Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 50 of 78
_Kiyi son ranki Dan lokacinki ne ta wajen mu🥱😂😂🚴🚴_
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 4ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
.......Smart ya samu zama da Daddy da ya shigo London a ranar da Lulu ke cika kwanaki biyar. A ranar sun buga wasa a cikin London É—in ne, bayan sun tashi ne sukai zaman tattaunawa su uku harda Uncle Yousuf da ya shigo domin kallon wasan shima. Daddy ya damÆ™a masa camara, tare da tabbatar masa Sulaiman yana shiri na musamman a kansu. Dan a yanzu haka akwai wata yarinyar baturiya da ya gano an turota ta shiga jikin Smart É—in. Shiyyasa ma yay azamar kawo masa matarsa kusa da shi saboda gudun kar'a samu akasi. Murmushi Smart yayi da firzar da iska. Kansa a Æ™asa ya ce, “Karka damu Daddy in sha ALLAH babu abinda zai faru. Kafin na mallaki iyali nafi Æ™arfin kaina ma balle yanzu da na tabbatar da har zuri'a na fara tarawa. In dai al'amarin Sulaiman ne yabar damunka, dan a yanzu haka a tafin hannunmu yake. Abinda nake buÆ™ata a wajenka kawai yanzu bayan wannan camara É—in shine list É—in abokan huÉ—É—arsa. Sannan ka sa su Hassan subar Abuja su koma Kano gabanku. Dan Sulaiman ya fara kai musu hari ta hanyar aboki, a yanzu haka ana gab da jan ra'ayinsu da wani kasuwancin da nake Æ™yautata zaton irin shigo-shigon da akai maka neâ€.
   Sosai hankalin Uncle Yousuf da Daddy ya tashi, dan sam Daddy hankalinsa bai kai wajenba saboda wani babban business da ya dauki hankalinsa kwana biyun nan. Smart kuma bai sanarma Uncle Yousuf ba dan yakan É“oye wasu abubuwan gudun tada musu hankali. Muryar Daddy har rawa take wajen faÉ—in, “Aliyu yaya akai kasan wannan kai da kake anan?â€.
  Murmushi Smart yay masa, cikin shafa kai ya ce, “Daddy koyarwarka ce ai. A yanzu idanuna a buÉ—e suke akan duk wani motsin su Sulaiman da tawagarsa. Sannan Usman ya sake zame min cctv camara. Dan yanzu haka yana Nigeria yin wani aiki da ya shafi hakan ma. Sannan Uncle Yousuf shine jagoran tafiyar,..â€
   Da sauri Daddy ya dubi Uncle Yousuf. Murmushi yay masa ya kauda kansa shima. Smart yay dariya shima da cigaba da cewa, “Mu yanzu fatanmu Daddy kaje ka kwanta abinka ka huta. Karka damu da duk wani Æ™ulle-Æ™ullensu dan biye muke da su. Yanzu haka a daren jiya sunyi zama kanka harma da Abba. Sannan akwai kayansu dake hanyar shiga Nigeria. Kayane masu nauyin gaske da suka haÉ—a kusan kaso bibbiyu na dukiyarsu domin kawosu, dan mugayen kayan shaye-shayen ne kawai a cikinsu da in har suka samu shigar da su zasu samu maÆ™udan kuÉ—aÉ—e. Target É—in mu yanzu muna zargin Sulaiman nada Company na sarrafa magunguna a É“oye, sai dai bamu san a ina Companyn yake ba, shine muke bibiya domin mu tabbatar...â€
    Ji Daddy yay kamar ya saki kuka, hannayen Smart da Uncle Yousuf ya kamo a cikin nashi, sai ma ya rasa mizaice da su. Sai ga hawaye kawai na gudu a fuskarsa. Da ga Uncle Yousuf har Smart rikicewa sukayi. A take suka shiga jera masa tambayoyi. Sai ya sakar musu murmushi yana goge Æ™wallar tasa da faÉ—in, “Kunga bafa wani abu bane. ALLAH yay muku albarka. Ban taÉ“a tunanin zanga irin wannan ranar ba a gareni. Domin na É“ata tsahon shekarun girmana a tunanin yanda zan É“ulloma wannan al'amarin ne. A duk sanda nayi hangen sako su Hussain a ciki sai zuciyata ta Æ™i aminta da hakan, saboda su sunada rauni. Sannan har yanzu suna a kan dokin Æ™uruciya ne ba komai suke kallo a mai muhimmanci ba. Aliyu kai É—an halak ne, nagodama ALLAH da yasa ka zamo mijin Mawaddat, na kuma godema É—an uwana da yay wannan haÉ—in alkairi. ALLAH yay muku albarka. Ya kare rayuwarku da ta ahalinmu gaba É—aya. ALLAH ya Æ™ara É—aukaka ku, ku zama abin alfahari da babu irinsu a wannan zamanin. ALLAH ya albarkaci rayuwar Aliyu Æ™arami da takwarana Isma'il (Ra'is) da Kamaluddeen, yasa suji Æ™anku fiye da yanda kuka jiÆ™anmuâ€.
    Cikin rauni Smart da Uncle Yousuf ke amsawa da Amin. Smart na Æ™ara jin Æ™aunar surukin nasa na ratsashi. Ga Uncle Yousuf Daddy ya juya. A hankali ya furta, “Nasha gaya maka Yousuf kaine babana a wannan matakin, narasa baba ne kawai a suna, amma ga babana a kusa dani.....â€
   Cikin katseshi Uncle Yousuf ya Æ™yalÆ™yale da dariya. Sai kuma ya rungumesa da faÉ—in, “Oh oh Yaya ni Wlhy kunya kake sakani, ni dai ba sai kace komai ba. Karka manta fa kaine na tashi nakema kallo a matsayin mahaifi kai da aunty Khareema. Kun raineni tun bansan kaina ba. Kun gatantani tun baku san minene daÉ—in Æ´aÆ´a ba. Wlhy raina fansa ne a wajen kare ku daga duk wani maÆ™iyi da zaice kune abin harinsa. Ni dai fatana ka cigaba da kwantar min da hankalinka kawai da mana addu'a. Sannan ka janye mana ra'ayin su Æ´an biyun kamar yanda Aliyu yace shine kawai aikinka.â€
   Kasa cewa komai Daddy yayi, Smart dake saurarensu yana murmushi ya É—an fesar da numfashi yana É—an jujjuya camara É—in. “Inaga a wannan gaÉ“ar ya kamata Mawaddat ta fara aikinta. Dan haka zan duba abubuwan cikin camara É—in nan tare da ita. Sai dai ina jin tsoron al'amarin ta dan bata da haÆ™urin kawaici ma abu, zata iya buÉ—e mana aiki da wuri wlhyâ€.
    Yanda ya Æ™are maganar cikin marairaicewa ya saka Daddy da Uncle Yousuf kwashewa da dariya. Dan kuwa suko suka san wacece Mawaddat. Daddy yace, “Aliyu kamar kasan abinda nake tunani kenan ALLAH. Dan Mawaddat yanda kasan zawayi haka take. Ballema ta Æ™ullaci Sulaiman É—in a yanzu, dan bakaga yanda taima Dada bane ba ma fa. Abinda kawai zamuyi shine da zarar kun gama gani sai mu samu lokaci mu zauna da ita mu duka kafin na wuce. SauÆ™in ma ga babanta da ya san matakan bida ita yanda ya kamata sai kaga tayi abinda ake soâ€
   Murmushi kawai Uncle Yousuf ya keyi shi dai. Yace “Ku gama gulmarta duk sai na faÉ—a mata ai, dama kun mata wayo kun kawota nan. kai kaine za'a hana tuwoâ€... Yau maganar yana nuna Smart.
   Dariya Smart da Daddy keyi, Daddy yace, “SauÆ™in abinma kaine gaba-gaba wajen Æ™ullawar dan nayi recording.â€
  Smart ya kasa daina dariyar waɗan nan mutane. Komai nasu a sauƙaƙe cike da ƙauna da soyayyar juna. Suna ƙara masa ƙaimi akan ƙaunar ƴan uwansa shima.....
   _______★
   A É“angaren Lulu tun fitar Smart itama ta fice a gidan. Asibiti ta nufa saboda maganar Smart dake cimata rai akan shi baya saÉ“a saiti. Haka kawai take jin tsoro a ranta, ita yanzu ta samu ciki kuma ai taga bonu. Yaushe ma yaronta yay Æ™warin hakan. Bawai bata son yara ba, amma dai tafi son ko zata sake haihuwa sai AA ya kai irin 5years haka. Yanzu kam tana ina zata fara haÉ—ama kanta cakwakiyar nan, ga business ga rainon AA, ga fitinar ubansa, ga rainon ciki da hidimar Æ™ungiya dana aikinta. Ta samu ganin likita, babu wani kwana-kwana tace planning zatayi, amma su fara tabbatar da babu wani abu a jikinta, duk da dai a ganinta haÉ—uwa uku bai zama lallai a samu wani abu ba, to amma idan tai la'akari da farkon haÉ—uwar aka samu cikin AA sai hankalinta ya sake tashi taji ta kasa yarda da kanta. Doctor dai ta mata dukkan abinda ya dace sannan ta bata magani, acewarta a iya bincikensu mahaifarta fresh take babu komai. Amma ga magani tasha koda ma an samu akasi marar zata sake wankuwa fass. Daga haka suka saka mata abu a jiki ta dawo gida tana jin hankalinta a kwance. Ta iske har lokacin Smart bai dawo gidan ba. Dan haka ta Æ™irÆ™iri aiki dan zama waje É—aya ya isheta. Tsaff ta gyara gidan tare da musu girkin Nigeria yau. Tana kammalawa tai wanka, kayanta da ya rage É—aya tak ta saka ta dawo falo ta zauna dan AA tunda suka dawo barci yake abinsa. Ta shagala a kallo ya shigo gidan da sallama hannunsa É—auke da kaya. Bata motsa da ga inda take ba ta dai zuba masa ido, shiko nashi idanun na kallon gidan ne da yanda aka gyara shi, aka canja zaman abubuwa da yawa. Gyaran mace dabanne. Ya ayyana a zuciyarsa yana ajiye kayan hannunsa a hankali. Kusa da ita ya kai zaune cikin yanayin gajiya ya ke faÉ—in, “Madam ya gidan?â€.
    Baki ta tura da faÉ—in, “Ni ALLAH idan baka daina cemin Madam É—in nan ba zamuyi faÉ—a ko kaima na saka maka suna. Sai kace wata tsohuwa?â€.
   “Oh da yarinya kike É—aukar kanki, ai kin tsufa tunda gaki da AA. Nan da shekara ashirin zaki ga anzo fara miki gaisuwar uwar mijiâ€.
     Dariya ta Æ™yalÆ™yale da shi, ta ce, “Kai kuma Baban miji koâ€.
   Murmushi yayi yana É—an girgiza kansa. Sai kuma ya lunshe ido ya sake buÉ—ewa a kanta. “Ina boss É—in gidanne naji shiru?â€.
    “Barci yake, shiyyasa nake hutawa ta ai.â€
  “Ai yanzu ga baban shi ya dawo hutu ya Æ™areâ€. Yay maganar yana kissing kuncinta da kwantar da kansa a kafaÉ—arta. A hankali ta sauke numfashi da lumshe idanunta itama. Dan zuwa yanzu duk yanda taso cigaba da riÆ™e kanta salonsa na barazanar tonata ne. Ƙarfin hali ne kawai da taurin kai irin nata. A hankali ta ce, “Yaya wasan?â€.
    “Alhamdullah bakin Æ™i zuwa kallo baâ€.
   “To ni Wlhy ban iya kallon Æ™wallo baneâ€.
  “Sai ki fara koyo aiâ€.
“Zan Æ™oÆ™arta in shan ALLAH kodan kai. Ni yanzu ma maganar da nake son maka shine jibi fa ya kamata mu komaâ€.
     Batare da ya buÉ—e idonsa da ga rufen da suke ba ya ce, “Ina kenan?â€.
   A shagwaÉ“e ta ce, “Nigeria manaâ€.
“Uhhyim yin me?â€.
Idanu ta zuba masa da mamaki, “Ya zakace yin me bayan kasan ayyuka na baro na taho nan, kuma ni da shirin sati É—aya na taho ko kwana goma. Wlhy inada abubuwa masu yawa acanâ€.
    KaÉ—an ya buÉ—e idanunsa yana kallonta, tsahon mintina kamar bazaiyi magana ba sai kuma ya firzar da numfashi. Cikin deep voice É—in nan nashi da babu wasa a cikin fitar sauti ta ya ce, “Mawaddat! Ke yanzu idan ance miki ki Æ™ara tafiya kibar mijinki sai ki tafi? Kiyi lissafi shekarar aurenmu É—aya da wattani takwas kenan fa. Amma bamu taÉ“a zaman cikakken wata guda ba har yanzu. Idan ke baÆ™ya jin damuwa da hakan ni gaskiya ina ji. Sannan haÆ™urina ya Æ™are ina buÆ™atarku a kusa dani yanzu. Shekarunmu tafiya suke bakwai komawa baya ba, ko sai Æ™arfina ya Æ™are sannan zaki fiskanceni a gaÉ“ar da bazan iya komai a gareki ba. Na waiga ma na ganku a kusa da ni farin ciki nake ji. A yanda nai wasa a fili yau kowa yasan ina cikin farin ciki mara misali, aure ibada ne fa bawai son zuciya ba ko ra'ayin kanka a yanda kaso tafiyar da shi. Dan haka maganar komawa na soke shi, ba yau ba, ba gobe ba babu ma rana kawai at all. Dan haka karma ki sake mun maganar data shafi hakan ranmu zai É“aci ne kawaiâ€. Ya miÆ™e fuska a tsuke ya bar falon zuwa bedroom........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.