Complete Hausa Novels

Bawan Allah Part 1 Compleete Complete Hausa Novel

Reading file: Bawan Allah Part 1 Compleete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 15

Page 7⃣

Jingina da bango yayi yana k'are ma Ummi kallon mamaki , bawai baya son Ummi bane , Ummi macen rufin asiri ce , yasan halin Ummi akwai hankali natsuwa da sanin yakamata uwa uba kuma tarbiyya , Ummi mace ce San kowa k'in Wanda ya rasa , tana da kyawu dai-dai gwar-gwado ba za'a kirata da mummuna ba , ita ba fara bace kuma ba za'a ce mata bak'a ba zamu iya kiran ta chocolate colour , ba tada tsawo sosai kuma ba gajera bace sannan yatsunta suna da tsawo , tana da dogon hanci da yalwatattun idanuwa ba tada fad'in fuska sosai, gakuma D'an k'aramin bakin ta , kai masu karatu Ummi kyakyyawa ce ba laifi🙅🏾‍♀

Wani gwauron numfashi ya ja ya zame agurin ya zauna yana kallon ta kamar wata sabuwar hallita ,

Ya kai kusan awa biyu a wurin yana kallon ta azuciyar shi yace "tabbas Ummi kyakyyawa ce amma me yasa yau naga kyanta ya fita daban, ? mutane suna ciwo suyi muzai-muzai , amma Ummi kyau ta k'ara ko ita din ta daban ce ko kuma ido nane ?"

Duk wad'an nan tambayoyin ba shida amso shin su Dan haka kawai mik'e wa yayi , ya fita yayo alwala ya raya daran da sallah ,

Ummi kuwa juyin barci tayi ta farka wani irin mugun fitsari taji ya matse ta , ga tsoro tana ji ba zata iya fita waje ita kad'ai ba sai matse matse take , Abdallah kuma alokacin ya idar da sallah yana jiran yaji an kira sallar asuba yana jingine idon shi a lumshe amma ba barci ya ke ba ,

Ummi kuwa da taga idan bata je tayi fitsarin nan ba to tabbas zata malale sabuwar katifar ta da fitsari ,

A hankali take kiran sunan "yaya Abdallah ? Yaya Abdallah? Yaya Abdallah?"

Shi kuwa ya na ji kasa amsawa yayi sakamakon wani Abu da yaji yana sukan zuciyar sa , ana ukun da ta kira shi ne ya daure ya ce mata

"Na am"

"Fitsari nake ji"

"To kije kiyi mana "

Cikin d'auriya da matse fitsarin tace "wallahi tsoro nake ji "

Azuciyar shi yace " ko a gida wake raka ta oho?"

Afili kuma sai cewa yayi" kiyi addu'a ki fita babu abin da zai same Ki da yardar Allah"

" wayyo Allah yaya zai zubo"

Dafe kanshi yayi a zuciya ya ce "ni kam naga ta kai na "

Azahiri kuma yace " tashi muje "

"To kayi gaba"ta fad'i cikin shagwab'a

Gaba yayi ya barta a baya tana tafe tana hard'e k'afafuwa , har ta isa nesa da bakin bayin ya tsaya tare da mik'a mata buta , sannan ya ce" adai yi addu'a "

"Uhum" kawai tace ta k'ara sa bayin aciki ma ta k'ara sa addu'ar ,

Bayan ta fito ta gan shi yana alwala cikin sauri ta fara duk Dan gudun kar ya gama ya barta a wajen , shiko tsaya wa kawai yayi yana kallon ikon Allah , har ta gama ta shige d'aki , nan shima yayi ya koma d'akin Dan ya dauki hular shi

Ita kuma ta tada kabbara sai ce mata yayi " wato ni da na raka Ki Dodon ya cinye ni ko?"

Bata ce komai ba , shikuma ya d'auki hular shi , ustazu ka fiye naci ya saka ya fita ,

Bayan sun idar da sallah ne ya so ya D'an kwanta a massallacin ya D'an yi barci amma Umar Sam ya hana shi sai tsokanar shi ya ke yake " Ango Ango sai wani k'yalli kake kamar tauraro" haka dai yayi ta masa shak'iyyan ci,

Abdallah kuwa tashi yayi ya barshi nan zaune yana dariya da dai ya ga da gaske fita zaiyi sai ya taso ya biyo shi dai dai kunan shi ya rad'a masa "ya kama ta kaje ka ji d'umin 'yar k'anwar ka" ya k'ara sa da kashe ido d'aya

Abdallah ko da abun ya bashi haushi sai ya ce " ka manta ne ba d'umin ta zanji ba jikin ta Zan shige "

"Yauwa mutumi na Ashe ka gane "

Dai-dai nan Abdallah ya shige gida ya bar Umar a tsaye yana dariyar mugunta Dan shi gani yake kamar an had'a Abdallah da aiki ne ,

Yana shiga gida ya CI karo da Hafsa tana alwala , wata harara ya watsa mata sannan yayi sallama d'akin Mama suka gaisa take tambayar shi ya Ummi da jiki ya ce mata taji sauki suka Dan tab'a hira ya ji yana jin barci sai ya mik'e ya ce mata "Mama ina zuwa"

D'akin su ya koma , Ummi kuwa tana jin motsi tayi sauri ta rufe idon ta , ko da yayi sallama yaji ba Wanda ya amsa mishi , ya yaye labule kutsa kai ,

Yana shiga ya ganta tana barci , ya koma inda yaga dadduma a shimfid'e ya kwanta nan wani barci yayi awan gaba da su duka ,,

Mama kuwa da taga har takwas tayi Abdallah be futo ba , sai ta aiki Hafsa ta siyo kayan tea a bakin titi, ta na dawo wa ta d'aura ruwa zafi ta had'a citta da kaninfari da Lipton ya dahu sai k'amshi yake , , ta juye a wani tsohon plas d'in ruwan zafin su ta juye aciki ta d'iban musu nasu saura kuma ta had'a da bread tayi k'ofar d'in Ummi

Sai da tayi sallama sau uku taji ba Wanda ya amsa kuma ba ta ji motsin kowa ba , murmushi tayi sannan ta d'aga labulen kad'an ta ajiye kayan ba tare da ta kalli d'akin ba , gudun kar tayi mugun gamo,🤣🤣

Ummi ce ta farka lokacin Tara tayi cikin sand'a ta mik'e gudun kar Abdallah ya tashi bata San shima ya tashi ba baya son yayi motsin da zata ji ne ,

Jakar kayan ta ta bud'e ta Ciro brush da MacLean ta d'auki butar ta ta fita bata lura da kowa a tsakar gidan ba ta tafi chan inda suke wanke wanke tayi brush d'in ta sai da ta gama ne d'ago kai suka had'a ido da Hafsa , aiko me Hafsa za tayi in ba dariya ba , Ummi kuwa murtuk'e fuska tayi Mama ta gansu amma sai tayi kamar bata ma gansu ba .

Jiki a sanyaye Ummi ta k'araso ta zauna kusa da Hafsa , cikin jin kunya ta gaida Mama , ta amsa cikin sakin fuska Dan Mama tana son Ummi sosai

Hafsa ce ta ce"Aunty Ummi ya jiki"

Ummi da mamaki ta ce "yau kuma Hafsa nice Auntyn Ki?"

"Eh mana AI tunda kin auri yaya Abdallah kin zama Aunty"

Wata hara ra Ummi ta zuba mata ta gefen ido

"Ummi tashi Ki je Ki karya kinji Ki k'yale wannan "

"To Mama"

Ai sai Ummi ta d'auki kofin shayin Hafsa tana fad'in "Mama AI wannan ma ya ishe mu ni da k'awa ta"

"Malama bani shayi na naki na d'akin ku" cewar Hafsat tana zumb'uro baki

Mama dai bata tanka musu ba

Ummi ta ce cikin k'asa-k'asa da murya "K'awa ta je Ki d'auko min nawa tea d'in , zan aje miki naki,"

"Tab AI ko ba zan je b....." Bata gama fad'i ba Ummi ta make mata baki

Mama kuwa murmushi kawai tayi

"Ke hafsa nan matsalar Ki ba wayau je Ki d'auko min Ki zo musha fira"

"Eh sannu uwar wayau..." Ummi ta k'ara make mata baki

"Wallah Aunty Ummi kika sake duka na sai na...
." ta sake gwabje bakin ,

Hafsa ta mik'e "Mama kina kallon ta ko ?"

Mama ta ce 'ai ni na gode gwanda ta min maganin Ki , wuce ki je Ki d'auko mata"

Cikin zumb'ura baki ta tafi
[12/17/2017, 8:56 AM] Maman Muhammad: *BAWAN ALLAH*

*MRS NN ONE💋*

*Wannan page d'in na sadaukar dashi ne ga masoya novel d'in BAWAN ALLAH aduk inda kuke Wanda na sani da Wanda bansani na gode Allah ya bar zumunci, ❤*

*BAWAN ALLAH fans wallahi ina matuk'ar jin dad'in comments d'in ku ku sani dani da ku muna mak'ale da juna🤞🤙*

*K'awwali ta da Ameenert gaisuwar ku da bance 💋*

® *_REAL PURE MOMENT OF LIFE WRITERS_*

_ɯɛ ɖơŋŧ ʝųŞŧ ɛŋŧɛřŧąıŋ ŋɖ ɛɖųĆąŧɛ, ცųŧ ɯɛ ąٳŞơ ŧơųĆɧ ɖ ɧɛąřŧ ơʄ řɛąɖɛřŞ_

# WWW.PMLWRITERS@GMAIL.COM
# *IG PML WRITERS*
# https://www.facebook.com/PML_-Writers-FANS-459256761123035
# http://maryamsbello.blogspot.com

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.