Complete Hausa Novels

Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel

Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt

Chapter 6 of 15

Page 8⃣-----🔟

Sai da tayi sallama sau biyu ba'a amsa mata ba , ana ukun ne ya amsa had'e da cewa,

"Mene ne?"

"Aunty Ummi ce tace na zo na d'auko mata shayin ta da magani"

Chan dai yayi shiru kamar ba zai bada amsa ba sai kuma yace "kije Ki ce mata tazo ta d'auka da kanta"

Har ta juya zata koma sai kuma yace "zo nan"

Ahankali ta d'aga labulen d'akin ta shiga ,

"Kwashe gasunan inda kika ajiye su"

Ba musu ta d'auka sannan ta fita jikin ta duk kyarma yake ,

Tana zuwa ta dangwarar da kayan a gaban Ummi " gashinan burinki ya cika kin tura ni wurin wancan zalimun mijin naki"

"Oho ko ma dai mene ne buk'ata ta tabiya tunda kin min abin da nake so" cewar Ummi tana murgud'a baki ,

"Idan kun gama wasan kwai-kwayon sai ku mayar mai da kayan shayin " Mama ta fad'i yayin da ta d'au buta tayi hanyar bayi

"To"dukan su suka ce ,

Mama na tafiya musu ya kaure tsanin Ummi da Hafsa akan Wanda zai mai da kayan shayi

Ummi na cewa "ke kika d'auko ke zaki mai da "

"Hafsa na cewa ke kuma ba mijin Ki bane ni ba runa wallah ba zan mayar ba"

Dai dai nan Abdallah ya fito ya , duk yaji me suke cewa , amma sai yayi kamar ma bai San suna wajen ba , Ya fara brush kenan Mama ta fito daga bayi , anan suka k'ara gaisawa alwala tayi ta shige d'aki shima alwalar yayi ya shige d'aki , duk da yana wurin musu tsakanin Ummi da Hafsa be k'are ba sai dai wannan karan a hankali suke yi , yana shiga ya tada sallar mai rabo (salatul duha),

Ummi ta gama tsumul- mulan shan shayin ta Dan Hafsat tuni ta gudu ta barta,

Hakanan tayi shahada ta d'auki kayan shayin ta nufi d'aki da shi sallama tayi sannan ta shi , ta same shi akan dadduma yana addu'a , kawai sai ta tsaya tana kallon shi da taga ya gama addu'ar sai tayi sauri zata fita kamar daga sama taji yace "ina zaki je?"

Sai ta hau kame kame,

"Yau ko gaisuwa ba zan samu ba kenan?" Yawani tsare gidan shi

Cikin sauri tace" yaya ina kwana?"

"Ah'ah Ki rik'e gaisuwar Ki indai sai na rok'a" ya sake murtuk'e fuska

Nan da nan ta tuna da nasihar Malam da ya ke cemata "ta guji b'acin ran mijin ta Dan zai iya kaita ga azabar Allah"

AI yana tuna wannan sai tayi sauri ta dawo kusa da shi ta zauna

Ta marai-raice murya "yaya Dan Allah kayi hak'uri , Malam yace idan kayi fushi dani zan iya shiga wuta"

Abin ya bashi dariya amma da yake bata so ya gane sai ya tsare gidan sa , azuciyar shi kuma cewa yayi "wato tanan kika b'ullo? Muje a haka game d'in zai fi dad'i"

Wani murmushi yayi sannan ya ce "idan kina so na daina fushi da ke kin had'a min shayi"

"Yo AI wannan mai sauk'i ne "cikin minti biyu ta had'a mai tea d'in ta bashi

Tana zaune a gurin ya gama karyawa sannan ya kalleta ya ce " ya jikin naki?"

"Alhamdulillah , naji sauki"

"To masha Allah , kinsha maganin Ki?"

Kai ta girgiza alamar bata sha ba

"Ummi Ki daina wasa da shan magani , tashi Ki d'auka Ki sha"

Ba musu kuwa ta mik'e ta d'auko maganin ta bud'e wata k'aramar randar ta ta d'ibi ruwa kamar abun arzik'i zata sha ,

Ga maganin ta Tara a gaban ta amma ta kasa sha ,

Shikuwa sai ya bita da na mujiya , wani abun mamaki bai wuce da ya tana zubar da k'walla ba , tana hawaye tana kallon maganin ,

"Lafiya? Ki sha maganin mana"

"Wallah yata magungunan ba dad'i "

"Ki daure Ki sha shi dama magani ba Dan dad'i ake shan shi ba"

Mik'e wa tayi tare da d'aukar ledar maganin zata fita ,

"Ina kuma zaki je Kuma?"

Cikin shagwab'a Ummi tace "zan je gurin Ummi name ita kad'ai zata iya bani nasha ba tare da nayi amai ba"

Shiru yayi na 'yan sakwanni sannan ya ce "zo na baki Ki sha"

"Ummi na fa lallab'ani take"

Wani murmushi yayi sannan yace" nima yayan Ki zan lallab'aki"

Jin hakan yasa Ummi kwasar ledar maganin tayi wurin shi ,

Zaman dirshan tayi a gaban shi sannan ta mik'a mai maganin , ya karb'a yace

"Ya Ummi take baki?"

Sai alokacin itama Ummi ta faki idon shi ta saki wani shu'umin murmushi azuciyar ta tace "anzo gurin ya ustaz"

"Ina magana kinyi shiru saifa kinsha maganin nan yau" yana magana yana d'aure fuska

"Dama sai ta gutsura maganin gida biyu sannan ta ta saka min d'aya a baki da ruwa , tana Shafa baya. Na har sai ta gama bani kuma tana yi tana fad'in , kiyi hak'uri Ummi na kisha , haka take ta fad'i"
😂😂😂😂😂

Bawan Allah sai da ya zaro ido sannan yace "to naji matso"
[12/18/2017, 1:47 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.