Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 13 of 42

daman Haka fadar gsky zatayi da rayuwata?
Hk son kwatar yanci zatayi sanadin tabarbarwa duniyata da tarwatsa rayuwata ?

Meyasa...?

meyasa zaka min hk ?
Sai km ya fashe da wani matsanancin kuka me tsanani da cin rai tare da taba zuci

BAYAN SHEKARA 2

Cikin ikon Allah Abdul ya fito lafiya lau, ya warke sumul babu abinda ke damunsa, sai matsanancin bak'in ciki da damuwa, da kuma wutar d'aukar fansa dake k'ara ruruwa a zuciyarsa in every second, koda Abdul ya fito bai bayyanawa kowa da duniya fitowarsa ba, ya b'oye kansa, babu abinda yasa gaba sai bincikin inda zai samo Sanata Sambo.

Tsakiyar 'cikin wata dokar daji Abdul yasamu yayi Buka tare da kebe kasan Daga shiga 'cikin mutane burinsa bai wuce yaga tagayyara rayuwar Sanata da dansa ba ..cikin wannan mahaukacin daji yacigaba rayuwasa shikadai .

Shiryawa yayi cikin dare, yayi shiga yadda babu mai gane shi, y nufi unguwarsu, a k'ofar gidan su ya tsaya, gaba d'aya an canjawa gidan tsari an mayar dashi gidan zamani sosai harda bene, gizo Mama, Ramlat, suka fara yi masa sosai yake ganin su a cikin idonsa, Ramlat na ihu cikin kuka take kiran sunansa, muryar Mama ya jiyo ta _"Abdullahi karka zo, karka zo Abdullahi ko kai kad'ai ne ka rayo danka d'aukar mana fansa_.

Sosai Abdul ya kwanta a wajan yana birgima a k'asa yan ihun kuka kamar ransa zai fita, ihu yake sosai yana sambatu kamar mahaukaci, kasancewar tsakar dare ne yasa babu wanda ya ganshi, ko ya gane shi, wani tsoho dake kwance a soron wani gida ya jiyo ihun Abdul, a hankali ya fito da touch light a hannunsa, har ya zo kan Abdul amma bai sai anzo kansa,b a dafa shi tsohon yayi yace " yaro lafiya? Kasancewar Abdul ya canja kama kuma ya tara k'asumba yasa tsohon bai gane Abdul ba, sai da tsohon yayi magana sosai sannan Abdul ya jishi, ya kuma dawo hayyacinsa, mik'ewa yayi bai yiwa tsohon magana ba yayi tafiyarsa, tsohon ya bishi da kallo me tattare da tausayawa .

Sosai Abdul ya shiga bincike akan Sanata Sambo da Haidar, Har Allah ya bashi ikon gano komai,da inda zai same su 'cikin sauki batare daya wata wahala ba sannu a hankali Abdul ya fara bin diddiginsu, tare da bin bayan su duk inda suka shiga, cikin sa'a Haidar ya fito da yammacin shi kad'ai a mota, .
Farinciki yakama Abdul sbd Ga dama tasamu bbu securities bbu kowa shi kadansa sai da Abdul ya bari yaje inda ba jama'a sannan ya jefa masa lemo wanda oready ya caccaka k'usa,ajiki Allah kuma yasa tayar motar Haidar ta taka,take motar taja birki kiiiiiiiiiiiiiii ta tsaya cak.
Shit abinda haidar ya furta kennan tare da daura kanshi akan sitiyarin motar yana takaici.
da sauri Abdul ya fito Daga motarsa ya bude motar haidar ya damki wuyansa 'cikin mazakunta ya rufe mishi baki yayi cikin kungurumin daji nan dashi.

Kasancewar Abdul mai k'arfi gaske ne, yayinda shi kuma Haidar duk shaye-shaye ya tsotse shi, yasa Haidar d'aukarsa cak aka, sai da Haidar yayi uwar tafiya me nisa dashi sannan ya isa Inda bukkarsa dake tsakiyar daji take wacce yake rayuwa acikin ta, yana zuwa bakin bukkar yayi wurgi da dashi, ya hau dukan Haidar ta ko'ina kamar zai kashe shi, kasancewar gaba d'aya zuciyar Abdul ta k'ek'ashi ta bushe bbu tsoro bbu fargaba ballanantana tsoro .

Yana cikin dukansa Sanata Sambo ya kira wayar Haidar dake aljihunsa, hannu Abdul yasa ya ciro wayar, yana duba screen din wayar yaga sunan Dad,yana yawo .
murmushi mugunta Abdul yayi ya d'aga wayar ya kara a kunne, cikin fad'a Sanata Sambo ya fara magana " bana ce maka karka sake ka fita ba, dan ubanka, bana hana ka fita kai kad'ai ba escorts ba, kasan fa muna da mak'iya kuma kai koyaushe a buge kake, komai yana iya faruwa dakai.

Wata irin mahaukaciyar dariya Abdul ya saka har da buga kafarsa daya sannan yace " kaji jaki mutun kai kanka kasan baka da gaskiya, kuma kasan kana da mak'iya musamman ma ni, dan nasan nafi kowa k'inka da ahlinka a hanlin yanzu duk duniya baka da wani mak'iyi daya wuce ni, yadda kamar ni ma bani da kowa haka zan mayar dakai baka da kowa, a duniya yanzu zan aiko maka da gawar tilon d'anka dan kaima ka fara d'and'anar abinda nake ji.

Sosai Sanata Sambo yayi muguwar firgita, hankalinsa yayi kololuwar tashi, saboda tsabar tsorata sai da yayi taga taga ya kusan fad'uwa , cikin rawar murya yace " Abdul kai ne ?
Yaushe ka fito har da bansani ba ?
kayi hak'uri dan girma Allah kada ka kashe min tilon dana zan gaya maka komai, please karkayiwa Haidar komai, sosai Abdul yayi dariya yace " ka kashe maciji ka manta baka sare kansa ba, yana fad'ar haka ya kashe wayar, in banda hello babu abinda Sanata Sambo ke ciwon yi duk ya firgita.y asona fita sense dinsa .

Cikin kuka Abdul ya kalli Haidar yace " mai mukayi muku? Idan ni nayi muku laifi mai 'yan uwana sukayi muku ni ya kamata ku kashe ba su ba, .
Basu da laifin komai akan lamarin Amman kashe min su .
cikin tsoro Haidar yake magana " wallahi ni ban san komai akai ba, kallonsa Abdul yayi yace " bazan kashe ka ba, amma zanci gaba da rik'eka anan har sai mahaifinka ya kawo min kansa, cikin rawar murya Haida yace " to, amma dan Allah karka cutar dani, ko kallan sa Abdul baiyi ba ya tashi ya d'aure shi sosai,a jikin wata katuwar bishiya sannan ya fita, direct kasuwa ya nufa, risho ya siya da tukunya, bokiti, ludayi, kasko, da dai sauran kasan buk'ata na gida, wajen masu kayan miya ya ya fara siya, jikin shi ne ya bashi ana kallon sa, a hankali ya jiya, dammmm!!! gaban sa yayi wata irin muguwar fad'uwa ganin Yasmeen tsaye ta kafa masa ido ko k'iftawa batayi,.
idonta duk sun cicciko da kwalla, shima ido ya k'ura mata ya kasa kawar da kansa daga kanta, cikin rawar murya, a hankali maganar can k'asan mak'ogwaro tace" Abdul, sai lokacin ya dawo hayyacinsa, kansa ya d'auke daga kallonta ya b'ata fuska, yaci gaba da siyayyarsa, gabansa ta dawo idonta na zubar da ruwan hawaye tace " Abdul me nayi maka?

Bayan duk satin duniya sai naje prison amma kak'i fitowa, ban kuma tab'a fasawa, kuma tunda nake zuwa baka tab'a fitowa ba, sai last month's naje satin dana saba zuwa aka cemin ai an sake ka, naita nemanka kamar mahaukaciya a gari, kallonta Abdul yayi yace " Malam waike wacece zaki zo kina min maganar banza anan, baki kawai Yasmeen ta bud'e tana kallan sa,cikin kuka tace" ko duk duniya zata kasa gane ka, ni zan gane ka, koda zakayiwa duniya basaja da b'adda kama Abdul banda ni, ko kowa zai manta kamanninka ni bazan manta ka ba, anan ya barta bayan me kayan miyan ya sallame shi, aiko Yasmeen ta shiga bin bayan tana yi masa kuka.

Duk inda yaje tana biye dashi, tana kuka, sai da ya gama siyayyarsa tsaf sannan ya juyo ya kalle ta, yace " nifa ban san ki ba, ban kuma san Abdul d'in da kike nufi ba, ni sunana Hamza, cikin kuka tace k'arya ne, tunda ka tsaya a kusa dani bugun zuciya ta ya k'aru tun kafin na d'ago ido na kalle ka, Abdul koda ido na zaiyi min k'arya nasan zuciya ta bazata yi min k'arya ba, Abdul kasan irin wuyar dana sha arayuwa a kanka, sau 5 ana saka man ranar aure ina bijirewa iyaye na akan ka, har barin gidan mu, da iyaye na, dangina akanka nayi, amma yau kai zaka ganni ka share ni.k ace baka sani ba duk duniya ni nafi cancarta mura farinciki mu tare hakazalika bakinciki .ka tausaya kada ka guje ni akan laifin wasu wlh bazan iya rayuwa bbu Kai ba yakarasa mgnr tana kuka ...

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.