Gadar Zare Complete Hausa Novel
Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt
Chapter 24 of 42
A hankali Fateeha ta d'ago idonta tace " a'a, na rasa mai nayi mishi idan na kira shi baya d'agawa, dan Allah Mama idan ya sanar dake wani abu daya faru ki sanar dani please, Hajiya bata b'oye mata komai ba, ta sanar da Fateeha duk abinda Dady yayiwa Khamal, sosai Fateeha ta razana, tace " Dady ne yayiwa Khamal haka? Hajiya ta k'ara da cewa " Khamal maraya ne, bashi da uwa ko uba, su biyu iyayensu suka haifa, ni Kakar su ce ta wajen uba, ni na haifiyar Abban su, daga shi har k'aninsa babu wanda yasan dad'in iyaye, shi Khamal yana da 3yrs iyayen sa suka rasu, shi kuma Hamza yana da 1yrs, basu san kowa nasu ba sani.
Tausayi Khamal da Hamza suka ya kama Fateeha, kuka tasa sosai, kamar ranta zai fita take kuka tace " Hajiya ban tab'a sanin Khamal maraya bane, bai tab'a sanar dani ba,dariya Khamal da Hamza suka jiyo, a tare suka shigo falon sai dariya suke, Hamza na ganin Fateeha yace " Alhamdulillah, ya nufe ta gadan-gadan dan Fateeha ita ce wacce yake haukan so, Fateeha ce wacce Hamza yake so akanta ne ya kamu da ciwon zuciya, yana ganinta yayi tunanin ko Fateeha tazo amsar soyayyarsa ne, ya d'auka ko tazo amincewa dashi ne, dan haka da sauri ya nufe ta yana murmushi, itama Fateeha ta mik'e ta nufe su, shi Hamza a tunaninsa ko wajen sa ta nufo, itako Fateeha bata ma ta lura da wani Hamza ba, hawaye na zuba a idonta tana kuma murmushi ta kalli Khamal tace " why why, mai yasa ka barni wannan hukuncin yayi min tsauri I love you, Hamza na hawayen farin ciki ya bud'i baki yace " I lov....... kafin ya k'arasa yaji Khamal yace " don't ever say u love me Fateeha, I hate you I don't want you in my life, just go, please live from my side, sandarewa Hamza yayi a wajen ya kasa kwakwaran motsi, cikin matsancin kuka tace " wallahi Khamal ina sanka, kai ne rayuwata, bazan iya rayuwa babu kai ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi.
" innalillahi wa'inna ilaihirraji'un kawai Hamza ke maimaitawa, wani iri juwa yake gani take idonsa suka fara ganin bibbiyu kuma dishi-dishi, numfashinsa ya d'auke,cak k'irjinsa ya fara bugawa da k'arfi, jiri ya fara d'ibansa, a hankali idonsa yake rufewa har ya dai na gani, d'if numfashinsa ya d'auke.............
MOMYN ZARAH
[16/11, 03:07] +234 706 099 2528: ```GADAR ZARE!!!```
_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDU*
15
Da kyar da taimakon Allah Hamza ya samu ya fizgo numfashinsa, a hankali a hankali yake bud'e idonsa harya samu yayi controlling kansa, dan baya son koda wasa Khamal ya fuskanci akwai wani abu tsakanin sa da Fateeha, ya daure ya doje yayi kamar ba wani abu, amma acan k'ark'ashin zuciyar sa ji yake kamar ya mutu da sauri k'irjinsa ke bugawa, mak'ogwaron sa ya bushe bakinsa ya rinka yi masa d'aci.
Itako Fateeha bama tasan Allah yayi ruwansa ba, gaba d'aya hankalinta yana kan Khamal, kwata-kwata bata cikin nutsuwar ta, sosai ta matsa daf dashi ta yadda kowannen su yana iya jiyo numfashin juna cikin sanyin murya tace " please Khamal karka barni, kai kanka kasan ina sanka, karka d'ora min laifin daba nawa ba, ya d'an matsa baya kad'an yana aika mata wani irin kallo, yace " kinga please ki tafi gida, kai ta shiga girgiza masa cikin kuka tace " a'a Khamal please karka barni, bazan iya jure rashin ka ba, wallahi idan ka barni mutuwa zanyi, ni kaina bansan ina yi maka wannan mugun son ba sai yanzu, Khamal kaine ruhi ne, idan ka barni tamkar ka tafi da rahi nane kabar gangar jiki na.
" Tunda nake ban tab'a yiwa iyaye na musu ko gardama na sai akanka duk abinda suka umarce bana yi musu gardama hakan ne ma yasa Dady ya yanke ranar aure na ba tare daya shawarce ni ba, cikin muguwar razana Khamal ya d'ago kai ka kalle ta, aiko karaf suka had'a ido, alama tayi masa da idonta na eh, taci gaba da cewa amma a kanka na kunya Dady na tubure nace a'a, akan ka nak'i yi masa biyayya, na bijire masa, yanzu haka Dady ko magana baya man, a kanka farin ciki da kwanciyar hanklin da iyaye na suka gina shekara da shekaru ke neman gujewa dan yanzu haka Momy da Dady neman rabuwa suke.
" Ashe duk tarin maganganun dakake fad'a min ba gaskiya, kasha fad'a min nice rauwarka, nice farin cikin ka, nice duniyarka, kace duk runtsi duk bazaka tab'a rabuwa da ni ba, Idan kasan baka sona mai yasa kace kana so, idan kasan bazaka iya rayuwa dani ba mai yasa ka koyamin yadda bazan iya rayuwa ba kai ba, idan kasan bazaka d'orewa so na ba mai yasa zaka koyar dani yadda zan soka, mai yasa Khamal mai yasa ta durk'usa a k'asa ta fashe da kula mai cin rai.
A matsayi na na mace mai kunya, daraja, k'ima, da Allah yayi min, na yarda jan aji na, na tako har gidan ku, amma duk da haka bazaka hak'ura ba, kai wanne irin mutum ne marar adalci wanda kansa kawai ya sani, baka damu da damuwar wani ba, taka damuwar kawai ka sani, wacce irin zuciya kake da ita mai kafiya marar yafiya.
Jikin Khamal yayi mugun yin sanyi, zuciyar sa ta harba da k'arfi, yayin da yake jin santa na k'ara ratsa ko'ina na jikinsa yana bin kowacce jijiya ta jikinsa yana bin jininsa, ya runtse idanunwa da gam, k'aunarta na fizgarsa zuwa gare ta.
Hamza ko zama yayi kamar ba mutum ya, ya sandare a waje d'aya, babu abinda zuciyar keyi sai bugawa, k'irjinsa nayi masa zafi, ji yake kamar ya mutu, dakyar yake iya controlling kansa, dan ji yake kamar zuciyar sa zata tsage, a gaban idon sa macen dayafi fiye da kowacce mace a duniya ke kukan son Yayar sa uwa d'aya uba d'aya, wanda duk duniya bashi da kamar sa, a hankali ya share siririn hawayen daya zubo masa.
Hajiya dake tsaye tana kallonsu, tausayin su ya cika mata zuciya, cikin sanyin jiki ta tako har inda Fateeha ke durkushe tana kuka, a hankali ta d'ago ta, takai ta kujera ta zauna ta shiga lallashinta had'i da bata hak'uri, a hankali Khamal ya tako ya durk'usa a gaban kujerar da Fateeha ke zaune, Hajiya ta shiga yi musu fad'a daga k'arshe ta zarce dayi musu nasiha, sosai nasihar Hajiya tayi tasiri a jikinsu, a hankali ya rik'o hannunwanta ya k'ura mata ido ya langwab'ar da kai yace " am sorry my life, murmushi tayi ta kama kumatunsa tace " bakai ne yace zaka iya rabuwa dani ba, " dariya yayi yace " wallahi pretending ne, ba gaskiya bane, dariya Hajiya tayi ta mik'e tace " ja'irai.
Mik'ewa Khamal yayi ya rik'o hannun Hamza ya kawo shi gaban Fateeha yace " my cweet ga brother na, mama da Baban mu d'aya, mu biyu iyayen mu suka haifa, Hajiya kuma grandpa d'inmu ce, ita ta rik'e mu tun bayan rasuwar iyayen mu, bamu san kowa na mu sai ita, ya kalli Hamza yace " Bro ga my heart, sai lokacin Fateeha ta kula da Hamza aiko da k'arfi k'irjinta ya buga, cikin seconds ta shiga tension, da sauri Hamza yayi mata signs ya girgiza mata kai, alamar a'a, da sauri yace " yau dai Allah yayi naga amaryar mu, ya kalli Khamal yace " kai Yaya ka iya zab'e she is very beautiful, murmushi tayi tace " nagode irin wannan kod'awar haka.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.