Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel
Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt
Chapter 3 of 15
Page 3⃣
*CIGABAN LABARI*
Haka suka k'araci zaga gurare da kasuwwani ba su samu komai ba har la'asar ta gabato , hakan ya sasu koma wa gidan ba Dan sun so ba ,
Da sallama ya shiga gida Mama da hafsa ne suke hirarsu jefi-jefi , suka amsamai sallamar ne ya shiga
Cikin sanyin jiki ya nemi guri gefe ya zauna sannan ya juya ya kalli mahaifiyar sa ya ce
"Kun wuni lafiya Mama?"
"Lafiya lau ya k'ok'ari bawan Allah?" Ta kalli D'an nata cike da tausaya wa
"Alhamdlillah Mama" cewar Abdallah daya ke k'ok'arin tashi , domin kiran sallar da yaji ,
Bayan sunyi sallah shi da aminin nashi islamiyar da suke koyar wa suka je ,
Abdallah shine malamin k'ur'an da tajweed ,
Umar kuwa yana daukan ahdari da tauheed
Suna zuwa kowa yake shiga ajin shi
Bayan sun dawo daga islamiya k'arfe takwas na dare suke zuwa d'aukar karatu wurin Malam Kabiru ,
Yauma kamar kullum sunje karatu Malam ke musu fad'a
" wai yanzun Ku haka zaku zauna ba zaku yi aure ba Ai aure shike sa aga mutum da daraja kullum"
"Insha Allahu idan lokaci yayi za'a yi "cewar Umar
Shiko Abdallah shiru yayi
Malam ya ce "Bawan Allah baka ce komai ba "
Ajiyar zuciya Abdallah yayi sannan ya ce " yanzun Malam a yadda muke d'in nan wa zai d'auki d'iyar sa ya bamu , bayan bamu da abinda zamu ciyar da ita dashi balle kuma sauran buk'atu na duniya "
Malam ya ce "hakane Abdallah amma ai ba'a rasa na Allah"
"Hakane Malam " cewar Umar
"Kuma ni gashi har na fara nema muku aure Dan zaman Ku ahaka baya min dad'i "
Cikin sauri Umar yace " Malam kad'an yi hak'uri zuwa nan gaba kad'an"
Malam yayi murmushi ya ce "Allah ya kaimu "
Abdallah kuwa cewa yayi "duk yadda kayi Malam dai- dai ne"
Nan Malam ya sa musu albarka sannan suka tafi ,
Suna fitowa Umar ya kalli Abdallah ya ce
"Ustaz naga kamar kayi na'am da maganar Malam ne "
Kallon shi Abdallah yayi sannan ya ce " Malam tamkar Uba yake aguri na Dan haka babu zab'in da zai min na bijire masa dole Sana'a zannema "
Umar ya zaro ido"wace irin Sana'a kenan?"
" zanyi tunani idan na yanke shawara zan gaya maka zuwa gobe da safe" cewar Abdallah yana k'ok'arin shigewa gida
"Allah ya jisshemu alkhairi " Umar ya fad'a da D'an k'ar fi ,
Suka yi sallama kowa ya shige gida
*DA SAFE*
Yauma kamar kullum ba komai agidan suna zaune sai ruwa da suke D'an sha jefi-jefi ,
Shiko Abdallah yana can d'akin shi kwance kan shamulokin katifar shi yana ta tunanin sana'ar k'arfin da zaiyi , idan yace wannan ya ce A'Ah daga k'arshe dai ya yanke shawarar yin sana'ar wanki da guga , wannan shawarar ya tsayar Dan haka ya mik'e ya saka rigar shi ya fita tsakar gida
Bayan sun gaisa ne sai ga Umar ya shigo da kwanon sha , a hannun shi ya d'ire a gaban Mama ,bayan sun gaisa Mama tace
"Umar me muka samu ne?"
"Murmushi yayi yace "koko ne Mama "
Mama tace "an gode Allah ya saka da alheri"
"Amin " dukkan su suka ce
Bayan sun gama shan kokon ne Umar yace " Abdallah wai wace Sana'a zamu fara ne"
Abdallah yayi gyaran murya yace "wanki da guga"
Umar ya zaro manyan idanun nan nashi ya ce "wanki da guga?"
"Eh, Kasan dalilin da ya sa na zab'e ta?"
Umar yace "A'ah"
"Saboda ita kad'ai ce samu yi ba tare da mun kashe ko sisi ba "
"Hakane Abdallah Allah ya taimake mu "
Dukan su suka amsa da "Amin"
Mama ma fatan alheri ta musu ,
Cikin sa'a kuwa suka samu kasuwa , da yake gidan su Abdallah akwai rijiya kuma ba yara nan suke taruwa suyi sana'ar su ,
Da yake basu sa ha'inci a sana'ar suba hatta masu hannu da shuni na kewayen su suna kawo musu ,
Hafsa ce zaune tana tsintar wake zata dafa musu garau-garau , nan k'awarta Ummi ta shigo tare da sallama , Ummi akwai ta da son barkwanci ta cewa hafsa
"Ah k'awata yaushe aka fara shiga kitchen?"
Wata harara hafsa ta aika wa Ummi sannan ta ce "kefa 'yar rainin wayau ce wallahi yau kika fara ganina nayi girki?"
Ummi tayi dariyar mugunta tace "to aike hafsa abinshi naki ne na ganin dama sai Mama tace kiyi kike yi"
Hafsa ta tuntsire da wata dariya tace " kamar ko kin sani"
Suka tafa Ummi tace "AI na sanki ne k'awata, ina Mama ,"
Hafsa tace "Mama taje gidan su yata Umar Gwago ce bats jin dad'i"
"Subhanallah Allah ya bata lafiya "cewar Ummi
Hafsa ta amsa da "amin"
Nan Ummi ta taya ta suka gama sukayi shirin islamiyya
[12/14/2017, 9:58 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
*Dedicated to Rabi'atu Baba Paki😘 ina yinki mumcy irin dayawa d'in nan*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
4⃣
Lokaci ya ja su Abdallah nayin wankin da guga suna samun na rufin asirin su , daga baya wani k'anin MAMAN Umar ya saman ma Umar tsaran shagon abokin shi acikin kasuwa , to daga nan Umar ya bar wanki da guga sai Abdallah kad'ai keyi , da haka idan ya cire kud'in da zasu CI abinci sai ya saka sauran a asusu saboda wasu idan yayi musu aiki over payment suke mishi,
Yanzun watan Abdallah shida yana wanki da guga wata , wata rana Malam ya aika a Kira shi , bai b'ata lokaci ba ya je,
Bayan sun gaisa Malam ya ce" Abdallah ya maganar aure?"
Wata irin muguwar fad'uwar gaba yaji amma sai ya d'aure ya ce"yanzun Malam akwai Wanda zai iya bani 'yarsa na aura yadda nake d'in nan?"
Malam yayi murmushi yace "sosai ma kuwa Dan an dad'e ma da baka sadaki kwai ake jira a d'aura aure"
Cikin firgici Abdallah ya d'ago ido ya kalli Malam
Malam yace " sosai ma kuwa idan kana da naira dubu bakwai ka kawo amatsayin sadaki , "
Gaba d'aya Abdallah ya diri-rice ya rasa me zai ce ,
Malam yace cikin sanyi murya "Abdallah dalilin da yasa na matsu kayi aure shine na dad'e ina lura da yanayin ka , sannan kuma ahalin yanzun da kake cike kana buk'atar mace ta gari da zata zamo natsuwa a gareka shiyasa kaga na damu"
Ajiyar zuciya Abdallah yayi Dan yasan zancen Malam gaskiya ne "Insha Allah bazai gagara ba , nagode Malam Allah ya saka da alkhairi ya k'ara girma "
"Amin "cewar Malam
Sannan sukayi sallama akan zai kawo sada kin gobe ,
Abdallah na koma wa gida ya sanar ma da Mama yadda suka yi da Malam , tayi murna sosai hafsa na d'aki na kwance ta fito tana "Mama lafiya?",
Abdallah ya turb'une fuska alamar be son raini yace" ke waye sa'anki a nan? dallah can koma d'aki"
"Haba Bawan Allah wannan ba 'yar uwar ka bace ai ya chanchanci taji abin alherin da yake shirin samun mu"
"Mama ni dai raini ne bana so" yana gama fad'in haka ya nufi k'ofar d'akin shi ya tura ya shiga ya fad'a kan shamulokin katifar shi yana tunani ,
"Shin ta ina za'a kawo wani mahaluki d'akin nan ya iya zama , ballan tana kuma Amarya?"
Mik'e wa yayi zaune yace "ya Allah ga Bawan ka nan mak'ask'anci daga cikin bayin ka ya Allah ka taimake mu ya Allah kafi kowa sanin halin da muke ciki " wasu k'walla masu zafi da tuk'uk'i a zuciya suka zubo mai ,
Da k'yar ya had'iye wani Abu mai kama da dutse a wuyan shi ya koma ya kwanta ,
Chan kuma yayi zumbur ya mik'e ya nufi gana most go d'in kayan shi ya ciro wani gwangwani , nan ya bud'e kud'i ne a ciki , nan ya hau k'irgawa , naira dubu takwas da d'ari biyar ne , ajiyar zuciya yayi sannan ya mai da kud'in ya ajiye , da yamma bayan sun had'u da Umar a islamiyya yake gaya mishi yadda suka yi da Malam
Umar sai da yayi dariya mai isarsa sannan ya ce " wato kai yanzun aure za'a maka ?, auren ma na dole"ya k'ara k'yalk'yale wa da wata dariya har yana rik'e cikin shi
Abdallah da yaga abin na Umar da rainin wayau aciki kawai sai ya mik'e ya fice ya bashi wuri ,
Umar ya biyo shi yana "ustaz tsaya mana ya muna magana zaka gudu kuma"
Abdallah be kula shi ba sai ma ture hanun Umar da yayi a kafad'ar shi cikin fushi ya k'ara sauri,
Umar na ganin haka ya ce "yau maza sun yi fushi , sai naje biko"
Abdallah kuwa yana shiga afusace ba kowa a tsakar gidan sai wani bokiti da aka cika shi da ruwa aka aje ,
Aiko ya suri bokitin yayi bayi dashi , haka ya ringa watsa ruwan a kanshi yana ajiyar zuciya ,
Hafsa kuwa ta fito d'aki daga ita sai zani tana 'yan wak'e- wak'en ta da sosan wanka a hannun ta ta k'arasa inda bokitin yake yace d'aukeni inda kika aje ni ,
Ta ringa zagaye a tsakar gidan tana fad'in" anan fa na ajiye shi "
Mama da ta fito da buta za tayi alwalar magrib tace"ke hafsa ke dawa kike ta surutu kamar kanki be miki dad'i"
Hafsa cikin muryar kuka tace "Mama ruwa na na ajiye a bokiti zanyi wanka na fito ban ganshi ba"
Mama tace "yanzun hafsa ba na hana Ki wankan magrib ba?"
"Mama to AI wankan tsarki zanyi gashi lokacin sallah ya kusa "
"Uhum" kawai Mama tace
"Duk ma aljanin da ya d'auka ya fito dashi kafin......."hafsa bata k'arasa maganar ba taji an buga mata wani Abu akai ta baya , tana juya wa taga Abdallah ne ya buga mata bokitin da take nema , AI sai ta hau kame -kame
"Dalla ni rufe min baki mare kunya kawai" ya sakar mata bokitin a k'afa
Aiko tayi tsalle tana "wayyo Mama ya karya ni"
Mama kam bata bi ta Kansu ba ta gama akwalar ta ta shige d'aki
*DA SAFE*
Abdallah yakai ma Malam sadaki bayan ya nuna ma Mama tasa albarka , na n Malam ya sa ranar d'aurin aure kwana goma kuma ya ce baya buk'atar komai ,
Abdallah yayi godiya sosai ya tafi
[12/14/2017, 8:13 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
*Dedicated to BAWAN ALLAH fans group ina jin dad'in comments d'inku so let's keep it up*â¤
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
5⃣
Kuyi hak'uri readers wasu na k'orafin ban fad'i wacece hafsa ba
Hafsa yarinyar wan Mama ce taje garin su dai-dai lokacin aka hafsa ta isa yaye sai aka bata ita ta taho da ita , da wan nata yaga ta nuna sha'awar a bar mata hafsa sai ya amince wannan ne dalilin zaman hafsa agurin Mama
Cigaban labari
Da biki ya rage saura sati d'aya Mama ta shirya domin zuwa k'auyen su Dan ta sanar ma 'yan uwa su , kud'in aikin da Abdallah yayi na ranar shi ya d'auka ya bata ta tafi ,
Alokacin da taje musu da zancen sun ji dad'i sosai har ma wan nata ya ce da lokaci be k'ure ba da sun zo sun ma Malam godiya , kwanan ta biyu ta ce zata koma aikuwa aka shiga had'a mata kud'i da kayan abinci Allah Sarki da taga abinda aka had'a mata sai da tayi kuka hatsine buhu guda aka mata sai kuma kud'i nai ra dubu hamsi , Mama tayi kuka har tace ba zata amshi kud'in ba sunyi yawa , Baban hafsa ne ya ce mata "idan ba kin raina bane Hindatu Ki karb'a" da haka ta karb'i kud'in tare da godiya ta dawo gida cike da murna da jin dad'i,
Abdallah ma kanshi ya ji dad'in ganin kud'in
Ranar talata da safe suna zaune sai Mama ta ce "Bawan Allah ya kamata ka gyara d'akin chan naka tun da dai ba wani sai shi "
"To " kawai yace
"Ke hafsa shiga Ki d'auko min lalita ta a d'aki" Mama ta fad'i tana nuna hafsa
Bayan hafsa ta kawo lalita Mama ta kwance ta Ciro kud'in nan ta mik'e mai ta ce ya k'irga
Ya gama k'irga yace "dubu hamsin ne Mama "
Tace"to ka dauki yadda zai isheka ka gyara d'akin chan kafin dangin Amarya su buk'aci sa wani Abu "
Nan ma "to" yace
"Haba bawan Allah ina ta magana kayi shiru sai dai ka Bini da to"
Cikin sanyin jiki Abdallah ya ce "Wallah Mama jiki name duk a mace gani nake duk yarinyar da aka had'a ta dani an cuce ta domin ba zan k'are ta da komai ba sai k'uncin rayuwa"
"Kayi hak'uri Bawan Allah , Allah da yayi mu ahaka bai manta da mu ba , wani hanin ga Allah baiwa ne sai dai kawai muyita gode ma Allah," Mama ta fad'i tana share k'wallar da ta gangaro mata
Abdallah kuwa ji yayi tuk'uk'in da yake ji sai k'aruwa yake
Umar ne ya shigo da sallamar shi , duk suka amsa , bayan gaishe-gaishe Mama ta ce
"To kaga ga Umar nan yazo tashi kuje Ku hanzarta lokaci na tafiya "
Nan dai ya mik'e jiki ba k'wari suka fita , suna fita Umar Umar ya dasa shak'iyyan cin shi ya fara " Ango Ango kasha k'amshi "
Ni irin kallo Abdallah ya masa sai Umar ya had'iye yawu , daga nan ya tsuke bakin shi be k'ara cewa komai ba
Siminti suka siyo da katako sai kuma net da penti suna dawo wa suka hau aikin abin su ,
Ba su suka gama ba sai dare sannan Abdallah ya bi Umar d'akin shi Dan ya kwana
Da safe
Misalin k'arfe shad'aya na safe wasu mata su biyu shigo gidan da sallama
Mama na tankad'an gari , hafsa na hura wuta ,suka amsa musu sallamar sannan suka k'ara sa shigowa wasu yara ne yan matasa biyu suka shigo da da wasu manyan ledoji guda biyu
D'aya k'anwar Malam ce d'aya kuma yayar amaryar Malam d'in ce
Da fara'a a Mama tace "ah 'ah sannun Ku da zuwa yaya ma'u"
"Yauwa"suka amsa suma cikin fara'a ,
Hafsa ce tayi sauri ta d'auko tabarma ta shimfid'a musu suka zauna ,
Bayan gaishe gashe suka ce sunzo gyara d'akin Amarya ne , nan Mama ta nuna musu d'akin suka hau gyara ,
Leda duka shimfid'a ,suka sa labule ,
Suka rufe d'akin suka Mama makullin kwadon suka yi sallama
Hafsa ce ta ce ma Mama "Mama komai yana son gyara kinga yadda aka gyara d'akin yaya kamar ba shi ba "
Mama tace " shiyasa aka ce mana tsafta cikon addini"
Hafsa ta ce" lallai kam , Mama bari naje na duba Ummi kwana biyu bana ganin ta a islamiyya"
"Aiko nima ta kwana biyu bata zo gidan nan ba ko lafiya ?je Ki dubo ta"
Hafsa ta suri hijab d'inta ta fita
*Wace ce Ummi*
Ummi ita kad'ai ce 'ya mace ga Malam wadda Amarya sa ta Haifa masa asalin sunan ta ZAINAB k'awar Hafsa ce tare suka taso
*cigaban labari*
Bayan sun gama d'aukar karatu a wajen Malam Abdallah yace
"Malam lafiya Ummi bata zuwa makaranta kwana biyu?"
Malam yace "Ummi bata jin dad'i ne amma dai ta ji sauki "
Dukkan su suka yi mata fatan alkhairi suka kwashi littattafan su suka k'ara gaba
*Ranar d'aurin Aure*
Yau take juma'a kuma da an idar da sallar juma'a ne za'a d'aura auren Abdallah da Amaryar sa ,
Abdallah kuwa yau tun safe da ya tashi yake fama da wani matsanan cin ciwon kai ga jiri da yake gani , Umar har fita yayi yaje ya siyo mai magani ya sha amma a banza , sai da Umar yayi ta mai addu'a sannan ya samu yayi barci ,
Umar kuwa da yaga Abdallah yayi barci wanka yaje yayi sannan ya shirya cikin yadin shi mai sauk'in kud'i ya fita wajen daurin auren amma me kafin ya k'arasa har an d'aura ,
Malam ne ya k'araso wajen da Umar ke tsaye yana mamakin har an d'aura aure
"Umar ina abokin naka yake?"
"Wallah Malam yana can d'akina kwance yana fama da zazzabi amma dai yanzun yayi barci" Umar ya bada amsa
Cikin tausayi Malam yace " subhanallah Allah ya sawak'e"
Nan suka zauna suka CI gaba da tattaunawa
Gidan su Mama cike yake da mutane 'yan biki , yamma nayi kowa ya fara watse wa Dan 'yan garin su ma motar da ta kawo su tana jiran su , Dan Baban hafsa yace ba zasu zo su d'ora mata d'awai niya ba ,
Hafsa ce ta shigo a guje ta ce ma Mama " Mama ga Ummi can an sata a napep za'a kaita asibiti ciwon ta ya tashi"
"Hasbunallahu wani'imal malwakil , Ummi Allah ya yaye miki wannan lalura" Mama ta fad'i cikin jimami
Hafsa ta k'ara cewa" Mama bari na bisu"
"Ah'ah hafsa baki San asibitin da zasu je ba kiyi hak'uri ki jirasu"
Hafsa ba Dan taso ba ta hak'ura , domin tasan ciwon k'awar tata idan ya tashi har suma take yi
Allah Sarki Ummi Allah Sarki Abdallah😥🤫
[12/15/2017, 11:17 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
*wannan page d'in ma naku ne ina matuk'ar k'aunarku kamar yadda kuke k'aunar BAWAN ALLAH*â¤ðŸ’‹
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.