Complete Hausa Novels

Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel

Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 15

Page 13___14

Shiko Abdallah tunda ya fita be dawo ba sai dare yana dawo wa ya shiga d'akin Mama ya gaishe ta sannan ya fita ya kwashe kayan wankin da yayi gashi yayi sa'a akwai wuta , kai tsaye d'akin su ya nufa , yayi sallama ya shiga , Ummi ya samu kwance tana baccin k'aryan da ta saba , be tanka mata ba ya shimfid'a sallaya ya hau gugan shi ,

Ita kuwa Ummi kallon mijin ta take yi cike da tausayi , azuciyar ta tace "shi ko gajiya baya yi?"

Abunda bata sani ba shine shima Abdallah hankalin shi yana kanta kuma sarai ya gane ba barci take yi ba kawai sai ya fuske yaci gaba da gugan shi , har wajen shabiyun dare ,

Ummi ce tayi wata mik'a tamkar me yin bacci sannan tace "yaya fitsari nake ji"

Fuske wa yayi ya ce "kije kiyi mana"

"Wallahi tsoro nake ji"

"Duk tsoron da kike ji da zaran kinyi addu'a zai tafi, ko baki iya addu'ar bane?" Ya k'arasa maganar kamar zeyi dariya

Zumb'ura baki tayi cikin shagwab'a tace"na iya mana"

" to sai kije kiyi kafin Ki min shi anan"

Ai sai ta hau shura k'afafuwa ita ala dole sai ya raka ta,

"Ya isa haka Sarkin shagwab'a tashi muje "

Zumbur ta mik'e tama manta da d'aukan buta Dan fitsarin ya matseta sosai , Abdallah ne ya d'auki butar ya bita da shi,

Bayan ta gama ta fito alwala ta d'auro sannan yayi gaba tana bin shi a baya kamar rak'umi da akala

Tana shiga d'aki ta hau katifar ta tayi addu'oi ta shafe jikinta dashi sannan ta kwanta , nan kuwa bacci yayi awon gaba da ita ,

Shiko Abdallah bayan ya gama gugan shi alwala yayi , yayi nafilfili sannan ya kwanta ak'asa , bayan ya kwanta kuma me ya tuna oho ya mik'e kamar an tsikare shi ya lallab'a ya kwanta kusa da Ummi ya D'an janyo ta jikin shi kad'an , ita ko mage Sarkin son jiki ai sai ta k'ara shige masa ,

Can acikin baccin ta take jin wani Abu yana ratsa ta , tadai ji kamar ana mata waiwayi , har wani D'an zillo take , bata k'ara dawo wa hayyacin ta ba sai da taji yana k'ara mulmula ta, cikin fargaba ta cire hanunshi da ke kan k'irjin ta ,

Shi kuma kunya ce ta kama shi yaji kamar k'asa ta tsaye ya shige , kawai sai ya juya mata baya ,

Ummi ta kira shi a hankali " yaya?"

Da k'yar ya iya cewa "uhum"

"Dan Allah kada kayi fushi dani da gaske tsoro nake ji"

Abdallah najin ta ce haka a zuciyar shi sai yayi hamdala yace "bari na buga sabon wasa" ya k'arike da murmushi

Juyo wa yayi ya kalle ta sannan ya ce "idan bakya so nayi fushi da ke to Ki barni na gama abinda na fara"

"Yaya da zafi fa"

"Karki damu zanyi miki a hankali ba zaki ji zafi ba "

Da haka ta yarda yana ta wasa da ita a hankali har bacci yayi awon gaba dasu ,

Da safiya tayi Ummi kunya Abdallah kunya , shi atunanin shi zata gaya ma Hafsa abinda yayi mata shi yasa yak'i sake wa ,

❤❤❤❤❤❤❤❤

Lokaci yana ta tafiya yanzun auran Abdallah da Ummi ana Neman wata biyu , kullum zaiyi 'yan wasanninshi da ita domin wai a cewar shi tausayi take bashi k'aramar yarinya ce ,

Ummi ce kwance akan cinyar Abdallah yana yi mata tsifa duk da ba iyawa yayi ba amma tasa daru ita sai ya mata ,

Bayan ya gama na ta ce "yaya juya bayan ka kaga wani Abu "

Shi ko yace "a ina?"

"D'an duk'awa za kayi wani Abu zan cire maka"

Juya wa yayi yace" gani cire min"

AI sai ta d'are bayan shi tana fad'in "na mishi wayau" harda gwalon ta

Murmushi yayi yace "sauka min abaya ke kullum ba kya girma"

Nok'e kafad'ar ta tayi a lamar A'ah

"Ummi kin cika rigima kamar wata 'yar yaye"

Dariya tayi tace "ka manta yaye na aka kawo maka"

Juyo da ita yayi yace "yarinya karki damu naku sa yaye Ki" ya k'arike yana kashe mata ido d'aya

Duka ta kai mai abaya tana fad'in" wallahi ni bana so"

Dire ta yayi yana dariya yace "wannan kuma ke kika sani ni na tafi masallaci"

Cikin dare suna cikin barci manne da juna kamar tip da tyre sai Abdallah yaji motsin Ummi yayi yawa , janyo ta yayi ya sake k'ank'ame ta yana fad'in "Ummi Ki natsu mana"

Sai da tayi wani D'an k'ara tace "wayyo yaya cikina zan mutu"

Zumbur ya mike ko da ya duba ta Ashe ta galabaita sai murk'usu take yarik'e ta yana fad'in "ina ne " amma ta kasa magana , kwantar da ita yayi sannan ya hau Neman maganin ta cikin kaya be sha wahala ba ya gansu cikin hanzari ya d'ebo ruwa ya d'aga ta ya na bata yana shafa bayan ta ahaka har ta shanye ,

Ahankali taji ciwon na sauka tare da wani bacci , a haka ya k'arasa baccin da ita a nannad'e ajikin shi,

Da safiya tayi ya je ya gaida Mama ya ke gaya mata ciwon Ummi ya tashi Dan haka zai je kasuwa ko zai samu dako , ya kaita k'aramin asibiti ,

Mama tayi mishi fatan alkhairi ya fita a hanya ya gamu da Umar shima kasuwar ya nufa bayan sun gaisa Umar ya D'an tab'a shakk'iyyancin shi sannan yace "ustaz sai ina haka"

Nan Abdallah ya gaya mishi dalilin fitowar shi gida Dama inda ya yanufa

"Allah Sarki Allah ya bata lafiya"

"Amin "Abdallah ya amsa

"Dama yau za'a sauke ma Alhaji Bello kaya a store d'in shi , yanzun ya kirani kayan sun iso muje mu rok'e shi ya bamu kayan mu sauke sai ya biya mu"

"To" kawai Abdallah yace Dan shi mafita kawai yake nema

Da suka je suka samu Alhaji Bello be hana su ba ya ce suyi domin shi mutum ne tausayi

Suna cikin kwashe kayan ne , wayar Abdallah ta hau ruri , bak'uwar number da ya gani sai da gaban shi ya fad'i

Yana d'aga wa muryar Mama tayi mai sallama tana fad'in " Abdallah ka dawo gida Ummi ba lafiya" Mama tayi maganar cikin muryar kuka sannan ta katse wayar

Juyawa yayi a dabur ce yace "Umar jikin Ummi ya tashi" AI sai ya kwasa a guje

Shima Umar ya runtuma ya bishi

🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀🙆‍♀
[12/21/2017, 1:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*Dedicated to Bawan Allah fans , kusani ina sonku ina k'aunar kuma saboda ku nake rubuta wannan labarin , Allah ya bar zumunci ya k'ara mana dank'on soyayyah❤🏹 one luv*🏌‍com

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

15+++16

Koda suka k'ara sa gida Ummi a sume take bata San ma inda kanta yake ba , Mama na rik'e da ita ita kuma hafsa tana duk'e gaban Ummi tana kuka tana fad'in "Dan Allah Aunty Ummi kar Ki tafi Ki barni inkika mutu bansan yadda zanyi ba "

Hankalin Abdallah yayi k'ololuwa gurin tashi , kasa yin komai yayi , Umar ne yayi k'arfin halin fita waje a guje cikin sa'a kuwa yaci karo da me Napep nan ya tsayar da shi ya gaya mishi asibitin da zai kaisu sannan ya juya dashi suka koma , inda Umar ya bar Abdallah nan ya dawo ya same shi , dafa kafad'ar shi yayi yace "aboki ga me Napep can na samo a waje ku kama ta ku saka"

Haka nan jiki ba k'awari suka saka ta a napep suka nafi wani primary health care da yake kusa da su ,

Suna zuwa wani likita ya duba ta yace musu ba zasu iya yi mata komai anan ba saboda ba suda kayan aiki , nan likitan ya rubuta ta musu transfer zuwa A B U teaching hospital dake tudun wada , hakalin kowa ya k'ara tashi sai alokacin ne Umar ya d'aga waya ya sanar ma Malam abinda yake faruwa yace gashinan zuwa shiko Abdallah ya zama kamar photo domin D'an zaman da yayi da Ummi ta riga ta zama wani jigo na rayuwar shi, tunanin shi d'aya idan ya rasa Ummi ba Wanda zai k'ara bashi 'yarshi ya aura , shi yasa kullum idan ya tuna da Ummi yake k'ara sonta gashi ita kuma halin da take ciki ,

Dai-dai nan Mama tazo ta tab'ashi tare da cewa " kamata muje"

Kasan cewar wurin ba'a rasa abin hawa yasa suna fita suka samu napep sai tudun wada ,

Suna zuwa akayi emergency da ita nan ma likitoci suka shiga aikin su , bayan awa biyu wani likita yazo ya tambayesu sune 'yan uwan Zainab Kabir? Suka amsa masa yace su biyo shi office d'inshi

Bayan suje office d'inne ya basu izinin zama sannan ya fara bayani cewar "wani k'ari ne ya fito mata a gefen k'odar ta kuma yayi girma Dan haka dole ayanke , amma kuma ba zamu iya yi mata aikin nan ba dole zamu tura ta Babban asibitin mu dake *Shika* Dan haka ku shirya"

Tunda doctor ya fara maganar Abdallah ke karanto "Inalillahi wa inna ilaihirraji'un"

Bayan fitowar su daga office d'in Mama tace suje suyi sallah , Hafsa kuma ta koma gida tunda sun bar gidan ba kowa ,

Bayan Abdallah da Umar sunyi sallah ne sai Umar yace "ustaz bari naje gida na dawo ba jimawa zanyi ba"

Kai kawai Abdallah ya d'aga masa , sannan Umar ya tafi ,

Yana zuwa gida ya fasa asusun da yake Tara kud'in auren shi duk da dai beda budur war🤪🤪

Ya fito kenan zai fita sai Maman su ta kirashi "ina zaka je ne haka?"
.

Nan ya Sanar da ita meke faruwa , ita tace bata ga ta zama ba,

Ko da suka koma asibiti sun tarar da Malam da uwar gidan shi can Wanda har yanzun ba'a basu ikon ganin Ummin ba

Daf da la'asar wani likita yazo yace ga Ambulance cen suje su shiga za'a wuce da Ummi Shika , Umar ne yaje yayi clearing komai ba tare da sun sani ba ,nan suka d'unguma suka wuce asibitin

Nan ma wani gwajin aka sake yi likitoci suka tabbatar da lallai saidai ayima Ummi surgery gobe domin abin yana gab da fashe wa kuma idan ya fashe mutuwa zatayi ,

Abdallah najin hakan yayi sauri yace "likita kuyi duk abinda ya kamata ni zan biya kud'in"

Kowa ya juya ya kalleshi tare da mamakin abin yace

Doctor yace shikenan ba damuwa ,

Abdallah ya sake cewa "kud'in zasu kai kamar nawa ?"

"Zaku iya kashe kamar dubu d'ari da goma "

"Shi kenan doctor kuyi duk yadda ya kamata"

Mama dai suman tsaye tayi da jin kalaman D'an nata ,

Umar kuwa cewa yayi "Allah yasa abokina ba haukace wa kayi ba"

Juyawa yayi ya kalli Umar yayi masa wani murmushi me wuyan fassara

Malam ne yayi k'arfin halin cemai "Bawan Allah Kasan me kake fad'a kuwa ?"

D'aga kanshi yayi alamar "Eh"

"To ina zaka samo wannan mak'udan kud'in"

Cikin sanyin murya yace"wallah nima bansan inda zan samu ba amma ina rok'on Allah ya bud'a min hanyar alkhairi kafin safiyar gobe"

Malam ya jinjina kai

Tunda Abdallah ya shiga masallaci sallar magrib ya duk'ufa sallah da addu'ar Allah ya kawo masa mafita dashi da Umar kwanan tsaye suka yi ,

Bayan sun idar da sallar asuba ne Abdallah ya tuna da wani Abu bashiri ya mik'e kamar an tsikare shi yace ma Umar bari yaje ya dawo

🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔🤔
[12/22/2017, 12:23 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIR RAJI'UN*

*KULLU NAFSIN ZA'IK'ATUL MAUT ( dukkan wata rai sai ta d'and'ani mutuwa)*

*AMADADINA DA SAURAURAN 'YAN UWANA WRITERS NA PURE MOMENT OF LIFE WRITERS MUNA MIK'A SAK'ON TA'AZIYYAR MU GA 'YAN UWAN ZAINAB MUHAMMAD (ZEE SOBA) ALLAH YAJIK'ANTA YAYI MATA RAHMA ALLAH KA GAFARTA MATA ALLAH KA KYUTATA MAKWANCIN TA ALLAH KA WANKE TA DA RUWA MAI SANYI DA K'ANK'ARA ALLAH KA GOGE MATA ZUNUBAN TA KAMAR YADDA KAKE GOGE FARIN TUFA DAGA DATTI , KA MUSANYA MATA GIDA MAFI ALKHAIRIN GIDAN TA , DA IYALAI MAFI ALKHAIRIN IYALAN TA ALLAH KASHIGAR DA ITA CIKIN AJANNAR KA , KAKARETA DAGA AZABAR WUTA . AMIN YA ARHAMARRAHIM*😰

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

17++++18

Abdallah na fita be zame ko ina ba sai tasha cikin sa'a saura mutum biyu motar ta cika , wata mace ce tazo ta shiga sannan driver ya ja suka wuce k'auyen su Abdallah,

Yana sauka gidan Baban Hafsa ya wuce yana zuwa yayi sa'a ko ya sameshi a gida bayan gaishe-gaishe ya gaya masa abun da ke damun sa sannan ya ce yazo ne ya bada jinginar gonar mahaifiyar su ta gado domin su samu kud'in da zasu biya ama Ummi aiki ,

Bamusu kawun nashi ya amince sukaje wurin me gari aka samu Wanda zai amshi gonar aka buk'aci Abdallah ya fad'i ko nawa yake so abashi , yace dubu d'ari uku nan akayi yarjejeniya aka mik'a mai kud'i daganan yayi godiya ya kamo hanyar zaria ,

Ya shigo Zaria bayan la'asar gida ya wuce Hafsat kad'ai ya tarar a gidan tana ganinshi ta taso "yaya ya jikin Aunty Ummi?"

"Da sauk'i "kawai ya iya ce mata ya karb'i mukullin d'akin su ya shiga, dubu d'ari da hamsin ya d'auka sannan yayi sallolinshi a gida ya kulle d'akin ya tafi da mukullin , yana fita mashin ya hau har k'ofar asibitin ya k'arasa shiga ciki ,

Umar ne ya hango shi yayi sauri ya k'araso yana fad'in "ustaz ina kaje ne har yi ma Ummi aiki baka nan"

Murmushi yayi yace "naje Neman kud'i ne "

"Abdallah Dan Allah karka je ka sama kanka damuwar da ta fi k'arfin ka , kaga yadda ka koma kuwa daga jiya zuwa yau?"

"Umar damuwa dole ce agareni , kanaganin 'yar mutane zata mutu ta dalilin gazawa ta dole na shiga tashin hankali "

"Hakane amma Kasan rayuwa da mutuwa duk na Allah ne idan kwanan mutum ya k'are ba tsumi ba dabara dole sai ya tafi"

"Allah kasa mudace " Cewar Abdallah yana rik'e hannun Umar suka k'arasa ciki

Har a lokacin bacci take yi Mama ce kad'ai AD'akin ta zabga uban tagumi ga carbi tana ja , har suka shigo ma bata sani ba ,

Sai da yace "sannu Mama "

Da sauri ta d'ago kanta tana fad'in "Bawan Allah ina ka jene?"

"Mama naje Neman kud'i ne kuma Alhamdulillah na samu"

"Ina ka samo kud'i?" Cewar Mama tana zare ido

"Bashi na samo kuma Dan Allah karki d'aga hankalin Ki nan bada jimawa ba zan mayar musu da kud'in su"

Shiru Mama tayi tana tunanin ina d'anta zai samo wad'annan kud'in harya ya biya , azahiri kuma saita bishi da fatan alkhairi,

Mik'e wa yayi yace ma Umar suzo suje su biya kud'in su dawo dayake akwai receipt a hannun su direct bank din cikin asibitin suka je suka biya kud'in , tare da siyan magunguna suka dawo ,

Satin su d'aya a asibitin aka sallame su duk wannan lokacin Abdallah be gayama mahaifiyar shi cewar gonar ta ya siyar Dan ya sama matar shi lafiya ba ,

Ummi kuwa kyakyawan kulawa take samu awaurin mijinta da Mama Hafsa ma ba'a barta a baya ba domin kullum ita ke kai mata ruwan wanka , bayan sati biyu da sallamo Ummi Abdallah yaje ya samu mahaifiyar shi ya sanar mata da gaskiyar inda ya samu kud'i , amadadin ya tayi fushi sai yaga murmushi a fuskarta tace " Abdallah banida wani magaji aduniyar nan sai kai duk abinda na mallaka halalin ka ne , Allah yayi maka albarka , ita kuma Allah ya bata lafiya , "

"Amin Mama na gode"

"Yanzun ina sauran kud'in suke?"

"Suna d'aki"

"To Sana'a ya kamata ka fara"

"Eh hakane Mama ni anawa tunanin me zai hana inrunk'a zuwa kano ina saro kayan provision "

"Hakane amma shago fa ?"

"Insha Allah ba matsala zan ma hadi me shago magana naji yace zai saida nashi zai koma k'auyen su".

"To shikenan Allah ya bada sa'a "

"Amin , bari naje na nemi Umar naji ya tafiyar zata Kasan ce mana"

"To adawo lafiya "

"Allah yasa" nan ya fita ,

Ya samu Umar yana shirin fita kasuwa inda yake tsaron shago,

Nan suka sauna suka tattauna suka tsaida ranar laraba zasuje kano , danan suka wuce gurin me shago suka fara ciniki Wanda da k'yar ya karb'i dubu ashirin ,

*LARABA*

Da safe bayan sun gama karyawa ,Abdallah yayi wanka , Dan sunyi da Umar karfe goma zasu bar gida , Abdallah ne ya d'aga waya ya kira Umar yake sanar masa da ya shirya Dan haka yafito su tafi ,

Bayan ya aje wayar ne Ummi dake kwance jikin Abdallah tace"yaya ji nake kamar karka tafi"

Murmushi yayi yace"bakiso naje Neman kud'i ko?"

"A 'ah ba haka bane kawai dai..."sai kuma tayi shiru

"Kawai mene ? K'arasa mana"

"Kawai inajin jikina ba dad'i ne?

Cikin sauri yace"bakida lafiya ne?"

"Lafiya ta k'alau yaya kawai dai tafiyar taku ce bana jin dad'in ta a raina"

"Kiyi hak'uri Ummi na nima yau tunda na tashi nake jin jikina duk ba k'wari kiyi min addu'a"

Wata k'walla ta share idon ta sannan tayi masa addu'ar fatan alkhairi , suna fitowa d'aki Umar yana shigowa gidan , yana ganin su ya saki wani murmushi, nan suka gaisa da Ummi sannan suka lek'a d'akin Mama fatan alkhairi tayi musu sannan suka fita Ummi sai da ta raka su k'ofar gida sannan Abdallah yace mata ta koma amma ta nok'e kafad'a ita baza ta koma ba

Azaure ta tsaya tana hangen su har sai da suka b'ace ma ganin ta sannan ta koma gida jiki a sanyaye , bata tsaya fira ba ta wuce d'akin ta tana ta juyi a gado irin wasan da suka yi jiya da Abdallah ne ya ke ta mata yawo a k'wak'walwa sai murmushi take tana dad'a matse pillown data rungumo

Abdallah da Umar kuwa bayan sun rabu da Ummi Umar yace ma Abdallah akwai mutumin da Alhaji Bello yake siyan kaya awajen shi a kantin kwari Dan haka suje chan d'in ,

Sun isa kano azahar tayi kawai sai suka tsaya wani masallaci suka yi sallah sannan suka k'arasa cikin kasuwa dayake Umar yasan shagon kai tsaye chan suka nufa,

Alokacin da suka isa ana sauk'e ma Alhaji Mati kaya Dan haka ya rok'esu da sujira agama Dan kar lissafi ya kwace masa ,

Bayan ya gama ya hau sallamar mutane sannan ya waiwayo kan su Abdallah lokacin had la'asar ta wuce , siyayyan kayan ciyaciye na yara su suka fi yawa sannan su omo da sabulai kaya dai sosai ya had'o , ko kafin su gama magrib tayi Umar ya kalli Abdallah ya ce "ustaz dare fa yayi mu kwana a garin nan da safe sai muyi sammako"

"Gaskiya bazan iya ba yau duk dare gida zan kwana "

Umar yayi dariya yace " kafiso kullum ka jika gaka ga 'yar k'anwar ka"

"To ya San ranka , dalla Malam wuce muje"

'Yan dako biyu suka samu suka d'aukan musu kayan sannan suka fita kasuwa suka hau adaidaita suka nufi tasha suna shiga wata motar Zaria tana tashi Dan haka dole sujira ayi sabon Lodi ,

Sai k'arfe Tara sannan motar ta cika akayi duk abinda ya dace mota ta tashi bayan sunyi kamar tafiyar awa d'aya kawai sai motar ta mutu da kanta , nan fa driver yayi duk iya dabarun shi tak'i tashi gashi sunyi nisa da gari gasu a k'ungurmin daji,

Sunan nan tsaye masu salati nayi masu zagin driver nayi wai lefinshi ne da bai duba mota ba ya kwaso su ,

Abdallah kuwa shiru yayi kamar ruwa ya cishi,

Kwai sai suka ga ana ta kashe musu ido da wani haske me shiga k'wak'walwa , wata razananniyar murya suka tsinkaya ana ce musu "sit on your kneels!"

AI sai kowa ya hau salati Ashe 'yan fashi ne,

Haka suka ruk'a rashin mutumci harzuwa wannan lokacin Abdallah yana cikin motar be fito ba sai da wani yazo ta jikin window ya hasko ko shi yace "oga kaga wani D'an iska ana magana ya zaune , "

Ogan yace fito min dashi na ragaje shi kawai zagayowa yayi ya damk'o wiyan Abdallah ya fito dashi dai dai lokacin idon Abdallah yakai kan Umar dake kwance jini yana ta zuba a hancin shi da alama suma yayi fincikewa yayi daga ruk'on da suka mai ya tafi wajen Umar aguje yana fad'in "Umar meya same ka ta...." Wani irin zafi yaji Wanda saida jini ya fito ta hancin shi Ashe bakin bindiga suka buga ma a kai

"Muzaka yi ma taurin kai to ba irin mu ake yima ba" haka suka yita dukan Abdallah duk da ya suma basu k'yale shi ba , saida suka tabbata sunyi mishi babbar illa sannan suka k'yale shi

Matan kuwa Dama su biyu ne nan suka tasa k'eyar su suka tafi dasu mazan kuma suka barsu kwance tare da k'wace duk wata dukiya dake tare dasu
[12/26/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*This page is mine💃💃 💃💃happy anniversary to my self I hope you ga _ys will wishes me*_ 😘🏌‍♀

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Kasan cewar dare ne kuma wurin ba wurin tsayawar mutane bane shiya sa basu samu temako ba sai da safe , wani me mota ne yazo wuce wa yaga mutane kwance kamar mattatu , nan da nan ya d'aga waya ya kira 'yan sanda , ba b'ata lokaci aka kwashe su sai asibitin Aminu kano , direct emergency aka wuce da su ,

Da bincike da bincike kowa D'an uwan sa ya runk'a zuwa amma banda mutum biyu , wato Umar da Abdallah , Umar ya farka sai dai be San inda kanshi yake ba , Abdallah kuwa har yanzun bema ko motsa ba, likitoci suna iya k'ok'arin su akan shi domin duk ciki ya fisu shan a zaba,

*ZARIA*

Ummi , Mama da kuma Hafsa kowa yayi cirko-cirko a tsakar gida , kowanan su da a binda yake sak'awa acikin ransa , iya k'ololuwar tashin hankali suna cikin su ,

"Ummi sake Kiran wayar muji" Mama ta fad'i cikin wata murya me ban tausayi

Ummi jiki ba k'wari ta danna number Abdallah , still a kashe wasu hawaye ne suka sake yi mata ambaliya a fuska ,

"Aunty Ummi swich up ko?"

Ita dai Ummi d'aga kawai tayi domin Sam ta kasa bada amsa ,

Haka suka zauna a wajen har kusan k'arfe biyu na dare , Ummi ce taga kukan ba zai fisheta ta ba ta mik'e ta d'auki buta yau ko tsoron ba ta ji , ta nufi bayi , tana fitowa ta d'aura alwala duk sai suka bita da ido , Mama a zuciyar ta tace "wannan ita kad'ai ce mafita"

Duk sai sukayi alwala suka shige d'aki, kowa ya kai kukan shi ga Allah Wanda shi kad'ai ne buwayi gagara misali mai biyan buk'atun bayin sa,

Koda safiya tayi suna zaune a tsakar gida sunyi jigum gidan tamkar ba mutane ,

A haka Maman Umar ta shigo da sallama Wanda da ganinta ita ma Kasan batayi kwanan dad'i ba , bayan sun gaisa sama-sama sai tace

"Wai yaran nan basu dawo bane? "

Mama cikin jimami tace"wallahi bamu gansu ba jiya kwana ne kawai ba muyi a tsakar gidan nan ba "

"Inalillahi wa inna'ilaihir raji'un, ya Allah ka sa muji alkhairi" cewar Maman Umar

"Amin " duk suka amsa

Hafsa ce tace "Mama ya kamata aje a fad'a ma Malam ko da temakon da zai iya yi"

"Hakane Hafsa kinyi tunani me kyau , yanzun tashi kije Ki sanar mishi "

"To Mama" ta mik'e jiki ba kwari ta fita ,

Ummi kuwa wata alwalar ta sake yi ta nufi d'aki ,

Mama ta kalli Maman Umar tace " ina jin tausayin kaina ina jin tausayin yarinyar nan jiya haka ta kwana banda kuka da sallah babu abin da take yi "

Maman Umar tace "wallah jibi yadda duk ta susuce , Ya Allah ka bayyanar mana da yaran"

"Amin" dukkan su suka amsa

Bayan Hafsa ta sanar ma da Malam halin da ake ciki ba shiri ya bazamo ya taho gidan Dan jin cikakken bayani ,

Mama ta fara magana "wallah Malam tunda suka fita jiya babu su ba labarin su har yau"

"Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un , ai ni Da naga ban gansu a masallaci ba da asuba inace ko gajiyar hanyace , Allah ka bayyanar mana da su"

"Amin" kowa yace

Dai-dai nan Ummi ta fito daga d'aki Dan ta jiyo muryar mahaifin nata , ahankali ta tako gefen Hafsa ta zauna tare da gaishe shi , bayan ya gaisa ya fara yi musu nasiha tare da kwantar da hankali , gami da cewar" Idan har dare yayi basu dawo ba to gobe shida wasu almajiran shi zasu tafi kano Neman su"

Nan dai sukayi godiya ya tafi ,

Mama ta kalli Hafsa ta ce "je Ki dama ma Ummi koko tasha magani"

"Mama nak'oshi"Ummi tace tana kifa kanta akan gwuiwoyinta

"Baki CI komai bafa Ummi rabon Ki da abinci tun jiya da rana shi d'in ma ba wani ci ka kayi ba kina ta jagwal-gwalawa , "

Ummi dai shiru tayi

Maman Umar tace " haba Ummi Ki yi hak'uri ko kokon Ki sha kinga ba lafiya ce ta wada ce Ki ba "

"To"kawai tace

"Ke Hafsa je Ki damo mata"

Wasa-wasa har dare ba wani chanji hakan yasa Malam ya nemi biyu daga cikin manyan almajiran shi da su raka shi kano , safiya nayi kuwa suka bazama,

*_kano_*

Tunda likitoci suka yi iya bakin k'ok'arin su akan Abdallah cikin ikon Allah numfashin shi ya dawo amma kuma gashi nan kwance kamar gawa , wani Babban Doctor suka kari yazo ya duba shi , koda yazo yaga Abdallah Sam ya kasa d'auke idanun shi a kansa , wani Doctor ne ya matso kusa yana magana

"Ka sanshi ne Doctor?"

Shiru yayi yana tunanin abinda zai ce sai kuma yace"ina 'yan uwansa suke?"

Nan wancen Doctor din ya kwashe duk tsautsayin da ya faru da su Abdallah ya fad'a masa ,

Cikin tausaya wa Doctor ya ce "wannan yaron wani mak'oci nane , ayi masa duk abinda ya dace",

Suka chanja Abdallah d'aki , ana fita dashi Umar ya farka , babu Wanda ya fara kira sai Abdallah ,

Bayan ya D'an huta suka fara yi mishi tambayoyi kamar haka

Wani Doctor Usman ya fara cewa "ya sunan ka?"

"Umar" a tak'aice ya bashi amsar

"Inane garinku?"

"Zaria"

"Mekazo yi a kano?"

"Munzo Sarin kaya ne nida d'an'uwa na Abdallah"

Doctor Usman ya maimaita Kalmar "D'an uwa fa kace?"

"Eh" inji Umar yana dad'a kallon Doctor d'in

"To gaskiya duk cikin Ku ku goma da aka kawo babu Wanda 'yan'uwan shi basu zo ne manshi ba sai kai"

"A'ah likita indai ina cikin asibitin nan to na tabbata Abdallah na ciki iyayen mu d'aya da shi "

"To mudai kai kad'ai ka rage mana anan "

Wani mugun fad'uwar gaba ne ya ziyarci Umar shidai yasan last seen d'inshi da Abdallah ya ganshi cikin mota tsaye kuma yaji sanda d'aya daga cikin 'yanfashin yayi magana akan Abdallah afili ya furta "innalillahi wa inna'ilaihirraji'un, Allah kasa ba sun tafi min da d'an'uwa na ba"

"Maybe sunzo basu gane ka bane dubi yadda ka chanja kammani gaba d'aya" Doctor ya fad'i yana nuna masa wani d'an k'aramin madubi

Daya kalli fuskarshi sai da gabanshi ya fad'i tabbas yasan ba kowa zai gane shi ba Dan ko shi kanshi badan yasan shine ajikin madubin ba daya k'aryata kanshi,

Doctor ne ya tsinke mishi tunani da cewa " idan ka haddace number d'aya daga cikin 'yan uwan ka kabani sai na sanar musu"

Shiru Umar yayi sannan ya tuna number Malam nan ya bada , alokacin Malam suka shigo garin kano wayar shi Nokia rakani toilet ta fara ruri , ganin bak'uwar lamba yayi cikin sanyin jiki ya amsa tare da sallama

Ad'ayan b'angaren ma aka amsa tare da fad'in "suna na Doctor Usman ina aiki a asibin Aminu kano dake cikin garin kano , muna da wani patient me suna Umar yace kai D'an'uwan sane"

"Alhamdulillah dama yanzun su muka zo nema"

Nan Doctor yayi ma Malam kwatancen inda zai same shi idan yaje asibitin , basu b'ata lokaci ba suka isa Kasan cewar asibitin yana farkon gari ne , koda suka k'arasa asibitin basu sha wahala ba suka samu Doctor Usman tunda akwai waya nan yayi musu jagora zuwa d'akin da Umar yake nan ya kaisu Malam cikin razani da tashin hankali ya k'arasa inda Umar ke jingine , gaba d'aya halittar shi ta sauya nan suka jajanta ma juna Malam ya tambaye shi labarin abinda ya faru , shi kuma ya kwashe ya sanar masa

"To ina Abdallah?"

Abinda Doctor dai ya gayama Umar shi ya gaya musu game da Abdallah nan hankali ya k'ara tashi har dare ana Neman Abdallah amma babu bayani

Washe gari da safe aka sallami Umar , suna ji suna gani suka kamo hanya ba tare da Abdallah ba kowa da zullumi acikin zuciyar shi , "me zasu ce ma Mama akan *Bawan Allah* ?????"
[12/27/2017, 8:23 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*To readers ina Wanda ya shirya zuwa kano Neman bawan Allah Sadiya neman bawan wa Allah Wanda rashinsa Sam baiyi mata d@d'i ba cikin sa'a ko ta samu abokan tafiya Maman sa'a tace ba'a barta a baya ba dole su nema wa Ummi farincikin ta , aceeya kuwa cewa tayi jirgin ya tsaya ajigawa ya d'auke , Amne kuwa da yake 'yar black stormach ce 🤪cewa ta ba inda za'a je saboda man fuel yayi tsada , Aunty axland ma tace ba'a barta a baya ba*🤣🤣🤣

❤ *Gaisuwar fatan alkhair agareku masoya masu bibiyar littafin bawan Allah sakon ku na fatan alkhairi yana isowa agarene nagode agaskiya bansan da bakin da zan gode muku ba amma kusa ni har cikin raina inajin dad'in yadda kuka amshi wannan litttafin nagode sosai Allah ya had'a fuskokin mu a aljannatul firdaus Amin ya Allah*❤❤❤. *one luv*😘

*Ameenart Nd fatima (MAMAN Sadeeq) wannan page d'in naku ne dama d'aukacin yan Bawan Allah fans , I really like your comments❤*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.