin farin ciki mara misalin kwatance. Sosai yake son ƴaƴa a rayuwarsa. Kodan ta tashi cikin yawa ne a gidansu shiyyasa oho. A hankali ya shiga bata sumba yana mai sanya mata albarka. Ita dai riƙe kukanta kawai takeyi amma ita tasan mi take ji. Bawai bata farin ciki bane ba. Tana jin tsorone kawai dan ita kaɗai tasan irin wahalar da tasha a lokacin haihuwar AA da sanda cikinta ya tsufa. Sai dai a yanzu tana tsoron nunawa kuma ta takaloma kanta bala'insa. Haka ta cigaba da shanyewa da barma ranta kawai tunda dai mai afkuwa ta afku, sai dai tana mamakin ciki a jikin mace nayan tayi planing, gaskiya mutumin nan maye ne, itakam taga takanta kenan. Shi da kansa ya shiryata yana ta dai ƙoƙarin danne dariyarsa, dan daya tuna abinda tayi kuma ga cikin da take gudu sai yaji dariya na taso masa, haka dai ya daure ya kimtsata sannan ya fita ya kawo mata kunun gyaɗar da tace tana so yanata fan murmushi sai dai baice komai ba duk da bakinsa fal yake da zance. Kaɗan ta sha tace ta ƙoshi, daya matsa ma sai ta fara yunƙurin amai. Dole ya ƙyaleta suka wuce asibiti. An dubata tare da tabbatar musu baby na cikin ƙoshin lafiya. Gajiya ne kawai yay mata yawa, dan haka sukace taje ta samu hutu sosai a gida dan tana buƙatar bedrest. Sai magunguna da suka bata na ƙarin kuzari da ranakun da zata dinga zuwa ana duba lafiyarta suka kuma cire mata abinda ta sakama jikinta kamar yanda ta buƙata, dan bataga amfaninsa ba kuma. A haka suka kwaso suka dawo gida Smart na kwasar dariya dan a wannan gaɓar dai ya gagara daurewa. Itako sai kawai ta sakar masa kuka dan ta gane abinda yakema dariyar. (Mugu ɗan masa kenan😂😂)
   A ranar dai duk ƙwaɗayinsa dole ya haɗiyesa saboda kwana tai babu lafiya, sai amai da take faman yi ko ruwa ta sha. Washe gari dole suka sake komawa asibitin. Kwantar da su sukayi suma dole. Gashi washe gari yana da wasa mai zafin gaske dan gab suke da kaiwa ƙarshen primier link. Alhmdllh Dan yana taka rawar gani sosai ga kuma team ɗinsu na gaba da kaiwa zagayen ƙarshe. Babu yanda zai yi dole ya shirya ya koma ya barta da su aunty Bilkisu....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.