Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 68 of 78
   ★Yaran Alh. Sulaiman nacan sun kasa sun tsare a tituna jiran fitowar Lulu da ga gidansu ko gidan Uncle Yousuf. Anan ko su har sun fice gidan Alh. Sulaiman sai fitar motar matarsa ya jiyo. Ƙwafa yayi dan yayi alwashin koya mata hankali itama dan yasan ita ke zuga masa yara suna mai rashin mutunci. Ranar matan sun masa akan dawowarta gidan. Jiya kuma Tajuddeen ya masa akan Dada. Bai damu da fitar tata ba dan yasan asibiti ta wuce. A asibiti sun samu jikin Dada yau dai Alhmdllh, da sauÆ™i irin na malam bahaushe da ake faÉ—i. Amma dai har yanzu bata gane komai, sai ambaton sunan Sulaiman da take a hankali hawaye na ziraro mata. Duk wanda ya shiga dubata sai ya fito da mamakin yanda ta damu da al'amarin yayan nasu Sulaiman haka, bayan rashin mutuncin da yake zuba musu salo-salo. Sai da ta koma barci ne Baba Garko ya ce iyayen su sameshi gaba É—aya a gida. Ganin haka sai itama Lulu tai kiran Smart kawai akan zuwa wajen Ammah. Sai da yay É—an jimmm sannan ya amsa mata da “Naga dai kin matsa da ganin Ammahn nan, É—an bani 10minut hakaâ€.
    Baki ta murguɗa masa tamkar tana gabansa....
   *_GARKO HOUSE_*
   Ƴaƴansa ne gaba ɗaya. Alh. Sulaiman da wanda suka rasu biyu mahaifiyar Lulu da Sultana ne kawai babu. Sunyi kusan zaman mintuna huɗu kafin ya fito. Bayan yakai zaune suka sake gaishe da mahaifin nasu. Da kai ya amsa musu yana gyara zama dan zuciyarsa sam babu daɗi. Sai da ya gama ƙare musu kallo ɗaya bayan ɗaya kafin yay gyaran muryar da ta sakasu sake maida hankalinsu garesa.
    “Na taraku anan ne a dalilin abinda yay sanadin kwanciyar mahaifiyarku asibiti duk da ni har yanzu ban san minene ba shiyyasa na buÆ™aci ganinku mu gani tare dan zata iya yiwuwa nima na tsinta kaina a yanayin da yafi nata ma...†cikin tashin hankali da ruÉ—ani duk suke kallonsa. Bai damu ba ya cigaba da faÉ—in, “Nasan wasunku sun san rikicin dake tsakanin É—an uwanku da matansa wasu basu sani ba. A watannin da suka gabata rikicin da bamu san tushensa ba ya É“arke a tsakanin Sulaiman da matansa su dukansu har suka wuce gida. Sai daga baya uwar Æ´aÆ´ansa ta dawo amaryar da al'amarin yafi tsamari a kanta taÆ™i ta koma. Na barsu ne naga iya inda abin nasu zai kai sai kuma gashi jiya ta samemu anan gida. Flash drive ta kawo mana ta tace shine sanadin rikicin nasu. Da ga haka batai mana wani Æ™arin bayani ba ta tafi. Bayan wucewartan ne mahaifiyarku tazo ta É—auki Flash É—in ta wuce da shi sai mai aikinta ta isarmin da saÆ™on gata can ta faÉ—i babu rai. Duk abinda zai saka mahaifiyarku a wannan mummunan yanayin bazai kasance mai sauÆ™i ba. Shiyyasa tun jiya na kasa dubawa ni kaÉ—ai na zaÉ“i mu duba tare da kuâ€. Ya Æ™are maganar yana jawo tab É—in Dada da har yanzu flash É—in ke a jiki. kusa da shi duk yay musu nunin su dawo. Haka suka zauna wasu kusa da shi a Æ™asa wasu a kujera. Babu wanda zuciyarsa bata kaÉ—a ba a lokacin da fuskar marigayiya Mawaddat ta bayyana. Kafin sukai karshen videon babu wanda jikinsa baya rawa a cikinsu, ga hawaye duk ya cika musu idanu. Auta da yafi kowa shaÆ™uwa da Sultana a gidan baima san sanda ya fashe da kuka ba tamkar Æ™aramin yaro. Kasa jurewa Baba Garko yayi ya miÆ™e jikinsa na karkarwa. Sai dai dole sukai saurin riÆ™osa saboda hajijiya dake neman zubar da shi a Æ™asa, shima sai kawai ya fashe da kuka. Kukan mahaifin nasu ya sake tayar musu da hankali. Suma duk suka fara sharar hawaye..........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 5ï¸âƒ£8ï¸âƒ£
.........Kiran Smart ya saka Lulu tashi ta koma gefe. Kafin ma tace wani abu ya furta, “Akwai matsala fa Baby luv. Dan Kawunki ya baza yaransa sosai nemanki. Fitarki a asibin nan ma inaga sai da jami'an tsaroâ€.
    Murmushi Lulu tai har yana iya jiyo sautinsa. Ta wawwaiga gefenta, tabbatar da babu kowa a kusa da ita cikin sake Æ™asa da murya ta ce, “Karka damu zan tafi yanzu. Ka turo min address na wajen kawai kai daiâ€.
  “Kin san mi kike faÉ—a kuwa. Taya zaki fita a gaÉ“ar da wannan mara imanin ke nemanki ruwa a jallo. Ayanzu haka asibitin yake shirin tahowa dan ya samu tabbacin kina a ciki. Ga Uncle Yousuf nan zuwa shi da Daddy maâ€.
       “Ka kwantar da hankalinka zamu wuce plan E ne yanzu a kansaâ€.
   “What! Plan E fa?. No no no Mawaddat. Bakya ganin halin da tsohuwar nan take ciki. Mu rushe plan E ma kwata-kwata bashi da amfaniâ€.
   “Shiko keda amfani musamman a wannan gaÉ“ar Mr A. Dan babu abinda ya rage mana kuwa sai plan E É—in. Dada ta riga taga video, shine ma dalilin kasancewar ta a wannan halin. A yanzu haka Grandpa da Uncles suna zaman meeting kuma nasan duk a kansa ne. So kaga abinda ya rage kawai mu Æ™arasa sauran aikin. Dan haka yanzu zan saki....â€
    Da sauri ya ce, “Maw....†kafin ya ma Æ™arasa sunan nata ta yanke wayar. Dan zuciyarta gaba É—aya ta riga da ta gama kaiwa bango. Duk kiran da yake mata bata É—aga ba. Cikin abinda baifi mintuna biyar ba ta gama sakin videon a É“oyayyun shafukan data É—auki tsawon lokaci tana raino da tara followers. Shafi ne da dama yake taka rawar gani akan harkar fyaÉ—e da shaye-shaye. Ta ginashi tun lokacin da su Dada suka saceta. Zuwa yanzu shafukan nada É—unbin mabiya saboda abubuwan da ake posting a cikinsu. Sunasa kuma guda É—aya ne a instegram, twitter, facebook, TikTok, da website. Sunan wanda ta saka, da abinda ta rubuta a saman video É—in yasa cikin Æ™anÆ™anin lokaci ya samu makallata masu É—unbin yawa, kafin kace mi an fara shearing É—insa.Â
   Yaron Alh. Sulaiman da suka kafa suka tsare a bakin asibiti na jiran fitowar Lulu ne ya fara cin karo da video ɗin, shima wani abokinsa ne ya tura masa yana tambayar ya duba wannan ba ogansa bane. Wani ihun tashin hankali ya fasa batare da ya farga ba. Har takai wanda ke ɗan wuwwucewa ta wajen suna kallonsa. Jiki na rawa ya shige mota. Kira ya dannama Alh. Sulaiman dake tsaka da yin online meeting shima a mota dan yana hanyarsa ta tahowa asibitin ya samu kira da ga Lagos. Sun buƙaci ya ajiye koma mi yake yi zasuyi online meeting na gaggawa. Hakan ya sashi samu waje yay parking hankali a tashe. Suna tsaka da tattaunawar akan batun kayansu ne dai kiran malami ya shigo masa. Bai yi niyar ɗagawa ba sai da yaga kira na biyar na sake shigo masa kuma duk da ga malamin ne. Yasan baya masa irin wannan kiran mafarautan, dan haka zuciyarsa ta bashi lallai akwai matsala. Dole yay excusing kansa ya ɗaga kiran.
    “Oga ka duba na tura maka saÆ™o ta WhatsApp. Wlhy akwai matsala. Babbar matsala ma kuwaâ€.
  Ba Æ™aramin faÉ—uwa gaban Alh. Sulaiman yayi ba. Babu shiri ya shiga WhatsApp É—insa. Ai kawai sai ga mutumin waya na neman suÉ“uce masa. Duk da shi ya ga video É—in amma tashin hankalinsa anan a ina malami ya samesa shi kuma? Ko amaryarsa da flash É—in ke'a wajensa ce ta tura masa? Kai ina. Rashin samun gamsashiyar amsa ya sashi kiran malami. Muryarsa har harÉ—ewa take wajen tambayarsa a ina ya samu video É—in. Malami da gaba É—aya yake a ruÉ—e ya ce, “Oga bama ni ba, a kowace waya zaka iya samunsa a yanzu. Dan an sake shi ne a wasu shafukan sada zumunta da ke a manyan apps da mutanenmu suka bama amanna. A yanzu haka wani abokina ne ya tura min wannan bayan na turo maka nima na shiga bincike wlhy tako ina videos É—in trending sukeyi. Acikin abinda baifi minti arba'in ba miliyoyin mutane sun kallaâ€.
   Karo na farko jikin Alh. Sulaiman ya shiga kakkarwa ta haƙiƙa. Bai gama dai-daita da wannan bala'in ba wani kiran ya shigo masa. Mai kula da ɓoyayyen Companyn sa ne na magunguna. Ruɗanin da yake ciki ya sashi ɗagawa batare da ya farga ba. Bai gama dai-daita wayar a kunnensa ba furucin Babban mai haɗa magunguna ɗin Companyn nasa ya daki kunnensa.
      “Mun shiga uku Alhaji jami'an tsaro ne zagaye da dajin nan da Companyn nan. Gasu nan sun gama shiryawa da bindigu suna bamu umarnin mu miƙa kammu ta sauƙi kosu cinnama Company ɗin wuta. Yaya akayi haka Alhaji? Taya suka san da wannan wajen duk taka tsantsan ɗin da mukeyi na tsawon shekaru. Shike nan na mutu Alhaji kofa aure banyi ba balle na bar mai mun addu'a†ya ɓarke da wani irin kuka da ya nema fasa kwanyar Alhaji Sulaiman da gaba ɗaya ya gama jiƙewa da zufa. Ƙitt ya yanke kiran tare da tada mota a haukace. Wani kiran yaga yana shigowa, baida buƙatar duba wanene ma balle ya ɗaga. Kai tsaye gidansa ya nufa cikin wani irin mahaukacin gudu. Kaɗan ya rage ya take maigadinsa da ya gigita da horn. Baiyi parking na kirki ba ya fita cikin gudu-gudu daya firgita ma'aikatan gidan. Dan babu abinda babbar rigarsa keyi sai tashi sama bulummm-blummm-blummm. Yana gab da shiga falonsa ya nema yin wani uban tuntuɓe sai gashi ƙasa wanwar. Fuskarsa ta wani irin dunguruwa da ƙasa. Duk da azabar datake ratsa masa lips da goshe da kan hanci bai damu ba ya miƙe cikin ƙarfin hali. Sai ga jini na ɗiga yararara. Falon ya afka a ɗari uku da sittin, yana ajiye ƙafarsa ciki wayar da abokan huɗɗarsa ne kawai a ciki ta cigaba da ruri. Kamar zai fasa ihu ya ɗaga....
    “Alhaji Sulaiman kayi takanka. Aiki ya buÉ—e wlhy yanzu haka an kame su Olu.....â€
   Wani irin kuka Alh. Sulaiman ya ɓarke da shi kawai tare da yakice babbar rigarsa da hular ya watsar. Sai kuma ya kwasa a guje zuwa cikin bedroom ɗinsa. (Gaskiya ka zare😂🤣😂🤣😂🤣😂🤣) Passport ɗin sa ya ɗakko, da gudu ya sake fitowa yana kai waya kunnensa. Malami yake kira yana ɗagawa ya ce masa ya siya musu ticket yanzun nan ta online nama kowacce ƙasane. Jirgin da zai tashi yanzu-yanzu dai yake buƙata. Yayi maza kuma su haɗu a airport.
     Hankalin ma'aikatan gidan nashi ya tashi ganin gaba É—aya kamar ya zare. A take sukai kiran Hajiya Turai suka sanar mata gida da babu lafiya. Dan sun gagara gane kan Alhaji gashi nan ya shigo a haukace, ya kuma fito ya shiga mota da alama sake fita zaiyiâ€. Kafin sukai Æ™arshen wayar ma shi ya fice a gidan a haukace......
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.