Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 6 of 42

Bayan mun gama secondary school ne, iyaye na suka nemi mu ci gaba da karatu kai tsaye na amince wanda hakan shine burina, amma abinda ya bawa kowa mamaki k'in amincewar Umar babu yadda iyaye na basuyi ba akan yacigaba da karatu kmr yadda zanyi amma fir Umar yak'i amincewa acewarsa yafi san yayi hakar kasuwanci.

'Cikin matsanancin damuwa Mahaifina ya kalleshi , yace " to Umar ko gaba karkayi kuka damu .
kayi kuka da kanka,sbd Shi ilimi abu ne me mahimmanci a rayuwar Dan Adam ban hanaka yin kasuwanci ba Amman nafi son ka dan samu illimi me zurfi .
Shi ilimi haske ne a rayuwa ,duk abinda mahaifina yasan zai yi Dan ganin umar ya amince da cigaba da karatu yayi km ya fada masa , babu irin shawarar da iyaye na basu bashi ba amma fir umar yaki amincewa yace shi sam a'a business yake da raayin .
Haka iyayena suka hakura suka barshi ba Dan ransu yaso ba sai Dan basa son matsa masa amatsayinsa Na maraya .

Bayan wasu kwanaki aka damu mahaifina da yawan kawo k'arar Umar jama'a kowa yace Umar yayi masa kaza ko yayiwa 'yarsa kaza.h k
mahaifina yasa me shi yayi masa fad'a sosai .

Amma mu a gidan da kuma kamanni duk inda kake neman mutumin arziki kona kirki Umar yakai, ko mahaifina da yakeyiwa Umar fad'a bawai dan ya yarda bane, dan matuk'ar yarda mun yarda da Umar.

*MOMYN ZARAH*
[16/11, 03:04] ‪+234 706 099 2528‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

~NA~

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

5

Sanu ahankali Cikin ikon Allah na samu gurbin karatuna anan University of Gombe, kullum k'orarin iyayen Mu shine suka inganta rayuwarmu tare da son faranta mana.ni da umar musamman sbd
, muguwar shak'uwar dake tsakanina dashi . dan duk inda ka ganni dole zaka ganshi, komai namu iri d'aya ake mana bbu wani bambanci atsakaninmu shiya wasu suke kiran mu 'yan biyu, babu wani sirri na da Umar bai sani ba.
haka Nina babu wani sirrin sa daban sani ba. Sosai nake matsanancin kaunarsa tare da maidashi tamkar Dan uwana Na jini .yadda nake jin umar acikin raina ko kanina da muka fito ciki guda bana yi masa irin son da nakeyiwa umar ..

Akwai wata yarinya a unguwar mu mai suna Yasmeen k'awar k'anwata tace sosai, sun yi masifar shak'uwa da junan su abin ma har ya wuce tunani, rana d'aya na tsinci kaina da mugun k'aunar Yasmeen amma babu wanda na baiyanawa .
Har Umar, nabar dai bar abin a raina. Ina cigaba da renan soyayyarta acikin zuciyata.

Haka zalika a b'angaren Umar ashe tuni sun tsunduma cikin soyayya shi da tilon k'anwa ta Ramlat, batare da wanda ya sani,b a.
tuni km har soyayya rsu tayi nisa.

"Umar wai bazaka raka ni bane, a 'yan kwanakin nan na rasa me kake yi a gida da dare idan nace kazo mu fita sai ka k'i,.Ko meyasa hk ?

murmushi kawai Umar yayi hade da yatsina fusakarsa yana kallon Abdul kasa kasa kana yace " kawai dai ban san fitar ne.
, nafisan na zauna gida tare da Mama da Baba ina taya su hira.
, kallon sa Abdul yayi da alamar rashin yarda atare dashi da km maganar sa.
" kai dai ka san dalilin dayasa kake kunshe kanka ciki gida yana maganar yana tafiya har dai yakarasa fice Daga gidan gabadaya.

Sakamakon ruwan saman da ake tsulawa yasa Abdul dawowa gida da wuri, yana danna kai 'cikin d'akinsu yaji hirar soyayya tsakanin Umar da Ramlat, d'an b'ata rai Abdul yayi sosai sannan yace " ke tashi ki fita, da fara'a Ramlat tace" Yaya mai ya faru?

"Nace ki fita ko, da sauri Ramlat ta fita,tana mamakin abinda yayanta yayi .
kallon Abdul, Umar yayi yana shafa sumar kanshi , Abdul yayi dariya yace"Ok dama wannan ne da yake hanaka fita kullum ko ?
ka lik'e a gida,kana sacewa kanwata zuciya ko ?
munafiki to Allah ya kamaka.

Dariya shima Umar yayi yace " kodai Allah ya kamamu, "kai da wa?

" ni kai cewar Umar yana dariya, shima Abdul dariya yayi sosai yace " kamar ya ban gane ba.
Kallosa Umar yayi da alamar zolaya ya fara wak'a "Yasmeen abar k'auna ta, dariya Abdul yayi sosai yakai mai duka, suka shiga wasa suna tsokanar junan su, Umar yace " haba d'an uwa har akwai abinda zaka iya b'oye man to ai har na tura mata sak'onka, ta kuma amince, ido Abdul ya zaro waje yace " kai haba?

" Wallahi da gaske nake maka sosai Abdul yaji dad'i had'i da rungome Umar ajikinshi yana yi masa godiya.

Washe gari Baba da Mama, da Umar da Abdul da kuma Ramlat da Auta duk muna zaune a parlor, muna hira Abdul ya kalli Mama yace " Mama d'anki fa ya fad'a soyayya, Ramlat naji haka ta zaro ido da alamar tsoro.
, Mama tayi dariya tace" ikon Allah ina kuma ya samu min sirikar?

Da sauri Umar ya mik'e ya rufewa Abdul baki yana janshi waje, yana dariya, shima Abdul dariya yake, dakyar Abdul ya kwace bakinsa yace " 'yarki ce ai, 'yar gida za'ayi, yana jin na fad'a ya sake ni yayi waje da gudu, Ramlat ma ta mik'e ta shige d'aki, sosai iyayen mu sukayi masifar farin ciki da soyayyar Umar da Ramlat dan su a tunanin su Umar yaran kirki ne, mai nagarta gashi nutsatstse zaifi rik'e musu Ramlat da daraja, shiyasa kowa ya nuna farin cikin sa da amincewarsa.

Soyayya sosai ta k'ara k'arko tsakanin Umar da Ramlat, a b'angaren Abdul da Yasmeen ma haka abin yake soyayyar su, dan kowa ya sani har iyayen su sun sani, dan haka aka tsaida ranar auren Abdul da Yasmeen, Umar da Ramlat da zarar sun k'are Secondary school.

Mummunar rana ta farko dabazan manta da ita arayuwata ba.
, lafiya lau muka ci abinci da Baban mu, mukayi hira yayi mana fad'a sosai akan gaskiya da rikon Amana, da zumunci, sosai yayi mana fad'a daga k'arshe yayi mana addu'a tare da fata na gari a rayuwar mu.
, ya shiga d'aki, da sallar asuba ma shiya tashe mu tare muka tafi masallaci, amma hukuncin Ubangiji yafi k'arfin wasa, da misalin k'arfe 7:00am najiyo kukan Maman mu tana kiran mu, da gudu muka fito muka iske ta a tsakar gida.

Sosai Mama take kuka ta kasa magana da hannu take nuna mana d'akin Baban mu dukkan mu muka shiga da gudu har Ramlat, Allahu Akbar rai yayi halinsa su Baba an riga mu tafiya gidan gaskiya.

Sosai mutuwar mahaifin mu ta girgiza mu, haka muna ji muna gani akayi masa wanka aka kaishi gidan shi na gaskiya, duk wanda yaga Umar yasan yashiga mugun taahin hankali wanda daga k'arshe mu muka dawo muna lallashin shi, sosai mutuwar Baba ta shigi Umar, gaba d'ayan mu jikin mu yayi mugun yin sanyi, kasancewar Abdul karatu yake bashi da wata sana'a,nauyin gidan gaba d'aya ya koma hannun Umar, kusan komai shi yake yi a gidan, har nauyin karatu na shiya d'auka yake yi.

Kwanci tashi babu wuya awajen Allah har Baba yakai wata biyar da rasuwa Mama ta fita daga takaba, cikin ikon Allah kud'in Baba ya fito dayake bamu da 'yan uba, shiyasa ba'ayi maganar rabaon gado ba, d'akin Baba aka fasa ta waje aka bud'e babban shago (shop) sosai muke ciniki dan duk unguwar babu shago kamar kamarsa, dan haka nauyi yabar kan Umar.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.