Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel
Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt
Chapter 15 of 15
Page 4⃣3⃣
Washe gari da safe haka ta tashi kamar an zare mata laka ajikinta komai cikin sanyin jiki take yinshi .
Tana kwance a d'aki har 11:00am batayi wanka ba Sai ga Mama tashigo d'akin ta kalli Ummi da kwaNce tamkar mai bacci , gefen katifar Mama ta zauna sannan ta dafa kafad'ar Ummi dake kwance tace "kiyi hak'uri Ummi nasan dukkan kowace Mace dole tayi kishin mijinta bai kamata Ki nuna damuwar Ki acikin mutane ba aro juriya zakiyi Ki sanya ma zuciyarki , sannan kada Ki kuskura Ki nuna ma kishiyar kin damuwar ki domin idan tasan lagwan Ki ta runk'a k'untata miki kenan , Ki zama mai juriya ta fannin kishi, Ummi ?" Mama ta k'arishe da kiran sunan Ummi wadda tuni idonta yake ambaliya da ruwan hawaye
Cikin sanyi Ummi ta d'ago ta kalli Mama tacw "na'am"
"Kiyi hak'uri da duk wacce zaki gani amatsayin abokiyar zamanki ba bak'uwar Ki bace kin Santa farin sani dan na tabbata zakuji dad'in zama"
Tunda Mama take maganar k'irjin Ummi ke dukan uku uku , kanta be k'ara kullewa ba sai da Mama tace mata tasan wadda Abdallah zai aure , mamaki take ita dai tasan bata San kowa Funtua ba to me hakan yake nufi?
Haka dai Mama tayita mata nasihohi sannan ta lallab'a ta taje tayi wanka ,
Da daddare Hafsa tashigo d'akin ta samu Ummi na zaune ta zabga tagumi, cikin tausayin k'awarta ta , zama tayi kusa da ita sannan ta fara magana
"Kiyi hak'uri Ummi nasan yaya bai kyauta miki ba , kin jajirce kinyi zaman jiran shi na shekara biyar duk da cewar bakida tabbacin cewar yana Raye ko akasin hakan amma kika jure, sai gashi da ya dawo babu abinda ya saka miki dashi sai kishiya, kiyi hak'uri Ummi wannan wata jarabawa ce daga ubangiji ya gwada kine don ya gane k'arfin imaninki, kuma nan gaba kad'an zaki samu *CHANJIN RAYUWA* tare da *RIBAR BIYAYYA* Kinji k'awata?"
Cikin sanyi Ummi ta d'aga kanta alamar "eh"
Hak'ik'a nasihar Mama da Hafsa ba k'aramar tasiri sukayi ba azuciyar Ummi har taji damuwarta ya fara raguwa.
"Yauwa k'awata to tashi muje ance Amarya na hanya muje mu tarbeta"
Harara ta juya ta watsa ma Hafsa sannan ta ce"to meye nawa kuma aciki?"
"Haba Ummi ba yanzun muka gama magana ba?"
"Eh amma Ki sani ba inda zani"
"To shikenan dama Malam ne yace lallai muje Dake tunda kince bazaki ba bari naje na gaya mai"
Bashiri Ummi ta mik'e ta sanya hijab d'inta tare da fad'in "Hafsa bomb "
Koda suka firo k'ofar gida motoci biyu ne dalla dalla sai d'aukan idanuwa suke ,
Abinda yaba Ummi mamaki bewuce ganin yayyen mamanta biyu da k'annin Malam biyu tana cikin Mamaki taji anjata zuwa jikin d'ayar motar da Babu kowa aciki , itadai Ummi haka ta zama rak'umi da akala, har suka isa gidan ,
"Masha Allah gida yayi kyau " haka mutane keta fad'i lokacin da suka gama zaga Gidan,
Hafsa da Ummi kuwa suna parlor Kamar suyi kuka dan takaici dan gidan ya tsaru komai ansa dadai na k'aramin mekud'e ,
Suna zaune su kad'ai a parlorn sai Ummi tace "ke nifa naji gidan shiru "
Hafsa tace "nima haka"
AI duk sai sukayi waje abin mamaki babu motocin da sukazo dasu babu Kuma matan da suka zo tare , nanfa suka fara salati kowa na bazai zauna ba ,
Suna zuwa bakin gate megadin ya taso yace "kuyi hak'uri 'yanMata an bani umarnin kar na bar kowa ya fita daga wancan b'arayin " ya k'arike yana nuna inda suka fito
Nan suka hau magiya da bashi hak'uri amma Sam yak'i hakanan suka koma ,
Hafsa Ce tace "yauwa bari na kira Aminullah ya zo ya maida mu gida ,"
Ummi tace" dad'ina na da ke akwai basira wani lokacin"
Alokacin da Hafsa ta kira Aminullah yace mata gasu nan a Hanya shida angon ,
Suna zaune tsumu kowa da abinda yake sak'awa azuciyar shi , suka jiyo k'arar tsayuwar mota,
Nan da nan zuciyoyinsu ya tsananta bugawa ,
Hannun k'ofar aka murd'a tare da turo k'ofar gami da sallama ,
Nan take numfashin Ummi yayi sizing na wucin gadi sakamakon idanuwanta da sukayi tozali da kyakkyawan angon ta ahankali ta furta "Subhannallahil khalk'il azim"
Abdallah ne a gaba sannan Saifullah sai Aminullah dake take masu baya ,
Abdallah kuwa direct kusa da Ummi yAje ya zauna yana fad'in "uwar gida sarautar mata"
Ta kaici ne ya kama Ummi ta yunk'ura zata mike kawai sai taji an jawota , unexpected taJi ta fad'o ajikin shi ,
Dariya Saifullah yayi yace "au tun bamu je ko ina ba?, ke Hafsa tashi mu tafi",
Shi dai bai ce komai ba harsuka kai bakin k'ofa , Ummi ko sai kick kici take tana son k'wacewa amma ta kasa Da dai taga dagaske tafiya zasuyi AI sai tace "ni ka k'yaleni zasu tafi subaRni,"
Ahankali ya rad'a mata. Dai dai saitin kunnanan Ta," ina zakije ne baby?"
"Gida" ta bashi amsa a tak'aice
Kallon yayi sannan yace " Ummi kina tunanin zanyi miki *Butulci* bayan *Hallacin so* da kikamin idan na miki haka banzama adali ba , Ummi kisani har *ABADAN* bani da tamkarki ke kad'ai ce Mata
AI mutumiyar taku duk ya kashe mata jiki da k'yar ta iya cewa "Amaryar taka fa?"
"It's just a plan"ya fad'i yana dariya
Cizo ta daddage ta ganna Mishi a k'irji saida yayi 'yar k'ara ita ko mik'e wa tayi taruga bed room aguje ya bita yana fad'in " saina rama"
Haka dai sukayita guje guje daga K'arshe dai sukayi abinda ya zamar musu wajibi bayan sunyi sunnoni sannan suka fuskanci junansu cikin soyayya da k'aunar juna ,
Tun daga wannan rana Ummi take samu kulawa ta musamman gami da soyayya
*Bayan sati biyu*
Saifullah ya aika aka nema masa auren Hafsa Kasan cewar da sannayya nan take aka bashi tareDa sa rana wata d'aya aiko Saifullah ya daka tsalle yace yayi yawa ina laifin sati biyu nan dai Aka sha kan Baban Hafsa ya hak'ura
An ragargaji biki Ummi itace Babban k'awar Amarya Sosai akasha shagali ,
Bayan biki Dr Ahmad yakira Abdallah ya sanar masa ranar ranar wata litinin asibitin shi bashiri ranar Sunday ya wuce Kano ,
Aiki yake sosai , ,sai ya kasance shi da Zaria sai dai week end ,
Allah Sarki Abdallah bai manta hallaci ba mak'udan kud'i ya d'auka yA ba Umar domin YakAfa kanshi
,
Bayan shekara d'aya Da Rabi
Tunda Nesa na hango shi yana Ta sunturi k'ofar labour room ya had'a zufa,
Bud'e k'ofar da akayo ne ya sashi saurin matsawa Dr da ya bud'e k'ofar D'auke da murmushi afuskarshi yace"congratulation Dr Abdallah your wife delivered healthy Nd safely "
Murnar Abdallah Sam tak'i b'oyuwa jiYake duk duniya ba Wanda ya kAI shi Sa'a, yana cikin murna sai ga Saifullah da Hafsa itama DA tik'ek'en cikinta, tare suka Shiga dakin saibarcin ta take ,
FArincikinSu bai Kara bayyanu wa ba sai da suka ga yara biyu kyawa wa Wayyo zokuga godiya ga ubangiji wajen Abdallah. Ranar suna yara Ahmad da kabir .
Bayan wata uku Hafsa ta Haifo sankaceceyar yarta taci sunan Hindatu (Mama)
Aminuallah kam yana chaina yana masters dinshi akan bussines
*ALHAMDULLIH*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.