Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 28 of 78
    Washe gari da yamma suka wuce Canada har da Smart dake jin wani irin faɗuwar gaba lokaci-lokaci, yakanyi sauri ya ambaci sunan ALLAH. Wannan ziyara tazo ma Lulu a bazatar bazata. Dan bata san wainar da ake toyawa ba sai kawai ganin Usman tai da baƙi. Lokacin da suka shigo tana toilet ne ita da Mamy dake gasa mata jikinta da towel kamar dai yanda ake cikakken wankan jego a Nigeria duk da Lulu tasha maganin da ya dace Mamy bata barta ba kullum sai ta mata safe da yamma ita da ɗan jinjiri.
    A hankali take tafiya Mamy biye da ita, tayi fayau da ita sai haske data Æ™ara da wani cikar ido irin na jego dan tana samun kulawa sosai irin ta malam bahaushe a wajen Mammy duk da cs akai mata. Alhamdullah kumburin ciki da tai duk ya saÉ“e amma baza'a kirata ramammiya ba kai tsaye. Sanye take cikin doguwar riga mara nauyi dake a buÉ—e sosai saboda yanayin inda aka yanka ta. Baya tai zata faÉ—i saboda firgicin ganin abinda idanunta suka gane mata, sai da Mamy ta riÆ™ota tana faÉ—in, “Mawaddat yi a hankali kinjiâ€. Daga lips É—in Lulu har zuwa jikinta rawa yake yi, É—aya bayan É—aya take binsu da kallo tun daga kan Daddynta har zuwa mutum na Æ™arshe da ke tsaye ya É—an jingina abango da harÉ—e Æ™afafunsa waje guda. Sanye yake cikin Suit milk da sukai masifar masa Æ™yau da fitar da cikar haiba da kamalar da ya Æ™ara, ga wani irin Æ™amshi mai sanyi da daÉ—in shaÆ™a, gaba É—aya ya canja da ga Smart na Nigeria zuwa wani baÆ™in bature mai aji a yanzu. Yanda yay tsaiwar Æ™asaita da harÉ—e Æ™afafunsa waje guda idanunsa a waya yana daÆ™ila kamar baya a wajen saika rantse ba shine ke zumuÉ—in azo ba fiye da kowa. Sai da Mamy ta ambaci sunan Lulu ne ya É—an É—ago idanun nasa a hankali da take kira na macizai kamar zai lumshesu sai kuma ya zuba mata su cikin shammata da bazata.
Wani irin girgiza zuciyarta tayi ƙirjinta na bugawa da sauri-sauri. Rashin mafita ya sata juyawa cikin tsumar jiki ta basu baya tana mai rumtse idanunta da masifar ƙarfi. Ammah ce ta taka a hankali zuwa gareta, cikin tausayawa da ƙauna ta kira sunanta. Kasa juyowa Lulu tayi sai jikinta da ke ƙara ƙarfin rawa. Riƙo hannunta Ammah tayi ta juyo da ita a hankali, sai kaiwa ta faɗa jikin Ammahn ta rungumeta tsam-tsam tare da sakin kuka mai tsuma zuciya.
A hankali Smart ya sauke idanun nasa Æ™asa yana wani irin haÉ—iyar zuciya da sauri-sauri. Dai-dai nan Ummita ta shigo É—akin da sallama bayanta goye da baÆ™on duniya dake barci. Turus tai tana kallonsu itama cikin tsoro da mamaki, yayinda su kuma suka zubama jinjirin bayanta ido. Uncle Yousuf ne yay Æ™arfin halin mata nunin ta kunto yaron. Sai ta kalli Mamy. Kai Mamy ta jinjina mata alamar ta kuntosa babu matsala, dan haka ta É—an saki ajiyar zuciya tare da kunto yaron ta miÆ™ama Uncle Yousuf É—in. Kamar ko ya sani sai ga idanu ya É—an buÉ—e yana motsa baki alamar neman abinci. Dariya Uncle Yousuf ya saki da faÉ—in, “Oh oh Aliyu dai kawai ne anan babu wani banbanci wlhy sai na shekaruâ€. Yay maganar yana Æ™arasawa gaban Abba da Daddy cikin sassarfa. A hankali Smart da idanunsa ke kan yaron ko Æ™yaftawa babu tun shigowar Ummita ya wani lumshe idanun da suka kaÉ—a a hankali yana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Jin al'amarin yake kamar a mafarki, shi Aliyu Hydar ne da É—a na mutum matsayin mallakinsa a wannan duniyar. Ya arrahaman ALLAH mai alkairi. Furucin Lulu da ke faÉ—in, Ammah nayi kewarku cikin kuka ya sashi buÉ—e idanun nasa ya zuba musu su. Murmushi Ammah da ke sharema Lulu hawaye takeyi, kafin ta kama hannunta ta Æ™arasa da ita a saman gadon da take jiyyar. Dai-dai nan Abbah ya Æ™arasa da Jinjirin ga Smart, nannauyar ajiyar zuciya Smart ya ja tare da fesarwa, sai yaji ma duk ya sake daburcewa. Fahimtar hakan da Abbah yay ne ya sashi sakin Æ™aramar dariya da sake miÆ™a masa yaron. A hankali ya miÆ™a hannayensa duk biyu Abba ya saka masa yaron a ciki, sai da yay masa kallon kusan sakanni goma kafin ya matsar dashi saman Æ™irjinsa ya rungume tsam-tsam dai ga hawaye sharrrr. Uncle Yousuf dake murmushi ne ya Æ™araso gareshi, cikin tsokana ya ce, “A'a Æ™anina kaga zauna karka zube mana a Æ™asa majiyatan su sake Æ™aruwa kumaâ€.
   Furucin Uncle Yousuf É—in ya sata sake É—ago idanu a karo na biyu ta kallesa, sai akai sa'a shima ita É—in yake kallo har yanzu yaron na'a rungume jikinsa sai dai ya share hawayen. Harara ta balla masa da É—auke kanta tana tura baki. Sai ya samu kansa da sakin murmushi yana wani Æ™asa-Æ™asa da idanu shima. Ammah da ke ankare da su su duka ta ce, “Babana zo mana naga sabon uba dana sake yi, danni kam kai da Mawaddat kun zama Kakannina yanzu kam tunda kun haifa mini Babanaâ€.
     A hankali ya tako gaban Ammah cikin yanayin nan nasa na nutsuwa da kasancewa jarumin namiji tsayayye. Maimakon ya miƙama Ammah babyn sai ya kai zaune a kujerar gaban gadon kusan da Mawaddat da hankalinta ke kan Uncle Yousuf da ke mata magana ƙasa-ƙasa.....
Bayan an gaggasa Lulu ta gama ma Daddy da Uncle Yousuf shagwaÉ“a da koke-kokenta suma sukai mata faÉ—a akan barin É—akin mijinta tabi Dada. Ta basu haÆ™uri da amsar kuskurenta. Sunji daÉ—in nuna nadamar tata kuwa a gaban kowa. Duk alkairin Ummita da Mamy da Usman gareta bata É“oye ba. Su Abba sukai musu godiya sosai da wannan karamci duk da akwai sannaya tsakanin mahaifin Usman É—in da Daddy. Bayan komai ya natsa an fahimci juna Usman yay ma su Abba jagora zuwa masauki, har lokacin kuma bakin Lulu da Smart bai saÉ“a ba, sai dai Æ´ar satar kallon juna, koda yake ma shike satar kallon nata, itako tayi biris kamar ta ma manta da shi a É—akin take nunawa. Baiji komai a ransa ba game da hakan dan halinta kuma ai sai dai ya bama wani labari yanzu. Lulu akwai jan aji, koda wasa bata yarda ta zama a Æ™asa ba akan al'amarinta. Lokacin da zasu wuce Usman ya ce ai shi Smart a barshi anan tare zasu wuce gida, suje su ya fara kaisu masauki sai ya dawo ya samesa. Mamy da Ammah kam dama tuni sun fice zuwa É—ayan É—akin gidan. Itama Ummita sai ta zare jikinta cikin dabara wai bari ta wanke kayan baby data jiÆ™a É—azun. Harara Lulu data fara tsarguwa da wannan Æ´ar zare jikin da ake É—ai-É—ai tabi Ummita da shi, sai dai batace komai ba dan Ummitan ta fita tana mata dariya...........âœï¸
*_😂Kar naji wani yace komai kuma ehe. Musamman ma dangi dangi Smart ɗinnan. 🙈Koda yake akwai su aunty fa🚴🚴_*
  Â
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.