Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 40 of 42

"Ka raka ni ina, tab sha zamanka bana gayya, Teemah tafi 1hr zaune a park tana jiran Zaid, dan haka koda yazo bak'aramin rarrashi ba kafin ya shawo kanta asha love, nan ya shayda mata maganar iyayensa suna san ganin ta dan haka ta shirya gobe zai kaita.

Washe gari wajen 5:00pm Zaid yakai Teemah gidan su, a falo ya ajiye ta yace " ina zuwa tunda Teemah ta shigo gidan su Zaid kanta ya buga dan ganin girma da kuma tsaruwar gidan, aranta tace "Allah kad'ai yasan mak'udan kud'in da aka kashe wajen tsara gidan, tana cikin wannan tunanin taji Zaid yace " Teemah meet my parents, ya fad'a yana nuna mata Ammi da Abba, a hankali ta d'ago kai ta kalli Ammi da Abba ganin mutumin da take gani a gidajen TV tsaya a gabanta yasa k'irjinta bugawa da k'arfi, murmushi tayi tana gaida Ammi da Abba tana daga zaunen akan kujera faran-faran Ammi ta amsa bata nuna mata alamar komai ba, ta karb'e ta hannu bibbiyu, Ammi ta umarci 'yan aiki dasu kawo mata kayan motsa baki aiko aka cika mata gabanta da kayan ciye-ciye fal, wani abun ma bata tab'a ganin sa a rayuwarta ba, babu kunyar komai cike da wayewa taci ta k'oshi ta cika cikinta fam, a hankali Ammi ta kalli Zaid da Abba, shi kanshi Zaid sai da yaji baiji dad'in abinda Teemah tayi ba, murmushi Ammi tayi tace " ya sunanki? kai tsaye tace " Teemah, "ok Teemah a wacce unguwa kike sannan suwaye iyayen ki? da k'arfi gaban Teemah ya buga zuciyar ta ta shiga lugude gami da harbawa, kafin ta gama nutsuwa taji Abba yace " ke 'yar asalin wanne gari ce?

Kasa magana tayi ta shiga in'ina sake kallon Zaid da Abba Ammi ta kuma a karo na biyu tayi murmushi, cikin rawar murya Teemah tace " ni mareniyya ce ni kai na ban san iyaye na ko garin ba, a gidan marayu na taso, ta fad'a tana share kwallar dake zubo mata, take tausayin Teemah ya cika zuciyar Zaid da Abba amma Ammi murmushi tayi irin nasu na manya tace " ikon Allah wanne gidan marayu kenan, cikin rawar baki Teemah ta fad'a musu gidan marayun data taso, daga Abba har Ammi sai da gaban su ya fad'i dan gidan marayun da aka d'auko Abraham ne, cikin rawar baki Abba yace " ok badamuwa, zamu bincika,sai bayan magrib Teemah tabar gidan su Zaid cike da kayayyaki da kud'i da Ammi da Abba suka bata.

A motar Zaid da Teemah zaune babu mai yiwa wani magana kowa da abinda yake sak'awa a ransa, ajiyar zuciya Zaid ya sauke a hankali ya kalli Teemah yace " mai yasa baki tab'a gayamin ke marainiyya bace, a hankali tasa hannu tana goge hawayen fuskarta tace " ina gudun karna rasa kane, ina mugun sanka Zaid idan ka barni wallahi mutuwa zanyi murmushi Zaid yayi yace " ke! ya kike irin wannan maganar ne, waya ce miki ni zan iya rabuwa dake? "Ni dai please ta fad'a tana rik'o hannunsa gam cikin nata yayin da hawaye ke zubo mata, wani mugun shocking Zaid yaji kasancewar yau ne rana ta farko da mace ta tab'a shi, taci gaba da cewa " dan naga kamar iyayenka bazasu karb'e ni ba, " saboda ya tambaye ta? "alama na gani kuma kaga ku masu arzik...... hannu ya d'aga mata yace " ni iyaye na ba haka suke ba, ba irin masu kud'in yanzu bane dan suna da fahimta da kuma adalci, abinda kikayi ne kawai bai kamata ba, " kasan ni ban san komai akan rayuwa ba, dan ban san gatan iyaye ba dole wani abun sai ana yin min uziri tunda kaga ba'a hannun kiyaye na ta taso ba basu suka yi min tarbiyya ba, jikin Zaid yayi sanyi, a hankali ya shiga kwantar mata da hankali, harya kaita ya ajiye.

Zaid yana komawa gida Ammi ta tada falli bata son Teemah wai ta waye da yawa kuma bata da tarbiyya, kayi ta lallashen amma fir tak'i babu yadda Mukhtar da Abba da Zaid basu ba amma ta rufe idonta tace " ya daina nemo wata amma banda Teemah akayi ta abu kusan wata d'aya amma tak'i yarda Zaid duk ya rame ya shiga damuwa da takura amma Ammi ko a kanta da ta kafe ta k'ek'ashe k'asa akan ita bata son Teemah, dakyar Abba ya shawo kanta ta yarda akan tana da sharad'i, Abba yace " bakomai sunji sun yarda, da safe Abba ya kira Mukhtar da Zaid duk suka zauna bayan sun gaida iyayen nasu, a hankali Ammi ta k'arewa Zaid kallo taga mugun ramar da yayi take tausayinsa ya shige ta, a hankali ta kalle shi ta kira sunansa "Zaid! cikin nutsuwa ya d'ago kai yana kallon ta had'i da amsawa, "na yarda ka auri yarinyar nan Teem.... ai kafin ta k'arasa ya nufe ta ya rungume ta "thank you, Ammi you so much, a hankali ta zame jikinta ta b'ata fuska tace bisa sharad'in d'aya gaban Zaid ne yayi muguwar fad'uwa k'irjinsa ya shiga bugawa dan yasan tunda Ammi ta had'e rai maganar babba ce, maganar sa na cracking yace " wanne irin sharad'i Ammi.............!

MOMYN ZARAH

```GADAR ZARE!!!```

_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_

~NA~

*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_

*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*

Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh

Gmail: Jiddarh012@gmail.com

Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh

*GARGAD'I*

```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```

~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*

*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*

23

Fuska ta k'ara b'atawa dan ya d'au maganar ta da mahimmanci tace " so nake ka auri mata biyu a lokaci d'aya a firgice Zaid ya mik'e yace " what Ammi? Mukhtar ma a firgice ya d'ago kai yana duban Ammi wacce tayi kamar ba itace tayi maganar ba taci gaba " zan barka ne ka auri zab'in ranka matuk'ar nima zaka karb'i nawa zab'in idan kuwa ba haka ba sai dai ka hak'ura da Teemah, a hankali ya durk'usa a gabanta ya shiga bata hak'uri akan tayi kyale shi, shi bashi da burin mata biyu amma sam Ammi tak'i, daga k'arshe ma mik'ewa tayi tace " idan ka shirya kayi min magana, da sauri ya rik'o k'afafunta dan ganin yana niyyar yin biyu babu, yace " na yarda Ammi, amma ban san inda zan k'ara nemo wata ba wannan d'in ma da kyar na samo ta, " ok to shikenan ni zan samo maka, " to please Ammi ki bari na fara auren Teemah tukunna, in yaso bayan wata uku sai na auri zab'in naki.

" ko kuma ka auran zab'in nawa in yaso daga baya saika auri naka zab'in, "please Amm.... da sauri ta d'aga masa hannunta tace" nifa ba matsa maka nayi ba, zab'i na baka, ganin damar kane kabi zab'in ko kuma ka hak'ura, shiru Zaid yayi kansa a sunkuye ya kasa cewa komai, ganin haka yasa Abba cewa tashi kaje kayi tunani tukunna, idan ka gama shawara sai ka dawo, a hankali ya d'ago kai yana kallon iyayen nasa, cikin sanyin murya yace " bakomai Abba na amince, murmushi Abban yayi yace " Masha Allah ka sanar da ita nan da wata d'aya za'a d'aura muku auren dukkan ku, kai ya k'ara risinawa yace " nagode, " tashi kuje Allah yayi muku albarka, " Amin ya Allah suka ce suna barin parlor'n.

Zaid na shiga ya fad'a gado ya rufe idonsa ya fara tunanin ta ina zai fara sanarwa da Teemah wannan maganar, a hanlaki Mukhtar ya dafa shi " friend kayi hak'uri kaji, in sha komai zaizo mana da sauki, ni dai ina mai baka shawara da kayiwa Ammi da Abba biyya, a hankali Zaid ya bud'e idonsa had'i da sauke ajiyar zuciya, " to yanzu Friend ta ina zan fara tunkarar Teemah da wannan maganar?

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.