Best Hausa Novels

Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: Ribar Biyayya.txt

Chapter 14 of 39

Page 14.

Da Kyar Fatima ta saki ranta dan sosai tafiyan uncle ya bigeta da lallashin su bilkisu da addua ta sami kwanciyar hankali ta mai da hankalinta ga kartunta.
Yau take asabar ranan visiting dinsu duk dalibai na waje wajen 'yan uwa da abokan arzikinsu banda fatima da sai yau take ganin amfanin visiting kasancewan tunda take makarantan visiting dinta kenan gidan uncle dinta yau shine karo na farko taji abinda wanda ba a zo musu ba suke ji.

Wata junior ce ta shigo ta sanar da ita ana neman tashi tayi cike da doki uncle ya zo mata sai dai me tun daga nesa ta hango adeeja rungume da diyarta ga basket na abinci da bagco a gefenta, da gudu ta karasa ta rungume yar uwarta cike da farin ciki adda kece ta fada cikin nishi? Gyada mata kai tayi tace " nice teema ya kike ya makaranta ? Lafiya alhamdulillah ban diyata inji duminta ta karbe yarinyan hannunta tana sumbatar kyakyawan fuskanta.

Zama suka yi akan dakalin fatima ta kalleta tace " adda ya akayi kika zo nan wa ya kawoki?"
Ajiyan zuciya ta sauke tace tun satin can baba karami ya kira baba yace dan Allah in tambayi mijina yana so inzo in je miki visiting shine baba ya fada min wallahi sai da muka haura da hameed muka sakko ya barni amma yace ko sisi ba zai ban kudin mota ba tunda bai aikeni ba nace na yarda kaman baba karami ya sani sai gashi ya turowa baba da dubu goma wai a bani inyo kudin mota zuwa bauchi sai yasa driver ya kawoni makarantan niko ganin haka na sai kazar hausa me kyau da girma na miki pepper soup da miyan stew gashi nan ta nuna basket din abincin wannan kuma na dan miki siyayya ba yawa ta karasa tana karyar da wuya kallon yanda duk ta lalace fatima ke yi ba wannan kyan kaman da tace adda me yasa kika ba kanki wahala ai ina da komi miyar ce ma da kaxan naji dadinta sosai amma uncle in muka tashi zuwa siyayya yake min fiye da yanda zai ishe ni.
Karyar da wuya tayi tace haka yayi ta fada yaya zan yi wahala wai baki da buqatar komi sai kudi ne ma ya ban dubu biyar in kawo miki baya jin dadi ne ya sa bai zo ba.

A rikice fatima tace adda meke damunshi ya jikin nashi? Adeeja tace da sauki sai karfin jiki fatima ki rike mijinki dan baba karami na sonki sai yanzu nake da na sanin bijirewa iyaye dan ba karamin azabtuwa nake a hannun hameed da matarsa ba kar kiyi tunanin naji son baba karami ne ko daya baba karami ina jinshi kaman yayana ne kuma har yau duk abinda mijina yake min ina jin sonshi sosai sai dai tunanina akan auran yaro ya canza na gane in dai har kayi dacen miji shikenan ka more be it yaro ko babba babu bambanci abin kawai dacene.
Gyada kai fatima tayi tace yar uwa kiyi ta addua kawai kuma ki kara neman gafaran iyayenmu dan duk basu ji dadin abinda kika musu ba.
To yar uwata na gode. Haka suka cigaba da hira su bilkisu isa ma suka zo aka gaisa bata bar makarantar ba sai biyar suka rabu cike da kewan juna.

💖💖💖💖💖💖

Hutunsu fatima yayi dai dai da saura kwana biyar baba karami ya tafi tunda fatima ta dawo taga canji wajen baba karami yanzu ya rage shishige mata baya mata wannan wasan asalima bai cika zaman gidan ba yana ta shirye shiryen tafiyansa sai yamma yake dawowa fatima ta rasa gane me ke faruwa har daren tafiyarsa.

Bangaren baba karami kuma kuma ya zabi nesanta kanshi da fatima ne saboda bayan barinshi makarantar shi kadai ya san azaban da ya sha na rashin wannan wasannin da yake yi da ita shine har da ciwo ba yaso a koma gidan jiya ne shi da yake kokarin barin kasar ba ma garin ba balle in jarabar sa ta ciwoshi ya dawo.

Sai dai me ganinta kadai na kokarin dawo mishi da ciwon likita ya shawarce shi da ko yayane ya rage abinda ke mararsa ko da kuwa zai daurashi kan pill zai samu sa'ida tafiya ce zaiyi me dadewa he might not get the chance zuciyasa tayi na'am da shawaran likitan duk da bai san ya zai tunkareta ba shi yasa ya bari sai yau daren tafiyarsa.

Kwance take cikin ac daga ita sai vest da wandonsa saboda zafin da take ji har bacci ya fara daukanta taji alamun mutum na lallubanta.

Kut amma mutumin nan ya rainani tunda na dawo yake wani shan kamshi yanzu jarabarsa ta motso mishi zai zo yana lallubata fatima ke fadan haka cikin zuciyarta

Ta juyo tare da daura hannunta kam kirjinshi da nufin ingizashi ganin haka yasa shi tura hannunshi cikin.......

_kuna ganin ya kamata sageer ya take fatima kafin ya tafi?_

SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖

By Sawwama A.

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.