Furar Danko Part 2 Complete Hausa Novel
Reading file: FURAR DANKO PART 2.txt
Chapter 1 of 78
ð“ð²ð©ð¢ð§ð 📲
 🫗 ð™ð™ð™ð˜¼ð™ ð˜¿ð˜¼ð™‰ð™†'ð™Š.....!!🫗
      ð‘©ð’Šð’ð’šð’ ð‘¨ð’ƒð’…ð’–ð’ð’ ð’„ð’†ðŸ¤™ðŸ»
ð•ð–”ð–”ð– ð–™ð–œð–”
ð‘ªð’‰ð’‚ð’‘ð’•ð’†ð’“ 1ï¸âƒ£
*_UK (LONDON)_*
........Kwance yake rai-rai a madaidaicin gadon nasa da mutanen Nigeria ke kira da 6-by-6. Sai dai wannan yaji katifa mai shegen laushi da bedsheet fari tas shima mai laushin gaske da ko'a ido ka kalla zaka shaida hakan. Yanda yake ɗan furzar da numfashi sama-sama da huttai ga zufa da tai ma jikinsa jagab zai tabbatar maka da ga training ya fito. Dan wandone na jc ƙarami da ya tsaya masa a fin rabin cinya da rigarsa. Sai takalma da aka san ƴan ƙwallo da su a ƙafarsa. Jikinsa ne a saman gadon ƙafafun zube a ƙasa. Iska mai nauyi ya sake furzarwa tare da buɗe idanunsa da launinsu ke a surke. Sam babu fara'a a tare da shi, dan fuskar nan ɗam take fiye da yanda kowa ya sanshi da rashin walwala acan baya....
     Cikin kuzari da ke nuna cikakkiyar lafiyar gangar jiki ya tashi zaune da ƙyau, ƙaramin tsaki ya ja tare da yamutse fuska ya fara saɓule takalman ƙafar tasa. Anan ya zubesu tare da miƙewa gaba ɗayansa ya kama rigar jikinsa ya cire cikin kamar yanayin jin haushi ya jefar da rigar ƙasa. Dogon glass ɗin da ya kasance kamar bango guda a haɗaɗɗen bedroom ɗin nasa ya nufa. Ya kai hannu ya danna wani ɗan maɓalli green. A hankali glass ɗin ya shiga raba kansa biyu har ya bada ƙofa. Shiga yay nan ma kamar a ɗan fusace, lafiyayyen toilet ne ya bayyana da ni kaina na zama baƙauya a kallo, kai tsaye ƙarƙashin shower ya nufa ya sakarma kansa ruwa yana mai jan wata nannauyar ajiyar zuciya...
    *_Aliyu Mika'il Idris Mawashi_* kenan da ke amsa sunan _Smart Mawashi_ a duniyar Æ™wallon Æ™afa. Duk da dai kwata-kwata watanninsa uku kenan da dawowa Æ™asar ta UK a London yay signing a club É—in Queen City. Du da kasancewar Æ™aramin club ne muna fatan ya zame masa wani tsanin kaiwa inda ba'ai zato ba. A yanzu Smart da muka sani na baya mai shiru-shiru da rashin sakewa da jama'a ya sake zarce hakan. Dan yanzu ba shiru-shiru ba, har miskilanci ma ya koyo. Hakan kuma ta faru ne a sakamakon faruwar shuÉ—aÉ—É—un abubuwan da suka faru a cikin watanni ukun nan da suka wuce. A gaÉ“ar da tafi kowace gaÉ“a muhimmanci a tarihin rayuwarsa. A lokacin da ya gama shiryawa da tsarawa kansa gina rayuwa mai ban sha'awa da birgewa tare da matarsa. A lokacin da yay shirin É—aukar dukkan yarda da amanar kansa data rayuwarsa domin damÆ™a mata. Sai labarin ya canja da ga yanda ya rubuta shi a zuciya zuwa rubutun Æ™addara.. Matarsa ta kufce masa a yayinda da burinsa na zama É—aya da ga cikin Æ´an Æ™wallo a wata Æ™asa ya cika. A hankali komai ya dinga dawo masa a zuciya dalla-dalla tamkar a yanzu ne yake faruwa. _(Bayan fitarsa gida a waccan ranar ya nufi gidansu cike da damuwar halin da ya jefa Lulu a ciki. Ya samu Asma'u taje aikan da Ammah tai mata gidan Aunty Bilkisu. Sai Maryam kawai da Ammah. Ko zaman kirki baiyi ba a daddafe suka gaisa da mahaifiyar tasa ya sanar mata yazo É—aukar É—aya daga cikin su Maryam ne dan Mawaddat babu lafiya. Hankalin Ammah ya tashi, ko neman Abba bata tsaya yi ba tace ya É—auki Maryam suje idan Abban ya dawo zata sanar masa, dan ita a nata zaton ko ciki Lulun ta samu. Cikin sauri Maryam ta kimtsa tare da É—ibar kunun gyaÉ—ar da sukayi domin tafiya da shi can su karya dan itama ko karyawar basu yi ba. Cikin Æ™anÆ™anin lokaci suka iso kasancewar safiya ce babu yawan go slow a hanya. Sai dai me tun a yanayin da sukaga Æ™ofar falon a buÉ—e da littafin da ya gani É—azu a saman gadon Lulu yashe a Æ™ofar shiga falon alamar an yarda bisa kuskure gabansa ya faÉ—i. Amma sai ya dake cikin Æ™arfin hali suka shiga, a falo Maryam ta zauna shi kuma ya nufi bedroom É—insa yana faÉ—a mata taje É—akin Lulun yana zuwa. Maryam ta amsa masa da to, yayinda shi kuma ya nufi É—akin nasa. Bai wani jima ba sai gashi ya fito. ÆŠan turus ya tsaya ganin Maryam kamar a ruÉ—e tana kai kawo. “K lafiya? Ba canai ki shigaba ina zuwaâ€. Da sauri Maryam ta juyo gareshi tana bashi amsa da “Yaya ai Auntyn bata nan ciki fa. Har toilet na leÆ™a babu kowa a ciki, hakama kitchen, sai dai duk an harmutsa wadrobe É—inta an É—iba kaya harma da akwati guda da aka bari kamar sauri ya hana a É—aukaâ€. Wani irin duka Æ™irjinsa ya dinga yi, sai kuma ya nufi É—akin da sauri shima. Kamar yanda Maryam É—in ta sanar masa haka ya gani, sai dai shi nashi idon ya Æ™ara masa ganin duk wani abu mai amfani a É—akin ma babu shi. Ƙafafunsa ne suka fara rawa, sai dai cikin dakewa ya cigaba da Æ™arfafa kansa. Takardar da idonsa ya sauka kanta a bisa gado ya Æ™arasa ya É—auka. *_Na tsaneka Aliyu, bana son sake ganinka a rayuwata, amma kaje na barka da ALLAH azzalumi. Ashe wa'azin naka duk na yaudara ne kaima baka aiki da shi. Ka manta da ni har abada, dan ko'a hanya nai maka tazara irin ta sama da Æ™asa, gabas da yamma. Idan ka wahal da kanka a nemana kai ka so, dan babu wanda ya isa sakani sake zama da kai koda Uncle Yousuf ne._* jiyay jiri na nan É—ibarsa yay saurin kaiwa zaune yana ambaton sunan ALLAH. Ya jima a wajen zaune kansa na yamutsa masa har Maryam ta gaji da jira ta shigo É—akin. Hankalinta ya tashi da ganin yanda Yayan nasu ya birkice cikin Æ™anÆ™anin lokaci. Kansa tai tana Æ™wala masa kira amma sai ya É—aga mata hannu da Æ´ar tsawa-tsawa yace ta fita ta bashi waje. Ta tsorata dan haka ta fita da sauri. Kamar an saita batafi minti É—aya da fita falo cikin É—aurewar kai ba sai ga kiran Ahmad ya shigo mata. Da sauri ta É—aya ta kai kunneta. Ko gaisawar kirki bata tsaya sunyi ba ta shiga faÉ—a masa abinda ke faruwa. Gaban Ahmad ya shiga faÉ—uwa shima da ga can, cikin Æ™anÆ™anin lokaci sai gashi a gidan. Tambayar duniya Smart yaÆ™i cemasa komai har sai da ya nuna fusata sanan a taÆ™aice ya ce masa, “Tabar gidanâ€. Duk da abin ya daki zuciyar Ahmad É—in. Sai ya shiga kwantar masa da hankali akan yana zuwa ya tabbatar bazata wuce gida ta tafi ba. Wayar Uncle Yousuf yay kira, da Æ™yar ya samu ta shiga. Bayan ya gaishesa bai wani tsaya kwana-kwana ba ya sanar masa halin da ake ciki. Hakan ya É—an É—imauta Uncle Yousuf É—in shima amma sai ya yanke kiran yace yana zuwa. Gidansa ya fara kira Aunty Saliha dake tsaye itama cikin tashin hankali ta É—aga wayar da sauri. Dan dama nemansa take tun É—azun ta gagara samunsa. Kafin ma yay mata tasa tambayar ita ta jeho masa abinda ke bakinta. “Abban Ra'is wlhy akwai matsala babba. Yanzu nan Khadijah tai kirana akan na shirya naje gidan Mawaddat babu lafiya na lallasheta da kwantar mata da hankali, banyi Æ™asa a gwiwa ba nai shiri dan na shiga tashin hankalin bayanin Khadijahn. Sai dai muna kan hanya sai ga text massege É—in ta ya shigo wai karmu nemeta, dan tayi nesa damu, na faÉ—a maka a kira Aliyu ya bata sakinta ta arziÆ™i inba haka ba zata sashi ya bada ta wuya. Duk da saÆ™on ya bani mamaki nacema driver yay sauri mu tafi gidan nata. lokacin da muke shiga street É—in mun haÉ—u da wata baÆ™ar mota mai tinted glass suka wuce muka wuce. Mun samu gidan buÉ—e da wani makwafcinsu tsaye a bakin gate É—in, driver na Æ™oÆ™arin shiga ya dakatar da mu cewar aiko baijin gidan nan da kowa. Dan yanzu yaga wata mata ta rirriÆ™o matar gidan tana kuka sun shiga mota sannan a loda akwatina a Hilux ma, shima ganin sun bar gidan buÉ—e ne ya sashi fahimtar babu lafiya, shine fa naketa nemanka ka kira Aliyu koka turo min Number sa amma na kasa smaunkaâ€. “Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un†Uncle Yousuf ya shiga maimaitawa. Nan É—in ma baice komai ba ya yanke kiran. Mommy ya kira, itama bai tsaya sun gaisa da Æ™yau ba ya jeho mata tambayar ko Lulu taje gidan. Da mamaki tace bata zo ba gaskiya, kuma batajin zatazo É—in, dan yau tanada Shari'a. Jin haka Uncle Yousuf ya É—an samu nutsuwa ya yanke kiran. Ahmad yay kira yace su maza court dan tana can zai turo Aunty Saliha yanzu su riÆ™eta. Da sauri Ahmad ya miÆ™e, shima Smart sai ya miÆ™e. Har Maryam basu bariba suka kulle gidan. Sai dai me koda suka isa can É—in ma babu Lulu, an kuma basu tabbacin bata zo ba. Sosai yanzu kuma hankalinsu ya fara tashi, dan kowa yasan duk rintsi fa Lulu akaran kanta bazatai sakaci da aikinta ba, musamman idan akai la'akari da yanda take matuÆ™ar son al'amarin. Sai dai yanda aka É—ibi kaya yayin barinta gidan na hargitsa ma kowa lissafi. Gidan Æ´an uwa da duk aka san zata iya nufa aka fara bubbuga waya, gidan Alhaji Garko ne farko, amma sai cikin tashin hankali Dada tace batazo ba, ba cikin Kano ba har wajen Kano amma dai amsa É—aya ce Lulu fa bataje ba. Tun kowa na É—aukar al'amarin wasa harya fara shan hankali, zuwa yamma dole aka shigar da report police station. ALLAH sarki Smart, yini guda baici komai ba sai ruwa, dolene a kallo É—aya ya baka tausayi, sai da Coach ya tsaresa bayan sallar magrib yasha shayi, yana gamawa kuma sai amai, sai zazzaÉ“i mai zafi. Dole ranar Ahmad da Abdull na gidansu sai anan suka kwana, dan suma dai tuni sun san mike faruwa Ammah duk kawaicinta a ranar sai da ta taka gidan Smart da ga ita har Abbah. Umma kam wani shegen daÉ—i takeji, dan a ganin ta in har wani abu ya samu Lulu iyayenta sai sun É—aure Smart na tsawon rayuwa.
     Al'amarin kamar wasa tuni Æ™aramar magana ta zama babba, dan kwana É—ai-É—ai har uku babu labarin Lulu Daddy da Uncle Yousuf tuni sun wancalakar da ayyukan gabansu sun dawo Nigeria. Hakama su twins duk suna Kano. Smart yay wata irin zabgewa, bawan ALLAHn ko murmushi baka gani a fuskarsa, ya duÆ™ufa kawai gayama UBANGIJI, dama Abba ya kai islamiyya da masallatai a taya addu'a, hakama Æ´an sanda nata faman kai kawo da bincike. A cikon kwana na biyar ne fa Addu'a bata faÉ—uwa Æ™asa a banza sai ga binciken Æ´an sanda ya fara maida akalarsa kan Dada, ba komai ya kawo hakan ba kuwa sai dalilin ganin sanda aka fita da Lulu da maÆ™waftansu yayi, dan Æ´an sanda basu barshi ya hutaba shima. Yana ganin Dada yace ma Æ´an sanda “A'a to ai wannan Maman ce na gani da yarinyar a waccan ranar, tare da wani saurayi haka mai É—an kammani da suâ€. A take kowa ya dubi Dada da duk ta daburce, sai kuma ta hau borin kunya. Ran kowa a wajen sai da ya É“aci idan ka cire Alh. Sulaiman da Tajuddeen da suka san komai. Smart kam wani irin kallo yakema Dada kawai, ji yake yau da ace bata da alaÆ™a da Lulu wlhy duk da tsufanta sai ya koyama matarnan hankali, dan sai ta tabbatar da ainahin Aliyu Hydar. Daddy ma dai da duk ya zabge a tsaye harda ciwo akan É“atan Lulun a wani irin rikice yake kallon Dada da Alh. Sulaiman a karo na farko, shikam dama ya zargi Alh. Sulaiman, sai dai Uncle Yousuf ya kwaÉ“esa akan hakan. ALLAH sarki Uncle Yousuf sarkin dattako, da ya fahimci faÉ—an na cikin gidane sai ya sallami Æ´an sandan kawai, da Æ™yar suka tafi dan sun ce dolene Dada ta fuskanci shari'a. To abinka da manyan mutane, a take akai kiran cp ya basu umarnin tafiya. Bayan wucewarsu ne fa gida ya hargitse, dan Dada tace bazata taÉ“a faÉ—ar ina Lulu take ba sai Smart ya saketa. Karan farko da tun faruwar al'amarin ya saki wani shegen murmushi mai Æ™ona zuciya a baÉ—ini mai kuma hasala abokin gaba a zahiri........âœï¸
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.