Gadar Zare Complete Hausa Novel
Reading file: ```GADAR ZARE BY HAUWA A USMAN JIDDA.txt
Chapter 36 of 42
Haka muka taso cikin gata, da so ga kulawar da muke samu, yayinda duk duniya ta shaida mu 'yan biyu ne ciki kuwa harda kakannin mu, tun tasowar mu Allah yayi Abraham d'an k'arya ne, Allah ya sanya masa girman kai da wuk'anci kwata-kwata baya son talakwa shi k'amar su ma yake yake ji gashi da tsinannan san matan tsiya tun muna yara yake soyayya, gashi da son gayu dan Abraham d'an kwalisa ne kaya da turarurrukan sa, takalma, agoguna ma abin kallo ne dan shi komai sai mai tsada first class yake sawa, yayinda ni kuma kwata-kwata mata basa gaba na, haka ma kayan mai tsada da k'arya dan ni komai na samu sawa nake ba ruwa na, haka ma a b'angaren hali na iyaye na na d'ebo dan Allah ya sani bani da k'amar talakawa dan lokuta da dama sanda ina yaro cikin masu gadi da drivers d'in mu nake cin abinci, ga ni da taimako da tausayi, haukan ko bak'aramin soyayya ya k'ara jawo min a wajen iyayena da mutane ba.
Haka dai muka ci gaba da girma yayin da munanan halin Abraham na k'aruwa iskancin sa na k'ara kankama, ga shi da shaye-shaye da son zuwa club, yayinda da halin da Abraham ya saka rayuwarsa yayi mugun damun iyayen mu, sun sha yi masa fad'a da nasiha amma a banza, halin Abraham yasa kwata-kwata bama shiri tun muna yara, bama tab'a zama inuwa d'aya nida shi ko'a makaranta kowa harkar gabansa yake ba mai shiga harkar wani, lokacin da muke primary school Allah ya had'a jini na da MUKHTAR.
Mukhtar ya kasance d'an mai gadin gidan mu ne, halayyarmu ce tazo d'aya ni da shi dan haka muka k'ulla abota da Mukhtar duk duniya bani da wani aboki kamar Mukhtar shine babban aboki na a duniya, Allah ya sani ina mugun son sa, shima Mukhtar haka, ganin haka da iyaye na suka yi yasa suma suke son Mukhtar har suka mayar da shi d'an gida kamar d'an su, dai-dai da makaranta d'aya Abba ya samu da Mukhtar komai tare yake yi mana dashi bai tab'a ban-banta mu ba, duk duniya idan da abinda Abraham yafi tsana a duniya to bayan Mukhtar yake, kwata-kwata baya san sa baya son ganin sa, dan haka nima sama-sama muke da Abraham, dan ba wani shiri muke da shi sosai ba, musamman ma da halayyar mu ba d'aya dashi ba, kowa da yanayin rayuwar sa.
Haka dai muka gama Secondary school, Abba ya fitar da mu waje karatu mu duka uku, ni ina karantar Business Adminstration, Mukhtar yana karantar Low (Barrister) Abraham yana karantar Medicine, cikin haka har muka gama masters d'in mu kowa ya fito da kwali mai kyau, haka ma b'angaren karatun islama babu wanda acikin mu bai sauke Qur'an ba, muna girma kyawawan halayenmu ni da Mukhtar na k'ara fitowa, haka munayen halayen Abraham na k'ara bayyana dan yanzu ya zama cikekken mazinaci d'an shaye-shaye, a b'angaren kyawawan halaye kuwa idan bance Mukhtar ya fini ba to ban isa nace na fishi ba, dan tunda nake dashi ban tab'a ganin yasa koda k'ananan kaya bane kullum yana cikin manyan kaya, koda muke karatu a waje Malam ake ce masa.
Duk duniya bani da aboki sama da mukhtar, he is my best friend, yasan komai nawa nima nasan sirrin sa, duk inda zama tare muke zuwa ko kaya kala d'aya muke sawa, komai namu tare sai ya zama na kamar shine Hassan d'in nawa ba Abraham ba, muka ware Abraham gefe babu ruwanmu dashi daga ni sai aboki na Mukhtar muke sabgar mu,babu yadda Abba da Ammi basuyi dan ganin rayuwar Abraham ta gyaru ba amma ina yayi nisa, iyayen mu sun sha kukan bak'in cikin Abraham amma a banza dan ko a kansa, duk abinda Abraham yakeyi su Abba basu tab'a kyamar sa ba, basu tab'a nuna masa wasu alamo ba, sai ma jan sa da suke yi a jikinsu, kozai gyaru, ganin mun girman mun gama karatun mu mun zama cikakkun mutane ne yasa Abba da Ammi suka matsa mana akan maganar aure, kowa ya fara kame-kame dan daga ni har Mukhtar babu mai budurwa dan bama mu tab'a tsayar da mace ba balle soyayya, shiko Abraham babu ma mai saka shi a lissafi.
Abba ya samarwa Mukhtar aiki a federal government, shiko Abraham Abba niyya yayi ya gina masa asibiti nashi na kansa, ganin rayuwar da ya zab'a yasa shi yi masa banza, haka ganin Business na karanta yasa Abba mik'a min gaba d'aya ragamar kasuwancin sa tun daga nan gida Nigeria har zuwa na k'asashen waje, komai ya dawo hannuna, Abba ya mayar da sunan duk wani company sa da sunana da kuma signing d'ina haka ma duk wasu kadarorunsa da account dinsa na bank ya zama nawa, Abba ya mik'a komai gare ni, ya kuma sanarwa da Abraham cewa saboda shi ya kauce hanya, kak'i nutsuwa kasan ka girma ya sashi yin haka dan bazai mutu yabar duniyar daya sha wahala da gwagwaryar duniya wajen tara ta watse ba dan haka ya mik'awa Zaid komai, ya kuma k'ara da cewa duk ranar daya nutsu ya dawo dai-dai yabi hanya ta gaskiya shima zai raba komai da kansa ya bashi.
To fa! wannan abu ya shi ya lalata komai, shine mafarin komai, shi tarwatsa komai ya kuma yi sanadin faruwar duk abinda ya faru, ya rora wutar tsana da k'iyayyata a zuciyar Abraham, harta kai kwata-kwata baya son gani na, ya tsane ni ko magana nayi masa baya amsawa sosai ya fara tunanin hanyar da zaibi dan ganin ya kawar da ni............
MOMYN ZARAH
[14/11, 02:55] Frd Din Fatima Saudia: ```GADAR ZARE!!!```
_(IT'S ABOUT DESTINY,HYPOCRITES, BETRAYALS, LIARS)_
~NA~
*HAUWA A USMAN*
_JIDDARH_
*🌈KAINUWA WRITERS ASSOCIATION✍🏻*
Facebook: Hauwa A Usman Jiddarh
Gmail: Jiddarh012@gmail.com
Wattpad: HauwaAUsmanjiddarh
*GARGAD'I*
```MATAN AURE KAWAI, BAN YARDA 'YAN MATA KO UNDER AGES, SU KARANTA BA```
~DEDICATED TO~
*AISHA A BAGUDO*
*BEST FRIEND FOREVER & EVER*
```ZAINAB ABDULWAHAB SHAGUMBA```
*~(UMMU AMAN)~*
21
Zaid kwance bisa makeken gadonsa mai kirar royal bed, yana tunanin ta inda zai fara neman matar aure don Abba ya matsa musu da maganar aure kusan kullum sai yayi musu maganar, shi gashi ko a cikin friends d'in su shi ba mai yawan magana bane, he is so silent & hand sum guy, dan Zaid yana matuk'ar kyau daga na fuska harna halitta, tunani yake amma ya rasa ta inda zai b'ullowa al'amarin, yana cikin wannan hali Mukhtar ya shigo d'akin d'auke da sallama.
Ganin Zaid baima san ya shigo ba balle ya amsa masa sallamar ba, ya sashi tsayawa a kansa yana k'are masa kallo yana murmushi , dan yasan tunanin me yake, a kusa dashi Mukhtar ya zauna amma har a lokacin bai ma san ya shigo ba, a hankali Mukhtar yasa hannu ya shiga jijjiga shi, aiko firgit ya dawo daga duniyar tunanin daya tafi, ya kalli Mukhtar fuskarsa cike da murmushi yace " Friend yaushe ka shigo?
Dariya Mukhtar yayi yace " tun d'azu mana, "kai haba amma ban san ka shigo ba, " toya za'ayi kasan na shigo bayan ka tsunduma duniyar tunani, murmushi Zaid yayi a karo na biyu ya shafa kwantacciyar sumar kansa yace " hmmmmm dan bai da san mai zai cewa Mukhtar ba, shima murmushi yayi dan yasan halin Zaid da muskilancin tsiya, ya kalle shi yace " kaji Class mate d'in mu sun had'a party ko?
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.