Gadar Zare Complete Hausa Novel
Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt
Chapter 26 of 42
Zuciyar Ja'afar ta k'ara yin zafi yaji kamar zai mutu, a harzuk'e yace " dolenki ki aure ni Fateeha matuk'ar kina raye ina raye baki da wani miji daya wuce ni, ya kalli Khamal wanda shiru kawai yayi zuciyar sa sai tafasa take, yace " kai kuma katon banza, matsiyaci zaman uwar me kakewa mutane anan, banza sakarai marar zuciya, uban yarinya yace bazai baka 'yarsa ba, amma dayeke kai maye ne ka nace, " dalla Malam rufewa mutane wannan k'azamin bakin naka, kai har zakayi maganar rashin zuciya, maye kawai wanda baison ciwon kansa ba, zuciyar Khamal ta k'ara hasala ganin yadda Fateeha ke ci masa mutunci akan Khamal, kuma yak'i tanka masa, ya kai hannu zai ci kwalar Khamal, cikin zafin nama Fateeha wacce bak'in ciki yayi mata katutu ta zabga masa zafafan mari,gaba d'aya hankalin jama'ar dake zaune yayo kansu, idonta yayi ja ta nuna masa hannu tace " wallahi koda maza sun k'are babu abinda zanyi dakai, ta nuna masa hanyar fita tace " get out from here, kad'an ya rage numfashin Ja'afar ya fizge tsabar firgicin daya shiga, lokaci ya d'auka yana kallanta da mamakinta, yace " ni kika mara akan wannan jakin matsiyancin, a tsawace tace " get out, da k'arfi babu wanda baiji ta ba, kai ya girgiza ya kalli Khamal yace " zaga ni, murmushi Khamal yayi yace " aini d'an gata ne, dan ina damai shigar min, kaga kuwa idan kana mayyi maka kai baka yi, tsaki Fateeha taja, ta rik'o hannun Khamal, sai da ta taka k'afar Ja'afar sunnan suka fice, suka bashi zuciyar sa kamar zata tarwatse.
Bayan kwana biyu zuciyar Ja'afar ta kasa akan abinda ya faru tsakanin shi da Fateeha, duk yadda yaso ya yakice ta daga zuciyar sa amma ya kasa, gashi idan ya kira ta a waya bata picking, babu abinda yake san gani kamar kyakykyawar fuskarta, ya rasa yadda zanyi, dan haka ya shirya a falo ya zauna kasancewar falon ba kowa, ya aika mai aikinsu ta kira amma fir tak'i zuwa, yayi aiken duniya tak'i zuwa, mik'ewa yayi cikin sanyin jiki zai tafi, Dady ne ya shigo falon ganin Ja'afar yasa shi sakin fara'a, da sauri Ja'afar ya nufe shi, ya gaida shi, ya kalle shi yace " yau she kazo, ko har kun gama da Fateehar ne?
Murmushi Ja'afar yayi yace " yanzu nazo ban iske kowa bane shiyasa zan tafi, Dady yace " zauna bari na shiga ciki na turo maka ita, dad'i Ja'afar yaji dan ko bakomai ya ganta koda zaginsa zatayi, murmushi yayi had'e dayi masa godiya, a d'aki ya same ta yace " kije falo Ja'afar yana jiranki kuma minti 2 na baki, idan ba haka ni da ke ne, ya juya, direct kitchen ta nusa, sob'on (zob'o) da Momy ta had'a ta d'auko, ta nufi inda yake zaune, sanye yake cikin farin boyel da gani sabo ne, tana zuwa bata yi wata-wata ba ta juye masa zob'on a jiki, da sauri ya mik'e yana kallonta ta kalle shi tace " wai kai wanne irin maye ne marar zuciya, ko dai kare ya d'auke maka ne?
Shiru yayi kawai yana kallonta, karka k'ara zuwa gidan mu idan kuma ka sake ka k'ara dawowa wallahi sai nayi maka abinda yafi haka dan harka mutu bazaka manta ba, murmushi yayi yace " ko k'in k'i ko kin so baki da wani miji daya wuce ni, kallon sa tayi shek'ek'e tace " wallahi matuk'ar Khamal yana raye bazan tab'a auren ka ba, a hasale yace " lalle kuwa Khamal zai mutu koda bai shiryawa mutuwar ba, lokacin barin sa duniya yayi, ke da kanki kikace idan baya raye zaki aure ne kinga kuwa dole ya mutu, ke da kanki kin jawo masa mutuwarsa kusa, bakin ki ya jawowa masoyinki mutuwarsa a kwana kusa daga yau daga wannan lokacin ki fara k'irga kwanakinsa na mutuwa, kin jawo masa bala'i sai saka shi kukan mutuwa, sai yayi tsere da mutuwar sa, sai na k'ulla masa *GADAR ZARE*, sai na ya tsani ratuwarsa, sai tsani duniya da abinda ke cikinta, wallahi hatta ke sai ya tsane ki Fateeha, kwalar rigar sa taci ta zaro idanuwa waje tace " wallahi k'arya kake Ja'afar babu abinda zai same shi sai alkhairi, Allah yana tare da, kuma ka sani komai za'a Khamal bazai tab'a tsana ta ba, kamar yadda nima ko rayuwa ta za'a cire min bazan tab'a rabuwa dashi ba.
Dariya ya tuntsure da ita yace " akan wannan lusarin jakin kike wannan haukan, hannu ta d'aga zata kifa masa mari taji caraf an rik'e hannun ta baya, taji saukar wasu fitananun marika, kuncinta ta rik'e ta juya a firgice Dady ta gane tsaye a matuk'ar hasale sai huci yake, kamar mahaukaci zaki ya fara..........
MOMYN ZARAH
[16/11, 03:07] +234 706 099 2528: ```GADAR ZARE!!!```
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
16
Ya fara k'ok'arin ball da ita, da sauri Momy ta rik'e shi, cikin b'acin rai tace " karka soma dukan min 'ya akan wani katon banza, kai a ganinka Abban Ja'afar zai iya marin d'ansa ne koda kai ya mara?
shima a fusace yace " wallahi Zainab ki fita daga ido na inba haka ba, ranki zaiyi masifar b'aci, "wani kallo Momy tayi masa murya ta a matuk'ar fusace tace " wallahi muddin ina da rai da lafiya a doron k'asa bazan tab'a bari Fateeha ta rayu cikin bak'in ciki ba, koda kuwa hakan na nufin rabuwar mu da kai, tana karasa fad'ar haka ta kama hannun Fateeha fuuuuuuuuuuuu suka yi ciki, ranta a b'ace zuciyar ta tamkar zata tarwatse.
Bayansu Dady yabi da wani kallo me cike da alajabi da mamaki a hankali kuma ya maida kallon sa ga Ja'afar dake tsaye yana kallonsu cike da takaici zuciyarsa na masa wani irin tsalle tamkar zata basa masa kirji,
muryar Dady a raunane yace " kayi hak'uri Ja'afar kasan yadda halin mata yake, murmushin yak'e Ja'afar yayi domin shi kad'ai yasan yadda yake jin kansa
kana yace " ba komai Dady, sallama suka yi sannan yabar gidan koda yaje gidansu a matuk'ar haukace ya shiga gidan kai tsaye part d'insa ya nufa ya sona cire kayan jikin sa ya bud'e washing machine ya zuba ya soma sintiri a d'akin yana had'a abubuwan da Fateeha take masa akan wani banza cima kwanace marar aikin yi jobless me zaman banza sosai ya dad'e yana zarya da saka da warwarar yadda zai salwantar da Khamal daga duniya kafin daga baya wata idea tazo masa, dariya ya saki , had'i dayin murmurshin mugunta ya ware hannushi duka yana dariyar samun mafuta had'e da shigewa bathroom.
Bayan kwana biyu tafiya takama Dady zuwa Abuja wanda a kalla zai yi kamar sati kafin ya dawo .
Yayin da a hankali kuma tafiyar Khamal Saudia ke k'ara matsowa wanda kwata kwata Fateeha batason tafiyar tashi dan wani lokacin har kuka take masa, ta rasa dalilin dayasa hanklinta yak'i kwanciya akan tafiyar Khamal bayan farin ciki ya kamata yayi, tun daren jiya sukayi da Khamal zai zo gidan su, ganin mahaifin ta baya gari,
ta shigo dashi har parlour bak'i, bayan Khamal ya shiga cikin wata rantsantsiyar shadda gizna, zama yayi a d'aya daga cikin kujerun dake falon, ya kafeta da ido, yayinda hannunta ke cikin nashi, maganar tafiyarsa yake son mata amman baya son abinda zai tada hankalin ta, itama shi take kallo zuciyarta na wani irin bugawa idan akwai abinda tafi so da k'auna a duniya yana bayan Khamal tana yi masa son da ita kanta bata san yadda zata misalta shi ba, a hankali ya bud'e bakinsa yace " Fateeha next week In sha Allah zanbar k'asar nan dan angama komai na tafiyata saboda... tun kan ya k'arasa magnarsa, hawaye suka cicciko sun fara bin fuskarta, zuciyarsa ta shiga bugawa da sauri da sauri ya rud'e,
kasa magana yayi illa jikinsa daya rungumo ta tsam, ya shiga rarrashin ta yana shafa bayanta muryasa a matuk'ar sanyaye yasoma magana " please Fateeha ki natsu ki kwantar da hankalinki wlh kece karfin tafiyar nan tawa ,kusan sbd ke zanyinta domin cigaban rayuwarmu kin dai ji abinda Dad d'inki yake fad'a akaina, ko bakya son cigabanmu ne?
ya k'arasa maganarsa yana sake k'amk'ameta.. muryarta na rawa tace " nifa..nifa bawai tafiyarka ce banaso ba rashin ganinka daba zan dinga yi bane na wani lokaci shine damuwata amman kamin alkwari duk rintse duk wuya bazaka barni ba bazaka juya min baya ba Khamal ina mugun sonka, rayuwata da komai nawa naka ne mallakinka ne Khamal.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.