Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 62 of 78
   Ni dai nace, “Hummm🥱🚴🚴â€.
__________★
   A ɓangaren su Alh. Sulaiman suna tsaka da kukan targaɗe sai ga karaya ta samu. Dan kuwa dai al'amarin Nadiya ma ya bayyana wa duniya. Inda ta tabbatar da cikin jikinta na su Hon. Nakowa ne dan su duka babu da wanda bata mu'amula. Ta kuma tabbatar da cewar su ɗin manyan diloli ne na miyagun kwayoyi, dan ko ita sune suka koya mata shaye-shaye. Ta kuma tabbatar da in har sunce ƙarya ne su fito duniya su musa zancenta ita kuma zata bada manyan hujjoji a kansu. Tace bayan itama akwai yara da yawa da suka lalatama rayuwa ta hanyoyin shaye-shaye da zinace-zinace. Wasu sun jima da rasa ransu, wasu iyayensu sun koresu a gida sun shiga duniya. Wasu kuwa a gidan iyayen nasu ake lalata musu rayuwa batare da iyayen ma sun sani ba. Acewarta Bama su kawai ba, akwai manyan ƙasar da dayawa sukai suna da nisa a irin waɗan nan al'amuran, su suyi ƴaƴansu suyi. Ba kunya Uba da ɗa za'a haɗu a club ko da ƴa anama juna kallon kallo. Akwai wanda ake kaima yara ƙanana gida suyi musu fyaɗe, wasu ma harda maza sukemawa. Ta tabbatar da idan zata tona asirin mutane da yawa akan wannan al'amarin tofa manyan nan da yawansu bazasu sha ba a bisa madafun ikon da suke kai. Dan haka a rufe rufau kawai. Wannan video ya girgiza al'umma da yawa. Yayinda ya bama wasu da ke fuskantar irin raɗaɗin da Nadiya ke a ciki fitowa suma suyi magana. Fiye da yanda ba'a zato al'amari ya sake rincaɓewa. Dan kuwa a ranar kame na hauka jami'an tsaro sukayi, kuma duk yaran su Alh. Sulaiman ɗinne da Nadiya ta dinga lissafowa a faifai. Inda kuma duk akayi dacen kamasu dumu-dumu da abinda ta lissafa ɗin kasancewar dama sai da aka shirya musu talala aka saki video ɗin.
   Zuwa yanzu kam su Alh. Sulaiman sun tabbatar da akwai mai musu zagon ƙasar nan. Duk da shi zai iya bugar ƙirji akan babu ruwansa da wata yarinya a cikin garin kwano. Iskancinsa a wajen Nigeria yakeyi sai ko Lagos. Dan budurwarsa ɗaya ce tak a Nigeria kuma a Lagos take zaune. Asalinta ma ba ƴar 9ja ɗin bace shine ya kawota ya ajiye. Sai dai kalmar fyaɗe da akace akwai masu yima yara kam ya girgiza shi, dan abune da anan kam baida tacewa. Dan haka idanunsa suka fara rufewa ya dannama Daddy kira dan ya fara ji a ransa anya Daddyn baida wata rawa da yake takawa a al'amarin nan kuwa. Duk da a yanzu haka ana tsaka da masa bincike akan *_AMM_* ɗin nan da ya aiko masa da takarda da hotuna, har yanzu kuma ya kasa hasaso kowa, ba komai ya jawo haka ba kuma sai kansa dake a birkice.....
★★ Daddy na a gidansa hankali kwance dan kallon wasan su Smart ma yake tare da su twins. Da farko kamar bazai duba mai ma kiran nasa ba sai kuma dai ya ɗauki wayar. Yasha mamakin ganin Alh. Sulaiman Garko. Har ya maida wayar ya ajiye da nufin sharesa sai kuma dai ya ɗaga tare da miƙewa ya shige bedroom ɗinsa.
    Cikin wata irin gigitacciyar tsawa Alh. Sulaiman ya ce, “Isma'il mai kake tunanin ka taka ne?!â€.
   Daddy ya saki murmushi mai sautin da har Alh. Sulaiman na jiyosa. Kansa tsaye babu alamar É—ar a tattare da shi ya amsa masa da faÉ—in,.......âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 5ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
.......“Banda abinka Sulaiman Garko idan kaji makaho yace ai wasan jifa ai ya taka dutse ne. Toni a wannan gaÉ“ar dutsina na taka bama dutse É—aya ba. Sorry fa, inata son zuwa na maka jajen abubuwan dake ta faruwa amma nayi busy da yawa. Sai kuma naji yau ma wata yarinya ta É“aro muku babban aiki, dan kaima banace bakayi ba. Wanda zai iya yima Æ™anwarsa uwa É—aya uba É—aya fyaÉ—e ai abune mai sauÆ™i yayma sauran Æ´aÆ´an jama'a ciki harda wanda ya haifa ma.....â€
     “Da hannunka kenan a ciki? Dama an tabbatar min da yarinyar Æ™awar Æ´arka ce ai. Isma'il karka manta ni zaki ne. Nakanyi farauta a duk dajin da yay min na kuma ci kowacce irin dabba na zauna lafiya batare da ko jin É—ar ba tattare da ni....â€
   “Banda Giwa, dan koda ka kadata namanta bai ciyuwa gareka sai da taron dangi Sulaiman Garko. Tabbas Nadiya Æ™awar Mawaddat ce bakayi Æ™arya ba, idan kuma kace zaka nuna wani giggiwa a wannan kadamin karan bana ne zai yi maganin zomon bana. Dan ka tabbatar da Mawaddat ce ta haifi Mawaddat, kasan kuwa tunanin zai iya zama duk iri É—aya, hakama jarumtar. Ballema a yanzu da take a jingine a jikin matashin *_ZAKI_* na haÆ™iÆ™a ba arar suna ba irin ka. Gefenta ga *_DAMISA_* Æ™i sabo. Sannan ga addu'ata biye gareta a dukkan motsinta. Ai nasha faÉ—a maka ni da Æ´ata da zuri'arta gaba É—aya *_FURAR DANƘO_* muke, *_A SHEKARA ANA DAMU BAMU FARAU-FARAU_*. Idan kai acan ka wuni, ni kwana nayi. Maza ka sake shiri *_MAZAN_* Æ™warai da *_MACE_* mai kamar maza ne tafe bisa kanka Æ™aramin biri......â€
    “Isma'illll!!!!!!â€
   Alh Sulaiman ya kira sunan Daddy cikin wata irin Mummunar tsawa mai razani. Kafin Daddy ya ce komai ya É—ora da faÉ—in, “Amma dai kasan zan iya karar da duk jama'ar asalin Æ™auyen da ka fito bama kai kawai ba ko??!!!â€.
    Dariya Daddy ya Æ™yalÆ™yale da shi tare da faÉ—in, “Ai ga fili ga mai doki nan Sulaiman Garko, zaka iya gwadawa idan har zaka iya, dan wlhy ba jama'ar garin jiÆ™amshi ba, koda Æ™asar jiÆ™amshi ka taka da manufa saina karya Æ™afafunka ta yanda bazasu Æ™ara É—aukar gangar jikinka ba har gaban abada. Amma kafin ka tafi jiÆ™amshin Æ™arar dadu ka tabbatar ka fara duba saÆ™o ga shi nan zai zo a hannun matarka shashasha Æ™aramin biri abin wasan yara a tsakkiyar kasuwaâ€. Ya yanke wayarsa.
  Haukacewa ne kawai Alh. Sulaiman baiyi ba da kalaman Daddy masu Æ™ona zuciya. A wani irin birkice ya É—aga wayar ya naka a Æ™asan tiles. Dai-dai nan amaryarsa ta shigo hannunta É—auke da leda. A É—an tsorace da ganin yanayin nashi ta ajiye ledar tana faÉ—in, “SaÆ™one aka kawo a baka, yanzu maigadi ya kaw....â€
  Yanda ya juyi a fusace ya hanata Æ™arasawa. Har ya juya shima da nufin baida lokacinta sai kuma ya juyo tare da wani irin fisgar ledar. Zazzageta ya shigayi cikin tsumar jiki. Babu komai a ciki face Flash drive. Cikin rawar jiki data ruhi ya kai zaune daÉ“ar yana mai janyo laptop É—insa ya saka flash É—in jiki. Gaba É—aya ya manta da kasancewar matarsa a wajen yay playing video É—in da ke cikin Flash É—in. Ba komai bane face fuskar mahaifiyar Lulu tana kuka da faÉ—in wannan shine kundin manyan laifuka na shi a ciki. Tana roÆ™on ko bayan babu ranta iyayensu su sani shine yayma Sultana fyaÉ—e....â€
   Ai bai ma kai ƙarshen video ɗin ba ya buga wata irin kuwwa da hankaɗa Laptop ɗin ƙasa itama ta kifu. Amaryasa data gama jin komai cikin firgita ta buga ihu itama tana neman hanyar fita a guje. Cikin tashin hankali yay tsalle ɗaya ya taɗota ta zube ƙasa. Idanunsa a rufe ya kai mata wata irin wariyar shaƙa. Tuni idanunta suka juye ta fara ƙaƙarin mutuwa.
    “Mi kika ji?!! Na ce, “Mikika ji!!? Dan uban uwarkiâ€.
  Kanta take jujjuyawa alamar bataji komai ba. Wawan mari ya É—auke fuskarta da shi ta bayan hannu da sake maÆ™ureta. “Idan ma kinji ko kin gani wlhy wlhy wlhy ki zama kurma. Idan ba haka ba da hannuna zan kashe ki, na gina rami a tsakkiyar falon nan na bizneki. Kuma har abada babu mai sake jin labarinki ko tambayata ina kike. BaÆ™ar mayya mai leÆ™e-leÆ™en masifaa!!â€. Ya Æ™are maganar da yarfar da ita Æ™asa. Ya wuce bedroom É—insa a birkice. Babu jimawa sai gashi ya fito. Har lokacin tana kwance a wajen yabi takanta ya fice abinsa. Umarni ya bama maigadi akan kada wanda ya fita a gidan. Daga haka ya birka motarsa da kansa yau ya fice a bala'in guje....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.