Complete Hausa Novels

Gadar Zare Complete Hausa Novel

Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt

Chapter 28 of 42

Sosai Khamal ke kukan mutuwa yana ihu kamar ransa zai fita, yace " haba bros bai kamata kayi min haka ba, bai kamata ka nemi hallaka ni akan mace ba, kai d'an uwana ne na jini, kai kad'ai gare ni, duk duniya bani da kowa sama da kai idan dan Fateeha ce meyasa baka sanar dani ba?

" me yasa baka sanar dani itace wacce kake so ba?

"haba my only blood bros, why Hamza?

ya k'ara fashewa da wani irin mahaukacin kuka mai cin rai da tab'a zuciya.

Hamza ko cikin farin ciki ya kashe wayar ya juya fuskarsa d'auke da murmushi, yana juyawa yayi arba da Hajiya wacce tunda ya fara waya da Khamal take tsaye akanshi tana sauraran sa, babu abinda jikinta keyi sai kerrma, gumi ya gama jik'a mata duk ilarin jiki, kamar wacce akayiwa wanka da ruwa, cikin tsoro da firgice take nuna Hamza da yatsan hannunta bakin ta na rawa tace " Ham...za Ham..za.. kai ne kuwa?

" Kai ne ka yiwa d'an uwan ka uwa d'aya uba d'aya haka, Hamza meka fara sha, ?

"mai ya sameka, meke damun Rayuwarka akan mace Hamza?
, kai ta fara girgizawa cikin tashin hankali tana "' a'a wannan bakai bane Hamza , bakaine ainahin Hamza na ba.
, "Hamzan dana sani na rik'a da hannuna jikana ba haka yake ba, murmushi yayi ya tako a hankali har gabanta ya tsaya ya zuba mata ido kana yace " Ok kinji abinda nace kenan?
, cikin tsawa yace " amma duk da kinji kika tsaya a gaba na kina yimin tamboyin banza da wofi tare da surutan iska cikin kuka Hajiya ta rufe shi da duka tace " Allah ya isa tsakani na dakai, bazan tab'a yafe maka ba, dan ba irin wannan tarbiyyar na baka ba.

Dariya yayi yace " da kinji nace ki yafe min ne, Hajiya tace" kaci amanar mu Hamza, ka yaudare mu, ka munafurce mu, kai mugu ne mai fuska biyu mai mugun nufi a zuciyarsa, azzalumi, in sha Allahu amanar mu daka ci bata ta tab'a barinka ka rayu cikin farin ciki da kwanciyar hankali ba.
"kuma alfarmar Ubangiji ko Khamal yana raye ko baya raye baza ka tab'a mallakar Fateeha ba, matuk'ar ina raye in sha Allah bazan tab'a bari Fateeha ta zama matarka ba.

A zuciye Hamza yayo kanta ya shak'e mata wuya yana gurnani yace" aiko lalle zaki mutu, kinyi ganganci Hajiya, dan duk wanda ya nemi yimin katanga wajen cikar buri na, to zan kawar dashi, daga doron k'asa batare da shakka ko tsoro ba.
Hajiya ta shiga haure-haure da shure-shure tana kokuwa da Hamza amma ina, bai sake ta ba sai da yaga ta daina motsi da numfashi alamar rai ya fita.

Gaba d'aya Idonta duk sun firfito waje,sunyi tulu tulu alamun shan wahala numfashin ta ya d'auke, ya wurgar da ita gefe, ya tsugunna a gabanta yana dariyar mugunta yace " sai ki hana ni mallakarta, shima yana hanyar biyo ki, gawarta ya d'auka yakai kan gadonta ya kwantar da ita, ya ja mata bargo ya lullub'e ta kamar mai bacci, shi kuma ya nufi d'akisa ya kwanta yana tunanin abinyi.

Cikin 2hrs labarin Khamal ya bazu a ko'ina a cikin kasashen duniya duk tashar daka kunna zancen akeyi, Aljazira, BBC, CNN, da sauran tashoshi, aiko nan da nan labarin ya cika Nigeria, Dadyn Fateeha na zaune a falo Abba ya kira shi yace " su kunna BBC ba musu Dady ya sauko falon k'asa inda Fateeha da Momy ke zaune suna hira, a hankali ya d'auki remote ya kunna TV, aiko pic d'in Khamal ya bayyana a jikin plasma, da sauri Fateeha ta mik'e tsaye jikinta na rawa ganin an rubuta Breaking news, (Nigerian baller he is an criminal ) live aka shiga nuna sanda aka kama koken a kayansa, har zuwa inda aka kai shi prison, wata mahaukaciyar k'ara Fateeha tasa ta zube a k'asa sumammiya.
cikin firgici Dady da Momy suka yi kanta, da gudu Momy ta d'auko ruwa tashiga zuba amma babu alamar motsi, aiko da sauri Dady ya sungume ta yayi mota, da gudu Momy tabi bayansu, suna shiga hospital direct emergency aka wuce da ita, Doctors sun kai 5 a kanta amma a banza, sai da Fateeha tayi 10hrs a hospital sannan ta farfad'o tana ihu, da sauri Momy da Dady sukayi kanta cikin kuka tace " wallahi Momy he is not criminal, k'arya suke yi masa sharri ne, nasan halinsa, bazai taba aika haka ba. .....ta fashe da wani irin mahaukacin kuka Momy ki taimake ni wlh sherri aka masa nasan Khamal d'ina bazai taba aikata mugun aiki irin wanna ba.
shafa kanta Momy ta shiga yi, tana rarrashinta, rungume Momy tayi tana sauke ajiyar zuciya, kusa da ita Dady ya zauna cikin sanyin jiki, jajayen idonta ta d'ago tana kallonsa tace" ka gani ko Dady?
Kaga abinda kaja ko, a sanadinka Khamal zai rasa rayuwarsa, mai yasa Dady, ta k'ara fashewa da wani sabon kuka, hawayen masu zafi ke tsiyayo mata.

Jikin Dady a matuk'ar sanyaye ya jawo ta jikinsa ya rungumeta yace " kiyi hak'uri Mama na, ba laifi na bane k'addararsa ce haka, in sha Allah zai fito, cikin kuka tace" Dady kana ji fa, sunce kashe shi zasuyi, " karki damu Mama na in sha Allah I will try my best, kinji, Momy dake zaune a gefe tana kallonsu hawayen tausayin tilon 'yarta na zubo mata.

Umman Ja'afar ko tunda taji abinda ya faru hankalinta yak'i kwanciya dan har ga Allah su Abba Ja'afar take zargi,
cikin tashin hankali ta nufi d'akin Abba tana kai kanta zata shiga tajiyo hirar Abba da Ja'afar, cikin sanyin jiki Abba yace " gaskiya na tausayawa yaron nan dan nasan bazai iya aikata irin wannan laifin ba, shima Ja'afar cikin sanyin jikin yace " nima bana tunanin zai iya aikata haka, dan gaskiya yaron yana da hankali da nutsuwa ina ganin dai ya had'u ne kawai da sharrin mak'iya, Abba yace " to sai dai mu taya shi da addu'a, Umma dake tsaye ta juya cikin mutuwar jiki.

Washe gari tunda sassafe Hamza ya fito k'ofar gida yana kukan mutuwa yana ihu da kururuwa yana d'ibar k'asa yana zubawa a jikinsa, mutane suka taru fal a kansa, suna tambayar shi lafiya, cikin kuka yace " sakamakon abinda ya samu Khamal zuciyar Hajiya ta buga, harta mutu ma, aiko ' yan unguwa sun girgiza da jin mutuwar Hajiya dan sun san macece mai kyawawan halaye, sunyi kuma masifar tausayawa Hamza dan sun san bashi da kowa sai Khamal da Hajiya gashi kuma duk babu su, bayan anyiwa Hajiya wanka da sutura dakyar aka raba Hamza da gawarta dan bori ya hauyiwa jama'a baza'a fita daita ba yana kuka yana kari .

Kwanan Fateeha d'aya aka sallamo ta daga asibiti, tana dawowa ta shirya ta fita batare data bari kowa ya ganta ba, dan tasan idan aka ganta baza'a bari ta fita a halin da take ciki ba.
direct gidan su Khamal ta wuce, Fateeha na shiga ana k'ok'arin fitowa da gawar Hajiya Hamza nata ihu da birgima, ai Hmaza na ganin Fateeha ya k'ara fashewa da kuka yana birgima, ya tubure, a slow Fateeha ta k'arasa shiga idan,tsayawa kawai Fateeha tayi ta k'urawa Hamza ido.

Ido Hamza ya zuba mata yace " Fateeha bani da kowa yanzu ba Yaya Khamal ga Hajiya ma ta tafi ta barni a dai-dai lokacin dana fi buk'atarta, sai lokacin Fateeha ta fahimci mai ke faruwa, durk'ushewa tayi a wajen ta shiga kuka kamar ranta zai fita, ba k'aramin tashi hankalin Hamza yayi ba ganin Fateeha na kuka, a hankali ya tsaida kukansa ya rarrafa zuwa gabanta, ya shiga lallashinta.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.