Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 56 of 78
    ★A lokacin da su Alh. Sulaiman ke nufar inda zasu haɗu meeting a lokacin jami'an tsaro sukai dirar mikiya gidan Alhaji Dikko dake ƙoƙarin sulalewa ya bar gidan batare da sanin ko iyalinsa ba. Aiko a take sukai ram da shi. Jiniyar motocin jami'an tsaron ne ya fargar da iyalinsa dama ƴan anguwa. Hankalin kowa a tashe, yaran sai kuka suke suna kiran yayunsu a wayoyi, ta hakane Aunty Khadijah da batasan mike faruwa ba tun safe da aka fara tone-tone a pharmacy ɗin mahaifin nata da ita kanta bata taɓa sanin nasa ɗin bane labari ya risketa daga bakin ƙaninta. A wajen ta yanke jiki ta faɗi tana tsaka da duba mara lafiya. Tun a daren Coach da Ahmad suka nufi asibitin cikin tashin hankali. Shine ma ya samu damar kiran Smart suka tattauna bayan aunty Khadijah ta farfaɗo an mata allurar barci mai ƙarfi. Zuwa safiya labari ya ƙara karaɗe ko'ina da ina, yayinda shugaban NDLEA na Kano dama na ƙasa gaba ɗaya suka ƙi ɗaga kiran su Alh. Sulaiman. Hakama IG da CP basu ɗaga musu kira ba. Abinda basu sani ba shine akwai wata ƙullaliya tsakanin gwamna da Alhaji Dikko, yana samun labarin abinda ke faruwa yay kiran CP da shugaban NDLEA na jiha yay musu gargaɗi. Tare da tabbatar musu in suka bari Alhaji Dikko ya ƙuɓuce musu a bakin aikinsu. Sannan Baba Garko ogan Gwamna ne na amana, dan haka yay kiranshi shima akan su IG da shugaban NDLEA na ƙasa. Shi baba Garko dama abune daya tsana a rayuwarsa, yake kuma yaƙi da masu alaƙa da shi, amma sam bai san akwai alaƙa tsakanin ɗansa Sulaiman da Alhaji Sadi Dikko ba sam...
   MatuÆ™ar tashin hankali sun shiga jin an cafke Alhaji Dikko, a take meeting É—in su ya canja akala zuwa shirya yanda zasu kashe Alhaji Dikkon kawai. Dan sunci alwashin bazasu taÉ“a barinsa ya tona musu asiri ba. Sai dai dolene suyi komai ta Æ™arÆ™ashin Æ™asa saboda gujema idon mutane a kansu. Sun nema amintattunsu dake cikin jami'an tsaron, kai tsaye suka basu umarnin kashe Alhaji Dikko ta hanyar guba. Kasancewar suma abokan cin mushen nasu ne sukai na'am da hakan. Dan in dai aiki ya buÉ—e suma nasu ya buÉ—e ai........âœï¸
_LABARAI MASU JAN HANKALI BAN TAUSAYI ZALLAR SOYAYYA MARA MANTUWA_
*KINSAN SUNAN LABARAN?,.....GASU KAMAR HAKA*
FURAR DANKO
Billyn Abdul
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR ‘KASHI
Safiyya Huguma
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at👇
1487616276
Access Bank
Bilkisa Ibrahim Musa
Sai katura shedar biyanka anan👇
09032345899
Idan katin waya ne kuma saika tura anan👇
09033181070
*_karki bari ayi tafiyar ZAFAFA BIYAR BABU KE!!!_*
*THANKS FOR CHOOSING US*🥰
Zafafa🫶🔥
*_ALLAH ya gafartama iyayenmuðŸ˜ðŸ™_*
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 4ï¸âƒ£9ï¸âƒ£
.......Kowa da abinda ya damesa. Duk da abinda ke faruwa a jihar ta Kano ya girgiza Abba hankalinsa a rabe yake gida biyu a dalilin halin da Ummah ke ciki. Duk da ma dai malaman da aka kawo a wannan karon su sunyi jarumtar tsayawa, sai dai daga kallo ɗaya da sukai mata sukace ta koma cikin ɗaki kawai. Sun tattauna da Abba akan dolene asan mushurikin da yay mata wannan aiki. Cikin nuna rashin amincewa Abba yace shi babu ruwansa. Babu inda zaije neman wani akan aikin da bai aiketa yi ba. Babu irin lallashin da ba'ai masa ba yace babu gudu babu ja da baya. Da ga ƙarshe dole ƴaƴanta ne suka nufi wajen Hajiya Naqiba da ke gida, dan asibiti sun sallamesu kamar yanda suka buƙata akaje akai mata ɗorin gida. Sun sami Hajiya Naqiba a yanayin daya tada musu hankali, dan ƙafarta tai wani irin mahaukacin kumburin da har tafi gangar jikinta girma. Kuka take sosai da ihu na azabar zogi da raɗaɗin da ƙafar kemata. An kira mai ɗori ya tabbatar musu ta sake gocewa, ma'ana dai ɗori baiyi ba. Ya kuma tabbatar musu da shi gaskiya bai san yaya zai yi ba, sai dai su nema wani kuma ya gwada sa'arsa. Daga haka yay tafiyarsa ma shikam. To shine fa ƴaƴan Umma suka samu ana shawarar neman wani mai ɗorin dan an tabbatar musu na gargajiyar dai yafi kar su maidata asibiti. Ga mijinta ya nuna kamar ma abin bai damesa ba duk da irin kiran sunansa da take famanyi shi da ɗanta Maheer. Shi Maheer ɗin da farko ya zauna, da ga baya yay ficewarsa acewarsa shi gaskiya ihun da take ya ishesa, yana fita suka haɗe da abokansa sukai tafiyarsu wajen ƙwalewarsu da kayan shaye-shaye. Dole yaran Umma suka dawo gida jiki a sanyaye. Sun sake iske tashin hankali Umma dake wani irin nishi a ɗaki amma kowa ya kasa shiga ya dubata, Ammah ce ma ta nuna zatai ƙarfin hali Abba ya tabbatar mata idan ta shiga sai ya ɓata mata rai, dole ta kama kanta cikin damuwa. Suma ɗin dai babu wanda yay yinƙurin shigar saboda tsoro....
   Har yamma babu wanda yasan halin da Ummah ke ciki, sai yayanta Jibirin ne ma yay ƙarfin halin bada shawarar a sake kiran malaman nan koda taimakon da zasu musu. Kowa ya bada goyon bayan hakan. Dan haka akai kiransu. Babu jimawa suka iso kasancewar akwai sanayayya tsakaninsu da Jibirin ɗin. Addu'oi sukayi da ƙarfin halin cusa kai a ɗakin, sai gasu suna rige-rigen dawowa a guje. Har yaran gidan dake tsakar gida na tayasu da afkawa ɗakunan iyayensu. Sun tabbatar da gaskiya bazasu iya ba, wannan mummunar halitta ganinta ai tashin hankaline ma. Sun tabbatar da shawararsu kawai ya kamata a bi aje a nemo mutumin da yay musu wannan aiki zaifi sauƙi fa. Wannan al'amari ya sake tayarma da kowa hankali. Dole ƴan uwanta suka tattaru neman mafita su da ƴaƴanta. Dan Abba dai da gaske ya juya musu baya.....
   ________★
 Al'amari kamar wasa Dada sai da ta kwanta asibiti na kwana biyu, randa aka sallamonta ta samu surukanta cike da gida sunata harkokin arziÆ™i akan zaman bakwai. Wannan abu ya sake dugunzuma mata zuciya. Baba Garko ya shigo dubata da daddare ta sanya masa kuka. Kallonta kawai ya tsaya yanayi, bawai baya jin tausayinta bane, ba kuma baya sonta bane. Ya riga ya É—aura É—ammarar horatane kawai. Dan ko auren nan nashi yayisa ne da gayya danya Æ™ona mata rai tunda yasan babu abinda ta tsana a duniya irin kishiya. Kuma ya samu nasara. A yanzun ma cikin É“acin rai yaja tsaki da faÉ—in, “Ni al'amarinki kam ya fara bani tsoro Hajara. Shin wai baÆ™in ciki kike da Æ™aruwar dana samu ko yayane? An faÉ—a miki haihuwa kin yanke jiki kin faÉ—i sumammiya, yanzu kin sakani a gaba kina kuka. Kin ganni nan ni bana son damuwa ina cikin farin ciki a É“ata min shi. Idan kinga zaki sakama ranki dangana ki saka, idan kuma kinga wannan halin da kike neman jefa kanki ne abin burgewa sai ki cigaba. Dan bakin alÆ™alami dai ya rigada ya bushe. Takardu sun jima da rubutuwa babu wata cleaner É—in gogesu. In sha ALLAHU nan da wata shekarar ma wasu biyun zata sake zubomin a gidan nan, sai ki shirya sake suma. Na barki lafiyaâ€. Da ga haka yay ficewarsa. Sama da Æ™asa numfashin Dada ya ringayi, jininta yay masifar hawan da har idanunta na koma mata dishi-dishi, ALLAH ne ya taimaketa Uncle Muneer ya shigo ya sameta a lokacin, da tabbas zuciyarta zata iya bugawa komai ma ya faru....
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.