Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 13 of 39
Page 13.
Ihu take yi iya karfinta discipline master ne ya karasa wajenta ya tsinka mata mari yace "ke meye haka kike cika mana kunne da ihu duk ba ke kika jawo aka yiwa mata da miji tozarci ba ?"
Baba karami ne ya tareshi da fadin abinda wasila tayi ba laifi bane tunda tayi kokarin kau da barna ne"
Uncle yunus yace ah ah wannan da kake gani tayi abinda tayi out of jealousy ne amma ba wai dan ta kau da barna ba" wani kallo sageer ya watsa mishi yace " koma meye nufinta lokacin da ta kawo batun duk ba ku duba wannan ba kuka yi kokarin daukan mataki dan abu ya juya bai kamata a juya zance ba." Zai yi magana malam sulaiman yace " haka ne ba wanda ya duba dalilinta lokacin da ta kawo mana maganan amma malam sagir kar ka ga laifinmu dole hankalinmu ya tashi tunda yaran nan amana ne a wajenmu dole mubi diddigi in munji wani batanci duk abinda wasila tazo da shi ko ma menene hujjanta tayi abu me kyau dan yau da fatimar ba matarsa bace da an bata lamban yabo wajen tona asirinsu.
Principal da tunda aka fara maganan yake binsu da ido yace " haka ne sai da kuka yi maganan nan wani abu ya fado raina ta yaya akayi wasila ta samu shiga Staff quarters alhalin in ba yara irinsu fatiman da suke da iyaye ko yayu a ciki ba dalibai basu da daman shiga ke ta yaya kika samu shiga ko kina da wani a ciki n?" Ya jefo mata tambayan da ya gigita ta ya rikitata ya sa ta yin da na sanin kokarin tona abin nan.
Malam ne yace yallabai ina ganin kawai a gajarta binciken nan kar a binkiciko abinda zai dagawa kowa hankali annabi yace ka bar abinda baka sani ba Allah kuma da kanshi ya hane mu da zurfafa bincike,kawai a tsaurara tsaro kawai a nan sashin malaman principal yace toh shikenan malam yanda kace haka za ayi ke tashi kar inji maganan nan abakin kowa ta gyada kai ta fice da sauri tana hawaye.
Fitarta yayi dai dai da shigowan alhaji sada aka kora mishi zance bai ce komi ba sai da sageer ya fito da wani envelope daga cikin jakar laptop dinshi ya ajiye bisa table din principal yace ga wannan resignation letter na ne na jima da rubuta shi kuma cikin satin nan nake shirin baka shi dan ku fara neman sabon malamin turanci kasancewan nima zan tafi karo karatu nan da wata 3 shi alhaji ya san da haka shi yasa nayi kiranshi,amma saboda faruwan abin nan ba zan iya cigaba da karantarwa a makarantan nan ba har zuwa karshen term dalibai na min kallom mijin fatima ba.
Gaba daya jikinsu yayi sanyi fatima kam tsananta kukanta tayi dan bata da labarin tafiyan wanda ko da aka sallameta ta koma hostel kuka take yi ba kakkautawa tambayan duniyan nan babu wanda ba ayi mata ba hala ta kwana washegari idon nan ya tashi ya kumbura ya kara kankancewa da kyar take iya bude idon ga wani radadi da suke mata banda ciwon kai da take ji.
Wurin 10am kiran uncle ya isketa kayanta ya bata wanda ya wanke ya goge mata a raunane ya kalleta ya ce zahra zan koma gida ki kula da kanki kiyi karatu sosai kar kisa abin nan a ranki ki toshe kunnuwanki inshaa Allahu zamu hadu kafin tafiyata ina kyautata zaton zaki dawo hutu ki sameni dauke mata hawayen idonta yayi yace kai bintoto ko chines ba zasu karbeki ba yanzu yanda idonki suka kuma kankancewan nan pls ki bar kukan nan ta gyada mishi kai kawai.
Tana ji tana gani yaja motarsa ya tafi wani kukan ta kuma rushewa dashi ta juya zata koma ciki idonta ya hasko mata wasila gadan gadan ta nufi wajenta........
😜😜😜😜😜😜
Bata damu da cewan wai senior dinta bace bata damu da yawan sauran students da suka zubo musu na mujiya ba tace " kinyi nasara kin yo nasarar raba uncle da makarantan nan amma ke kinyi kadan ki rabani da dan uwana mijina Allah ma ba zai taba baki nasarar shiga tsakanin ma'aurata ba wato dama kin dade kina bibiyata kina mana labe ban so ya zama idonki abinda ya gane miki kadan bane naso idon naki ya kai ki ganin abinda ya fi wannan watakila da kin farka daga mafarkin da kike yi na malllakan mijina toh ki sani mijina nawa ne ni kadai ba wata shegiyar da ta isa ta raba ni da dan uwa na" cikin karaji da muryan kuka ta bude murya tana fadin wannna auran hadin Allah ne hadin iyaye kuma hadin zuciyoyi ba wacce ta isa ta shiga tsakanin mu muna fatar zamu fanshi *RIBAR BIYAYYA* a nan duniya da lahira ba wani mahalukin da ya isa ya shiga tsakaninmu da wannan ribar.
Ganin yanda ta fice daga hankalinta tana magana ba kai ya saka bilkis isa zuwa taja zuwa cikin hostel aka bar wasila da dumbin jin kunya junior dinta ta tozartata gashi bata da daman hukuntata dan ko giyan wake tasha bata isa ta dau mataki kan fatima balle ga aure kanta hasalima fatimar tsoro take bata yanzu.
Kafin kace kobo maagana ya yadu fatima matar uncle sageer ne wasila tayi kokarin raba su amma ba a san ta wani hanya ba bilkisu isa taji haushin kawarta sosai na boye mata wannan babban sirrin har tasa ta gaya mata tana son mjinta a tunaninta daan uwanta ne kawai ganin halin da fatiman ke ciki yasa ta sakko tana lallashinta.
Baba karami..........
_Hameeda ta daina sona_😫
_Aunty zuwairat ta daina sona_😫
_Surbajo ta daina sona_😫
Wayyo🙆🏼ni sawwama kowa ya daina sona.
SAWWAMA QAWWAMA😘
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.