Best Hausa Novels

Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ribar Biyayya.txt

Chapter 37 of 39

Page 37.

Dan bude idonta tayi da sauri ta mayar ta rufe saboda hasken da ya kashe mata ido kokarin kara bude idon take amma maganganu take ji a nesa da ita.

Fatima fatima kina jina kin san ni kin ganeni? Dr zakiyya ke jero mata tambayoyi bata amsa ba adeeja ta shigo.

Kaman jiran shigowanta take ta fara samabtu yah sageer ina sonka ab zan juri ganinka da wata macen ba adda adeeja kiyi hakuri mutukar ina raye yah sageer mijina ne kiyi hakuri adda ina son mijina mutukar ina raye baza ki taba mallakansa ba duk da dumbin sonshi da nake hangowa a cikin idonki tabbas in na mutu ke kika fi kowa dacewa da shi da sauri adeeja ta fice a dakin. Ita kuma fatima ta koma bacci.

Kallon dr zakiyya sageer yayi yace meke faruwa da ita ne ? Murmushi tayi tace abinda ke ranta kenan kafin a mata aiki sambatu ne kawai da ta kuma farfadowa zata dawo normal cikin damuwa sageer yace that is when? Murnushi ta kuma yi tace soon kar ka samu damuwa ya gyada mata kai kawai.

Adeeja karkashin wani bishiya ta samu ta zauna tana rizgan kuka meke faruwa da ita ne wannan wani irin bala'i ne ta yaya akayi har tayi saken da fatima ta lura da son da take yiwa mijinta innalillahi wannan abin kunyan da me yayi kama lallai zaman bauchi ya kare a wajenta tunda har fatima ta gane halin da take ciki game da baba karami anya zata iya kara hada ido da fatima kuka take sosai ranta cike da dana sani.

Sai da ta kwashi awa uku tana bacci sannan ta farka wannan karon a cikin hayyacinta ta farka cikinta ta fara shafa taji wayam da sauri tayi kokari mikewa sageer dake fitowa daga toilet ne ya ankara da sauri ya karaso wajenta ya mayar da ita ta kwanta ganin yanda take cije lebe ya san cewan she is in pain zuwa lokacin sauran mutanen dake dakin sun san ta farka

Wayarsa ya ciro a aljuhu ya danna number din dr zakiyya cikin minti biyu ta shigo da yake tana asibitin duddubata tayi sannan tayi murmushi tace komi normal welcome back mommy twins waro kananan idanunta tayi wanda suka kara komawa ciki daya bayan daya take kallon kowa a dakin wanda duk murmushi ne a kwance a fuskarsu idonta ne ya sauka kan cribs din babies dinta

Lumshe ido tayi hawaye ya zubo daga idonta hawayene na farin ciki wai yau itace da yara har biyu saurin bude idonta tayi lokacin da taji duminsu a gefe da gefenta sageer ne a tsugune a kanta yana sakar mata murmushin shin nan me tsada kiss ya manna mata a goshi yace baby ga yaran mu nan da Allah ya bamu kyauta kin gansu nan masu kama dani. Har eyes din? Ta furta a hankali lokaci daya kuma ta kume bakin dan jin wani wari da bakin yake murmushi yayi Ya shafi kanta yaji dadi sosai da yaji maganan ta duk da abinda ta fara furtawa ya bashi dariya wato ita dai da maganan manyan ido shi bai ga aibin idonta ba they arw sexy wani murmushin ya saki yace har eyes din kafin ya tashi, daga tsugunon da yake yace adeeja miko mana silver bowl din nan da ruwa i think your tootbrush is in this drawer ya fadi hakan yana jan drawern ya zaro brush da toothpaste.

Now bari *Saifuddeen da Salahuddeen*😊 su bar mamansu ta huta ya kwashesu ya kai su crib dinsu adeeja ce ta kawo bowl din da ruwa ta ajiye zata taimaka mata ta tashi ya karaso yace no kar ki damu wannan aikina ne gefe ta matsa gabanta na cigaba da faduwa cikin kulawa ya tadata zaune ya kuskure mata baki sannan yasa brush ya brushing mata adeeja na tsaye tana kallonsu cike da sha'awan yanda yake bata kulawa abinda bata taba samu ba a wajen Hameed hana karya daren amarcinsu da safiyar ranan, juuyawa tayi ta fita daga dakin idonta cike da kwalla

Tea ya hado ya kawo mata tasha sannan ya fita ya kirasu hajiya da mama dake waje sannu suka yi mata sannan dr zakiyya ta bata magungunan ta Allah Allah take ta kara jin dumin yaranta kaman sageer ya sani ya dauko daya ya samata a cinyanta yace ga saifuddeen nan rikeshi kuji dumin juna for sometime kafin nan ya ba kaninshi waje shima murmushi tayi ta rungume abunta kallonshi take yaron kyakyawa dashi fari kal ga suma da ya sauko goshinshi kaman diyan larabawa hajiya ce ta matso tana rike da dayan tace fatima kin ga kyautar Allah ko biyu kyautar Allah wanda ba kowa yake bawa ba mikawa sageer dayan tayi ta karbi salahuddeen ko kadan basu da bambanci da juna identical twins ne( yah Allah ka bani🙏🏾😭)kallonsu take tana yiwa Allah tasbihi.

Kwananta biyar da haihuwa aka sallameta taji sauki sosai bakin nan ya bude sai surutu take in hajiya ta shigo ta samu tana zuba zata ce ke gafara can ki rufe mana baki ke da kika kusan lulawa da ragon mijinki a wajen ai babana ban san kai rago bane sai ranan daga kai har khadeeja duk na fiku jarumta ga wata likita ma me ragon zuciya me yiwa patient kuka.

Sai duk wajen anyi dariya dr zakiyya tace ai kam hajiya kin fimu jarumta fatiman ce ta kidima mu fatima tace iyyee ashe dai ana sona hajiya kema fa naji labarin kasa zuwa ki dubo autanki kika yi kina like da kofata yah sageer nafa kwace maka fada.

Haka sukq kasance cikin farin ciki da annushuwa gidan hajiya aka kaita inda sageer ma ya tattaro ya dawi gida abinshi shirye shiryen suna aka fara sosai sosai hajiya ta kira dukka ya'yanta da wanda ta haifa da wanda ba it ta haifa ba(yaran mijinta) tace duk kowa ya dawo ayi suna dashi dan anyi haihuwar da ba a taba gin irinta ba a dangi haihuwar biyu kuma daga autanta ai dole ma ayi gagarumin biki.........

_next page is for my _ _sweet adeeja tunda ni kadai ke sonta_☹

SAWWAMA QAWWAMA😘

SAWWAMA QAWWAMA😘

SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖

By Sawwama A.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.