Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 18 of 39
Page 17
*Nenne dada kairuji Nenne da komoi dada k'ini en be mard'o dada be baba Allah beddu jutal bald'e a rink'a wannu go Amin barka, Amin*
Wanda yaji haushi ya yi nasa yaren😜
Ban mantaku ba:
_mmn gmby jdda_
_mom ilham_
_my daughter_
_da amaren bani nayi kaina ba fans_
Lallabawa tayi ta hau gadon taja bargo ta rufe jikinta cikin bacci hajiya taji an labta mata kafa a firgice ta farka bakinta dauke da addu'a. Ta lalubi switch ta kunna wutan dakin.
Waro ido tayi ganin fatima a dakinta daka mata duka tayi ta tashi tana mitsike ido tare da sosa wajen da ta daketa.
"Uban me kike min a daki?" Hajia ta tambayeta tura baki tayi tace toh ni ba tsoron kwana nake yi ni kadai a can ba".
Hajia tace maza tashi ki je ki tashi ladi ta tayaki kwana ko ke ki kwana dakinsu"
"Tab ni da wallahi ba zani ba a nan zan kwana kawai" ta kara gyara pillow zata kwanta hajiya ta janye pillon tabe baki tayi ta kwanta tare da yin pillow da hannunta kasa kasa tace "ni ba zan iya da masifar kin nan ba dadaren Allah"
"Me kika ce dan gidanku?"
"Ni fa ban ce komi ba kawai bacci nake ji kuma wallahi a nan zan kwana" ta ja bargo har ka hajiyan ma ta koma ta kwanta sai tsaki take ita kad'ai da fatima ta ga tsakin ba zai kare ba tsam ta mike tayi hanyan waje.
"Ina zaki kuma"ta tambayeta ba tare da ta dago daga kwancen ba.
Dakinsu ladin zani naga ke kin kasa bacci nima kuma kin hanani" shiru tayi tana tunanin in ta barta a dakin masu aiki ba ta yiwa autanta adalci ba har fatima ta dora hannunta a kan handle din kofan sai hajiya tace " dawo ki kwanta jarababbiya" komawa tayi ta kwanta a zuciyarta tace danki ne jarababbe.
Haka fatima da hajiya ke shan cabta dan kullum cikin fada suke fatima neman tsokana hajiya mita
Tun da sagir ya tafi yake kaucewa magana da fatima duk da tsananin son jin muryanta da yake yi haka kawai ya tsinci kanshi da jin nauyinta ya san bai mata adalci ba ya kamata ko da lafiyanta ya tambayeta amma ya kasa. Duk da yana jin komi wajen hajiya.
Fatima kam abin ba karamin haushi yake bata ba wato ya sami abinda yake so ko ta kudurta sai ta rama tana nan tana jiranshi daga nan har shekara goma
Ana saura kwana uku ta koma school ta shiga kitchen tayi ta kwabe kwaben madara wai zata yi su iloka da kakan dadi waye waye hajiya tazo ta sameta tayi ta masifa tace " haba kiyi kizo ki koma makaranta ni na gaji Allah Allah nake ki tafi wallahi" budan bakin fatima sai cewa tayi "baki san yanda nake ji kaman in janyo lahadi bane wallahi" abin dariya wai sai ga hajiya na mitan dan me zata ce kaman ta janyo lahadi wato ga masifafiya ko.
A haka ta cinye hutunta ta koma makaranta.
💖💖💖💖💖💖
Kin san Allah ni ba baby mashin na siyo ba haba wani irin ciki sai kace wata akuya wallahi tun wuri ki san yanda za kiyi dani ba yara zaki cika min ba wanda nake dasu sun isheni ina laifin dayan da kika samu kar ki manta fa ina da uku da zaliha hudu fa kenan uban waye zai kulan min dasu?"
Cikin sheshakan kuka tace "Allah, Allahn da ya baka shi zai kula da su hameed ba muyi haka da kai ba ni baka ce min ba zan dinga haihuwa ba haba hameed kar ka manta fa kai kana da uku ka zama adali mana"
" ohhhh kina gaya min ya'yana da na haifa da zaliha ba yaranki bane sai wanda kika haifa da cikinki toh ba zai yuwu wannan cikin zubdashi za ayi."
"Wallahi inda karyanka yasha karya kenan haba ace mutum kanshi kawai ya sani bayan tauyeni da kayi kasa ban karasa karatu ba ka aureni ka zubar min da ciki har sau biyi wallahi wannan karon kayi kadan sai dai duk abinda zai faru ya faru. "
"Haka kika ce ko toh shikenan zaki ga abinda zai faru mutuqar baki bi abinda nake so ba" fuuuu ya sa kai ya fita yayin da adeeja ta zauna shakaf akan kujera ta rike kanta tana wani irin kuka.
Zaliha ce ta shigo.........
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.