Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 11 of 42

Kasancewar su manya ne a k'asa ba'a wani sha wahala ba, aka samu address d'in, Abdul har gida Sanata Sambo ya aiko aka tafi dashi cikin aminci da kwanciyar hankali, babu wata alama ta wulak'anta duk da dakyar Abdul yaje dan da farko k'in zuwa yayi sai da Mama ta matsa masa, bayan Abdul ya bayyana a gaban Sanata Sambo ne, Sanata ya gabatar masa da buk'atar sa, murmushi Abdul yayi yace " gaskiya bazan iya ba.
Alahakikanin gaskiya acin zarafin yarinyar an cuceta an cuci rayuwarta da iyayenta.
Idan Na amsa bukartaku Na cika muku burinku na rufa muku asiri naje nakaryata abinda yake gsky ne akan siyarsarku ni km meyye hukuncina agurin Allah?
babu yarda Sanata Sambo baiyi da Abdul ba.. amma fir Abdul yak'i amincewa bukartasa sosai Abdul da Sanata Sambo sukayi cacar baki da musayar magana amma ba cikin fad'a, ba Abdul ya zage ba tsoro ballanantana wata fargaba ya dinga gayawa Sanata magana sosai daga k'arshe yace " idan kashe ni zakuyi kuna iyawa amma gaskiya banza iya cin amanar mamaci ba.
, mai yasa d'anka bai yiwa bakin jijiyarsa key ba, ai yasan dakai da km siyarsarku amma yaje ya aikata san ransa.dan kawai yana takamar Ku wasu acikin kasa .
, dan haka wallahi wallahi banza tab'a karya alk'awari dana daukarwa yarinya ba.
Sai naga an durkufar danka gaban koto an yanke masa hukunci daidai da kaifinsa ta yadda ruhin yarinyar nan zai samu salama , yana kaiwa nan ya mik'e tsaye jikinsa a sanyaye yayi waje.yana takaicin masu hali irin Na senata sambo masu fifita harkar siyasarsu akan rayuwarsu wasu ..

Da wani irin kallo Sanata yabi bayan Abdul yana murmushi 'cikin kasan ranshin , yace yaro baisan wuta ba saiya taka,i Dan kasan wata bakasan wata ba zan b'ullo maka ta yadda bazakayi tsammani ba, zan baka mamaki yaro, idan ko har kasa burina .
Na siyatata yak'i cikawa saina saka kuka .idan
har ka tsani kuka, sai na saka yin kukan jini da idanunka Sai Na gigita rayuwarka Na wujijiga duniyarka da farinciknka ta yadda har ka mutu bazaka daina kukan bak'in cikina .....

*MOMYN ZARAH*
[16/11, 03:05] ‪+234 706 099 2528‬: ```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY, HYPOCRITES, BETRAYALS)_

~NA~

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES , SU KARANTA BA```

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

8

Gida Abdul ya wuce Kai tsaye cike da alhinin abinda yashiga tsakanina da senator , yana shiga ya iske Mama a tsakar gida tana shara, tana jin shigowarsa ta mik'e tsaye tana kallonsa tace " yaakayi ?
Ya kukayi da su ne?,tayi masa tmbyr ajere.
Acikin tsanake Abdul ya zayya ne mata komai , shiru Mama tayi na d'an wani lokaci, sannan tace " ni dai Abdul ina jin tsoro kar wani abu ya sameka fa, mutanen nan ba imani gare su ba, akan cikar burinsu babu abinda bazai iya ba.

"Bakomai Mama in sha Allah babu abinda zai faru sai alkhairi, Allah ya sani dan shi nayi nasan kuma bazai tab'a bari a wulak'anta ba.

Km ma mama kece kika bani kwarin ya km naga duk jikinki Yayi sanyi ?
, jikin Mama a sanyaye tace "to shikennan Allah yabada sa'a Abdullahi, Ubangiji ya tsare min ka, Daga sharrin su Yasa kayi nasara akansu " Amin Ameen Mama,t are da shigewa d'aki.

D'aki ya iske Umar yana sallah, zama yayi yana jiran ya idar, shima ganin Abdul d'in yasa bai ja doguwar sura ba, yana idarwa ya juyo .
Ahankali ya kalli Abdul din yace " bro lafiya dai naganka hk ?

Guntun murmushi Abdul yayi sannan ya shiga bashi labarin duk abinda ya faru tun daga kan had'uwar shi da Aisha har zuwa yau din nan da Sanata Sambo ya nemi son ganinsa.
, shiru Umar yayi sosai yana tunani tare da nazarin mgnr , sai kuma yace " gaskiya nima dai ta bakin Mama wallahi tsoro nake ji, bana san su cutar dakai.
, dan idan wani abu ya faru da kai, wallahi bazan tab'a ragawa iri irin su ba, dan sai na fi baya zama terror, sai na addabi ahalinsu gabadaya.

Murmushi sosai Abdul yayi yace " da yardar Allah ma babu abinda zai faru balle na tuna maka jiya, " Allah yasa haka inji cewar Umar.

Tun daga ranar da Sanata Sambo ya had'u da Abdul yaji ya k'ara tsanarsa fiya da koyaushe burinsa kawai yaga ya kawar da Abdul a doron kasa amma ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin saboda kar jama'a su farga.
, saboda ga dukkan alamu Abdul ya tarwatsa masa siyasarsa, shiyasa a yanzu bashi da wani buri daya wuce yaga ya tarwatsa rayuwar Abdul, burinsa kawai yagan shi ya tagayyara, dan haka ya shiga binciken hanyar dazai b'ullowa al'amarin, cikin sa'a kuwa sanata ya samu labarin Umar, yasa akayi masa bincike akan sa sosai, ya samu cikekken bayani akan dangartakar su, da kuma halin Umar na baya, murmushi Sanata Sambo yayi sanda ya samu wannan damar, sannan yace " da d'an gari kan ci gari.

Nan da nan yasa aka nemo masa Umar aka gawo masa shi gabansa, kallansa Sanata Sambo yayi yace " Umar ko? da ido kawai Umar ya bishi baice masa komai ba, Sanata Sambo yaci gaba " d'an fashi, d'an daba, d'an maye, sannan wanda ya makance akan san abun bazai taba samun saba wato Ramlat, d'an niger wanda iyayensa suka mutu, ya taso a hannun mak'otansu.

Tsaki Umar yayi yace " kaga ni ba shirme da b'ata lokaci ne ya kawo ni ba, idan baka da abincewa ni zanyi gaba, dariya Sanata yayi sosai sannan yace " ni ko ke da abincewa, ai abin cewar ne ma yasa ni kiranka, " Ok ina jinka, " nasan halinka, nasan sirrinka, nasan abubuwa da dama akan kawanda kai kanka baka sani ba, nasan baka da wani buri daya wuce na mallakar Ramlat, kuma kasan hakan bazai taba faruwa ba, idan Abdul yana raye, kai Ramlat kake so ni kuma rayuwar Abdul nake so, shiyasa na kiraka dan mu had'a hannu wajen cikar burin mu, saboda idan har Abdul yana raye bazan tab'a samun siyasata ba, haka kai ma bazaka tab'a samun masoyiyarka da Ramlat ba.

Dan hak......... Wata mahaukaciyar tsawa Umar ya dakawa Sanata Sambo wanda yasa shi yin shiru da bakin dole,batare daya dasa aya ba .
Umar ya mik'e tsaye yayiwa Sanata muguwar shak'a yace "wallahi in banda nayiwa Mama da Abdul alk'awarin na daina munayen halayen na da anan take zan murd'e maka wuya na jefar da wulak'antacciyar gawarka.

Saboda nasan ko awajen Allah kai wulak'antacce ne banza kawai wanda bai san darajar amana, halacci da alk'awari ba, iyayen na su mutu tun ina da 6yrs, mutanan nan suka d'auke ni, duk unguwar babu wanda ya kalle ni balle yasan Allah yayi ruwa na, sune ci na, sune sha na, sune sutura ta, sune komai nawa, su sukayi min komai arayuwa babu abinda basuyi min, sun yi min gata, sun rik'e ni kamar d'an cikin su, tunda nake dasu basu tab'a yi min wani abu na b'atanci ba, sannan dan kai jaki ne, jahili, wanda bai san me yake ba kace naci amanar wad'annan mutanan, wallahi Allah ya rufa maka asiri baka same ni sanda nake HORROR ba, da tuni ka tsufa a lahira, yayi jifa da Sanata yayi tafiyar sa, sosai Sanata ya bugu sakamakon jifan da Umar yayi dashi, bayan Umar Sanata Sambo yabi da kallo, yana murmushi bak'in ciki.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.