Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 23 of 39
Page 22.
So?
Juyawa yayi yana kallonta saurin girgiza kai tayi.
Hadiye bacin ranshi yayi ya nunawa saurayin hanya yace malam dan Allah ka fita wannan daka gani matar aurece matata ce.
Wani murmushi saurayin me suna auwal yayi yace " haba malam wannan yarinyan ne zaka ce min matarka ce ta ina tayi kama da matar aure kawai kace min kaima kana ciki ne da farko nayi zaton kai yayanta ne amma yanzu na ga tsagwaran kishinta a idanunka kawai malam kowa ya gwada sa'arsa."
Wani shaka sageer ya mishi cike da bacin rai yace kai dan ubanka har ka isa inyi takara da kai akan matata in bana so in maka jinajina bane kayi gaggawan fitar mana a gida fatima matata ce tafi karfin kanana karnuka kaman kai."
Duk da irin shaka da yasha bai hana shi tambayan fatima wai da gaske ke matarsa ce?"
Girgiza kai tayi ganin wannan ne damanta na fusatar da baba karami duk da tsoron da take cike dashi.
Wani kukan kura sageer yayi ya dunkule hannu ya sauke mishi naushi a hanci sai ga jini hanci ya karkace hanakada shi yayi ya kwalawa mai gadi kira fatima na shirin guduwa ya cabkota.
Mai gadi na karasowa cikin fada baba karami yace " har yaushe xaku dinga bari ko wasu irin mutane na shigo mana gida ka fitar min da wannan jakin a gidan nan.
Janta yayi zuwa ainahin site dinsu tuni ido ya raina fata dan tunda take da baba karami bata taba ganin shi haka ba.
Wurgata kan kujera yayi yace" da izinin ubanwa kika fita? Baki da hankali kike yawo a titi da aure na da irin wannan shigan?
Doguwar riga ce a jikinta ta rolling gyale amma saboda firgici gyalen ya bar kanta yana wuyanta.
Cikin dakewa tace aure? Aure? Ni ba auren kowa kaina ka manta wannan lokacin shine dai dai da lokacin rabuwarmu
Ka manta yanzu na gama makaranta na mallaki hankalin kaina?
Ka manta a matsayin kanwarka kawai nake ba wani abu wai shi aure a tsakaninmu.
Meye laifina dan na tsaya da saurayi kana rabani da wannan kaddararen auren wani auren zan yi in auri wanda bai hada komi dani ba ,bai daukeni a matsayin kanwa ba rather mata.
Gaskiya ni kana kashe min kasuwa wallahi kai ba sona kake ba sannan masu sona kuma kayi kokarin rabani dasu ah ah wallahi ba zai yuwu ba ka barni inje inyi rayuwa da wanda yake sona dan ma kawai ka cuceni ka cuci masoyina ka rabani da budurcina amma mun yafe kawai.
Dagota yayi yana jijigata dan kalmominta dai dai yake da ana zuba mishi ruwan dalma yanda take kiran rabuwa a tsakaninsu take kiran wani da namiji bashi ba.
Stop it stop all this shit ki daina kira min wani shege kar ki kara mafarkin wai zaki rabu dani.
Itama cikin daga murya tace don me rabuwa tsakaniu ya zama dole ba yanda za ayi muyi zaman yaya da kanwa kaman da.
Rintso ido yayi ya wurgar da ita ya rike kanshi da hannu biyu saboda yanda yake sara mishi kallonta yayi da jajayen idonshi yace dont you get it i love you...........
Aunty A'ee wlcm😘
SAWWAMA QAWWAMA😘
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.