Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 17 of 39
Page 16.
*kun zama ni na zama ku komai in zanyi dole sai da ku*
*kun riga kun san weak point din Sawwam*
*kun san irin son da take muku bazata juri bacin ranku ba*
*toh gani na dawo amma dai ba kaman da ba still a can zaku karasa karantawa*
💖💖💖💖💖
_gareku aminan kwarai ko da a ko wani shafina zan ambace ku ba zai wadatar ba_
_Hassana danlarabawa_
_maman usuf_
_Halima sahad_
_feedohm_
_Hafsat sharif namcy_
Ina yinku sosai.
Kankantar da ido tayi cike da masifa sai kuma ta danne masifarta ta kama lallaminta ta shiga ruwan ganyen magarya da bagaruwa, haka tana mita tana komai tayi ta dauwainiya da ita.
Bangaren baba karami cike da wani irin nishadi ya tafi jinshi yake kaman ango ko da yake angon ne haka ya shiga cikin jirgi cike da farin ciki fuskarsa dauke da murmushi me kayatarwa sai shafa kanshi yake da sajenshi sai dai in ya tuno halin da ya bar zahran sa duk sai yaji hankalinshi ya tashi ga wani kunyanta da ya lullubeshi Allah ya soshi sai da zai yi tafiya haka ya faru da bai san ya zai kalleta ba yar karama da ita ya introducing dinta to abun manya haka yayi ta sake sakenshi har suka kai paris inda zai jira flight dinshi zuwa us nan da 2hours da wannan daman yayi amfani bayan yayi sallah ya kira hajiyarsa.
A wannan lokacin gimbiyar har tayi bacci a site dinsu hajiyar ta dau wayar bayan sun gaisa cike da kunya ya tambayi jikin fatima
"Da sauki babana wannan yarinya yar daru ce wallahi haak kake fama" murmushi yayi dan ya san ansha drama a tsakaninsu katse mishi tunani tayi da fadin "bata dade da samun bacci ba yarinya sai masifa" dariya yayi sosai jin wai hajiya ke cewa wan me masifa fatima for that matter su dai kaman mage da bera suke gefe daya sai ya samu kanshi da sauke ajiyan zuciya dan dama bai san me zai ce mata ba in da idonta biyu hakuri zai bata na janyo mata jinyan da yayi ko na tafiya da yayi ya barta da jinyan da shine sanadi.
Haka suka dan taba hira sannan suka yi sallama hajiyan ma taje ta kwanta
Can wajen 10pm fatima ta farka ta ganta ita kadai a daki a gigice ta fito compound din tayi hanyan main house Allah ya taimaketa ladi na shirin rufe kofar falo ta shigo a firgice kaman an hamkadota a dari ladin ta arta zuwa kitchen itama fatiman ta bita har ta manta ma da wani ciwo da take ji gudun tsira dabban yake da na kamu.
Rufe kofan kitchen din suka yi suka tsaya mai da numfashia "wa ya biyoki ?" Ladin ta tambayeta tana mai da numfashi fatima tace ba kowa tsoro nake ji shine nazo nan.
Zaro ido ladin tayi sai kuma suka fashe da dariya ganin shirmen da suka tafka sai da suka tsagaita ladi tace hajiya ta kwanta zo in rakaki dakinta.
Jagora ta mata har kofar dakin ta bude ta shiga hajiya ta gani tana bacci itama ta lallaba ta hau gadon.......
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.