Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel
Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt
Chapter 14 of 15
Page4⃣2⃣
Su Abdallah anata shirye shiryen bikin Babban aboki , acikin kwana uku ya Samar ma Umar gidan haya me dan sauk'in kud'i .
Alokacin da biki ya rage saura sati d'iya sai Mama ta kira Abdallah tana masa fad'a , ranar ba kowa agidan su Ummi duk sun tafi makaranta ,
"Kai ma ai ya kamata ka d'auki taka matar kusan inda dare yayi muku "
Shiru yayi yana Sosa k'eya sannan yace "to Mama ina zamuje?"
"Kai ma hayar zaka nema kuje can Ku bani guri in sarara"
Sai da yad'anyi nazari sannan Yace " ni da Mama na bari ne idan na fara aiki na samu kud'i sai in siyan mana wadataccen gida sai mu koma gaba d'aya"
"Eh tunanin ka yayi kyau amma dai yanzun kafin wannan lokacin ka nemam muku wani gurin da zaku D'an zauna"
"Shikenan nan Mama bari a gama bikin Umar sai na fara Neman gidan"
"A'ah *BAWAN ALLAH* ni so samu ma Ku tare rana d'aya da abokin naka"
Kunya ce ta kamashi ya mik'e yana Sosa k'eya yace " to Mama sai anjima"
"Mu juma da yawa" ta fad'i tana murmushi .
Bayan ya dawo da daddare ya samu Malam ya fad'a masa yadda sukayi da Mama fatan alkhairi ya bisu dashi Sannan suka k'ara tattaunawa daga nan ya rok'i alfarmar kar asanar da Ummi komai har sai ta tare Malam dai murmushi kawai yayi,
Daga nan ya koma gida bayan yayi wanka yayi shirin baccin shi tsaf sannan ya kira Dr Ahmad shima cikin jin kunya ya sanar masa , cike da jin dad'i da murna yayi masa fatan alkhairi Sannan sukayi sallama,
Ajiyar zuciya Abdallah ya sauke sannan ya furta a fili "komai ya kusa zuwa k'arshe" murmushi yayi tare da jero addu'oi sannan yayi bacci,
Washe gari da safe Umar yazo gidan dama sunyi da Abdallah zasu je funtua gidan Amaryar Umar d'in, bayan sun gama shirya wa tsaf suka fito. Abdallah ya sha kwalliya kamar wani sabon ango sai fara'a yake , Ummi dake zaune d'akin Hafsa tunda ta k'yallara ido ta ganshi sam ta kasa kauda idonta ba dan k'yafta ido dole bane to da Ummi bata yiba tasan Abdallah kyakkyawa ne amma bata tab'a ganin asalin kyanshi ba sai yau .
Shikam tunda ya juya suka had'a ido sau d'aya bai k'ara waiwayar inda take ba , ya nufi k'ofar Mama , yana shirin yin sallama ita kuma tana fitowa, hakan yasa duk suka zauna a k'ofar d'akin kan tsaftacecciyar tabarmar dake gurin ,
Bayan sun gaisa Mama tace "Umar ina zuwa haka wannan shiri kamar yaune za'a kawo mana suruka "
Caraf Abdallah ya amshe da " wata surukar za'a je nemo miki"
Cike da mamaki Mama tace"wata suruka kuma AI ni na gama aurar da yarana maza sai dai na jira suruki kuma"
Dariya Abdallah yayi sannan yace " to Mama suruka ta biyu za'aje ne mammiki" ya k'arishe maganar yana langab'ar da kanshi tare da had'e hannunshi guri d'aya alamar pleading ,
Mama ta gane zolaya yake ji sai tai murmushi ta ce "Hakan yana da kyau AI Allah ya sanya alkhairi "
Duk suka amsa da "amin"
Umar yace " Mama AI yarinyar ma k'awar Maryam ce "
"Masha Allah Abu yayi kyau" nan dai sukayi ta barkwancin su sannan suka fita .
Ummi kuwa tunda suka fara maganar take jin zuciyar ta kamar zata tarwatse , mekunanta ya ke jiye mata ne ?tun kafin ta tare Abdallah zai mata kishiya ? , wani kuka ta fashe dashi , Hafsa kam ya kwance a d'aki tana sharar baccin ta har Ummi taci kukanta ta gaji , har tayi shiru
Shikam Abdallah ko ajikin shi fita ma yayi harkarta duk da hakan bai mishi dad'i shirye shiryen kawai yasa agaba
A b'angaren Dr Ahmad kuwa zuzurutun kud'i ya turama Abdallah yace su sha shagali shida aminin shi
Abdallah kuwa wani gidan haya ya samu unguwar me kyau gashi babu hayaniya
Plat uku ne agidan da ya wadatu da manya manyan dakuna 2 bedrooms ne sai Babban parlor mai tare da dining area gefe kuma kitchen ne da madai daicin store aciki balaifi gidan yana da tsari mai kyau
Wajen Ummi Mama da ummanta gyara suke mata sosai da tambayi dalili duk amsa d'aya suka bata suna so 'yarsu tafi ta kowa kyau , Babban abinda abinda ke damun ta kuwa shine yadda Abdallah ya d'auke k'afa agidan sai ya kwana bai shigo ba bata San yana can ya k'ok'arin karb'ar Amarya ba ,
Akwana a tashi ba wuya agurin mai rai yau ta kasance juma'a, Wanda gobe asabar za'a sha shagalin biki,
Ummi na zaune ita da Hafsa ad'aki yayin da Mama tana tsakar gida tana Taryar bak'i daga danginta zuwa dangin Baban Abdallah , wata daga cikin k'annen MAMAN Ummi tashigo d'akin da sallama bayan sun amsa mata tace "Ummi yaya tace maza Ki tashi muje gidan su Habiba mai kotso da k'unshi ayi miki"
Shiru tayi kamar bata jita ba da yake ba wani girman Ummin sosai tayi ba.
Hafsa tace" ummi dake fa ake magana ,"
Azuciye ta juyo dan bak'in ciki duk ya gama cikata tace " naji sai mene ? Ni ku k'yaleni da kinibibin kU ba inda zanje"
Zuwaira k'anwar Umma taji haushi ta fita kai tsaye Mama ta sanar ma duk yadda sukayi da Ummi , murmushi Mama tayi tace "muje gurin Ummin "
Ummi najin sallamar Mama sai ta hau kuka ita bazata ba da k'yar da sid'in goshi Mama ta lallab'a ta ta tafi ,
Daren ranar kuka ta kwana yi sai ta d'aga waya zata kira Abdallah dan ta gaya mai irin dumbin k'aunarshi da take yi sai kuma ta kasa domin zuciyar ke gargad'in ta muddin tayi hakan to zaiga zak'ewar ta bare ma yanzun da yake rawar jiki za'a kawo mai sabuwar Amarya zai yi auren soyayyah acewar Ummi fa kenan🤣
[2/7, 10:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*
*MRS NN ONE💋*
® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*
_ɯɛ ɖơŋŧ ÊÂųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ É– ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_
# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com
_Assalamu_ _alaikum_ _readers anan Zan tsaya da littafin*bawan Allah*sakamakon wasu dalilai ina fata zaku yi min uzuriðŸ™Âsai mun had'u a sabon novel dina mesuna RAYUWA TA ina fatan shima zai nishad'antar damu ngd_
*GODIYA*
_Godiya ta musamman ga k'ungiyar REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS,like I said b4"sisters we are the best ever so let's keep shining like a stars in the sky🌠🌠_📚âœÂ
*jinjina gareku readers*
*Bawan Allah fans bansan ta inda zan fara ba duk fad'in social media bani tamkarku ina yinku irin sossai d'in nan Allah ya bar zumun ci*
*my bestie I miss you (Ummu Sadeeq)*
*Ameenert*
*Rahma Ismail*
*Sadiya illa*
*acceya*
*Maman hanan*
*Ummu adil*
*fareeda*
*nafi khan*
*matar me kake*
*sadeeya*
*MAMAN sa'a*
*Binta mala*
*aisha saleh idrees*
*Kai aradun Allah kuna da yawa ba zaku lissafu ba Kawai Kudai Ku sani kuna mak'ale azuciyata*🤞🤸â€Â♀
*miss husnah*no more hawan water yanzun agayama likita bawan Allah yazo k'arshe dan haka ya ajiye ya ajiye makaman aikinsa agefe wannan ba fanni shi bane Maman Muhammad ce zata yi aikin ta🤣
*Maman Mimi*
*MAMAN Abdul*
*ummul khairi Gj*
*ummul khairi Jibril*
*hussaina sanee*
*Rabi'atu paki*
Love you guysðŸ˜Â
Kuyi hakuri readers idan nace zan lissafoku to kunfi k'arfin fige d'aya mai d'auke da read more goma fatan kun gane
🤣🤣🤣🤣🤣🤣
ðŸâ€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡Ã°Å¸â€Å¡
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.