Ribar Biyayya Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: Ribar Biyayya.txt
Chapter 3 of 39
Page 3.
Fatima na zaune a kan dakalin cikin gidan tana wankin kayanta mama kuma na tsinke ganye adija na d'aki dan tunda abin ya faru zaman tsakar gidan ya gagareta.
Sallama yayi cikin muryarsa mai cike da aminci tsalle fatima ta daka sai gata a gabanshi tayi kaman ta rungumeshi sai kuma ta fasa ta tsaya tana yarfa hannu tana ta washe baki dogon hancin ta ya ja yana dariya yace me idon china.
Bakinta ta turo ta juya zata tafi hannunta ya riko yana gaishe da mama ta amsa amma ta kasa had'a ido da shi tana jin kunyan abinda yarta ta mishi,baba ne ya shigo da sallamarsa aka gaisa sannan suka shige d'aki mama tasa fatima d'aukan abinci in kai musu. Bayan sunci abinci sun gama Nasiha baba ya dad'e yana mishi kafin ya bashi hak'uri da cewa yarinya tak'i Allah ya kawo mishi wata cike da ladabi yace ameen baba wallahi ba komi ai matar mutum kabarinsa wani bai auran matar wani. "Haka ne haka ne baba k'arami Allah yayi maka albarka" ya amsa da "ameen baba ni zan wuce dan ban zo da niyyan kwana ba" toh shikenan babana Allah ya tsare hanya. Yace "ameen yana mik'ewa sallama ya masu hannu ya mik'o mata yace fati zoki rakani zan tafi mak'e kafad'a tayi tace uhm uhm ba inda zan rakaka tunda bazaka kwana ba" murmushi yayi ya juya yace toh shikenan ni na tafi tunda bazaki rakani ba ya juya ya tafi kallonshi take kaman wacce aka hanata binshi har ya fita a gidan. Bayan fitanshi baba yayi wani tunani lek'owa yayi daga d'akinshi yace fatima maza kira min yayanku kafin yayi nisa da sauri ta tashi har d'ankwalinta na fad'uwa amma bata tsaya d'auka ba, fita a gidan tayi da gudu can ta hange shi yana tafiya da gudu ta bishi tana kiran uhmmmm bah k'arami uhmmm kai kai uhmmmm yah sagir juyowa yayi da sauri ta k'arasa gabanshi tana haki. Kallon k'aramin figure d'inta dake gabanshi sai kanta ba d'ankwali sai dogon shukunta da yake nuna alamun warewa ko kuma rashin kamuwa jujjuyawa yayi yaga ba wanda hankalinshi ke kansu kasancewar anguwar ba musulmai sosai yace" k'awas ya dai kin biyoni rakiyar ne ko d'ankwali babu?"
Shafa kanta tayi tace " wallahi fad'uwa yayi ni kuma ina sauri kar ka b'ace min baba yace in kiraka inace ma a mota kazo kar kayi nisa" kai ya kad'a yace ai na bar motar a bakin hanya ana wanke min" haka suka k"arasa suna hirarsu. Baba ne ya kalleshi bayan ya shiga d'akin ya zauna yace" babana dama wata shawaran na yanke me zai hana ka komo kan fatima tunda ita bata da wani damuwa asalima bata san meye soyayya ba. Gabanshi ne ya fad'i jin batun kawun nashi a kasalance yace " kawu baka ganin za a shiga hakkin yarinyan da da karatunta? Baka ganin tayi k'ank'anta da aure?" Murmushinsu na manya yayi yace " ko d'aya fatima dai rashin jikin girma gareta amma ai ta isa aure shekara goma sha biyar aiko ta kai aure watan d'aya zata cika shekaru goma sha biyar mamakine ya k'ara cika sagir jin wai y'ar shekara sha biyar ce ta kai aure ai ko a karkara sai haka shifa ko da yace yana son khadeeja ba wai yana nufin suyi aure nan take bane shima d'in ai yaro ne gaba d'aya shekarunsa 26 kuma so yake yaje ya karo karatunsa zuwa phd.
"Kayi shiru babana ko baka son fatiman ne daman nayi k'wad'ayin had'in zumuncin ne kar kaji komi in baka sonta ka gaya min" ah ah baba Allah yayi zab'in alheri zan sami hajiya da maganan kafin kazo.
Haka ya musu sallama fateeman ta fito raka shi taga duk jikinshi a sanyaye hannunshi ta kamo kallon cute face d'inta yayi yace " ya dai mai suffan y'an korea?" Zaro idanu tayi tace" au na tashi daga mai kama da 'yan china na dawo 'yar korea?" Murmushi yayi kawai duk da k'arancin shekarunta ta san da ciwo ace ba a sonka marairaice fuska tayi ta kirashi da sunan da ta san yafi son a kirashi da shi wato sunansa na gaskiya "yah sagir kayi hak'uri k'ilan ba alkhairi tsakaninku ne shi yasa abin bai working ba kayi hakuri Allah zai kawo maka wacce ta fita hali da komai wacce zata kawo farin ciki rayuwarka, ka daina damuwa kaji ta k'arasa maganan kaman zata yi kuka.
'Dan dogon hancinta yaja yace wa yace miki na damu ni ai har na sami matata" alhamdulillah" shine abinda tace. Sai yaso yaji cikinta dan yaran yanzu baka shaidansu mussaman akan soyayya " ke kuma waye saurayinki" ya tambayeta a dai dai lokacin da suka iso wajen motarsa dafe k'irji tayi tace "ni shegiya inji d'an daudu ina ni ina wani saurayi" dariya yayi sosai ya d'an jujjuya ya duba yanayin anguwan yace ke dai gaki baki girma cikin hausawa ba amma ya aka yi kika iya hausa haka" itama dariya tayi ta rufe idonta tace "ai ina zuwa islamiya a kwana shagari kuma ai kaga anguwan hausawa ne kuma akwai wata yarinyan ajinmu in malam bai shigo ba tayi ta karanta mana littafin hausa. Had'e rai yayi yace ashe ma ba karatu kike zuwa jin karatun littafin soyayya ke kai ki da sauri t girgiza kai tace ah ah ah ba littafin soyayya bane irin su iliya d'an mai k'arfi da magana jari ne fa kuma ma sai in ba malam a ajin" "duk da haka ai gwara kuyi muraja'a"
Haka suka yi sallama ya kama hanya yana me dana sanin fara furta kalman so akan khadeeja da yanzu bai shiga tsaka mai wuyan nan ba
💖RIBAR BIYAYYA💖
By Sawwama A.
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.