Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 63 of 78
   *_★UK★_*
 Cikin tashin hankali Lulu ke kallon Smart. Dan duk abinda ke faruwa tsakanin Alh. Sulaiman da matarsa akan idonsu ne kasancewar sun saka direct camara a jikin Alh. Sulaiman batare daya taɓa farga ba. Sun yi wannan aikinne kuma a lokacin da ya tafi jiyya bayan jami'an tsaro sun sake sa akan kidnapping ɗin Lulu da yayi. Sun haɗa baki da likitansa aka saka masa camara a gefen kunne ta wajen wuyansa a zuwan wani tabon theatre da akai masa ne a wajen wai na'urar na rike jijiyar kunnensa. Wannan aikin Uncle Yousuf ne, sun zaɓi saka masan ta yanda bazasu gansa ba sai dai suga abinda yake aikatawa saboda yanayi na yau da kullum irin na ɗan adam. Wanka da makamantan hakan. A kuma duk lokacin da zai shiga ɗaki da matansa ko aikata wata Masha'arsa da karuwansa sukan tsaida gani daga wajensu domin kiyaye dokar ALLAH. Ta wannan direct camara suke sanin duk wani motsin Alh. Sukaima batare da shi ya farga da hakan ba dan yana kallon abinda aka saka masan ne a yanda aka faɗa masa cewar tana riƙe jijiyar kunnesa da ta samu matsala.
    “Wannan mahaukacin fa zai iya kashe matar nan. Ya kamata muyi wani abuâ€. Lulu ta faÉ—a cikin tashin hankali itama ganin yanda Kawun nata ya fita a hayyacinsa. Murmushi kawai Smart yayi yana É—an lumshe idanu da zamewa ya kwanta. Kamar bazaice komai ba sai kuma zuwa can ya firzar da iska yana bata amsa da, “Babu abinda zai maita, wannan hargagin da kikaga yanayi na rashin mafitane kawai da ruÉ—anin da yake a ciki. Amma ba itace a gabansa ba yanzu Daddy ne da ke sai kuma mu da yake son sanin su wanene. Ina mai tabbatar miki yanzu haka gidan Daddy zai jeâ€.
    Da sauri Lulu ta ce, “What! Gidanmu fa kenan?†sai kuma ta fisgo computer ɗin gabanta ta sake buɗewa batare da jiran amsar Smart ɗin ba. Ilai kuwa sai ga Alh. Sulaiman na kwaɗa gudu a saman titi. Cikin ƙanƙanin lokaci sai gashi a anguwarsu, a ma ƙofar gidansu. Sai dai ya gagara ƙarasawa saboda jami'an tsaro da ke zagaye da street ɗin ma gaba ɗaya musamman jikin gate ɗin gidan nasu. Wani irin duka ya kaima steering ɗin kamar zai fasa ihu. A haukace yay reverse ya koma ganin jami'an tsaron sun yo kansa.... Bata ma san lokacin data kwashe da dariyar data saka Smart buɗe idanu yana kallonta ba...
___________________★
   Abubuwa tako ina suna cigaba da kwaÉ“ema Alhaji Sulaiman Garko. Domin kuwa da zaman meeting na maganin matsala da yayi musu. Dan kullum a cikin yinsa suke. Kowace hanya sunbi domin ganin sun cutar da Daddy ko zuri'arsa al'amarin ya gagara. Yanda Daddyn ke zagaye da jami'an tsaro lamari ba'a cewa komai. Sun kai hari gidan su Smart shima dai, sai dai anyi rashin sa'ar samun gidan a baje sai masu aikin gini. Iya bincike kuma kowa a anguwar sai yace bai san inda suke ba a yanzun. Fahimtar kamar raina masa wayo sukeyi ya sakashi komawa gida rai a É“ace neman mafita. Kowa bai nema ba a matansa ya nufi sashensa kamar zai tashi sama. Wani irin kallon É“acin rai yabi falon da shi, ganin yanda ya barsa a harmutsensa haka ya dawo ya tadda abinsa. Abinka da mai zuciya a kusa, tuni ransa ya sake É“aci. A dai-dai nan Hajiya Turai ke shigowa sashen nasa. Ganin ko'ina a harmutse ga shi yanata faman huci ya sata zuba masa ido. Sai kuma cikin dauriya ta ce, “Alhaji lafiya kuwa kake miya sameka haka?â€.
    “A'a a cikin turnuÆ™un yaÆ™i nake? Ke ban san iskanci fa da rainin wayoâ€.
  “Ikon ALLAH, ALLAH ya baka haÆ™uri da ga tambayaâ€.
 Bai sake tanka mata ba, itama saita fara Æ™oÆ™arin tattara falon. TaÉ“a Laptop É—in sa da tayi ya sashi tunawa da Flash É—in dake jiki. Cikin tsawa ya ce, “K bani ita nan!â€. Bata musa ba ta miÆ™a masa zuciyarta na sake shiga mamakinsa. A fisge ya amsa. Sai dai me babu Flash É—in a jiki. “Ina Flash É—in jiki yake?â€.
   “Flash kuma? Ni banga wani Flash ba, a gabanka fa na É—aga taâ€. Wani irin kallon zan kashe ki na binne anan ya shiga binta da shi. Hannu ya miÆ™a mata alamar bani. Sai duk ta sake dabircewa. “Wai Alhaji kana lafiya kuwa. Wlhy ban É—aukar maka wani Flash ba. A gabanka fa na É—aga Lap-top É—in nan ba wani waje naje da ita ba balle kace.â€
    Babu zato babu tsammani taji saukar mari har biyu. Kafin ta gama dawowa a hayyacinta ya sake miÆ™a mata hannu da tsananin tsawa yace, “Turai!! Baniâ€.
      “Wlhy tallahi Alhaji ban É—aukar maka komai ba. Wai yau ka fara zama dani ne? Koka taÉ“a ajiye abinka ka nema ka rasa da har zaka É—aga hannu ka maran!â€.
    “An mareki ko zaki rama ne?â€.
  “Bazan rama ba, amma zan barka da ALLAHâ€. Ta faÉ—a tana ficewa fuuu. Mutumin naku tuni zuciyarsa neman fitowa take ta baki, amaryarsa da ya bari a falon nasa ta kuma ji komai ce tazo masa a rai. A harzuÆ™e ya nufi sashenta, babu ko sallama ya banka Æ™ofar ya shiga. Baiko kalli Æ™anwarta dake gaishesa a falo ba ya wuce bedroom É—inta kamar zai tashi sama.
    “Wlhy aunty ba Æ™azafi bane ba naga komai fa da idona, kuma na faÉ—a miki Æ™anwar nan tasu data rasuce ma fa a video É—in, É—ayar kuma Æ™anwar tasu ce ta É—auka mahaifiyar yarinyar nan da ake cema Lulu....â€
  WaÉ—an nan kalamai da suka nema fasa zuciyar Alh. Sulaiman ne ke fitowa da ga bakin amaryarsa. Abinda kuma yaji na tabbatar masa taga komai da komai kuma ta faÉ—a ma wadda suke wayar. Ta buÉ—e baki zata sake magana idonta ya sauka a kansa. Zabura tayi, kafin ya iso gareta ta kwasa da gudu ta shige toilet ta banko Æ™ofar. Yana dannawa tana dannowa har dai ALLAH ya bata sa'a ta murza key. Wasu manya-manyan ashariya ya fara mulmula mata yana jijjiga Æ™ofar tamkar zai cireta. Itako duk da a tsorace take faÉ—i take, “Wlhy ko zaka kasheni bazan bada baâ€.
  Ashariya ya cigaba da ingiza mata da tabbatar mata wlhy sai ya kasheta.......âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 5ï¸âƒ£4ï¸âƒ£
.......Hankalin ƙanwarta da ke jiyosu a tashe ta dannama mahaifiyarsu kira. Tana ɗagawa ta sanya mata kuka da faɗin suzo dan gida babu lafiya. Ga mijin auntyn ta nan zai kasheta. Wannan kalmar ta kisa ta ɗaga hankalin mahaifiyar tasu, babu ɓata lokaci kuwa sai gasu sun iso. Iya ƙoƙari iyayenta sunyi Dan ganin ya kwantar da hankalinsa an sasanta komai amma yaƙi sauraresu. Ya kuma babbake ƙofa yana jiran ta fito. Dole mahaifinta yay kiran Baba Garko. Baba Garko yaso ƙin shiga maganar, sai da ya jiyo manya-manyan ashariya da munanan kalaman bakin ɗan nasa ta cikin waya sannan ya shiryo yazo. Karo na farko kenan da suka haɗu tun bayan badaƙalar auren Lulu. Da ƙyar aka fidda amaryarsa a gidan bayan yasha mari a hannun Baba Garko. Sam bakinsa bai mutu ba, faɗi yake sai ya kasheta idan bata bashi abinda ke wajenta ba. Itako tana rantsuwar bazata bada ba. Ana tsaka da wannan rikici itama Hajiya Turai ta fito ƴan aikinta janye da akwatuna. Bayan ta gaida Baba Garko cikin girmamawa yake tambayarta mike faruwa a gidan haka. Tana kuka ta sanar masa iya abinda ta sani, harda marin da itama yay mata. A cewarta tasan itama amaryar tasa babu abinda ta ɗauka masa, ya jefa abunsa wani wajene kawai ya huce a kansu, dan haka ita gida Sokoto zata wuce. Baba Garko bai hanata ba dan shi yama rasa abin cewa gaba ɗaya.....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.