Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 26 of 39
Page 25.
*ummulkhairi kawata kanwas😜 this page is dedicated to u as promised, the others are yet to come*
Murmushi yayi ya shafi kanta da ke bisa kirjinhi cikin kwanciyar hankali yace "baby bazaki ba"
A gigice ta dago daga jikinshi tace " uncle ban gane ba zani ba ya bazani ba yake?" It has been long da nje gida fa me yasa zaka hanani zuwa?"
Hannayenshi ya dag yasa a bayan kanshi hakan ya bawa muscle dinshi daman flexing
Yace saboda kema baki min abinda nake so me yasani zan miki abinda kike so?
Toni meye bana yi maka kuma menenen kace inyi maka da ban yi ba?
Murmushi yayi yana jefanta da wani irin kallo yace hakkin mana kike hanani kin hanani abinda Allah ya hallasta min na rasa gane me kike nufi dani.
Tashi xaune yayi ya cupping fuskanta a hannunshi yace baby ina sonki ina son kadaicews dake amma ke na rasa inda kika dosa sai gudu na kike kaman ba zahrar da na tafi a bari ba wanda bata kaunan rabuwa dani wace take san kasancewa dani duk runtsi saboda tana sona.
Zaro idanunta tayi cikin mamaki murmushi yayi ya gyada mata kai yace yes kina sona tun can baya sai dai baki san hakan ba saboda yarintan da ke tattare dake.
Ina hango kishina a tattare dake a duk lokacin da kike bani labarin yan matandake son shigar da kansu a wajena.
Me yasa kike son bawa zuciyoyinmu da gangan jikin mu wahala me yasa bazaki bari mu mori son da mukewa juna ba? Baby wallahi ina sonki ina sonki zahra ke wata babban jigo ce a rayuwata na nuna son auren yar uwarki amma ba da nufin in aureta a lokacin ba sai gashi Allah cikin ikonsa yayi nufinsa aka samu tangarda abin ya juya min ta inda ban zata ba.
Zahra munyiwa iyayenmu biyayya munci *ribar biyayya* kasancewan mun tsinci kanmu cikin son juna dumu dumu.
Amma ni me yasa ba zaki min biyayya ba ki kawo min kanki shimfidata
Ya kureta da ido suna kallon juna kowa na karantan idan dan uwanshi
Kasa tay da idanunta dan ba zata jure kallon da yake yi mata ba.
Zahra a zan iya bari kiyi nisa dani ba ba zan iya barinki zuwa jos ba.
Kumama ba zan kara tursasaki a shimfidata ba
Amma kina iya samawa kanki mafita, jim yayi yana kallon reaction dinta kafin ya cigaba da fadin saura kwana goma sha hudu ko kasa da haka mu tare saboda any moment furniture dinmu na zuwa cikin wadanan kwanakin kina iya kawo min kanki in kawar da kishin dake tare dani for over a year ni kuma da kaina sai in kaiki jos ko kuma kina iya haqura mu koma gidanmu in karba a nan zuwa jos kuma sai randa Allah yayi dan ba zai yuwu ina honeymoon ki tsiro da wani tafiya bawatakila ma sai in kin je wankan gida.
Kallonshi take baki a bude hawaye na zarya a idonta yaushe uncle ya dawo haka su dai maza basu da kunya wallahi in dai suna son wannan abun ba abunda ya shafesu ko ta halin kaka sai sun samu ji yanda yake manuplating dinta kaman ba uncle dinta ba.
A zai iya jure ganinta tana hawsye ba sai ta karyar mishi da zuciya hakan yasa ya mike ya zira jallabiyarsa.
Har ya kai kofa ya juyo yana fadin lokacinki ya fara daga yanzu ne fa adadin bata lokacinki adadin kwanakinki a jos.
The more you west the less you spend in jos.
Ban miki haka dan in muzguna miki ba ko dan in saki dole ba ah ah sai da nemawa kanmu mafita kin san Allah ya amince min in zi miki ko da yaushe kina so ko ba kya so.
Amma na baki wannan daman kina iya amafani da ita kina iya ajiyeta dabara ya rage ga mai shiga rijiya.
Ya sa kai ya fita ya barta da tunanin ta ina zata fara.
💖💖💖💖💖💖💖💖💖
Durkushe take hanunta dafe da mararta sai mukurkusu take tana kuka tana kiran sunan Allah.
A gigice Hameed ya shigo sai kuma ya saki murmushi yace ahhh maganin ya soma aiki kenan.
Cikin kidima ta dago duk da tsananin zafin ciwo da take ji bai hanata jefanshi da tambayan Hameed mai kake nufi wani kwaya ka saminna sha da yaushe ta karasa tana cije lebe.
Gefenta ya samu ya zauna yana shaf kanta yace khadeeja ina sonki ina jin dadin kasancewa dake dan kina bani nutsuwa sosai sai dai ke din ce kamar akuya wajeb haihuwa da an tabaki sai ciki ni kumaAllah ya gani na gama haihuwa ki bari mu more kinki ni kuma shine na dau matakin sa miki ido ina kallon duk wasu moves dinki ina reading cycle dinki.
Yanzun lura nayi da alamun kina da shigar ciki duk da ban tabbatar ba nayi kasadar sa miki wani kwaya shine kika sha baki sani ba wannan ciwon cikin da jinin dake zarya a jikinki ya tabbatar min da kina da shigar ciki kuma yana hanyan bin rariya ya karasa fada cike da annushuwa.
Kanta ta kifa a jikin gado tana wani irin kuka mai cin rai wannan wani irin rashin imanine haka anya Hameed na da tausayi Kasheta yake sonyi yanzu cikin ma da bata sa da shigarsa ba shine yayi sanadinsa lallai duk wanda ya bijirewa maganan iyaye yana tare da tarin nadama.
Cikin kuka tace Hameed ina soyayyar da kake ikrarin kana min wannan ce kalar soyayyan ana cutar da mutum sannan baka kaunan hada jini dani wallahi ina dana sanin aurenka dalilin aurenka ba abinda ban gani ba amma da wannan kake son saka min kana neman kashe min rayuwa.......
Cikinta ne ya murda ta cije baki tana yarfa hannun banda tana tsoron wani jarabawar zata kuma shiga da ba abinda zai hana tambayar hameed saki.
Shshshshhs ki daina ba wa kanki wahala kiyi shiru ki bari cikin ya karasa zuba in taimaka miki kiyi wanka ki kimtsa wajen tunda zaliha bata nan.
Duk da azaban da take ji sai da ta wurga mishi wani mugun kallo wato ma ba zai kaita hospital ba dan rashin imani.
Da kyar ta iya furta gwara dai ka kaini hospital su karasa wanko maka abinka in ba so kake in mutu ba mara imani Allah ya mana tsari da irin wannan rashin so.
Me yasa kike cewa bana sonki ne in bana sonkj zan aureki har mu haifi sani ne wallahi d bana sonki da tuni na rabu dake tih adeeja ke dince gardi gareki
Cikin jin zafin ciwo tace ka..... Ka....ccce.....minnnn...kawai.....s..........kana sha'awata ammmma ba wai kana ssso so....naahh ba Ham..........d
Kawsi sai ta karasa zubewa a wajen babu alamun numfashi a tattare da ita.
SAWWAMA QAWWAMA💖
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
_nayi mistake a last page 25 muke na saka 24 yanzu zamu tashi 26 kenan._
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.