Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 37 of 42

D'ago kansa yayi yana kallansa daga bisali kuma yace " a'a ban sani ba wanne daga ciki?

" wad'anda mukayi karatun Mastrs dasu a Dubai, shiru Zaid yayi yana kallon Mukhtar, "ko bazaka je bane? cewar Mukhtar, " eh to gani nan idan ina da time zanje wacce rana ce?

" this coming weekend ne, Saturday, " ok zaka je? Zaid ya tambayi Mukhtar, murmushi Mukhtar yayi yace " idan zaka je amma idan baka zuwa nima babu inda zani," hmmmmm gadukkanin alamu dai kana son zuwa, " eh mana ko ba komai ai a sada zumunci kuma ma ai munyi missing juna cewar Mukhtar, " ok badamuwa Allah ya kaimu, "Amin Mukhtar yace yana mik'ewa kallonsa Zaid yayi yace " sai ina kuma?

"Baka ji an kira sallah bane? " banji ba wallahi ya fad'a yana duba agogon hannunsa, ganin lokaci yayi ne yasa shi saurin mik'ewa, yayi toilet, bayan sun idar da sallar direct cikin gida suka wuce a parlor suka samu Ammi zaune tana kallon Aljazira English, har k'asa suka duk'a suka gaida ita, fuskarta cike da fara'a ta amsa, kusa da ita suka zauna gaba d'aya, Mukhtar yace "Ammi da abinci kuwa?

Ban sani ba! kullum kuzo ku dame da neman abinci ance kuyi aure kunk'i sai kuzo ku rink'a cinye min abincin gida acici kawai ta fad'a tana dariya da sigar tsokana, dariya sukayi gaba d'ayan su Mukhtar ya langwab'ar da kai cikin shagwab'a yace " kai Ammi idan bamu ci naki ba nawa kike son muci? "Na matan ku mana, ni fa lokaci na baku idan kuma ya cika ko gida na bazan bari ku rink'a shigo min ba, ni ban tab'a ganin yara irin ku ba kwata-kwata basa san maganar aure balle auren ma, "dariya suka kuma yi Zaid yace " da Abban mu nan daya shigar mana a... "Aiko wannan karon bazan shigar muku ba bayan matata ni ma zanbi cewar Abba dake shigowa cikin parlor d'auke da fara'a Mukhtar yace " kai Abba harda kai kuma yau? " eh harda ni nazan yarda kullum a rink'a damarmin mata da maganar abinci ba ana zuwa ana hana ta baccin dare da hira murmushi Zaid yayi yace " kyale su Friend idan muka tashi mu full tank zamuyi dan sai munyi 4 dariya Abba yayi yace " idan kunji haushi kuyi 1000 yau ma.

Haka dai suka ci abincin cike da fara da barkwanci dan daga Abba har Ammi sun kasance mutane masu fara'a da wasa da dariya da iyalan su, suna cikin haka Abraham ya shigo da sallamarsa fuskarsa d'auke da murmushi ya nufi wajen Ammi da Abba, burki yaci dan ganin wad'anda yafi tsana a duniya take ya murtuke fuska ya had'e rai yadda kasan anyi masa sammacin mutuwa.

Cikin fara'a Abba yace " yawwa babban d'a k'araso fuska ya k'ara b'atawa yace " no Abba badamuwa bari naje waanka zanyi, murmushi Ammi tayi sannan tace " haba d'ana zo kaci abinci kaji, murmushi yayi mata yace " ok Ammi but not now, Abba ya kalli su Zaid yace " baku ga Yayan ku bane? "Ai da muka ga kuna magana ne, a tare suka had'a baki Yaya ina wuni? ko kallan inda suke bayyi ba a ciki ya amsa da lafiya, hakan ma dan agaban idan su Abba ne, ya wuce abinsa, gaba d'aya suka bishi da ido ita ko Ammi ajiyar zuciya ta sauke tana mai matuk'ar bak'in cikin halin da Abraham yasa kansa, ganin gaba d'aya yanayin Ammi ya canja yasa Zaid da Mukhtar tare da Abba kwantar mata da hankali da bata hak'uri.

Abraham na shiga d'aki ya banko k'ofar d'akin, yana ta faman huci kamar maciji, kayan jikinsa ya cire ya shiga cilli da dasu, zama yayi a bakin gadinsa yana furzar da iskar bakinsa, da sauri ya mik'e ya d'auko sigarinsa ya hau busawa sai da yasha mai isarsa sannan ya shiga bathroom ya sakarwa kansa shower, yakai kusan 30 minutes sannan ya fito ya fad'a kan gadonsa yayi rigingine kansa yana kallon sama ya shiga tunanin ta inda zai b'ullowa Zaid, sai da ya b'ata lokaci sosai sannan ya samu mafita, mik'ewa yayi zaune yana murmushi gefen baki dan ya samu hanyar dazai k'ullawa Zaida GADAR ZARE.

Ranar Saturday wajen k'arfe 8:00pm babban hall din kuma tsadadje cike yake da jama'a had'add'u 'yan gayu kuma 'yan book kai gani kasan naira ta zauna da gindinta a wajen, don kuwa ka gani kasan yaci ya tada da ita, yayinda duk jama'ar dake wajen maza da mata fuskokin su cike da fara'a da sanyayyan murmushi Zaid take tsaye ya hango wani abokinsa sosai da tunda suka gama karatu bai ganshi ba, shima abokin nasa idonsa ne suka sauka akan Zaid aiko cikin zumud'i fuskarsa d'auke da wadataccen murmushi ya nufo Zaid shiko Zaid tsayawa yayi yana kallonsa shima yana mayar masa da martanin murmushin suna gaf da had'uwa ne aka kashe wutar wajen.

Hankalin Zaid kwance ya k'arasa nufar abokin nasa ya rungume gam cike da farin ciki " I miss you so much frien...... maganar tasace ta sark'e masa a mak'ogwaro sanda aka maido da wutar hall d'in, ya sandare a tsaye yana kallon yarinyar daya rungume a tunaninsa abokin nasa ne, sakinta yayi da sauri yayi baya durk'ushewa tayi a wajen d'an kwallin kanta ya fad'i gashin kanta daya sha gyara ya zubo mata a fuska ya rufe mata face, cikin b'acin rai ta mik'e tasa hannu ta kawar da gashin daya zubo mata, baki Zaid ya bud'e yace " am sor.... kasa k'arasa maganar yayi sakamakon kyau da had'uwar yarinyar daya firgita shi, take nutsuwarsa ta d'auke ya k'ura mata ido baya ko kiftawa, itama cikin tsiwa ta bud'e baki tace "Would take your hand off, please, tana sauke idonta a kansa gabanta yayi mummunar fad'uwa, shida baima ma san har a lokacin hannunsa na kanta ta yayi saurin d'auke hannunsa amma idonsa na kanta fuskarta ba yabo ba fallasa tace " what are you staring at?, never seen a girl before? ta fad'a tana barin wajen, murmushi Zaid yayi yabi bayanta da kallo yace "I have but not a girl who entered my heart, at first sight.

Duk inda yarinyar tayi idonsa yana kansa, ya kasa daina kallonta, tana sane dashi amma tayi kamar bana tasan tana yi ba, haka har aka gama taro, Mukhtar yace " muje ko? " kaje kawai ni ba yanzu zan tafi ba, cikin mamaki yace " me zakayi, ina zaka biya? "kaje kawai zamu had'u a gida cewar Zaid yana barin wajen, da ido Mukhtar ya bishi kawai, duk yadda Zaid yaso yayi magana da yarinyar amma taki bashi dama, har taron ya watse, cike da matsanancin bak'in ciki yake tuk'in motar yayinda yake cizon d'an yatsansa, danja ce ta tsaida shi dole ya tsaya badan yaso ba, wasu samari ya gani cike da mota suna bin wata motar a guje, da gudu motar da ake bin ta bigi wani gani dake gefe ganin haka yasa samarin barin wajen a guje, da sauri Zaid ya fito ya nufi motar da k'arfi ya b'elle k'ofar motar, tsaywa yayi cak dan ganin yarinyar ce acikin motar amma ta suma, gabansa ne yayi muguwar fad'uwa, da sauri ya d'auke ta yasa a cikin motarsa yayi aaibiti da ita.

Bayan Doctor ya gama duba ta ya fito yana yiwa Zaid bayani "her blood pressure is low, but everything is okay otherwise, not a serious wound, I think she has lost consciousness because of fear, I have administered the injection she'll be fine by morning, murmushi Zaid yayi yace thank you doctor, you are welcome Doctor ya fad'a yana barin wajen, a d'akin da aka kwantar da ita anan Zaid ya kwanta kan doguwar kujera, tun asuba daya farka yayi sallah bai koma bacci ba, zama yayi a kusa da ita ya k'ura mata ido yana ganin tsantsar kyau ya hankali yace " da gani ba baushiya bace dan tafi kama da turawa, sai wajen 8:00am ta farka bakin ta d'auke da salati hannunta ta saka duka biyun ta dafe kanta da sauri Zaid ya nufe ta, a hankali ta tashi zaune ta fara ware idonta tana bin ko ina da kallo, idonta ne sauka akan Zaid da sauri ta k'ara zaro ido tana kallon sa tace "you agai?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.