Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel
Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt
Chapter 4 of 15
Page 6⃣
Abdallah be farka ba sai wajen k'arfe shida na yamma , yana duba agogon wayar shi yaga lokacin sallah yayi yamik'e cikin sauri ya d'auki buta yayi cikin gidan , Maman su Umar ma bata nan , tana can gidan biki , alwala yayi ya fara jero azahar da la'asar bayan ya idar yayi addu'oi sannan ya fito ya kulle gida ya gangara Neman Umar ,
Yana cikin Neman shi ne yaji ana kiran magrib , kawai sai ya wuce massalaci , sai da aka idar da sallah yazo zai fita yaji an dafa kafad'ar shi yana juya wa yaga Ashe Umar ne ,
Murmushi ya masa ,
Shima Umar murmushin yayi sannan ya ce "Aboki ya jikin naka?"
"Alhamdulillah"abdallah ya amsa ,
Sannan suka jero suna tafiya ,
Anan ne Umar yake gaya ma Abdallah Malam yana Neman shi , daga nan kai tsaye gidan Malam suka nufa , amma da suka je aka ce Malam yaje asibiti duba Ummi ,
Cikin hanzari Abdallah ya kira wayar Malam , ringing biyu aka d'aga , banji me aka ce a d'ayan b'angaren ba naji Abdallah ya ce "to Allah ya kawo ku lafiya "
Banyan sunyi sallar issha sai suka Kama hanyar gida , Anan suka had'u da Malam shima ya dawo massalaci Dan basu ganshi a can ba ,
Bayan sun gaisa malam yace "Abdallah ya jikin naka?"
"Alhamdulillah Malam na samu sauk'i , ya jikin Ummin?"
"Jiki yayi sauk'i tana gida ma yanzun haka "
"To Allah ya k'ara lafiya"
"Amin" Malam ya amsa , sannan ya buk'aci su biyo shi rumfar k'ofar gidan shi ,
Bayan sun k'arasa sun zauna Malam ya fara magana,
"To Abdallah yau dai Allah ya nuna mana ranar da ka zama cikakken mutum , domin shi aure shi ne yake cika kamalar D'an Adam , ina fatan zaka yi hak'uri ka zauna lafiya da duk macen da ta Kasan ce matar ka , kuma kayi hak'uri da halin yarin tarta , na zab'a maka ita ne saboda nasan cewar zaku zama natsuwa a tsakanin junan ku, inai maka fatan alkhairi , Allah ya Sanya albarka acikin wannan auran yaba ku zaman lafiya da zuri'ah mai albarka Amin"
Tunda Malam ya fara koro bayani jikin Umar da Abdallah yayi sanyi lak'was , Abdallah duk jarumtar shi sai da k'walla ta zubo mai ,
Umar kuwa bubbuga bayan shi yayi
Abdallah ya fara magana cikin rawar murya " insha Allah Malam bazan baka kunya ba , zab'in ka shine nawa tamkar mahaifi kake agurina nagode Allah ya saka da alkhairi "
"Ba komai Abdallah da kai da Umar kun chan-chanci fiye da haka aguri na , Allah ya jikin iya-yen ku ya k'ara kyautata mak'wancin su"
"Amin "dukkan su suka ce nan Malam ya k'ara yi musu nasiha , sannan ya ce su tashi su tafi dare na dad'a yi , har sun mik'e sai Malam yace ,
"Abdallah sun kai maka Amaryar ka tun d'azun ba kowa ma agidan"
"To" d'in da ya saba fad'i ita ya fad'i yanzun ma , suka yi sallama suka fita
Suna fita Umar ya shek'e da dariya " yau abokina zai angwance kai Allah ya samu a danshin ku"
Abdallah Ya kawo hannu zai kai masa duka kenan Umar ya gudu yana fad'in "Aboki karka rufe k'ofar gida zan kawo ma Mama sak'on ta"
Bai bi ta kanshi ba ya kulle k'ofar gidan ya shige abin sa ,
Yana shiga yaga Mama da hafsa suna kwance a tsakar gida suna fira Kasan cewar ana D'an zafi lokacin
Da sallama ya shiga , duk suka amsa masa ya janyo bokiti ya zauna yana fad'in
"Ina wuni Mama ?"
"Lafiya lau " ta fad'i yana k'ok'arin mik'e wa zaune
Sannan ta k'ara cewa "ya jikin naka?"
"Alhamdulillah naji sauk'i"
Nan suka D'an tab'a fira sannan Mama tace mishi" su zasu shiga su kwanta dare yayi "
Mik'e wa yayi yaje kusa da hafsa ya shure ta da k'afa sannan yace " ke baki iya ma mutane sannu bako?"
Cikin murya me kama da ta barci tace "yaya barci fa nake"
"Dallah rufe min baki tunda ga waje nake jiyo hirar Ki Ki ce min wai barci kike yi"
Mama kuwa tunda suka fara ta kakkab'e tabarmar ta ta shige d'aki
Yana ganin mama ta shige ya juya ya kalli hafsa "to uwar gulma ko anan zaki kwana ne?"
Pillow d'inta d'auka ta runtuma d'aki aguje.
Tsaki yaja , ya nufi k'ofar d'akin shi , yana isa ya d'aga labulen tare da sallama , mutum ya gani kwance cikin hijab cire takalman sa yayi ya k'arasa shiga d'akin ,
Azuciyar shi yace "lallai ma wannan baccin ta ma take sha"
Pillow ya ja ya kwanta ak'asan Leda , can dai yaji bazai iya hak'uri ba yana son ganin wace ce amaryar tashi , zaga ya wa yayi ta inda fuskarta ke kallo , ganin ko wace ce ya sa shi yin taga-taga zai fad'i
Masu karatu kunsan wa ya gani 😱
Cikin tsananin mamaki yace"Ummi?!"
To fa muje zuwa Dan jin yadda zama zai Kasan ce tsakanin Ummi da Abdallah
[12/16/2017, 9:38 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.