Complete Hausa Novels

Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel

Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt

Chapter 12 of 15

Page 4⃣0⃣

Sai da ya watsa ruwan ajikinshi yaji wani sanyi yana ratsa shi , haka nan dai ya k'arasa wankanshi ya fito sai rawar sanyi yake yana Shiga d'akin ya fara Neman bargo chan gefen katifa yaga bargon Wanda da alama an ajeshine aka manta ba'a d'auka ba , aiko ba shiri ya d'auki bargon ya lullub'e har kai wanda duk da hakan bai hanashi jin sanyin da yake ji ba Wanda k'afafuwan shi da hannayen shi sukayi sanyi tarara sai wani kyarma yake.

A d'akin Hafsa kuwa Ummi keta k'orafi sai Hafsa taje ta d'auko mata bargon ta , ita kuma Hafsa tace bazata ba .

Da dai taga da gaske Hafsa take kuma ga dare yana dad'a yi ga sanyi yana k'ara sauka hakan ya sata fita ba shiri dan sanyi ya gama ratsata.

Da sallama ta Shiga d'akin idon ta duk ya rufe bargon ta kawai take hange bata lura da Abdallah dake ta rawar sanyi ba ta kai hannu tafara yaye bargon , bata Ankara ba taji an janyota an wurga ta cikin bargon tare da k'udundune ta , tafa ihu kenan taji an toshe mata baki , cikin muryarshi dake rawa yace

"Shhh ba abinda zan miki d'umin jikinki kawai nake so"

Ruk'on da yayi mata ya sata kasa k'wacewa a hannun shi , tana ji tana gani ya runk'a murza duk wata gab'a da keda d'umi ajikin ta Ummi tun tana 'yan k'ana nan kukan ta har ta daina domin ta fara jin dad'in abin , dukkan su basu San iya lokacin da suka d'auka awanan yanayin ba ita dai Ummi taji Abdallah shiru ne sai wata sassanyar ajiyar zuciya da yake hakan ya tabbar mata da cewar yayi bacci .

D'agowa tayi ta kalleshi yana ta sharar baccin shi azuciyar ta tace " kai maza kunyarsu ragagga ce " kayanta ta d'auka tasa sannan ta koma ta kwanta ajikinshi ta k'ank'ameshi tamkar zata farka taga bashi.

Tofa masoya ansha bacci Abdallah ne ya fara farkawa yaga da kyakyawar fuskar abar k'aunarshi ya fara tozali murmushi yayi ya furta a hankali " you are always beautiful my Queen" ahankali ya zameta ajikin shi ya mik'e sai alokacin ya lura da yadda gari yayi tangaras , dafe kanshi yayi yana fad'in "ya subhanallah"

Cikin hanzari ya zura jallabiya ya fita bokiti ya d'auka ya nufi kitchen dai dai lokacin Hafsa ta d'aga tukunyar ruwan zafi zata shek'a ma kama ya ce

"Ke! Ke! Tsaya"

tsaf ta gane me yake nufi dan ta d'ago ta kalleshi amma sai ta k'ara seta tukunyar da bakin bokitin

Cikin kirne fuska yace " ina mai tabbatar miki kika juye ruwan nan duk zafin shi sai kin shanye shi"

Yadda yayi maganar ya bata tsoro shiyasa ta aje tukunyar , aje bokin yayi yace" zubamin" ta d'auki tukunyar ta zuba ruwan rabi , ahasale yace " wai ke kinraina nine ko to duka zaki juye "

Sai alokacin tayi magana " to kokon fa?"

"Ki dafa wani ruwan dallah ni juyemin "

Ahaka tana k'unk'unai ta juye ruwan ba don ranta yaso ba .

Wani bokitin ya d'auka ya raba ruwan zafin biyu duka ya tafi rijiya ya surka su sannan ya aje bokiti d'aya a k'ofar d'aki ya tafi da d'aya bayi .

Hafsa ko baki ta saki kamar wawiya azuciyar ta tace "idan baka mutu ba baka gama ganin abun mamaki ba " hakanan ta sake d'aura wani ruwan kokon.

Ummi kuwa tunda ya fita ba dad'e wa ta farka kunya ce ta hanata motsi Sam tana zaune har Abdallah ya fito wanka tana jin motsinshi tayi sauri taja bargon tafe har fuskarta da sallama ya shigo tana ji bata amsa ba

A hankali ya fara magana " Ummi kije ga ruwa can a k'ofar d'aki kiyi wanka 8 ta kusa "

Zumb'ura baki tayi ta yaye bargon ko kallon inda yake bata yiba, yadda ta d'aga labulen ta lek'a ba k'aramar dariya ta bashi ba aciki yake dariyar .

Tunda ta lek'a ta hango ba Mama a tsakar gidan sai Hafsa da ke shara yasa ta fita ta d'au bokitin , me Hafsa zatayi inba dariya ba .

Lokacin da tagama wankan Mama ta fito tsakar gidan Ummi tana tsaye a bayan k'ofar bayin ta na lek'e ita ala dole sai Mama ta Shiga d'aki zata fito .

Kamar ance Mama ta kalli k'ofar bayin ta hango Ummi a tsaye ta d'aura hannu akai , murmushi Mama tayi ta mik'e ta Shiga d'aki Ummi na ganin haka ko tsayawa d'aukan bokitin batayi ba fella d'akin Hafsa .Hafsa ko sai shak'ar dariya take abinta .

Ummi na Shiga ta chanja kaya ta tada kabarar sallah.

Abdallah kuwa tunda ya jira Ummi bata shigo ba nan ya mik'e ya fito ba kowa a tsakar gidan hakan yasa kai tsaye d'akin Mama ya nufa ya sameta tana ta gyaran 'yar tsohuwar drower kayanta cike da tausayin mahaifiyar tashi ya gaisheta ta amsa mai fuska a sake , d'akin ya d'anyi shiru sai Mama ta katse shirun da cewa " abincin Ku nanan a k'ofar kitchen " to kawai yace ya mik'e dan gaskiya yana jin yunwa , yana bud'e kwanon yayi arba da d'umamen tuwon masara miyar busashen kub'ewa " oh my GOD" abinda ya fad'i kenan ya rufe kwanon ya fita machine ya hau yaje wani restaurant yaci abinci sannan ya kira number Umar ya tambayeshi yana ina , Umar yace" yana gida yanzun zai wuce kasuwa"

"Kajira ni ganinan zuwa " ya kashe wayar

Ko da yakoma gida yayi karo da motar Saifullah a k'ofar gidan su k'arasawa yayi ya gaida Malam da keta fama da almajirai , sannan ya bar gurin ya Shiga gida still bai ga Saifullah ba , nan ya kira wayarshi ringing biyu ya d'aga bayan sallama Abdallah yace

"Aboki ya naga motarka ban ganka ba?"

Dariya Saifullah yayi yace " gatanan aro na baka kafin kasiya taka amma ka sani idan ka tashi mayar min sabuwa zaka siyan mun"

Abdallah ma dariya yayi sannan yace " to waya gaya maka ina San kwancen wasu "

Haka dai sukayi ta barkwanci daga k'arshe Saifullah ya ce mai "key d'in motar yana bayan k'ofa a sagale a zaure "

Da haka sukayi sallama irin tasu ta abokai.

Fita ya sake yi dan so yake yaje ya siyo kayan abinci dan gaskiya ba zai iya cimar nan tasu ba ya saba da irin cimar turawa 😨

A b'angaren Ummi kuwa Sam tak'i fitowa saboda kunya sai da Hafsa ta kaimata abinci , sannan ta ce mata ta shirya suna da lecture anjuma , wannan dalilin ne ya fata mik'e wa daga inda take ta fara shiri , ahankali take fitowa sai da tazo dai dai k'ofar d'akin ta sukayi clashing da Mama ta fito band'aki , akunyace ya gaisheta Mama ta amsa sannan ta wuce ita kuma ta wuceta d'auko abunda take buk'ata ta fito ,

Lokacin da suka je makaranta suka samu lecturer yace bazai Shiga ba sai 4 kowa yana ta Allah wadaran halinshi , kowa ya fita ya kama sabgogin gaban shi ,

Hafsa kuwa Aminullah ta kira ya Zo shima suka zauna suka dasa shiriritar su , ita kuwa Ummi tsaninta dasu ido , ana haka suka tsinkayi muryar Saifullah yana cewa "to na mamajo"

Aminullah na had'a ido dashi ya d'aure fuska dan yasan yanzun zaizo ya takura mai

Zama yayi kusa da k'aninshi sannan ya ce ma Ummi" Madam d'in mu ina wuni?"

Akunyace ta amsa da taso ace ita ta fara gaisheshi , Hafsa ta gaidashi a dak'ile shima a dak'ilen ya amsa mata , juyawa yayi ya kalli Ummi yace

"Wai wannan k'anwarki ce "

Ummi tambayar ya bata dariya amma sai ta kalli Hafsa taga yadda ta d'aure fuska itama sai ta tsare gidanta tace "eh k'anwa tace "

Hafsa dan takaici kamar tayi kuka .

Sai kuma ya sake jefo mata wata tambayar " k'anwarki ta jini ko kuwa"

Tsaki Hafsa Hafsa tayi ta tashi tabar gurin , Aminullah me zaiyi inba dariya ba

Ummi tace "ah ah k'anwar yata Abdallah ne shima kuma y'ar wan Mama ne"

"That's great ina jin nan zan maida shek'ata"

Da sauri Aminuallah ya juyo yace " what do you mean?"

"Abinda kunannan ka yaji "

" to da sakel inji Fulani , wai kai yayan nan duk abunda nace ina so sai ka yi k'ok'arin rabani dashi " ya ko had'e rai ya juyar da fuskarshi gefe

Saifullah gyara zamanshi yayi yace " mekake nufi ?"

" ina nufin ina son Hafsa haka sanda ina tsak'a da son Ummi ka fara k'ok'arin rabani da ita wannan kam bazan barma ita ba I have already win her heart , go and find your own"

Ummi kam rufe fuskarta tayi ta runk'a shek'a dariya abinta....

Follow me readers*

*Maman Muhammad d'inku ce*😎
[1/27, 9:12 PM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

*Nafi khan Nd k'awalli wannan page d'in nakune zamuga Wanda za'a yi ma gwalo kwando kwando*😜😜

*Amma fa kar ace nayi nayi son kai ehe*😉

*ina gefe ina cin daria*😁🤭

*edited by husnah beauty love you sis*😉

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.