Gadar Zare Complete Hausa Novel
Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt
Chapter 10 of 42
Shiru Mama tayi, Sosai cikin mutuwar jiki tace " Allah ya zab'i abinda yafi alkhairi, " Amin Mama addu'a ya kamata kiyi mana, "addu'a kam kullum akanta ake Abdullahi, murmushi Umar dake labb'e yayi ya girgiza kanshi kawai kwalla takaici na zubo masa a fili yace " na cuci kaina, jin Mama na niyyar fitowa yasa shi saurin barin wajen.
Dayake Abdul Medicine yake karanta, cikin ikon Allah aka tura shi Practical a General hospital din dake Gombe, Allah yasa ya fara practical a sa'a tunda yake aiki bai tab'a samun wata matsala ba, har Allah yasa yayi wata biyu.
ranar wata Monday da wuri Abdul ya tashi ya shirya ya nufi hospital, yana zuwa yaga an kawo wata yarinya a matuk'ar galabaice, za'a shiga da ita Emergency, sai jini ke zuba ta k'asanta,yayinda numfashi ma da kyar take fitarwa tsabar tashin hankali datake ciki bata ko iya magana bata iyawa , da sauri Dr ya kira Abdul akan yazo ya taimaka masa , cikin rawar jini ya shiga,dakin aka kwantar da wannan yarinyar.
Abdul na shiga Dr ya d'age gaban yarinyar, " Innalillaihi wa'inna ilaihirraji'un abinda Abdul ya shiga furtawa kenan yana dauke idanunsa da sauri .
Saboda ganin yadda gaban yarinyar yayi da sauri ya runtse idanushi tare da kansa gefe, sai ji yayi caraf an rik'o masa hannu a d'an tsorace ya bud'e idonsa, yarinyar ya gani rik'e da hannunsa, hawaye na zubo mata,tana dubansa agalabaice bakin da k'asanta jini sai zuba yake, da kyar ta iya bud'e baki tace " sunana Aisha, ina karatu a Government Girls ina SS1, d'an gidan Sanata Sambo ya ganni yace yana sona, nak'i amince masa ballanantana Na kulashi to shine dan nak'i kula shi, suka yi min fyad'e shi da abokan sa, ni 'yar talakawa ce iyaye na basu da wani k'arfi dasu daukar min mataki akan abinda aka min .
dan Allah , ina neman taimako d'aya a wajen ka, ta rik'o hannayan sa duka ta yunk'ura alamun tana son tashi amma ta kasa tashi sai uban jini ne kawai ke fita daga jikinta,.
hannayen damke cikin nasa tace " ka duba School Bag dina nayi video nayi recording komai, dan girman Allah ka yad'a labari nan karka b'oye shi sannan ta fashe da wani irin matsanancin kuka,me ban tausayi da cin rai numfashinta Na sauka ahankali tace " ka d'auke ni tamkar k'anwar pls kayi min alk'awarin zakayi min abinda nasaka tallafa kamin gata , ka tona masa asiri, ta yadda mahaifinsa bazai samu nasarar ci zab'en takarar governor daya tsaya ba, pls kayi min alk'awari tana ta maimaita pls kayi min alk'awari zakayi har numashinta ya tsaya cak alamun mutuwa tayi hannunta still damke cikin nasa.
Mutuwar tsaye Abdul yayi ya kasa koda kwakwkwaran motsi balle yayi magana saboda rik'on datayi masa dakyar likitoci suka kwace hannunta daga 'cikin nasa, shi kansa hawayen tausayin yarinya ke bin kuncinsa yana fitowa daga Emergency yaga iyayenta suna kuka kamar ransu zai fita.
, direct School Bag d'inta ya d'auka ya wuce gida, shi bai ma san me yake yi ba, koda yake tafiya babu abinda yake tunawa sai yarinyar yaddda take kuka
tare da nacewa _ka taimake ni kayi min alk'awari zakayi_.
Yana k'arasawa gida ya zube agaban mahaifiyar sa, sai daya kusan 30 minutes baice mata komai,ba Mama sai tambayarsa take lafiya, Abdul ?
Meyye faru da kai hk ?
amma ina ya kasa magana sai kuka yake yana tuno da yarinyar da irin illar dakayiwa rayuwa hakika maci amana irinsu basu cancin rayuwa a doron kasa ba .kuka yake sosai har shesheka , sai can iya bud'e baki ya fara magana bai b'oyewa Mama komai ba ya kwashe duk abinda ya faru ya zaiyane mata,d dangane da wannan yarinyar .
sosai Mama ta firgita,d a jin lamarin sai da saita kanta sannan tace " kai yanzu meye shawararka? Sannan km meyye abinyi Abdul ?
Kallon Mama yayi sosai kana muryarsa cike da kuka yace " ni bani da wata shawara ko abinyi, Mama ta kalle shi tace " kamar ya?
"Mama nima ban san me zanyi ba, ban san ya'ya zan taimakawa wannan yarinyar da,akazalinta aka yanke mata farinciki rayuwa ta hanyar yi mata fyade murmushi me cin rai da zuciya Mama tayi tare da cewa " karkayi haka Abdul ka tuna hannunta cikin naka ta mutu tana zubd hawayen takaicin abinda akayi mata tana k'ara nanata maka kalmar, bata sanka ba amma tasamu yak'i ni akanka harta yarda dakai ta dank'a maka amana, a hafin hannunka ta mutu tana zubar da hawaye, yanzu idan Ramlat akayiwa haka, kuma fa .
Nasan ita bazakace bakasan abinda zakayi ba nasan kana da hujja yadda zakayi, .....da wani irin mugun sauri Abdul ya d'ago kanshi ya xubawa mama idanunshi yana kallonta cike da jin tsoron kalmar data fito bakinta , .
Ahankali muryarsa Na rawa ya furta sunan Ramlat ....can km yasoma girgiza kanshi yana cigaba da kallon mahaifiyarsa hawaye km Na tsiyaya Daga idanushi murmushi takaici mama ta sake yi tana jin tayi daci da radadin ciwon abinda akayiwa diyar mutane duk da bata ganta ba Amman abun yata ruhinta da gangar jikinta .
Muryarta a sarke tace " ita dayake 'yar uwarka ce ba, shine duk ka frigice kadawo wani mutun abin tausayi , ba lalle sai d'an uwanka na jini kadai zaka iya taimakawa ba arayuwa .
, kamata yayi ka fi taimakon wanda yake da yak'ini akanka fiye da jininka.
, ni dai inda zan baka shawara ka kai gidan jaridu, TV, radio a buga labarin a ko'ina.
Ta yadda za ka samu sauke nauyin da Allah ya d'ora maka. Allah sarki yarinya karama hk abar tausayi ko a wani hali yanzu iyayenta suke ciki ?
Ko yaya zasu ji idan suka samu labarin mutuwarta mama takarasa mgnr zuciyarta cike da alhinin mutuwar yarinyar dabata San kowace ce ba..
Shiru Abdul yayi yana sauraron mahaifiyar tasa, sosai ta k'arayi masa nasiha ta k'ara masa k'arfin gwiwa, a YouTube Abdul ya fara d'ora video daga bisa yakai wa wani abokinsa dake aiki a gidan TV a gaban Abdul aka nuna video had'e dayin bayanin da yarinyar ta sanar dashi, duk da ba Abdul dinne yayi bayanin ba, daga direct gidan jarida ya wuce ya biya aka buga masa labarin.
Bayan kwana biyu labari ya kaiwa sanata Sambo, aiko hnklinsa ba k'aramin tashi yayi,ba.
cikin k'ank'anin lokaci labarin ya yad'a ko'ina duk gidan TV ko radio daka kunna maganar da akeyi kenan, sosai hankalin Sanata ya tashi, saboda hakan yana nufin rugugujewar siyasar shi.
Nan da nan sanata ya kira taron gaggawa, na manyan 'yan siyar sa, ciki kuwa harda Haidar d'an sanata wanda yayiwa Aisha fyad'e bayan kowa ya zauna an natsa Sanata ya kalli Haidar yace " kai ka fad'a min gaskiya kayiwa yarinyar nan fyad'e? kai tsaye Haidar yace " eh Dad, cikin fushi sanata yace " dan ubanka baka da hankali ne bakaga zab'e ya kusa ba, gashi nan sbd da sakarcinka kana neman ka watsar min siyasata danayi shekara da shekaru ina ginawa, ya kai dubansa ga sauran mutane yace " meye shawararku yanzu akai ?
Babban yaronsa yace " gaskiya ranka ya dad'e kar muyi wani motsi yanzu saboda idon jama'a yana kanmu, yaron zamu nemo musa ya k'aryata kansa, yace kud'i aka biyashi dan ya b'ata maka suna kaga daga nan zamu k'ara samun d'aukaka, kowa ya yarda da wannan shawara.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.