Complete Hausa Novels

Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel

Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt

Chapter 10 of 15

Page 21----22

Haka nan su Malam suka tattara suka koma Zaria ba tare Abdallah ba zuciyoyin su cike da zullumin me zasu gaya ma mahaifiyar shi da kuma matar shi , ahaka suka sauka a tasha suka hau napep , direct gidan su Umar suka wuce ,

Aiko Maman Umar na ganin shi sai kuka domin yadda ta Ganshi ba k'aramin firgita tayi ba nan k'annen shi suka hau ihu " yaya Umar oyoyo !"

D'an autan su ne ya fita da gudu yaje gidan su Abdallah Ummi na alwalar la'asar Mama na kofar d'aki Hafsa kuma tafito daga bayan gida ,

Yaron ya k'arasa kusa da Mama cikin zumud'i yake ce mata "Mama yaya Umar ya dawo "

Cikin zafin nama Ummi ta waigo tana kallon shi

Mama ko cewa tayi "da gaske ?!"

"Eh Mama amma ya dawo kanshi a d'aure da wani Abu"

AI nan Ummi ta yarda butar hannun da dama already akwai hijab ajikin ta AI sai ta nufi k'ofar gida ,

"Ke Ummi ina zaki je ?" Mama ta fad'i yadda taga Ummi zata fita kamar zautacciya

"Ina zuwa Mama "kawai Ummi tace tasa kai

Hafsa da sai yanzun ta k'araso waje sai k'wala kira tayi "Aunty Ummi jira ni"

AI ina AUNTY Ummi gudu-gudu sauri-sauri ta runk'a had'a wa ,

💔💔💔💔💔💔💔💔

*Kano*

Yau kwana bakwai kenan ana fama da Abdallah amma Sam be san ana yi ba gashi zuciyar shi tana aiki amma kuma gangar jikin shi bata motsi , duk sun sare da al-amarin shi,

Yauma kamar kullum likitoci ne zaune awani k'awataccen office suna tattaunawa akan Abdallah , wata nurse ta shigo cikin sauri ta fara gaya musu patient din room no 18 ya farka kamar jira suke nan suka mik'e cikin sauri suka k'ara k'ofar d'akin ,

A zaune suka same shi akan gadon ya sakko da k'afafun shi k'asa , ya rik'e kanshi dake tsananin Sara masa ,

Koda suka bud'e k'ofar suka shigo kallo kawai ya bisu dashi domin be tab'a ganin su ba ,

Doctor d'in nan ne da ya ce ya sanshi ya matsa kusa da shi ya fara magana

"Ni sunana Dr Ahmad , zan iya sanin naka sunan?"

Shiru yayi bece komai ba , Dr Ahmad ya sake cewa "ko zan iya sanin naka sunan?"

"Ban sani ba" ita ce amsar da ta fito daga bakin Abdallah

Dukkan su likitocin suka kalli junan su

Dr Ahmad ya sake jefa mashi wata tambayar "ya sunan garin ku?".

Girgiza kai yayi nan ma alamar be sani ba

Nan likitoci suka sake firgita wani likita ne ya ce mai "nan ina ne ?" K'are ma d'akin kallo yayi tas sannan ya runtse idon shi gami da matse hannun shi kamar zai kai naushi

Dr Ahmad ne yace su k'yale shi ya huta , nan suka yi mai allurar barci ya koma

💔
[12/30/2017, 10:59 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣5⃣

*Cigaban labari*

A b'angaren Dr Ahmad kuwa be b'oye ma iyalin shi komai game da Abdallah ba ,

Hajiya Ramla tayi farin ciki sosai har ta k'osa safiya tayi taga me kama da d'anta,

*Zaria*

Yau kusan sati uku kenen ba labarin Abdallah hakan bai sauya akalar damuwa acikin zuciyoyin dangin sa ba musamman ma mahaifiyar shi da matar shi ,

Ummi kuwa yanzun wani irin tsantsar son Abdallah ne ke damun ta gashi yayi mata nisa , Dan yanzun gani take bayan iyayen ta babu Wanda take ma so da k'auna tare da mararin gani irin Abdallah,

Malam kuwa ya duk'ufa addu'oi ba dare ba rana ,

Umar kuwa Alhamdulillah ya ji sauk'i sai dai damuwar rashin d'anuwan shi amininshi, shi kad'ai ke tayar mai da hankali akoda yaushe

Hafsa ce keta fama da Ummi akan taci abinci " haba Aunty Ummi yanzun ke kullum sai an ta fama da ke wajen cin abinci kamar k'aramar yarinya ?"

Ummi dai bata ce komai ba iya kacin k'walla da keta gudu a kan kumatunta ,

Hafsa ta sake cewa , " ayyah k'awata Dan Allah ciki kinga rabon Ki da abinci tun jiya da rana gashi yanzun Kusan k'arfe uku"

Kallon Hafsa tayi tace "zanci amma sai in zaki bani a baki " ta k'arasa maganar cikin shagwab'a

"Naji duk wannan me sauk'i ne "

Nan Hafsa tayi ta ba Ummi abincin tana ci , haka Mama ta fito ta samesu duk sai suka bata tausayi,

*Kanon Dabo*

Kamar yadda Dr Ahmad ya tsara acikin sati uku ya samar masu *Visa* shida D'an mak'ocin sa kamar yadda yake fad'i , basu bar garin ba sai da yasan yadda yayi ya masamar ma Abdallah takaddun makaranta sannan suka d'aga birnin *London*

Sosai Abdallah yayi k'auyanci Kasan cewar bai tab'a sanin wani Abu makamancin k'asar ba ,

A wani hotel suka sauka , bayan sun D'an huta sannan Dr ya nema masa Wanda zai runk'a koya mai turanci

Ba da jimawa ba ya saman mai admission a London university , inda zai karanci medicine,

Sosai Abdallah ya maida hankali wurin karatun shi saboda bashida damuwar kowa acikin k'wak'walwar shi,

Sai da Dr ya tabbar da Abdallah ba shida matsalar komai sai nan ya dawo Nigeria tare da barin shin amanar shi awajen wani Bature

💟💟💟💟💟💟💟

Wasa-wasa dai yanzun wata takwas da b'atan Abdallah ko wanda yaga me kama da shi basu gani ba,

Abun da yake k'ara d'aga ma Ummi da Mama hankali bai wuce duk in sunyi istikhara suna samun natsuwa ba hakan ke nuna musu Abdallah yana cikin kwanciyar hankali, to amma yana ina ne? Mai ya sa yayi nesa da su? Shin baya tunanin halin da zasu shiga ne? Wad'an nan tambayoyi su suke ta yawo a k'ak'walen su amma kuma kaf babu mai amsa masu su,

Wata rana Mama tashir ya taje gidan su Ummi domin su tattauna da mahaifiyar ta akan makomar auren Ummi da Abdallah,

Bayan sun gaggaisa tace " Dama nazo ne akan maganar wad'an nan yaran , kinga yanzun wata takwas amma bawan Allah shiru , shine nace ko za'a raba auren Ummi idan ta samu wani mijin tayi aure"

Maman Ummi tace " amma Maman Hafsa sai naga kamar yayi wuri afara wannan maganar balle ma muna sa ran insha Allah ba da jimawa ba zai dawo"

Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace " to AI shikenan ni dama naga k'a'idar musulunci wata shida ne shiya sa kuma da naga babu rabo a tsakanin su"

"Hakane Maman Hafsa my dai k'ara hak'uri"

Nan dai suka gama maganar su ta tafi ,

Ummi na kwance a d'aki tunani duk ya isheta Mama ta d'aga labulen d'akin ta shigo da sallama amma Ummi Sam bata ma anayi ba ,

Sai da Mama ta dafa ta sannan ta waigo a firgice ta kalleta "yanzun Ummi ba zaki cire wannan yawan tunanin a ranki ba ,? Shi wanda kike yi Dan shi d'in yana chan hankalin shi kwance bema San kina yi ba , Dan Allah Ki rage tunanin nan kar ya haifar miki da wata matsalar kuma"

Cikin jin kunya Ummi tace "to Mama"

💟💟💟💟💟💟💟

*BAYAN SHEKARA D'AYA DA RABI*

*London*

Wa ni had'add'en guy ne na gani na fad'a zaune a cikin library yana karatu fuskarsa d'auke da wani farin glass , kamar daga sama , yaji an ce mai

"Hi"

D'agowa yayi yakalli wanda yayi maganar shima matashi shi ne kyakyawa , "hi"kawai yace masa ya maida hankalin shi zuwa littafin da yake dubawa

Matashin ya sake cewa " please can I have a sit?"

D'aga mishi kai kawai yayi , ,

Shi kuma wancan ya zauna yana murmushi, mik'amai hannu yayi yace " I'm saifullah from Nigeria "

Sai alokacin mai karatun ya aje littafin tare da cire glass d'in idonshi sannan ya mik'a masa hannu sai ya ce " Abdallah also from Nigeria"

*Nikam nace lallai ma lallai Ashe Abdallah ne gaskiya ya k'aro wulak'anci*

Cike da murmushi Saifullah ya ce "Ashe dai nasamu D'an uwa"

Murmushi kawai Abdallah ya mai ,

Saifullah irin mutanan nan ne masu shegen surutu ba irin su Abdallah ba miskilai,

Ba jimawa suka saba sosai har suka k'ulla abota
[1/1, 6:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣6⃣

Mama ce zaune a tsakar gida ta zabga tagumi tana kallon Ummi da keta faman wanki , hak'ik'a yarinyar tana matuk'ar bata tausayi tayi aure amma bata San miye auren ba balle ta tantance dad'in shi , babu abinda ta tsinta a cikinshi sai wahala ita irin tata k'addarar auren kenan , can kuma ta mik'e kamar an tsikare ta , ta zari Hijab d'inta da ke sagale jikin k'ofa sannan ta juya ta ce ma Ummi "bari naje na dawo"

"To Mama adawo lafiya"

Mama na fita bata zame ko ina ba sai gidan su Ummi ta ci sa'a ta samu Malam yana nan bayan sun gaggaisa ta fara fad'in abin da ya kawo ta ,

"Dama Malam Maganar Ummi ne ya kawo ni"

Malam yace "to Allah yasa dai ba laifi tayi ba"

"Ko kad'an Malam Ummi bata laifi , sai dai mune muke k'ok'arin yi mata laifi"

"Kamar yaya kenan?"

"Malam tunda kaga har yanzun Abdallah bai dawo ba kuma gashi shekara har ta gota Dan Allah anema ma yarinyar nan sauk'i a raba ta da wannan auran"

Shiru Malam yayi sannan yayi ajiyar zuciya yace "maganar Ki gaskiya ne amma kafin mu yanke hukunci ya kamata muji ta bakin Ummin , Dan haka idan kin koma Ki turo min ita "

"To shikenan Malam mungode Allah ya k'ara girma"

Nan suka k'ara tattaunawa akan maganar sannan Mama ta yi musu sallama ta tafi ,

Mama kuwa bayan sallar isha ta kira Ummi tace mata taje Malam yana Neman ta , sai da ta D'an ji gaban ta ya fad'i amma kuma ta daure ta tafi ,

Kai tsaye cikin gidan su ta nufa bayan gaishe-gaishe suna D'an fira da k'anan ta a tsakar gida sai ga Malam ya shigo , Maman Ummi ta shimfid'a mai tabar ma ya zauna suka gaisa sannan ya k'ara da cewa " Ummi dama ba wani Abu bane yasa nakira Ki akan auran Ki ne da Abdallah shin kin yarda a raba ko kuwa zaki iya hak'urin jiran shi?"

Tunda Malam ke magana hawaye suke ambaliya a fuskar Ummi , ta kasa magana ,

Malam ne ya sake magana "ina jinki Ummi baki ce komai ba "

Ummi ta fara magana muryar ta na rawa " Baba Dan Allah karku raba ku D'an k'ara mai lokaci Dan Allah Baba"

Shiru Malam yayi domin ya fahimci 'yar tashi tana son mijin ta "shikenan Ummi mun k'ara mai shekara d'aya idan be dawo ba ko ba da yardar Ki ba za'a warware auren nan"

"Baba na amince na gode"

"Shikenan Allah yayi miki albarka shi kuma Allah ya bayyanar mana dashi"

"Amin" Ummi tace sannan kuma tayi shiru

"To tashi Ki tafi dare nayi ko kuma akwai Wani Abu ne "

Shiru tayi kamar bazata ce komai ba sannan kuma ta fara magana bakinta na rawa "Baba dama alfarma nake nema"

"Ki fad'eta ko menene indai bai sab'a ma addini na ba zanyi miki shi "

"Baba dama so nake Dan Allah ka barni na cigaba da zuwa makarantar boko"

D'agowa yayi ya kalli 'yar tasa cikin natsuwa sannan yace "Ummi ba nak'i kiyi karatu bane , ah'a imani ne yayi rauni a zukatan wasu , duk da cewar bani da kokwanto akan tarbiyyar da na baki , amma igiyar auran da ke kanki?"

"Insha Allah Baba nayi maka alk'awarin kare mutunci na ko ina da aure ko banda shi , Dan Allah Baba ka amince min karatun shi zai rage min damuwa"

Jinjina kai yayi tare da gamsuwa da zancen 'yar tasa sannan yace " kije zanyi shawara duk abin da na yanke zaki ji"

Godiya tayi sannan suka yi sallama ta Shiga d'akin Ummin ta , sukayi sallama sannan ta Shiga d'akin abokiyar zaman Umman nata ta fito ta koma gida ,

Da sallama ta Shiga Hafsa da Mama ne a tsakar gida sai kuma Umar da ke zaune gefe d'aya yana sharb'ar tuwan dawa miyar kuka da taji daddawa , dukan suka amsa mata sannan suka gaisa da Umar , tayi ma Mama barka da dare ta wuce d'akin ta ,

Katifar ta tahau ta yi matashi da pillow d'aya d'aya kuma ta rungume shi tsam ajikin ta kamar za'a k'wace mata shi , wasu zafafan hawaye suka gangaro mata a fuska a hankali ta fara magana " mijina *KADAWO GARENI* ( by Rafee'at D/Dukko) suna shirin rabamu , hakan yana nufin rabuwa ta har abada domin duk randa na aka katse igiyar auran mu na tabbata bazan moruba" nan dai tayi ta Sumbatun ta har bacci yayi gaba da ita

Kamar yadda ta saba karfe uku na dare take tashi ta gabatar da nafilfili har sai alfijir ya keto sannan ta had'a da raka'atanil fijri sannan bayan tayi sallah tak'ara da karatun littafi mai tsarki sannan ta fito tsakar gida Susan abinyi ita da sahibar ta, wannan itace d'abi'ar Ummi,

A b'angaren Abdallah kuwa karatun shi kawai yasa gaba ba ruwan shi da kula 'yan mata , kuma har sun gaji da naci idan ma suka dameshi har mari yake had'awa dashi , sau dayawa Saifullah yana k'ok'arin tank'wara shi amma ina Abdallah kaifi d'aya ne baya tank'waruwa , haka rayuwa take cigaba da wanzuwa atsakanin su,

Ab'angaren Ummi kuwa ranar wata juma'a Malam ya aiko mata da wata takarda a nannad'e a cikin Leda yaron yace mata gashi ita da Hafsa ,

Tana bud'ewa form ne na wata makarantar gwamnati ya sama masu , ai aguje ta ruga d'akin Hafsa tana k'wala mata kira ,

Saida ta Shiga d'akin sannan ta b'oye takardar tare da fad'in " nazo miki da albishir amma sai kin ban goro"

Hafsa da ta farka daga bacci ta fara magana had'e da mik'a "lallai AUNTY Ummi wannan al-amarin mai girma ne tunda na ganki cikin farin ciki"

"Ke nidai Ki daina b'ata min lokaci Ki bani goro nabaki albishir "

Hafsa tace "to naji zan siyan miki biscuit d'in nera goma "

Ummi ta bita da harara tare da fad'in " saboda kin maidani k'aramar yarin ya ko? To Ki bari lokacin da kika tanadi goron kizo Ki karb'i albishir d'in naki " ta kama hanyar k'ofa

Cikin hanzari Hafsa ta bi bayan ta tana fad'in " haba Aunty Ummi tawa , Aunty Ummi ta yaya Abda...."

Ummi ta katse ta tare da nuna mata form d'in dai dai nan Mama ta fito tana fad'in "hayaniyar me nakeji ne?"

Ummi ta gayawa Mama ko mene ne , Mama taji dad'i sosai sannan ta bi Malam da addu'ar fatan alkhairi sannan ta ce ma su Ummi suje suyi mishi godiya

@08165728746
[1/2, 7:22 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*Dedicated this page to you my k'awalli , Allah ya raya mana Sadeeq, kekuma Allah ya.....🤭 kindai gane ba sai na k'araso ba*🤣

❤ *Much love dear*❤

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣7⃣

Cikin sa'a Ummi da Hafsa suka fara zuwa makaranta , uniform d'in yayi musu kyau Kasan ce warshi Navy blue da white sunyi matuk'ar kyau a cikin shi , SSS1 aka sasu , Kasan cewar makarantar tana da d'an nisa da unguwar su amma sabo tsabar son ayi karatun haka suke takowa suje a k'afa su dawo a k'afa , babu ranan da zasu fita maza basu biyo su ba sunan Sam magana da su amma Sam basa sauraran su hakan yasa dole Ummi ta fara sa nik'ab amma duk a banza , Dan wasu ma da suka gane gidan nasu kai tsaye suke zuwa Susa yara suyi sallama , duk da Hafsa tasha gaya musu cewar Ummi matar aure ce amma Sam basa yarda , tun Malam be San meke faruwa har yazo ya sani amma dai ya zuba mata ido ne kawai lokacin da suka d'iba ya ciki,

A b'angaren Dr Ahmad kuwa komai zai yi ma Abdallah tsakani da Allah yake yi mai baya la'akari da cewar bashi ya haife shiba duk wani Abu na more rayuwa ya mallaka mai tun daga kan suturar sawa har zuwa mota me tsada tare da sauran a bubuwan more rayuwa Dr baya k'yashin sai mishi , yanzun haka yana nan yana gina wani tamfatsetsen asibiti da niyyar idan Abdallah ya dawo ya mallaka mai shi,

A b'angaran Abdallah kuwa karatun shi yake sosai ya madai hankalin shi , shima Saifullah ba baya ba yana da k'ak'walwa sai dai shi wani lokacin yana da barkwanci kamar Umar, a haka suke karatun su Wanda ko Hutu akayi basa dawo wa Nigeria,

*BAYAN SHEKARA D'AYA*

Ummi ce zaune gaban Malam , Ummin ta , Mama da kuma Inna a bokiyar zaman Babar ta duk sun tsura mata ido , ita ko sai faman k'walla take share wa ,

Cikin sanyi Malam ya fara magana "Ummi tun d'azun muke miki magana baki bamu amsa ba gashi sai kuka kike yi "

Cikin kukan ta fara magana " Baba Dan Allah kar ku raba in da yaya Abdallah wallahi ni ina ji ajiki na yana Raye be mutu ba "

Mama ce tace "to yanzun Ummi ai ba zaki zauna kiyi ta jiran shi ba yan zun kusan shekara uku fa , kiyi hak'uri Ummi "

Ummi ta kalli Mama tace "yanzun Mama har da ke ake shirin rabani da Abdallah ?"

Karin Mama tayi magana Inna ta amshe " Ummi muna sonki muna k'aunar Ki shiyasa mukayi wannan tunanin Ki fahimce mu ba muna nufin cizguna miki bane"

Malam yayi gyran murya yace " shikenan Ummi na sake k'ara miki shekara d'aya amma kisani daga wannan ba k'ari ,"

Shiru tayi sannan kuma ta jinjina kanta alamar ta yarda ,

Sannan Malam ya ce ta tashi ta tafi ,

Tana Shiga gida Hafsa ta samu tana shara , Hafsa na ganinta ta shigo idon nan jajir ga k'walla suna sintiri a Kumatun ta ta saki tsitsiyar ta nufi kanta tana fad'in

"Aunty Ummi lafiya ?, mai aka miki?"

Cikin sauri Ummi ta k'arasa kusa da Hafsa tan rungume ta tana kuka tana fadin " Hafsa zasu raba ni da farin cikina da jin dad'i na ,"

Hafsa cikin d'aurewar kai ta ce "Aunty mene ne wannan abun da za'a rabaki dashi ?"

Cikin kukan ta sake cewa "zasu rabani da yaya Abdallah bayan duk sun San ba mutuwa yayi"

Cikin sigar lallashi Hafsa take shafa bayan Ummi tare da fad'in " kiyi shiru Aunty Ummi , babu Wanda zai raba ku , kuma insha Allah yaya zai dawo gare Ki"

Sun kusan minti goma atsaye Hafsa tana ta faman lallashin Ummi sannan ta hak'ura ta tafi d'akin ta kan katifarta ta fad'a tare da dafe kanta da take ji kamar ana sa gatari ana Sara mata shi, ahankali kuma take fad'in

"Yaya Abdallah meya ka nisanta dani? Shin baka San ina sonka bane ? Shin baka tunanin halin Dana ke ciki?, yaya rashin ka zai sa su guntule igiyar auran mu"

Ta k'arasa tare da sakin kuka mai siririn sauti nan da nan jikin ta yayi zafi sai zazzab'i chan kuma ta hau rawar sanyi ,

Shiko Abdallah suna zaune a d'aki shi da Saifullah suna buga game sai Saifullah yaji abokin nashi yayi shiru juyawa yayi ya kalleshi tare da fad'in "bro's how far?"

Kai Kawai ya girgiza mishi domin wani irin bugawa da ya wuce misali yake jin zuciyar shi tana mishi , Wanda har ya kasa magana,

Sake tab'ashi Saifullah yayi sannan yace "ba kada lafiya ne aboki na ?"

Cikin rauni ya kalli Saifullah ya girgiza gami da dauriya suka cigaba da game d'in .

Hafsa kuwa data ga Ummi ko alwalar magrib bata fito tayi ba gashi har an idar da sallar Isha yasa ta d'auki kwanon abincin su ta bita ta d'aki tana Shiga ta same ta tana ta rawar sanyi , ahankali ta k'arasa kusa da ita tare da tab'a wuyanta zafi rau ga wani irin numfashi da take yi sama sama , a tsorace Hafsa tace

"Aunty Ummi bakida lafiya ne?"

Ummi kawai ido ta bita dashi sai wasu zafafan k'walla dake gangaro mata,

Hafsa na ganin haka ta mik'e cikin sauri ta fita , fitarta yayi daidai da sallamar Umar ta amsa shi cikin firgice ta sanar ma da Mama halin da Ummi ke ciki, dukkan su suka d'unguma suka Shiga d'akin

Cikin tausayin Ummin , Umar ya ce ma Mama ta D'an shafa mata ruwan sanyi bari ya he ya siyo mata magani ya dawo ,

Haka kuwa akayi ba'afi minti ashirin sai gashi ya dawo d'auke da ledar magani ,shafa mata ruwan sanyin da mama tayi yasa ta D'an ji dama-dama

Cikin sanyin murya yace mata "sannu Ummi"

"Yauwa "ta fad'i sannan ya mik'a ma Hafsa maganin tare da fad'in "ku bata ta sha idan taci abinci , no zan Shiga gida sai da safe"

Godiya suka yi mai ,shiko rashin jin dad'in hakan yasa shi yamutsa fuska tare da fad'in"haba Mama yanzun Dan nayi muku wani Abu sai kun gode min idan kina gode min sai naga kamar kin ban-bantani da Abdallah Wanda bana jin dad'in hakan"

Ajiyar zuciya Mama tayi sannan tace "Allah yayi muku albarka , Allah ya jib'inci lamuran ku ya kare ku daga sharrin masharranta ya sada ku da alkhairin sa"

Cikin jin dad'in addu'ar mama duk suka amsa da "amin"

Sannan Umar yayi musu sai da safe ya fita,
[1/3, 3:37 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*Readers bansan da bakin da zan gode muku ba akan addu'oin fatan alkhairi da kuke min nagode nagode Allah ya bar k'auna Allah ya sada mu a aljannatul firdaus*🤝

*Fiddausi (maman junior)*❤

*k'ungiyata abin alfaharina ina jidaku ina alfahari da ku da bazarku nake rawa REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS Allah ya k'ara mana hazak'a da basirar nishad'antar da masu karatu*🤝

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣8⃣

Ummi kam kwanan ta uku taji sauki har ta fara zuwa makaranta sai dai damuwa da yayi mata yawa tana yawan tunani wani lokacin sai kazo kusa da ita ka gama duk abinda zakayi bata sani ba ,

Hafsa kam ta shiga damuwa ganin halin da k'awarta take ciki ,

Wata rana suna school antashi break Hafsa ta fita ta samo musu D'an abin da zasuci , tana fita Ummi ta dasa tunani har Hafsa ta dawo bata San ta dawo ba, saida ta tab'ata tare da fad'in

"Wallah Aunty har za'a iya sace Ki baki sani ba "

Harara ta balla mata tare da fad'in "tunda na zama gunki ko?"

"A'ah ni bance kin zama gunki ba , nidai CI Waran nan Principal yana Neman mu a office d'in shi"

D'an kwab'e baki tayi sannan suka fara ci , Hafsa tana tunatar da ita illar tunani , ahaka suka gama ci sannan suka nufi office din P C kamar yadda suke Kiran shi , ko da suka suka isa sun Tarar da students takwas gefen P C vice d'in shine yana rik'e da wani file a hannun shi , bayan sun gaida su P C ya fara magana kamar haka ,

"Lura da yanayin k'ok'arin ku a aji shiyasa muka zab'eku , kuna da k'ok'arin da yawuce ace kuna SSS2, Dan haka mun yi muku alfarma kuje ku sanar ma iyayen ku zasu biya Rabin kudin jarabawar W A E C sauran kuma gwamnati zata biya "

Cike da jin dad'i d'aliban suka fara godiya gami da nuna farincikin su ,

Vice Principal ya ciro receipt me d'auke da iya yawan kud'in da zasu biya , sannan suka k'ara godiya suka koma classes d'in su ,

Ummi da Hafsa kuwa sai zumud'i ake akoma gida , Dan Ummi har ta manta da bak'in cikin da take tare dashi ,

Bayan an tashi kai tsaye gidan Malam suka nufa suka gaya mai shi kanshi yaji dad'i sannan yace musu suje gida ba wani damu wa insha Allah bazai gagara ba , da murna suka tafi,

Gidan Mama kuwa da sallama suka Shiga Hafsa ce tayi turus ganin mahaifinta cikin sanyi ta k'arasa Ummi kuwa Dama bata San Hafsa ta tsaya ba nan duk suka gaishe shi tare da tambayar mutanan gida sannan Ummi ta nufi d'akin ta Mama ko tana band'aki basu sameta a tsakar gidan ba,

Baban Hafsa ya kalleta cikin kula yace "ya makaranta ba dai wata Matsala ko ?"

Bayanin da PC yayi musu shi tayi mai ,murmushi yayi sannan yace " to ai ba damu wa idan na koma gida zan turo Bello da kud'in " cike da jin dad'i Hafsa ta fara godiya Baban ya sake cewa " Hafsa Ki natsu Ki maida hankalin Ki kiyi karatun nan Dan nan gaba inyi alfahari da ke"

"Insha Allah Baba ba za'a samu wata Matsala ba"

Dai dai nan Mama ta fito tana fad'in " 'yan makaranta an dawo?"

"Eh Mama ya gida ?"

"Lafiya lau "

Hafsa ta tashi ta Shige d'akin ta domin ta chanja kaya tayi sallah ,

Ummi kuwa da yake ba sallar take ba kwanciyar tayi har saida Ummi ta kawo musu abinci sannan ta tashi suka ci,

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

Ko wani Uba ya jajirce wajen Samar ma 'yar sa farin ciki kuma yanzun Alhamdulillah an dace Dan yanzun har sun gama zana exams d'insu both NECO , WAEC Nd JAMB, admission kawai suke jira,

Cikin sa'a kuwa suka samu admission a A B U ,dukan su zasu karanci Medicine bak'aramin dad'i suka ji ba mu sammam ma iyayen da su kad'ai suka San kud'in da suka kashe,

Bayan suyi registration da wuri ba har sai da aka fara lectures , sannan suka gama suka fara attending ,

Mutane da dama suna son yima Ummi magana daga mazan har matan amma rashin sakin fuskarta kesa su kasa zuwa wurin ta , ita ko bata San ma suna yi ba , Hafsa ce mai D'an sakin fuska har tayi k'awaye,

Watanni sunja lokaci ya tafi wata rana umma na zaune a class d'in su sai ga wani lecturer ya aiko wai a kira masa Zainab Kabir ,

Wani fad'uwar gaba ne ya Ziyarci zuciyar ta kawai sai ta fara fad'in "INNALLILAHI WA INNA ILAIHIR RAJI'UN"

Hafsa dake gefen ta tace"Aunty Ummi kefa ake kira"

Jiki a sanyaye Ummi tabi bayan shi har zuwa office d'in mutum , ita dai bata taba ganin shi ba amma , gashi kallon da yake mata kad'ai yana sa hanjin ta juyawa ,

Mutumin ya kalli Wanda suka shigo tare ya ce masa "you can go"

"Ok Sir" matashin ya bada amsa tare da barin office d'in

Juyawa yayi ya kalli Ummi wadda da ka ganta Kasan a firgice take "zauna mana 'yammata" yafad'i tare da nuna mata kujerar dake opposite d'in shi ya ,

Cikin sanyi ta zauna ,

Murmushi yayi sannan yace " Malam Zainab nasan baki sanni ba amma ni nasan Ki kuma ina bibiyar Ki , Ki bani dama in yaye miki k'unci da kewar dake addabar zuciyar Ki"

Cikin zaro ido da firgici Ummi tace "Subhanallah nifa matar aure ce"

Ido ya kanne mata irin nasu na 'yana duniya yace "karki damu Zainab dama ba aure zamuyi ba kawai zamu d'an huta ne mu mori junan mu "

Ummi kam salati kawai take ta faman rafsawa

Shikuwa k'aton banzan sai ya sake ce mata "karki damu babu Wanda zai San meke faruwa a tsakanin mu daga ni sai ke , kuma nayi miki alk'awarin samun nasara arayuwar duk abinda kike buk'ata indai kud'i nayin shi zanyi miki "

Cikin hasala ta fara magana "kaico kaico shin da kake cewa babu mai ganin mu Allah da ya hallice mu fa? Idan ka manta bari na tuna maka , Allah ne ya hallice mu baki d'aya Dan haka ko k'asa muka hak'a muka shige Allah yana kallon mu kuma baka isa kai D'an Adam kayi Katanga tsakaninka da mahaliccin ka ba, kuma ka sani bana buk'ar taimakon wani abun hallitta balle kai azzalumi Allah ne gatana kuma shi na dogara shi kad'ai zai biya mun buk'atuna "

Wata dariyar mugunta yayi sannan yace" duk kalaman Ki bazasu sa na chanja k'uduri na a kanki ba baby kin had'u , Ki taimaka min na lashi zumar nan"

Wani bak'in ciki ne ya turnuk'e Ummi gashi tana so tayi kuka ta kasa kai sai ta mik'e zata fita , takai dai dai wajan k'ofa tajiyo muryar shi yana cewa "baby na baki kwana biyu kije kiyi tunani Idan baki amince ba kuma duk abin da ya biyo baya ke kika ja"

Wani dogon tsaki taja tare da fad'in "Allah ya fika "ta fita

Shiko jingina yayi yana jin sha'awar ta yana k'ara azazzalar shi,

Ita kuwa Ummi kanta ne yake juyawa nan ta lallab'a wa tana tana tafiya a hankili Chan sai ta fara ganin duhu ba tare da tasan inda take ba ta duk'e awaje ta jingina da glass d'in da yake hanyar mutane basu cika wuce wa sosai Shiya sa ta d'au tsawon lokacin da ita kanta bata san lokacin da ta d'auka awajen ba,

Kamar daga sama taji wata sassanyar murya tana fad'in "Baiwar Allah lafiya kike zaune anan ?"

Ahankali ta d'ago kanta tare da sauke idanun ta akan matashin kallo d'aya tayi mai ta sake kauda kanta domin gaskiya guy d'in ya had'u ga iya dressing fa kyau kuma da ganin alama iyayen sa masu k'unbar Susa ne ba tare da Cewa komai ba mik'e wa tayi har ta juya zata tafi sai kuma taji ya k'ara cewa " Sis ga jakar Ki"

Ba tare da ta juyo ba ta karb'a tare da fad'in "thanks"

Murmushi yayi tare da biyo ta abaya yana fad'in "Suna na Aminullah Alhassan ina department of business administration ina two hundred level"

Bata bashi amsa ba sai ma k'ara sauri da tayi , domin ita duk atunanin ta shima shed'anar yazo mata dashi,

Sake jin muryar shi tayi yana cewa " tunda dai ba zaki yi sharing k'uncun Ki dani ba to Dan Allah ki saurareni bai kamata kitafi kina d'auke da fuskar shanu ba" ya k'ari ke yana murmushi ,

Ita ko kalaman shi na k'arshe yasa ta juyo wa daidai lokacin kuma ya saki murmushi

"Me kake nufi da fuskar shanu?" Ta k'ara tamke fuskarta

D'aga kafad'ar shi yayi sannan ya ce "ba abinda nake nufi ,amma da zaki runk'a yin dariya tauraruwar Ki sai ta fi haskawa"

Ta bud'e baki zata yi magana kenan ta ji an tab'o ta ta baya rud'e ta juya , Hafsa ce tsaye sai nishi take kamar wadda tayi gudun famfalank'i duk da yana yin da Ummi ke ciki taso tayi dariya amma sai ta daure tace

"Ke kuma fa lafiya? kinzo sai nishi kike kamar wata zakanya"

"Eh dole Ki ce haka mana bayan duk kin gama ba mutane wahalar nemanki for more than an hour Ashe kina nan"

"To ina ruwanki da nema na ko ni yarinya ce da zan b'ata?"

Cikin b'acin rai Hafsa tace "naga Wanda ya fiki shekaru ma ya b'ata har yanzun ba labarin shi bare ke , to Ki sani ko kin b'ata ba zanje Neman Ki ba"

Nan Ummi ta had'a girar sama da k'asa tsabar bak'in ciki ma ta rasa me zata ce

Hafsa na ganin hakan tasan k'awar tata fushi tayi kawai sai ta rungumeta tana lallashi cikin sigar tsokana har sai da tayi dariya sannan ta jata suka bar gurin

Shiko Aminullah tunda suka fara yake kallon su har suka tafi yana binsu da ido , ahankali kuma ya furta "I love your dramer"
[1/4, 8:49 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

2⃣9⃣➕3⃣0⃣

Tunda suka koma gida Hafsa ta lura Ummi tana cikin wata damuwar da tafi tada tana so ta tambaye ta amma kuma ta kasa , wani tunanin ne kuma ya sake bijiro matashin saurayin da ta ganshi tare da Ummi meye tsakanin su?, ita dai takan Ganshi amma ba kullum ba kuma tana Ki k'ayenta na yawan yin zancen akan suna son shi, wata zuciyar kuma tana cewa karki zargi k'awarki domin kema kinsan ba halinta bane , daga k'arshe dai ta yenke shawarar zuwa ta tambayeta ,

Koda ta Shiga d'akin ta sameta a zaune atsakiyar katifa ta had'a kanta da gwuiwoyin ta tana kuka bilhak'i da gaskiya ,

Azuciyar Hafsa ko cewa tayi "ita kam Aunty Ummi kuka baya mata wuya" k'arasawa tayi kusa da ita cikin tausayi ta dafa kafad'ar ta , har wannan lokacin Ummi bata d'ago ba ,

Cikin sanyin murya Hafsa tace "k'awata me ke damun Ki ne ?, ko maganar da na fad'a miki d'azun ne?"

Girgiza kai tayi alamar "A'ah "

Hafsa ta sake cewar " to mene ne ? Kinji yadda jikin Ki yayi zafi kuwa?"

Cikin kuka Ummi ta sanar ma da Hafsa abin da wannan lecturer d'in ya fad'a mata har had'uwar su a Aminullah ,

"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un lallai wannan anyi D'an iska , insha Allah ba zai samu nasara ba "

Nan dai Hafsa tayi ta kwantar mata da hankali har ta D'an saki ranta ,

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*THE NEXT DAY AT SCHOOL*

Bayan sun samu interval d'in lecture suka fito waje suna shan iska ita ko Ummi zuciyarta cunkushe yake da fargaba domin bata San me zai faru gobe tsakanin ta da wannan shed'anin ba,

Hafsa ce ta gaji da shirun tace " Aunty Ummi ba dai tunanin wannan fasik'in kike ba ?"

Ajiyar zuciya Ummi tayi sannan ta ce " dole inyi tunanin shi mana Hafsa kaidin wani mutum d'in yafi sharrin shed'an"

"Hakane amma Allah ba zai bashi galaba a kanki da yardar Allah"

Ummi ta bud'i baki zata yi magana kenan taji wani k'amshi ya doki hancin ta juyawa tayi ta kalli Hafsa taga ita ma ita take kallo a tare suka d'aga idanuwan su suka zuba kan Aminullah, nan da nan dukkan su suka d'auke Kansu ,

A cikin Takun da baifi uku ba ya k'araso inda suke tare da sallama ,

A dak'ile suka masa mai murmushi yayi sannan ya ce "sisters ya kuke ?"
Ba samu amsa daga bakin Ummi ba sai dai Hafsa ce tace "lafiya " itama a dak'ile ta amsa ,

Kallon Ummi yayi yaga ta wani d'auke kai murmushi yayi yace "sis ba dai fushin jiya ya shafe ni ba?"

Nan ma bata tanka mai ba sai ya koma kusa da Hafsa kujerar da ke kusa da ita ya zauna tare da fad'in "sis wai me ke damun k'awar Ki ne tun jiya nake ganin ranta a b'ace jiya da k'yar nayi bacci saboda halin da na ganta ciki"

Hafsa ko baki ta saki azuciyar ta tace "lallai wannan bashida hankali "

Daya ji shirun yayi yawa ne yace "au kema shiru zaki yi ?"

Wata zuciya ce tace ma Hafsa Ki fad'a mishi abinda ke faruwa ko zai iya temaka muku,

Nan ta bashi labarin komai daya faru ,

Cikin b'acin rai yace "ya sunan lecturer ?"

Shiru tayi tana so ta tuna sunan da taji an fad'i jiya da k'yar ta tuna

Ta kalli Aminullah tace "D'an Asabe"

Murmushi mugunta yayi yace" hakane na tuna jiya akusa da office d'in shi na ganta dama kuma ina da case dashi double fire kenan "

Matsawa yayi kusa da Ummi ya ce "karki damu sis insha Allah daga kanki bazai k'ara marmarin zina ba ",

Da k'yar ta iya cewa "nagode"

Sallama yayi musu tare da fad'in "ku jira result zuwa gobe "ya Shiga motar shi domin k'arasawa department d'in su

Ummi ce ta juya ta ce ma Hafsa "ke banza ce wallahi ya kawai daga ganin mutum zaki zauna Ki saki baki kina ta surutu , to yanzun da kika gaya mishi me zai iya yi?"

"Haba Aunty Ummi Ki fahimceni ni ba da wata manufa na fad'i mai ba kawai gani nake zai iya taimakawa amma idan banyi miki dai dai ba to Ki yafeni"

Ajiyar zuciya Ummi tayi tare da fad'in "shikenan ya wuce" nan dai sukayi ta hirarrakin su daga k'arshe suka koma class ,

Shiko Aminullah tunda ya tafi yake shirya k'ulum botom da zai shirya ma D'an Asabe cikin murnar samun mafita yace "zaka ci ubanka" ya saki wata dariyar mugunta,

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*AT NIGHT*

Wata dalleliyar mota ce k'irar CRV ta faka a parking space din Quarters d'in lecturers da ke cikin makarantar b'arayin me zaman banza da b'arayin driver aka bud'e , wasu matasa ne guda biyu cikin bak'ak'en kaya d'aya yana zuk'ar segret d'ayan kuma yana tofar da miyau gami da toshe hanci yana fad'in "wallah kai banza ne nagaya maka bana son warin wannan abar amma saboda tsabar iskanci sai ka shata a gabana ".

D'ayan yace "guy charge nake domin naji dad'in karta rashin mutum ci ",

Dai dai nan suka isa inda suke son Shiga , tab'a k'ofar sukayi suka jita a bud'e , sai d'ayan ya cema mai shan segret d'in ya lek'a ta window'n' ko akwai matsala , bayan minti biyu ya dawo yace"ya sama kanshi jaraba ba dole ya manta ya bar k'oda bud'e ba yana chan yana shanawa"

Cike da takaici d'ayan yayi k'wafa ahankali suka tura k'ofar suka Shiga tare da lab'e wa abayan wata kujera dake lungu ,

Sai alokacin na gane waye d'ayan Ashe Aminullah ne , tab

Lokaci zuwa lokaci suna duban agogo suda suka zo tun k'arfe goma gashi gashi yanzun shabiyu , d'ayan ya bud'e baki zai yi magana kenan suka ji an bud'e k'ofa lakwaf sukayi wata budurwa ce ta fito cikin wasu tsinannun English wears sai wani taku take cikin yauk'i , sai da wuce da kimanin minti talatin sannan suka mik'e suka kashe kulle k'ofar har zasu bud'e k'ofar bedroom d'in sai abokin Aminullah yace tayani mu harmutsa d'akin nan sai da suka ma d'akin biji-biji sannan suka kashe globe d'in d'akin suka fad'a bedroom d'in

🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣
[1/5, 9:22 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

3⃣1⃣

Ko da suka Shiga d'akin yana kwance akan gado ya lullub'e da alama barci ya fara yi , Aminullah ne yayi ma abokin shi nuni da ya zagaya ta d'ayan b'arayin koma ya nemi kan bedside drower ya zauna tare da d'ora k'afa d'aya kan gadon , sunsa D'an Asabe a tsakiya ,

Wata 'yar k'aramar wuk'a Aminullah ya Ciro a aljihun shi me kama da ta wanzamai , ahankali yake yawo da wuk'ar akan wuyan D'an Asabe , mak'wat ya had'iye wani miyau chan dai dayaji waiwayin ya isheshi sai ya kawo duka zafin da yaji a hannunshi shi ya sashi farkawa ciki magagin bacci azabar dake k'ara ratsa shi ne yasa shi bud'e ido me zai gani jini ne keta zuba a hannun shi cikin firgici ya d'aga kanshi yayi tozali da Aminullah wani wawan mari ya sakar mai yanda sai da ya daina gani na 'yan sakwanni , wata muguwar dariya ce yaji abayan shi yana juyawa yaji an sake d'auke shi da wani Marin cikin firgice ya fara fad'in,

"Wayyo Allah na Dan Allah me na miki?, su waye ku?"

Cikin wata irin murya Aminullah yace " zakasan ko mu su waye , zaka San ko me kamana amma sai kayi laushi tukun , oya come down my friend!"

Jiki na rawa ya sakko a gadon kamar Wanda beda jini ajikin shi ,

Abokin Aminullah ya ce "maza kayi frog jump sau hamsin"

Cikin zarana D'an Asabe ya ce "Oga ina da matsalar ciwon k'afa fa "

"Keep quite sanda kake turmushe 'ya'ya da matan mutane kana tuna k'afarka na ciwo ne banza kawai" ya had'a mai da wani Marin ,

Chan kuka ga D'an Asabe yahau tsallen kwad'o , shiko Aminullah gefe ya koma ya barshi da gwaska

A wahale D'an Asabe yayi frog jump ashirin shima yana yi ya tuntsurawa dukkan ninsu dariya suke ta cikin k'yallen da suka rufe fuskokin su , sai da wahala sannan Aminullah ya taso daga inda yake yace "guy tale min shi namai kaciya ".

Nan D'an Asabe ya hau muzurai da ido jikin shi sai kyarma yake ,

Nan guy ya Fara kici-kicin cire mai wando , cikin magiya D'an Asabe yace "Dan Allah Dan Allah kar ku min wallahi anmin tun ina D'an shekara bakwai"

Wata harara guy ya wurga mai sannan cikin k'arfi ya ja gajeran wandan ya yi k'asa , hankalin shi be k'ara tashi ba sai da yaga Aminullah yayo kanshi da Aska AI ba shiri ya zabura zai gudu gajeran wandon shi ya tad'iyeshi ya fad'i ji kake TIM!! , D'an Asabe yasha k'asa , da dai yaga har yanzun k'ara Mateo shi yake AI sai ya tak'ark'are yayi parlour a guje haba basai wani sabon satin ba ji kuke k'um! Gwaram !!,

D'an Asabe ko na chan parlour yana cin karo da kayan d'akin da aka yamutsa idan yayi sai yaci karo ko ya hantsala ,

Sukam su Aminullah suna chan suna jiyo ihun shi , sukam sai dariya suke ci ma'ishin su sai da suka gama dariyar sannan suka fita parlour suka kunna switch d'in gloves d'in D'an Asabe ne zigidir a tsaye tsakiyan center table sai muzurai yake fuskar nan duk ta kumbura ga wata uwar zufa da ke ketomai kamar yayi gudun famfalank'i

K'arasa wa suka yi kusa da shi sannan Aminullah ya fara magana "wato kai k'wallan D'an iska ko iskan cin naka ya koma kan matan aure ko to kad'an ma ka gani muddun zaka ci gaba da irin haka"

Cikin rawar baki D'an Asabe yace "wallahi yallab'ai indai wannan ne na daina amma Dan Allah ku k'yale ni haka"

Cikin tsawa guy yace "kai! Kana tunanin zamu tafi ne bamu tab'a lafiyar jikin ka ba to kayi k'arya "damk'o shi yayi turmushe yace "Man zo ka D'an sha jinin shi"

D'an Asabe sai zillo yake amma ya kasa k'wacewa , yana ji yana gani ajikiyi mai siririn yanka ajikin shi sannan suka k'ara mai da gargad'in yaje ya ba Zainab Kabir k'uri in na haka ba next time kaciya zasu mishi

Jiki na rawa yace" wannan duk mai sauk'i ne ai "

Suka tafi suka barshi suna ta shek'a dariya

🤣🤣🤣🤣🤣🤣🤣

Washe gari da yake juma'a su Ummi basu da lectures d'in safe Dan haka sai k'are biyu suka je school suna Shiga class sai ga wani yazo ya ce" Zainab Kabir taje inji Malam D'an Asabe " sosai firgici ya bayyana a fuskarta , tana cikin tunani sai taji mutum akan ta Aminullah ne tsaye cikin manyan kaya brown d'in shadda ne ajikin shi anyi mata aiki da coffee din zare hular kanshi ma ratsin coffee da brown Kasan ce warshi fari sai abun ya k'ara sajewa farar fatar shi murmuahi kawai yake mata yayin da d'ayan hanunshi yake sanye cikin aljihun shi , ahankali ya matso kusa da ita yace " minti biyu please" yana gama fad'in hakan ya juya ya fita ,

Hafsa ce ta kalleta tace "Aunty Ki je mana maybe ya Samar mana mafita ne "

Jiki a sanyaye ta fita yana hangota sai ya fara tafiya ahaka har sai da suka kusan office d'in D'an Asabe sannan ya tsaya tana K'araso wa ya fara magana a hankali ,

"Karki ji tsoro kije hak'uri kawai ze baki , na ruga da na gama da shi" ya k'arike maganar cikin murmushi

Kallon shi tayi sannan tace "Anya wannan ba wani *SABON SALON YAUDARA* bane kuka zomin dashi?"

Cikin sanyin murya yace "Ki yarda da ni Zainab bazan tab'a cutar da wata 'ya mace ba most especially ma ke da nake so kinga bazaki je ba shikenan dama hak'uri zai baki"

Ummi wata fassara tayi daban cikin tsiwa tace" owoo dama badan Allah zaka taimaka min ba saboda na kub'uta a hannun kai na fad'o naka hannun ko , to bari kaji idan baka sani ba ni nan da kake ji da gani matar aure ce na wuce na tsaya kuna ball dani kuyi duk abin da kuka ga zaku iya ni *DA ALLAH NA DOGARA* " tana kai wa nan ta koma da baya tana tafe tana share k'walla har ta bangaje Hafsa da tazo Neman ta tafad'a ma anshiga ajinsu ita kuma ganin Ummi ta wuce a fusace kamar zakanya chan kuma ga Aminullah ya d'ora hannayen shi duk biyu akai sai abin ya d'aure mata kai

Shiko Aminullah duka biyu ne Ummi tamai ga mummunar fassara gashi ta ce mishi ita matar aure ce ,

Cikin sauri Hafsa ta k'araso kusa da Aminullah tana fad'in meke faruwa ne ?"

D'ago jajayen idanuwan shi yayi ya fara magana cikin sark'ak'yar murya "wai dagaske Zainab na da aure?" Ita ce tambayar da ya watsa mata. .

With confidence Hafsa tace "Eh matar yayana ce"

"To ina mijin nata yake ? Meyasa bata sanar masa matsalar ta da D'an Asabe ba?" Yasake jeho mata wata tambayar

Ajiyar zuciya tayi tace " is a long story"

Katseta yayi da cewar "I need to know"

Bada b'ata lokaci ba tayi mishi briefing wace ce Ummi,
[1/11, 1:06 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*HAPPY ONE YEAR ANNIE PURE MOMENT OF LIFE WRITERS❤*

*Dedicated to REAl PURE MOMENT OF LIFE WRITERS sisters we're the best ever , let's continue shining like a ster in the sky🌠🌠😍*

*Readers ina mai Baku hak'urin rashin jina da kukayi kwana biyu wani uziri ne na musamman ya tsayar da ni amma insha Allah zaku rink'a jina akai akai*❤

*godiya mai tarin yawa gareku masoya na da fatan alkhairin da kuka yi agareni nagode Allah ya bar k'auna,*😍

*BAWAN ALLAH fans kullum burina shine nishad'an tar daku , Allah ya barmu tare*🤝

❤ *k'awalli*🤪 ❤

3⃣2⃣

Ummi kuwa bata zame ko ina ba sai gida , tana shiga gida Mama ta kalle ta da mamaki tace " a 'ah Ummi har an da wo?"

"Eh Mama"

Mama ta sake tambayar ta " ina 'yar uwar taki take ?"

"Tana chan baya ni nayo gaba ne " Ummi ta fad'i tana tura k'ofar d'akin ta ,

Mama ta girgiza kai cike da al'ajabin hali irin na Ummi

Ummi kuwa koda ta Shiga d'aki wurgi tayi da jakar makarantar ta fad'a katifar ta tana ta tuno kalaman Aminullah tabbas tasan da babu Abdallah ikon Allah ne kad'ai zai iya sa bata auri Aminullah ba domin yafi Abdallah'n' da ta sani had'uwa sai dai kuma bata San ya zuciyar shi take ba ga kuma zargin da take mishi , haka tayi ta juyi tana tunani ,

koda Hafsa ta shigo class Neman ta suka ce bata dawo ba tayi Neman har ta gaji daga baya dai ta yanke shawarar komawa gida ko ta koma ,

Ta fito dai dai bakin gate taga motar Aminullah yana ta zabga mata horn da dai kamar zata wuce sai kuma ta tsaya ,

Fitowa yayi daga cikin motar da kaganshi zaka gane hankalin shi ba'a kwance yake ba Dan har idon shi yayi ja cikin sanyin muryar shi yace "Hafsat ina zuwa ne ?"

"Gida " ta bashi amsa atak'ai ce

"To muje na sauke Keki mana kinga ana wuyar mota "

"A ah ka barshi zan jira "

"Hafsat kenan saboda na b'ata ma k'awarki rai shine zaki hau fushi dani ?"

"Ko kad'an yanzun muka je gida dakai kuma Kasan laifin kaina zai dawo "

"Babu Wanda zaisan Nina maidoki Idan kuma baki yarda da ni ba I can't furse you"

Shiru ta yi na D'an lokaci tasan dai indai bata bishi ba to batasan ranar samun abun hawa ba nan tace mishi "shikenan muje"

Nan da nan yaji zuciyar shi tarage suyar da take mai domin yasamu hanyar ba Ummi hak'uri ,

Bud'e mata motar yayi ta Shiga sannan ya rufe shima ya zagaya ya Shiga sai da ya hau titi sosai sannan ya juya yace mata " sis ina zamu je ne ?"

Kwatan chan tamai cikin 'yAr dariyar shi da iyakarta fuska yace "Ashe ma bamu da nisa"

"Uhum" kawai tace ta maida kallon ta titi , daga nan kuma babu Wanda ya k'ara magana ,

Dai dai sanda ya Shiga unguwar su ana ta kiraye kirayen sallar issha , agurguje yayi parking motar a k'ofar gidan da ta nuna mai ta fito daga motar kenan sukayi ido biyu da Malam yana ta sauri zashi masallaci , kallon da taga Malam ya mata ya sata shigewa gidan aguje , Aminullah ma nan bar motar shi ya wuce masallaci ,

Yadda Mama taga Hafsa ta shigo ba natsuwa yasa gabanta fad'uwa "ke lafiyarki kuwa kinwani shigo kamar an koroki "

Hafsa ko sai zare ido take ,

Mata ta daka mata tsawa"ke Dan gidanku!?

Zumb'ura baki tayi tace "ba komai fa Mama"

Ta d'aga labulen d'akin Ummi ta fad'a ganin Ummin na sallah ne ya sata fita domin itama ta sauke nata faralin ,

Malam kuwa banyan sun idar da sallah ya tsaya bakin masallaci domin jiran saurayin da ya ganshi da Hafsa domin yana son yasan mene ne tsakamin su?

Bayan Aminullah ya fito daga masallaci ya fara tafiya kenan sai yaji sallama a bayan shi , cikin natsuwa ya juya tare da amsa sallamar Dattijon ya k'ara da cewar "ka wuni lafiya Baba?"

"Lafiya lau D'an samari , amma kai bak'o ne a unguwar nan ko?"

"Eh Baba "

Shiru ya biyo baya sai Malam ya sake cewa "na ganka tare da 'yata lafiya dai ko?"

Aminullah shiru yayi sannan daga baya ya ce "ni D'an makarantar su ne ganin yamma tayi gashi babu abun hawa shi yasa na dawo da ita"

Duk da cewar Malam ya yarda da nutsuwar yaron amma sai yaji hankalin shi bai kwanta ba musamman ma da yagan su su biyu ba tare da Ummi ba ,

Ya kalle shi yace" to ina 'yar uwarta?"

"Baba Zainab ta dad'e da barin school ina tunanin yanzun haka tana cikin gida "

Dai dai lokacin suka k'araso k'ofar gidan su Hafsa

Aminullah ya juya cikin kulawa yace "Baba ni zan wuce a huta lafiya"

"Ah d'ansamari ko ruwa baka sha ba bari nasa akawo maka ruwa "

D'aya daga cikin almajiranshi ya yafito , sai gashi cikin sauri ya k'araso Malam yace " Shiga ciki kace Hafsa ta kawo ma bak'o ruwa" ya fad'i yana nuna gidan su Hafsa

Sannan ya juyo ya kalli Aminullah ya ce "Bawan Allah zauna mana"yanuna mishi dakalin k'ofar gida sai da yazauna sannan yace "Baba suna na Aminullah"

"Masha Allah suna me daraja "

Alokacin da d'an Aiken Malam ya Shiga Mama ce kad'ai a tsakar gidan Hafsa na d'akinta tana shimfid'a Mama ta k'walla mata kira bayan ta fito taji sak'on Malam sai da gabanta ya fad'i nan dai ta daure tace "Mama ina Aunty Ummi ?"

"Taje gida duba Sani yana zazzab'i "

Jiki a sanyaye ta d'auki wani jug a d'akin Ummi ta kamfato ruwan randa a fita tana ta sak'e sak'e azuyarta,

Tana fita tayi kicib'in da Malam da Aminullah suna ta hirarsu kamar dama sunsan juna ,

Gaban tane yayi mummunan fad'i amma sai ta daure ta gaida Malam tare da aje ruwan , ta juya kenan zata Shiga gida ta ga Ummi a k'ame tana mata kallon tuhuta ,

Ahankali ta furta "Aunty Ummi?" Cikin tsoro ta k'arasa maganar

Sai lokacin su Malam suka lura da ita awajen , Malam ne ya kalleta ya ce " ke Ummi mekike awaje a irin wannan lokacin ?"

Murya na rawa tace "Baba Sani naje dubawa "

"Maza Ki shige gida "

Zata wuce kenan Aminullah yayi zumbur ya mik'e "tare da cewa Baba Dan Allah ka min izini nayi magana da Ummi"

Ummi najin haka ta fad'a gida aguje , kamar zai bita sai da Malam ya rik'oshi , Malam ya kalleshi cike da takaici yace

"Bata gaya maka ita matar aure bace?"

"Hafsa ta gayamin komai Baba laifi na mata shine nazo na bata hak'uri ne"

Malam dai abin ya d'aure mai kai kawai sai ya daure ya tambayeshi "wani irin laifi ?"

Nan dai Aminullah ya kwashe labarin farkon had'uwar shi da Ummi har zuwa yanzun ya fad'a ma Malam ,

Malam hankalinshi ya tashi jin wani yana farautar mutuncin 'Yarsa nan ya fara fad'a har yana cewa ma makarantar ta daina zuwa ,

Sam Aminullah baiji dad'in zanchan Malam ba nan ya fara fahimtar da Malam amfanin karatu da illar rashin sa ga al-umma musamman ma d'iya mace mai bada tarbiya Dan wani b'arayin dole anabuk'atar mata ,daga nanan yayi mishi alk'awarin kula da su matuk'ar yana numfashi ,

Gaba d'aya jikin Malam yayi sanyi da jin kalaman Aminullah kuma yayi na'am da zanchan shi Malam ya kalli Aminullah ya ce

"Yakai *AMINTACCAN BAWA* na baka amanar Zainab da Hafsa kamar yadda ka buk'ata duk abinda ya faru da su dakai zanyi kuka"

Duk da cewar gaban shi ya fad'i amma sai ya dake yace "insha Allah Baba babu abinda zai faru dasu sai alkhairi"

Hafsa da Ummi dake mak'ale a zaure suka kalli juna sukayi tsuru tsuru

Cikin mutumci da girmamawa Malam da Aminullah sukayi sallama bayan Aminullah ya ba Malam dubu biyu amma firr Malam yak'i amsa ahaka sukayi sallama
[1/12, 5:43 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*k'ungiya ta abin alfahari na😘*

*DEDICATED TO ALL HAUSA NOVELs WRITERS ina mana fatan alkhairi Allah ya bamu ladan fad'akarwa ya k'ara mana hazak'ar tunatar da masu karatu Amen*🤞

*Readers ban manta daku ba muna godiya bisa soyayyarku ga littafan mu*😍

*Masu cewa na manta da Abdallah, ku sani ba yadda za'ayi na manta da Abdallah domin shine jigon labarin ku biyobi a hankali Dan jin ya zata kasance*❤

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.