Gadar Zare Complete Hausa Novel
Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt
Chapter 35 of 42
Khamal ya kalli jama'ar da yake bawa labari yace" kunji labari na, kowa a wajen ya jinjina had'i da alheni, Al'amin ya kalli Khamal yace" yanzu ina Ayuba da iyalansa sannan kuma ina Hamza?
Murmushi Khamal yayi yace " Hamza yana gidan yari har yanzu, amma ya tuba ya koma ga Allah sosai, dan naji ance ma yanzu shine liman a prison, kuma kullum yana cikin istigfari, Ayuba ma yana nan tare damu sai dai baya cikin 6'S STARS, shi ya zame mana makar babban yaya ne, duk inda muke kuma yana nan, haka ma iyalansa suna tare dashi, haka ma Dady da Momyn Fateeha sunan a raye kuna garin Kaduna sune suka zame min kamar iyaye, Abban Ja'afar shima yanan ya tuba ya koma ga Allah, Ja'afar yayi aure shima.
Yana kaiwa nan ya mike yace " dare yayi sai kuma zuwa gobe sai mu Zaid ya fara, dukkan su suka mik'e suka nufi waje, gaba d'ayan su a gidan Ammar suka zube suka ci abinci suka yi sallah.
Washe jama'ar data zo wajen ta ninta ta jiya sau 10 dan sai da aka k'ara tsaro sosai,Ammar ya kalli Zaid yace " Bissimillah.......
*LABARIN ZAID*
MOMYN ZARAH
[16/11, 05:58] Frd Din Fatima Saudia: ```GADAR ZARE!!!```
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*
20
*LABARIN ZAID*
"Ainahin sunana Zahradeen Muhammad Bature, ni d'an asalin garin Bauchi ne, Allah ya azurta mahaifina da tarin dukiya dan duk Nigeria idan kace Muhammad Bature babu wanda bai san shi ba har yau har gobe sunansa yana yawo a nan gida da sauran k'asashen duniya, Mahaifina d'an kasuwa yana da companies na shi na kanshi a kalla sun kai 10, zan iya cewa mahaifina bai isa yasan yawan abinda ya mallaka a duniya ba.
Duk tarin dukiyar nan da Allah yayi masa amma baya cikin nutsuwa dan Allah ya rage shi da abu d'aya shine rashin haihuwa sun kai 10yrs da aure da mahaifiyata amma ko b'ari bata tab'a yi ba, anyi neman maganin har an gaji, zan iya cewa yawancin k'asashen duniya sunje akan neman haihuwa amma ko ina maganar d'aya ce lafiyarsu lau Allah ne dai kawai bai kawo lokaci ba, mahaifina ya sha d'ibar malamai sama da 50 ya kai su Saudi Arabia dan su rok'a masa Allah ko Allah yasa a dace amma shiru.
Duk da wannan jarabawar da Allah yayi masa hakan baisa ya kauce ba, dan gaskiya Abba ya kasance mutum mai tsoran Allah, adali mai taimako, da jik'an talakawa, ya kasance cikekken malami makarancin Al'Qur'an yana da matuk'ar tausayi, dan yana da gidan marayu, islamiyoyi, bohol, da masallatai bazasu tab'a k'irguwa ba, kai duk inda kake neman mutum na Allah Abba na yakai, shiyasa mutake ke kiransa da GARKUWAR TALAKAWA, haka ma mahaifiyata wacce muke kira da Ammi ta kasance mace mai biyayya, hak'uri, sanin ya kamata da taimako, itama kamar Abba haka take shiyasa ake kiranta da UWAR MAKAYU.
Babu yadda mahaifiya ta batayi da Abba akan ya k'ara aure ko Allah zai sa a dace ba amma yak'i, a cewarsa komai na Allah ne, da haka suka yanke shawarar zuwa gidan marayu su d'auko d'a, Ammi ce tajewa Abba da wannan shawarar aiko da sauri ya amince, ranar Monday da safe suka shirya su biyu suka tafi gidan marayu, basu tafi da kowa kasancewar a sirrin ce suke son aiwatar da komai.
Bayan su Abba sun gama kwarorowa shugaban gidan marayun buk'atar su ne ya sauke ajiyar zuciya yace " Alhaji dan yara akwai su amma matsalar d'aya ce babu sabuwar haihuwa kamar yadda kuke da buk'ata, Abba yace " ok badamuwa ba lalle sai yanzu ba idan aka samu sai kay..... bai k'arasa ba sakoman wata mata data shigo da gudu ta zube a gaban shugaban gidan marayun tana haki tace " ranka ya dad'e mahaukaciyar nan ta haihu an samu d'a namiji, sai dai tana cikin mawuyacin hali, da sauri suka mik'e har su Abba suka biyan matar.
Suna shiga d'akin suka iske matar rik'e da d'anta a hannu cikin jini tana ta fisge-fisge da sauri Ammi ta k'arasa inda take ta rungumo ta tana ta faman jera mata sannu dakyar matar ta d'aga kanta ta kalli Ammi ta mik'a mata yaron dake ta faman tsala kuka cikin rawar murya tace " ga d'a na nan amana kiji tsoran Allah ki kular min dashi kamar d'an cikin ki, ki bashi ingantacciyar tarbiyya kamar ke kika haife shi duk abinda kikasan zakiyiwa d'anki kiyi masa, yunk'urawa tayi da niyyar ta tashi amma ta kasa, dakyar ta bud'e baki tace " mu 'yan asalin Yobe ne cikin garin Yoben, sunana Khadija mahaifin yaron nan sunansa Isma'il ta bud'e baki zata kuma yin magana amma ina Allah bai bata iko ba, taita salati har rai yayi halinsa, a hankali Ammi ta kwantar da ita a k'asa ta rungume yaran tana zubar da hawaye.
Jana'iza akayiwa matar aka kaita gidan ta na gaskiya shugaban gidan marayun ne ke gayawa su Ammi had'ari matar sukayi ita da mijinta shi mijin ya mutu tun a lokacin ita kuma matar ta haukace, su Abba sun jinjina al'amarin sosai, duk wasu ka'idoji da ake bi wajan karb'ar yaro daga gidan marayu sai da su Abba suka bi, an ciccike takardu sannan suka tafi da yaron su wanda suka sawa suna IBRAHIM suke kiransa da suna Abraham, bayan sati d'aya da karb'ar Abraham Ammi ta tashi da wani mugun zazzab'i dan har bata iya ko d'aga hannunta, Family Doctor Abba ya kira ya duba ta, ganin yanayin ciwon yasa shi zargin ko ciki ne da ita dan haka ya buk'aci fitsarinta, bayan Abba ya bashi fitsarin ne yace zaije lab yayi test zai dawo da daddare, gwajin farko Doctor ya gano Ammi na da shigar ciki harna tsawon wata bakwai, bayan sallar ishsha yaje gida a falo ya samu Abba cike da farin ciki Doctor ya mik'ewa Abba hannu yace" congratulations sir your wife is pregnant, da sauri Abba ya mik'e tsaye yace " are you serious Doctor? Cikin fara'a Doctor yace " kwarai kuwa harna 7 mnts ma, sujjada Abba yayi yana godewa Allah.
Fad'ar farin ciki wajen Ammi da Abba ma b'ata lokaci ne, kuka sosai sukayi aka rasa mai rarrashin wani a tsakanin su, Doctor kuwa yasha kyauta kala-kala, haka Abba ya rink'a haukan rabon duniya kamar a rijiya yake hak'owa, bayan wata biyu Ammi ta haihe ni, aka saka min sunan kakana Baban Abba na ZAHRADEEN ake kira na da ZAID, kunga Yaya na Abraham ya bani wata biyu kenan, dayake duk duniya babu wanda yasan maganar Abraham babu wanda ma yasan dashi har aka haife ni, dan haka Ammi da Abba suka shaidawa duniya mu 'yan biyu ne, duk duniya babu wanda yasan mu ba 'yan biyu bane balle har a san Abraham ba d'an Abba da Ammi bane ba, saboda sun riga sun gama tsara komai shiyasa cikin Ammi yana isa haihuwa Abba ya fitar da ita waje, a turai Ammi ta haihu shiyasa asiri ya k'ara rufuwa, ko mu kan mu ni da Abraham bamu san mu ba twins bane ba, gaba d'ayan mu Ammi ke shayar da mu.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.