Complete Hausa Novels

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: NAKASA BA KASAWA BACE PART 1.txt

Chapter 26 of 27

*PAGE 27*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Cikin tsananin sakin fuska da cikar mutuntaka da
martaba, Baba malam ya mik'e tare da cewa.
"Ha Malam Ashiru kaine yau a gidan namu."
Sai kuma yayi saurin isowa inda suke tare da cewa.
"Kai Alhamdulillahi yau inada manyan bak'i wa nake gani kamar Aliyu?"
cikin happy Baban Ishaq yace.
"Ikon Allah kace dara taci gida kenan."
dariya Baba malam yayi irin tasu ta dattawa masu mutunci da cikar kamala haÉ—i da ilimi,
hannu yasa ya jawo hannun bappa Ali tare da nunawa su malam Ashiru inda zasu zauna,
kana ya kalli Baban ishaq da Aminu da kuma abokinshi malam Adam mukhtar kana sai Ahmad da yanzu ya shigo musu da ruwa cikin nuna sanaiyya Baba malam yace.
"Wannan ai k'anin mune,
Limamin masallacin fadar garinmu dukku ne.
Kuma mahaifinsu ne ya fara d'igamin Alifun akan allona, shine malamina a wurinshi nayi karatu har nayi sauk'a Al'qura'ani mai girma."
Sai ya kuma nuna malam Ashiru kana yace.
"Wannan kuma shine abokina tun na k'uruciya."

Sosai sukaji dad'in wanna abu,
cikin dattaku Dirankad'i baban ishaq kenan yace.
"Alhamdulillahi, wanna abu yayi kyau."
Cikin kamala malam Adam yace.
"Ainun kuwa."
Ya Ahmad ne yayi murmushi tare da gaidasu cikin nitsuwa, murmushi Bappa Ali yayi kana yace.
"Kaddai Ahmad ne ya girma haka?"
Murmushi Baba malam yayi tare da cewa.
"Shine fa, shima yanzu harda yara gareshi."
"Ikon Allah girman d'an adam babu wuya."
Cewar Malam Ashiru.

Shi kuwa malam Adam gyara zama yayi tare da cewa.
"Bisa alamu dai bakuyi rik'o da zumuncinku bane,
shiyasa har kuka gaza shaida yaran."
Dirankadi ne ya d'an k'urb'i ruwan da Ahmad ya zuzzuba musu cikin kofuna kana yace.
"Ato yanzu dai igiyar zumuncin muka zo neman k'ullawa."
Murmushi mai kama da dariya sukayi baki d'aya,
kana suka d'anyi gaishe-gaishe da tambayar bayan rabuwa sosai sukaji dad'in ganin juna, shiru suka d'anyi.
Sai kuma Baba malam ya d'an kalli Bappa Ali tare da cewa.
"Ina d'alibi na, Hamman Zaleeha?."
cikin murmushi bappa Ali yace.
"Saifuddeen ne yana nan lafiya."

Jinjina kai baba malam yayi tare da cewa.
"Shima yayi aureko?."
Malam Ashiru ne ya amshe zancen da cewa.
"To yana dai da niya."

"Masha Allah. Allah Ya sanya al'khairi, Allah Ya jib'anci lamuranshi, yaji tausayin maraicinshi ya bashi mace ta gari."
cewar baba malam
"Amin Amin" Suka amsa baki d'aya.
Kana duk sai sukayi shiru tare da meda hankalin su kan Dirankadi, daya gyara zama tare da yin gyaran murya, kana ya kalli Baba malam da Malam Adam cikin nitsuwa yace.
"To Alhamdulillahi, komai zaizo da sauk'i tunda sanaiya ya shigo cikin lamarin."
Kai suka gyad'a baki d'ayansu alamun gamsuwa, shi kuwa cigaba yayi da cewa.
"To wannan tafiya dai ko ince ziyara ta d'alibin naka ne."
cikin sakin fuska Baba malam yace.
"Masha Allah Saifuddeen ko?."

"Na'am shi dai."
Cewar Malam Ashiru.
Aminu da Ahmad kuwa sunyi shiru kansu a k'asa domin girmama iyayen nasu.
Dirankadi ne yaci gaba da cewa.
"Shi dai Saifuddeen naka, shine yaga 'yar wojenka, to ya yaba da tsarin tarbiyan ta,
har yayi sha'awar ta zamo mata gareshi kuma uwar yaranshi in Allah ya nufa."

Cikin tsananin farin ciki Baba malam yake jinjina kai, domin shi dai yasan su waye Baffa Ali, yasan tushensu ya kuma san tarbiyar Saifuddeen wacce kusan shima ya tarbiyantar dashi,
dominko d'alibinshi ne, a wurinsa Saifuddeen yayi hadda bayan sauk'an karatu da yayi a wurin kakanshi.
Yasan Saifuddeen farin sani, yasan sababin ciwon da ya jaza mushi kurumta, yana tsananin son d'alibin nashi sosai, irin soyayyar da malami keyiwa d'alibinshi mai gwazo da ilimi da basira, nakasar da Saifuddeen É—in ya samu ta k'ara samishi tausayinshi acikin ranshi,
shiyasa koda yaji cewa Saifuddeen ne ke son d'iyar tashi, ya cika da tsananin farin ciki. Wanda ya kasa b'oyuwa akan fuskarshi.
Haka kawai Ahmad yaji yana mugun son Saifuddeen, saboda ganin yadda jin sunanshi kawai yasa mahaifinshi farin ciki.
Sai Kuma suka meda dubansu kan Bappa Ali da yayi gyaran murya kana yace.

"To koda ya shaida mana, yana sonta, ya nemi da muzo mu nema mishi izinin gabatar da kanshi a gareta,
in ba'a tsaida mata mijiba,
to shine dalilin zuwanmu dan sama mishi izini daga bakin iyayenta, kamar yadda shari'a ta tsara mana."

Malam Adam ne yayi murmushi kana yace.
"To Alhamdulillahi ba'a rigada an tsaida mata mijiba,
kana dama duk masu zuwa gareta bata tsaida gwaniba,
fatanmu in yazo ta ganshi su dai-dai ta tsakanin su."
Sosai Aminu ma kejin dad'i dan tabbas yasan wanna mutane ne masu mutunci wala Allah Zaleeha ta amince dashi,
dan yana sane da shak'uwarta da Saifuddeen.
Shi kuwa baba malam kai ya jinjina musu alamun.
"Eh abinda amininshi ya fad'a hakane a ranshi.
Ajiyan zuciya mai nauyi bappa Ali ya sauk'e tare da gyara zamanshi,
kana ya fuskancesu da kyau sannan yace.
"To amman fa wani hamzari ba guduba,
kasan Saifuddeen yanada larurar nakasa,
kunaga hakan bazai zama matsala ba?."
Gyara zama baba malam yayi kana yace.
"Uhumm Aliyu kenan, to me a cikin nakasa? ai ita NAKASA BA KASAWA BACE,
kuma ai ko wanne d'an adam bai san k'arshensa ba."
Malam Adam ne ya karben zancen da cewa.
"Hak'k'un don duk d'an adam ba'a gama mishi halittarsa ba har sai randa ya kwanta dama."

Cikin d'an jin dad'i, da kwarin guiwa bappa Ali yace.
"Malam Bashir, bayan kuramtanfa Saifuddeen ya kuma samun nakasar spinal cord injury! shekara d'aya daya gabata."
Da sauri Ahmad da Aminu suka d'ago kai suka zuba mishi idanu, cikin alamun tambaya,
shi kuwa Malam Adam cikin son samun k'arin bayani yace.
"To kuma zaiyi aure? Ya yanayi tsaurin cutar, kunfa san cutar lakar jiki ba k'aramar nakasa bace."
Baba Malam ne ya d'ago kanshi tare da girgizawa abokin nashi kai.
tuni tausayin Saifuddeen ya cika mishi zuciya, sai dai ya sani su Baffa Ali sun san abinda sukeyi, in har cutar ta Saifuddeen ta tsananta bazasuyi yunk'urin nema mishi aureba.
Shi kuwa Baffa Ali wayarshi ya zaro kana ya shiga Gallery d'inshi, sashin pictures d'in Saifuddeen ya shiga,
wanda sunfi hamsin kuma duk Hayatuddeen ke tura mishi su,
Aminu ya mik'awa wayar tare da cewa.
"Gashi nan zaune a kan wellchair d'inshi."
Da sauri Aminu ya amashi wayar ya fara kallon hotunan shida Ahmad.
gaba d'aya jikinsu yayi sanyi ganin k'addara da k'udurar ubangiji a kan wanna kyakkyawan hallita,
gashi da cikar haiba,
tuni Ahmad baisan yana zubda hawayeba, ganin wani hoton Saifuddeen dake zaune bisa sofa, Umminshi na zaune kan hannun kujerar ta rik'e mishi haba shi kuwa ya d'an raba jikinta duk suna dariya,
Hayatuddeen kuwa na gefe bisa wellchair d'in Hamman nashi, yana kallonsu yana turb'una fuska waifa shine auta,
Ahmad kuwa mijin Raliya, na tsaye kan Hayatuddeen d'in yana mishi dariya,
Raliya ce ta d'aukesu hoton da yayi masifar kyau.
Hannu yasa ya sharte hawayenshi tare da mik'awa malam Adam wayar, bayan ya gama kallon hotunan ne wanda wasu Saifuddeen Yana kan sallaya, wasu kuwa yana tura welchair d'insa,wasu kuma yana konce kan gado ko 3 sitter, sam bazaka tab'a yarda yanada matsalar spinal cord injury ba.
mik'awa Baffa Ali wayar yayi, tare da maida hawayen tausayin Saifuddeen da suka cika masa idanu, kana a hankali yace.
"Shin zai iya aure har ya iya kusantar mace har in Allah ya nufa su samu haihuwa!?."
Wani sassanyar ajiyar zuciya Baffa Ali yayi kana ya, musu duk cikekken bayanan da doctors sukayi musu ya k'ara da cewa.
"Likitoci sun bamu tabbacin cewa zai iya aure harma da haihuwa, domin nakasarsa bata shafi jijiyoyin mazantakarsa ba.
Kuma ko jiya da sukaje suka sameni da batun saida na kuma tambayarshi batun lafiyarshi.
Ya bani tabbacin shifa baida matsala ko kad'an."
Jin haka yasa Baba malam yin murmushi tare da cewa.
"Alhamdulillahi, na bawa Saifuddeen dama yazo ya gabatar da kanshi a wurin Zaleeha, in dai tayi mishi to in sha Allah Zan bashi ita."
Wani matsainacin farin cikine ya rufesu baki d'aya,
Aminu da Ahmad ma sun aminta da Saifuddeen, domin suma ai basu san k'arshensu ba.
Malam Adam ne ya gyara zama tare da cewa.
"An bashi dama yazo ya gabatar da kanshi, fatanmu Allah ya dai-dai-ta tsakaninsu."

"Amin Amin." Sukace baki d'aya kana,
daga nan suka ɗan taɓa hira, daga bisani su Baffa Ali suka mik'e da niyar tafiya,
Har bakin gate wurin motocinsu, Baba malam da abokinshi Malam Adam dasu Aminu sukayi musu rakiya.

Kai tsaye gidansu Saifuddeen suka nufa,
Wanda yake zaune a falon side É—inshi shida Ahmad da kuma ishaq,
hira suke amman gaba É—aya hankalinshi baya kansu, duk tunaninshi naga su Baffa Ali,
tsoro yakeji kar suje ace musu anyi mata miji.
Ahmad ne ya kalleshi tare da cewa.
"Wai mene sai kayi wani shiru, in ma an bada ita, ai akwai wasu matan."
Hararanshi yayi tare da girgiza mishi kai, kana ya mishi alaman "Itace muradin zuciyarshi, kuma abincin ruhinshi."
mik'ewa Ahmad yayi cikin yin dariya kana yace.
"To nama jiyo muryar Baffa Ali a parlour ku taho muje muji dame suka dawo."
Kusan a tare suka fito,
yayinda Saifuddeen yaketa musu kallon nazartar fuskokinsu.
Murmushi yayi ganin Dirankadi na cewa Ummi.
"Alhamdulillahi tafiya tayi kyau, abuma duk namune."
wani irin sassanyan ajiyan zuciya Ummi tayi tare da cewa.
"Gidan mutunci ne ko?."
Da sauri baffa Ali yace.

"D'iyar Bashiru nefa d'an abokin babanmu,
kin tuna malamin su Saifuddeen na islamiya?."

Da sauri Ummi tace.
"La Bashir kam ai bazan mantashi ba,
lokacin da muke karatu su sunyi sauk'a, kusan sune manyanmu a wurinsu muke biyawa in kawu baya kusa."
Cikin dariya malam Ashiru yace.

"Ato baki mance mu ba ashe."

Kai ta gyad'a cikin jin Kunya dan tuno k'uruciya.
Dirankadi ne yace.
"To Zaleeha d'iyarshi ce ai?."
Ahmad ne yace.
"La Zaleehan Malam Bashir ce? D'alibar Saifuddeen lokacin in bashine zai bata haddaba sam bata tab'a iya kawoshi dai-dai."
Sai ya kuma juyawa ya kalli Saifuddeen da ya kauda kanshi kamar ba shiba.
Baffa Ali ne ya shafa kanshi, tare dayi mishi cikekken bayanin irin tarbar da suka samu, da irin karra masu da akayi, da kuma basu izinin ya fara zuwa zance duk sanda ya shirya.
Wani irin tarin farin ciki yakeji a ransa, a fili kuwa sai hannu ya bawa Dirankadi da Malam Ashiru tare da yi musu alamun godiya da jinjina.
sosai Ummi ke lura da irin yadda fuskarsa ke cike da farin ciki,
Amman kunyarsa ta boye hakan.
Sosai sukaji daÉ—i daga nan Ahmad ya É—auki su Baffa Ali ya maidasu Dukku,
Ishaq kuwa yabi babanshi suka tafi.

Bayan duk sun fitane,
Saifuddeen ya sarrafa whellchair É—inshi har zuwa gaban Ummi dake tsaye,
yana isa inda take ya ruggumeta cikin farinciki da salama.
Murmushi tayi itama tare da tallafo haɓarshi cikin son abinda ɗan nata keso tace.
"Allah ya sanya al'khairi a cikin wannan lamarin naka,
Allah ya shige maka gaba ya tabbatar maka da ingantaccen farin ciki!!."
A saman lips É—inshi ya amsa da "Amin Amin my Ummi."
Sai ya kuma sarrafa whellchair É—in nashi ya nufi falonsa.

Ummi kuwa da sauri ta haura sama, inda Hayatuddeen ya tasa Raliya a gaba ala dole sai ta share mishi d'akinshi.
A parlour ta samesu ita tana shara, shi kuwa yanata zuba mata surutu, hannunshi rik'e da pillet d'in kifin margi special yanaci yanata zuba mata zance, kana yana watsar da k'asusuwan a bayan inda ta share.
Cikin gajiya tace.
"Wlh na gaji Ummi autanki zai samin ciwon baya dana kunne, duk inda na share yana b'atawa kuma ya cikamin kunne da surutu kamar kabari."

Baki ya turo gaba tare da cewa.
"Ummi wai dan ina bata labarin wata mawaƙiya, Asma'u Ahmad Matawalle ce da take son Hammana kamar ta mutu, ɗazu muka gama waya da ita wai in gaisheki."
Cikin mamaki Ummi tace.
"Mawaƙiya kuma?."
"Eh" Yace yana lumshe ido tare da kurb'ar juice d'in dake hannunshi.
Kauda zancen Ummi tayi da cewa.
"Su Baffanku sun dawo harma sun koma."
Cikin tsalle Hayatuddeen ya diro daga kan firijin da yake zaune tare da wurga kwalin juice d'in yace.
"An bawa Hamma na ita ko yaushe ne auren?."
Cikin dariya Ummi tace .
"Oh ya Allah ka kimtsa min autana ya zama nitsastse kamar Saifuddeen."
Jin Raliya na cewa.
"Ummi an bashi izini zuwa zancen?."
Cikin gyad'a kai tace.
"Eh an bashi sosaima suka samu karramawa, d'iyar Malaminshi nefa Malam bashir, wanda kuma yake shirin Hanyar tsira na gidan radion vission FM."
Tsalle Hayatuddeen ya kumayi tare da cewa.
"Yanzu kuwa zan tafi gidan Adda Rahma inje musha hira."
Kafinma su ankara tuni ya fice abinsa.
Nan Raliya ta samu daman gyara mishi É—akin nashi.

Ummi kuwa falonta ta dawo ta zauna taci gaba da karatun da takeyi.

Shi kuwa Saifuddeen dake zaune akan lumtsuma -lumtsuman sofan dake falonshi, gyara zamansa yeyi.
Wayarshi ne a hannunshi da alamu hira yakeyi da ishaq.
"Kai yaro kaji dai ko mun samu karɓuwa.
Yanzu yaushe zamuje ne dan gabatar da kanmu?."
Cikin tsokana Ishaq yace.
"Sai next week ko?."
Da sauri ya rubuta mishi.
"Kayi hauka ne, ai zuciyata zata narke kafin nan."
Dariya sosai Ishaq yayi kana yace.
"To yaushe zamuje?."
Cikin gyara zamanshi yace.
"Anjima da yamma zamuje, kafin nan Ahmad ya dawo."
Dariya Ishaq ya kumayi kana yace.
"A a sarkin sauri, gsky ka bari sai gobe da yamma.
Dan yau zata gabatar da program ɗinta na mushaƙata."
Badan ya soba sai don dole haka ya haƙura.

6:00 pm. Zaleeha ce ke cikin É—akin watsa shirye-shiryen su.
Zamanta ta gyara bisa kujerar da take kai, tare da ɗan rage sautin waƙar da tasa, kana cikin irin muryarsu na ma'aikatan gidajen radio tace.
"Assalamu alaikum, al'ummar jihar gombe da kewaye, barkanmu da war haka sannunmu da sake saduwa cikin shirin Mushaƙata, tare dani Zaleeha Bashir Sulaiman Dukku."
Sai kuma ta ɗan dakata tare da ƙara sautin waƙar nan ta. Nura M Inuwa mai taken.
"Kaso a soka yafi ƙawance cika taso a soka kanaso."
sai kuma ta ɗan range sautin tana mai bin waƙar, yadda ake iyajin muryarta dana mawaƙan na tafiya atare.

Raveel dake É—akin kula da shirin dake fita, dariya yayi domin yasan dashi da manager akeyi.
Ita kuwa Zaleeha tuni shauƙin sonshi ya rufeta, saboda zafafan waƙoƙin so da take sakawa.
Cikin shauƙi ta katse wata waƙan Nura M Inuwa mai taken.
"So makaho ne, kamar walƙiya ya kamani, gashi na zautu al'umma sunata nunani!."
Sai kuma ta yi magana a hankali, inda tace.
"Da fatan dai kuna jin daɗin waɗan nan zafafan waƙoƙin da muke kawo muku daga tasharmu ta Vission FM.
Ku gyara zama domin jin waƙarmu ta ƙarshe sakamakon ganin lokaci na hararanmu.
Sai ta kuma saki wata zazzafar waƙa mai tsuma zuciya, inda jarumar ciki ke cewa.
"Zo muyi zance masoyi na kajiya."
Sai ta kuma sai-sai-ta waƙar tare da dai-dai-ta muryarta data waƙar tana bin baitin.
"Karda ka kauce, kasa ai mini dariya.
Saida na tace na zaɓo ka guda ɗaya, babu irinka aduk faɗin duniya."
Sosai akejin muryarta na tafiya da sautin waƙar.

Dai-dai lokacin kuma Baba malam da Ya Ahmad da Aminu, suna gidan Inna wacce ya samu tana jin radio.
Cikin kaÉ—a kai tace mishi.
"Ka jiko Bashiru ka haifi zabiya mawaƙiya,
Kaji da kunnen ka ko,
Yanzu aka gama gabatar da shirinka na masu imani, Kajita ko ita kuma amara zabiya kantalla mai son kiÉ—e-kiÉ—e da raye-raye kamar jikar dujjal."
Shiru baba malam yayi cikin jin kiɗan da Zaleeha ta ƙure ta haɗe da muryarta yana hawa mishi kai.
Kai ya jujjuya dai-dai lokacin da take bin waƙar inda ake cewa.
"Kai d'aya gaiyya mazaje kubi baya.
Babu irinka na duba duk nahiya!."
Cikin takaici Ahmad yasa hannu ya kashe radio'n, dan ya lura ran mahaifin nasu ya ɓaci sosai da sosai, shi kuma sam baya ƙaunar duk abinda zai ɓata mishi rai ko ya taɓa ƙimarshi.

Ita kuwa Zaleeha cikin Shauƙi ta gama gabatar da shirinta kana ta fito.
A bakin ƙofa suka haɗu da Bilkeesu mai gado, dan zata shiga gabatar da shirin labaran duniya.
Cikin kula tace.
"Kadafa ki manta Dukku, gobe da yamma zamuzo gidanku nida Rashida zamuje gidan Adama ta haihu muyi mata barka."
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Ba matsala sai kunzo dama gobe ba inda zanje."
Daga nan sukayi sallama,
a bakin motarta ta samu Raveel dariya ya mata tare da cewa.
"Gani nazo muyi zance kar ai miki dariya, ni d'aya gaiya na isheki a duniya, dukka buƙatunki zanmiki ba inkiya."
Murmushi tayi dan dama ai Raveel natane yanada abin dariya dasa mutun Shauƙi.
Motarta ta shiga tare da cewa.
"Kafi kyau a hakanka ka zauna matsayin abokina."
Murmushi yayi tare da rufe mata k'ofar motar.

Kai tsaye gidan Addanta Maryam ta biya dan tace mata,
Yau awaran couscous takeso tayi mata.
A dinning table suka zauna tana cin awaran da aka soya da ƙwai.
Sai miyan tarugu damn albasa da dusan kifi.
Cikin kula Maryam tace.
"Kina addu'o'in da na baki ko?."
Kai ta kaÉ—a mata tare da cewa.
"Inayi Addana inata rok'on Allah ya baiyana minshi ya kawo minshi gareni in har shidin al'kairi ne a gareni."
Cikin sanyinta da haƙuri tace.
"Yauwa yar uwata, ki kuma rage jin kiɗe-kiɗe ki yawaita jin karatun Al'Qur'ani. Ƙinga inma aljanine kamar yadda mama ke faɗi zai rabu da ke."

Kunun ayan dake gefenta ta kurɓa tare da cewa.
"Mutun nema my Adda na, ina sonshi, ina son abuna."

Murmushi maryam tayi kana tace.
"Allah ya tabbatar miki da al'khairi!."

"Amin Amin." Tace tare da miƙewa, ta ɗauki kular da Maryam ɗin ta cika da awaran tace a kaiwa Aunty Lubna da ya Ahmad.
cikin kula Maryam tace.
"Ki tsaya kiyi salla mana."
Kai ta jujjuya tare da rataya hand bag É—inta kana tace.
"Kin san baba malam baya son in kaiwa dare a waje."
Kai ta gyaÉ—a mata kana ta rakata har wojen motarta.

Bayan anyi sallan ishane, Ya Habu ya shigo falon Mama inda ya samu Zaleeha da Zahira da Aunty Lubna suna hira,
cikin yanayinshi na rashin sakin fuska dan shi ya gadi rashin fara'ar Mama amman shi yanada mutunci fuska a haÉ—e yace.
"Ke Zaleeha kije Baba malam na ƙira."
Da sauri ta dafe ƙirjinta tare da cewa.
"Ya Habu meya faru?."
"In kinje ai zakiji."
ya bata amsa ataƙaice,
jin hakane yasanya ta miƙe da sauri tare da zumbula hijabin sallanta, wanda yake har ƙasa ta nufi parlour'n Baba malam ɗin.
A bakin ƙofar parlour'n tayi kiciɓis da ya Ahmad, cikin sauri ta kamo hannunshi tare da cewa.
"Please ya Ahmad muje ka rakani dan Allah!."
Murmushi yayi sannan yace.
"To muje."

Shiru sukayi baki É—ayansu a gaban mahaifin nasu,
yayinda Aminu ke gefe riƙe da wani littafi.
Ganin shirun yayi yawane murya na rawa tace.
"Baba malam gani."
tsareta yayi da ido kana yace.
"Na ganki ai, ke nake jira inji ko kin fidda tsayeyye kamar yanda na umurceki."
Kai ta jujjuya a hankali kana tace.
"A'a."
Murmushin girma yayi tare da cewa.
"To ba matsala, ni na zaɓa miki,
zai zo gobe ki ganshi, in ya miki shike nan, in kuma bai mikiba ba dole na baki kwana biyar daga goben sai ki kawo wanda kike so,
In kuma har kwana biyar ya cika baki kawoba to tabbas zaɓina ya zama naki."
Da ƙarfi ƙirjinta ya wani irin wawan bugawa, take tsoro mai tsanani ya rufeta,
da sauri ta rumtse ido jin Ya Aminu na cewa.
"Gobe da yamma zaizo kuga juna kada kije ko ina."
Kai ta É—ago da nufin zatayi magana kenan.
Baba Malam yace.
"Tashi kije sai da safe, Allah ya muku al'barka."
Da kyar ta iya cewa.
"Amin. " kana ta miƙe ta fita.

Kafinma ta isa falon tuni hawaye sun ɓata mata fuska.
kai tsaye É—akinta ta nufa.
Da sauri Aunty Lubna tabi bayanta tsaye ta sameta ta kifa kai jikin gini tana rera kuka.
Kamota tayi suka zauna kan gado.
Cikin sassauta lafazi tace.
"Meyasa bazaki zama jaruma ba wurin tinkarar matsalarki abu kad'an ki fara kuka."
Cikin zubda ƙwalla ta gaya mata abinda Baban nata ya gaya mata.
Gyara zama tayi tare da share mata hawayenta kana tace.
"To ai da sauƙi tunda har yanzu dai an baki damarki,
ki kuma dage da addu'ar Allah ya kawoshi gareki kafin kwanakin da Baba malam ya faÉ—an su cika.
Kuka ba naki bane addu'ace ta kama ceki."
cikin jin ƙarfin guiwa ta gyaɗa kai.
Haka dai tayi ta rarrashinta har ta sake.

Sannan ta fita ta koma side É—in Mamy, inda ta samu tuni Mamy ta tafi wurin Baba malam.
Ɗakin da take sauƙa idan sunzo ta shiga, nan ta samu Ahmad ɗin na yiwa yaransu addu'a.
yana gamawa suka dawo parlour'n Mamy nan yake bata labarin komai a kan Saifuddeen, shiru tayi a ranta tana cewa nakasasshe kuma? a fili kuwa lafewa tayi jikin mijinta.

A can wurin baba malam kuwa sosai yayiwa Mamy bayani sanin tanada nisuwa kuma Alhamdulillahi don ai ita tasan Saifuddeen farin sani.

Ita kuwa Mama Allah-Allah takeyi girkinta yazo, ta shigar da batun Abdussalam a wurin baba malam, akan zata ce mishi Zaleeha ta amince dashi.

Washe gari da yamma ƙawayen Zaliha Bilkisu da Rashida suka zo,
inda tuni itama ta shirya,
har zasu fita Ahmad yace
kada su fita su bari sai gobe in yaso suje,
ya fake da yasan Rashida ta iya zana lalle yace ta zanawa Lubna.
Sosai suke ganin daraja da girman Ya Ahmad É—in, dan haka ba musu suka amince.
Nan Rashida ta fara zanawa Aunty Lubna lalle,
ita kuwa Zaleeha kamar ta mutu dan baƙin ciki, dan tasan abinda yasa Ya Ahmad ɗin nata yayi musu haka.
Bilkeesu kuwa gyara kwanciyarta tayi tana kallon film d'in Sanam Teri Kasam da ake haskawa a tashar MBC Bollywood.

Biyar dai-dai Ahmad ya shigo tare da ishaq.

Kai tsaye parlour'n Saifuddeen suka nufa.
zaune suka sameshi bisa wellchair É—inshi, mai kalan golding ash.
Wani irin murmushi Ahmad yayi tare da cewa.
"Fatabarakallahu fi hasanil Kaliƙin, tsarki ya tabbata ga ubangijin sammai da ƙassai da yayi wannam kyakyawar halitta."
Ishaq ne ya amshi zancen da cewa.
"Masha Allah!."
Murmushi Saifuddeen yayi wanda yake sanye da wata É—anyen yadin getzner mai azabar kyau kalar dark green mai turuwa, irin dark mai shinng É—innan, yayinda aka zubawa kayan wani fitinennen É—inkin half jumper and pencil trouser, daga wuyan rigar kuwa aka watsa mishi wani tattausan zaren surfani.
yayinda ya murza wata kyakyawar hular damanga mai ratsin dark green akansa,
daga ƙafansa kuwa wasu irin fitinannun toms mai kalan shaddarsa yasa, ƙiran company'n Gucci, me matuƙar tsada,
still kuma zazzafan agogon company'n Gucci ne ke É—aure atsintsiyar hannunsa wanda kuÉ—insa kaÉ—ai ya haurawa 80k,
sai wayarshi ƙiran iphone 11 pro max daya zura cikin al'jihun gaban rigarshi, wanda abayyane ta saman al'jihun rigartasa, kake iya hango kyawawan camera's ɗinta guda uku dake jere reras, biyu asama ɗaya aƙasa.
Yanayin shigar tasa ta matuƙar ƙara fito da farar fatarshi kai ka rantse da Allah cewa balarabe ne.
Sajen nan nashi yayi wani lub-lub yayiwa fuskarsa ƙawanya sai sheƙi da ƙamshi yake,
red colour lips É—inshi sai shinning skeyi tamkar an shafa mishi mai a kansu.

Shida kanshi ya sarrafa whellchair É—inshi suka fito zuwa parlour.
Ummi suka samu ita da Hayatuddeen azaune.
gabanta suka tsaya
cikin shirinsu na fita, murmushi tayi tare da godewa Allah daya bata wannan kyakkyawan É—an, cikin gane batun da ya mata tace.
"Allah ya kaiku lafiya, ya dawo daku lafiya, Allah ya baku nasara da sa'a kan abinda zakuje nema.
Allah ya sadaku da al'khairin dake cikin tafiyar ya rabaku da sharrin dake tare da tafiyar."

Da "Amin." Suka amsa baki É—aya.

Shi kam Saifuddeen wani sanyi da farinciki ne suka rufeshi sabida addu'o'inta gareshi.
Shiko Hayatuddeen sai hotuna yaketa musu.

Daga nan suka fita,
har bakin gate Hayatuddeen ya rakasu, saida yaga sun fita sannan shima ya ɗauki machine ɗinsa ƙirar UD, ya nufi gidan Inna dan zaije wurin Zakariyya.

Su Saifuddeen kuwa suna isa G.R.A.
Ahmad ya rinƙa bin ƙwatancen da Baffa Ali yayi musu,
suna isa bakin gate É—in suka danna horn, sunyi biyu ana uku aka wangale musu makekem gate É—in.
Cikin nitsuwa Ahmad ya dai-daita parking É—in motar,
a hankali ya buÉ—e marfin motar ya fito cikin shigarsa ta al'farma,
both É—in motar ya buÉ—e tare da fiddo whellchair É—in Saifuddeen,
ta inda yake yazo, buÉ—e mishi murfin motar yayi kana ya gyara mishi keken.
Yayinda tuni Ishaq kam ya fito.

Yana gama gyara zamanshi kan whellchair ɗin sai ga Ahmad ya fito daga cikin gidan hannunshi riƙe da Unaisa
ganinsu yasa cikin sauri ya nufi inda suke,
ganin haka Ahmad Abban farida ma ya saki fuska kana ya nufi inda suke hannu suka bawa juna,
Abban Farida ne ya fara magana, inda yace.
"Assalamu alaikum."
"Ameen wa alaikassalam, barkanku da zuwa."
"Yauwa barka dai."
Murmushi yayi tare cewa.
"Ahmad yayan Zaleeha."
cikin sakin fuska Abban Farida yace..
"Ni kuma Ahmad yayan Saifuddeeen."
Murmushi sukayi baki d'aya,
sannan suka taho inda su Ishaq ke tsaye,
cikin tsananin son Saifuddeen ya sunkuyo ya bashi hannu sukayi musabaha,
sannan suka gaisa da ishaq wanda shi sam bai gane cewa Ishaq makaho bane.
Jagora yayi musu zuwa BQ inda dama yasa Lubna ta gyarashi fes tunda safe.

Bayan sun zauna ne yace.
"Bari naje na turo muku ita ko."
cikin fara'a Abban Farida yace.
"Ayi haka babban yaya."
"Ai anyima." ya bashi amsa yana É—an murmushi, kana yafice daga cikin babban falon BQ É—in.

Shiru sukayi kowa da abinda ke ransa,
shi kuwa Saifuddeeen azkar yakeyi azuciyarsa cikin nutsuwa.

Zahira yasa ta kai musu abin sha, kana ya nufi side É—in Mama.
A Parlour Mama ya samesu suna hira sama-sama dan kowacce da abinda takeyi.
cikin tsare girar sama data ƙasa yace.
"Ke Zaleeha tashi kije BQ kinyi baƙi."
wani irin tsuke fuska tayi tare da yamutsa fuskar kana tace.
"Baƙi kuma ya Ahmad."
Ya Habune da yanzu ya fito É—akin Mamansu yace.
"Ke shi sa'anki ne yana miki Magana kina zaune,
Zaleeha kifa kiyayeni nagafa baki da kunya ji kike kamar kin kamomu ko?."
Da sauri ta jujjuya mishi kai tare da miƙewa jiki na tsuma domin ita dai Allah ya sani tana tsoron ya Habu da Ya Aminu mugayene na bugawa a mujalla yazu zasuce zasu kai mutun mari.
"Maza ɗauko mayafinki ki ɓace mana daga nan."
Da sauri ta nufi É—akinta,
shi kuwa ya fice daga falon.
A zatonta yana nan shiyasa tayi maza ta fito tana mai yin rolling kanta da É—an kwalin lafiyayyar Arabian gawn É—in dake jikinta,
ganin baya nanne ta zumbura baki tare da cewa.
"Bilkisu muje ki rakani."
Kai bilkisu ta jujjuya tare da cewa.
"Tab ina cikin kallon wannan film É—in ai babu inda zani,
Rashida ta rakaki mana tunda ta gama zanen da takewa Aunty Lubna."
Ahmad É—inne ya kalli Rashida cikin bada umarni yace.
"Rashida rakata ko."
"To" tace tare da miƙewa ta ɗauki mayafinta.
Suna gab da fita aka tafi talla,
ganin haka Bilkeesu ta miƙe tare da cewa.
"MBC Bollywood iyayen talla sun tafi,
muje inga sahibin namu kafin in dawo sun gama tallarsu na tsiya."
dariyan mugunta Rashida tayi, kana suka nufi BQ.

Shi kuwa Ya Ahmad parlour'n Baba Malam ya nufa.
Yana shiga ya samesu da Mamy da Mama da kuma Baba Malam É—in.
Gefen da littatafan addini wanda suke jere ya nufa yana mai cewa.
"Baba Malam su Saifuddeen sun zofa."
kai ya gyaÉ—a alamun to kana yace.
"Ka tura mishi Zaleehan"
"ai tama tafi."
ya bashi amsa yana me zama kusa dashi,
kai ya É—an kwantar cikin sanyin sauti yace.
"Naji tausayin Saifuddeen baba ya bani tausayi, mutun kyakkyawa matashi Allah ya jarabceshi da nakasa mai zafi,
wlh Baba sai ka ganshi yama fi kyau a zahiri akan a hoto,
in dai Zaleeha ta yarda dashi to haƙiƙa tayi dace da miji managarci,
domin sam nakasarsa bata zame mishi kasawa ba, in ka ganshi kamar ba kurmaba, haka inba dan wellchair ɗin da yake zaune a kaiba bazaka taɓa cewa gurgu bane."
Cikin mamaki Mama ta ƙara haɗe fuska tare da cewa.
"Wai maganar me kukeyi hakane ban gane inda kuka dosaba,
Gurgu kurma wurin waye yazo!?."
Cikin isa da tsare fuska Baba Malam ya mata bayanin komai akan Saifuddeen ya ƙara da cewa.
"Kuma ni yamin na yaba dashi muddin bata fidda waniba to niko zan aurawa Saifuddeen ita!."

Kaƙa ƙara ƙaƙa wayyo Mama ina wuta ta faɗa ciki, don baƙin ciki da takaici,
cikin tsananin hatsala da takaici tace.
"Kurma! gurgu!? Yar tawa zaku haÉ—a baki kuce gurgu zaku aura mata?
ai Wallahi bazata taɓa saɓuwa ba."
Mamy ne tayi saurin cewa.
"Kiyi mata fata da addu'an abinda yafi al'khairi zaifi akan mugun furuci baki san inda rabonta yakeba."
Wani irin mugun kallo ta watsawa Mamy tare da cewa.
"Mugun furuci? Akwai wani mugun furucine daya wuce abinda kuka haÉ—a baki kuna cewa,
dan tsabar son k..".
Shiru tayi da bakinta sabida yadda taga Baba malam na watsa mata kallon ki shiga hankalinki kana ya nuna mata ƙofar fita.
Kamar kububuwa haka ta fice cikin zafin zuciya da takaici,
tana isa parlour'nta ta rinƙa kai mari ta kai gwarzo cikin tarin takaici tace.
"Shike nan ga irin ta nan, ni dama sam-sam ban taɓa yin farin ciki da wannan aiki na Zaleeha ba,
ta ƙare lokutanta cikin waɗannan kurame da makafi da guragu,
abinda nike tsoron shike bina,
in banda tsinennen gurgu mai shegen tsaurin ido inashi ina É—iyata da Æ´aÆ´an ministers ma basu isheta kalloba,
wayyo Allah ni Halima Allah ka dubeni da idon rahama wannan kurma kuma gurgu ya Allah tsole idonsa ya zama makaho inga ta inda zai sake kallarmin Æ´a bare yace yana sonta."
zama tayi bisa sofa cikin zafin zuciya da tarin masifa, sai ta kuma miƙewa tamkar an tsikareta, cikin ɗaga sauti tace.
"Ina ai wlh muddin ina raye bazata taɓa saɓuwaba, ɗiyata ta zama matar gurgu kurma nakasasshe.
lallai shima Ahmad, wato ɗan ubanci zai nunawa Zaleeha dan ya gadi munafurcin uwarshi, a rinƙa musu kallon salihai kuma mugaye ne." haka dai tayi ta safa da marwa tana surfa bala'i.

A parlour kuwa tana fita sukaci gaba da abinda ya damesu,
inda Ahmad ya matso mahaifin nashi yana karantar dashi.

A can BQ kuwa suna shiga Zaleeha tayi mamakin ganin Ishaq so sai ta saki ranta a zatonta kawai ziyara ya kawo mata ba wanda Baba malam yace zai zo É—in bane.

Cikin É—an sakin fuska tace.
"Malam Ishaq kaine yau a gidanmu kai lale marhaba."
cikin jin daÉ—in yanayin muryarta yace.
"Yauwa ƙanwata yau kam dai gani na kawo miki ziyara."

"Ai kuwa ka kyauta naji daÉ—i sannunku da zuwa."
ta ƙarisa maganan tana mai kallon Ahmad.
"Yauwa Amaryarmu." Ahmad ya faÉ—a cikin sakin fuska,
da sauri ta É—an waro idanunta wanda kuma sai lokacin ta kalli Saifuddeen dake gefen Ahmad,
kamar abin tsafi idanunsu suka sarƙafe cikin na juna.
wani irin azabebben faɗuwa taji gabanta yayi, wanda a take ta janye idanunta dan sam bata iya juran kallon cikin ƙwayan idanun wanna ɗan ruwan injita da faɗi.
Wani dogon tsaki taja tare da cilla mishi wani zazzafan harara, kana ta janye idanunta da sauri.
wanda ganin haka yasa fara'ar Ahmad daƙushewa.
Rashida ce ta kalli Ahmad cikin kamala tace.
"Ina wuni."
jiki a sanyaye yace.
"Lafiya lau ya gida."

"Alhamdulillahi"
Bilkisu tace dashi,
ita kuwa Zaleeha juyawa tayi ta fuskanci Ishaq rai a ɗan ɓace tace.
"Ya Ishaq ya mutane na?."
gyara zamanshi yayi tare da shafa cinyoyinshi irin yadda al'adar makafi take yace.
"Duk suna lfy sunce in gaidaki."
Cikin É—an sakin fuska ta kuma cewa.
"Ina ko amsawa."
sai kuma ta É—an daure ta É—an kalli Ahmad a fizge tare da cewa.
"Ina wuni."
A gajarce yace. "Lafiya!."

Juyawa sukayi kan Bilkeesu jin tana cewa.

"To waye ne angon namu a cikinku?."
Dan so take taje taci gaba da kallonta.
Ahmad ne ya kalleta cikin cikar haiba ya nuna Saifuddeen da yake hukunta Zaleeha da ƙwayar idanunshi kana yace.
"Gashi nan wannan shine angon naku mai jiran gado in Allah ya yarda."
Kusan a tare su duka uku suka zuba mishi ido.
ita Zaleeha wani irin mutuwar zaune furucin Ahmad ya jaza mata,
hatta bakinta data buÉ—e dan cewa hahhhh Allah bai bata iko da damar rufeshi ba.

Bilkeesu da Rashida kuwa wani irin kallo sukewa Saifuddeen tare da cewa.
"Masha Allah. Kai angon nan da amaryarnan sune sirrin kyau."
sai kuma Rashida ta kalleshi cikin mutuntaka taka tace.
"Ina wuni ango mai jiran gado."
shiru bai amsaba sai ta kuma yin murmushi tare da cewa.
"Rowar murya ne angon zai mana?."
Ahmad ne ya d'an tab'ashi wanda sai yanzu suka lura cewa kan whellchair yake zaune.
kusan a tare suka kalleshi suka kalli Zaleeha sai kuma suka kalli juna cikin tarin mmki.
Bilkeesu ce tayi ƙarfin halin cewa.
"Ina wuni angon Zaleeha."
Kai ya jinjina mata alamar lfy,
tare da yi mata mgna cikin body language.
"Ya kuke."
tofa abin ya fara zarta zatonsu cikin son gano gaskiyar abin Bilkeesu tace.
"Wai meyasa baya Magana ne? Kodai zuwanmu tarene ya ɓata mishi rai?."
Ishaq ne ya É—anyi Murmushi tare da cewa.
"No, ai kurmane bayaji kuma baya Magana."
Ya ƙarishe maganar cikin rashin damuwa dan shi a wurinshi sam nakasa ba kasawa bace.
Da ƙarfi suka haɗa baki wurin cewa.
"Toh kurma kuma gurgu a kan whelchair!."
sai kuma Bilkeesu ta tuntsure da wata iriyar dariya mai cike da jin daɗi kana ta bugi ƙafar Zaleeha tare da cewa.
"To Hajiar babu nakasashe sai rago. Lallai yau shirinki ya miki rana kin samo zankaÉ—eÉ—en saurayi kurma kuma gurgu."
ina ita ma Rashida tuni dariyarta da take dannewa ya subce mata.
Ahmad kuwa wani irin haÉ—e fuska yayi tamkar zaiyi ruwan jini.
Ishaq kuwa cikin kaushin murya yace.
"Ke Zaleeha waɗan nan ƙawayen naki wasu irin muta nene da basu san daraja da ƙimar ɗan adam ba?
me a jikinmu da zasuyi ta mana dariya."
cikin dariya Bilkisu tace.
"Kai tafi daga nan makahon banza makahon wofi.
In banda iskanci ina wannan gurgun ina zankaÉ—eÉ—iyar baby kamar Zaleeha."
Cikin zafin rai da tsawa Ishaq yace.
"Ke Zaleeha ki dakatar da wannan mahaukaciyar ƙawar taki da wanna hauk..".
Shiru yayi ba tare daya ƙarasa zancen nasa ba jin wani irin kuka mai cin rai da Zaleeha ta saki da ɗan ƙarfi cikin ɗaga murya tace.
"Ya isa! Ya isa!! Ya isa!!! Haka malam Ishaq ka farka daga wanna wawan baccin da kakeyi har ya kaika dayin mummunan mafarki.
Ƙawata ba mahaukaciya bace,
sai dai ko wannan dutsen da ka zo dashi shine mahaukaci."
Cikin tsananin fushi Ahmad ya yunƙura,
sai ya kuma koma ya zauna jin wani irin zazzafan riƙo da Saifuddeen ya yi mishi wanda ya zubawa su Zaleeha da ƙawayenta ido yana gane duk abinda suke faɗin.
Cikin zafin rai Ahmad yace. "Waye kike cewa dutsen?."
A zafafe ta kalleshi tace.
"Shi wannan halittan ruwan da kuka zomin dashi.
Me marabarshi da dutse, kurma kuma gurgu, kalleshi kamar al'jani dan kyau.
Ginennen taɓo kawai."
Sai ta kuma juyo ta kalli ishaq cikin kuka ta haÉ—e hannayenta duka biyu wuri É—aya alamun neman al'farma tamkar yana ganinta tace.

"Dan Allah Malam Ishaq kada ka sake min wanna haukan, kadai san ina ganin ƙimarka da darajar ka, so please bana sonshi na tsaneshi!."
Sai kuma ta juyo ta kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Wallahi kurwata kurr ko kaine sarkin mayu to ni nan Zaleeha nafi ƙarfinka, nan gani nan bari, ƙwalelen kare da hantar kura, mcheeww banza kawai!! "
Hannu tasa ta jawo hannayensu Bilkisu daketa dariyar ƙeta tayi, fuuuuu suka fice daga cikin falon...

Ina Ahmad fa bazai iya magana ba, dan tsananin ɓacin rai da jin tsanar Zaleeha a ranshi.
Miƙewa yayi a fusace ya koma bayan Saifuddeen tare da tura whelchair ɗin cikin ƙunan rai yacewa ishaq.
"Mu tafi ishaq."
shima ishaq rai a ɓace ya miƙe yabi bayansu.

Mota suka shiga, kana Ahmad ya figi motar ya bar harabar gidan.

Suna isa gida ko Dai-dai ta parking baiyi ba ya fito tare da kawowa Saifuddeen whelchair É—inshi ya zauna kana suka nufi cikin gida.
Kai tsaye parlour Ummi suka shiga,
suna isa tsakiyar parlour'n Ahmad yayi wani irin z...!

By
*GARKUWAR FULANI*
8/19/20, 2:32 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

         *NAKASA BA KASAWA BACE*

                          *Page 28*

   *NA*
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Zamewa Ahmad  yayi ya zauna bisa kujerar dake bayanshi tare da sanya hannayensa duka biyu ya dafe kansa, dake bala'in sarawa, wani irin kukane ya ƙwace masa ransa cike yake da ƙuna haɗi da takaicin abun da Zaleeha tayi musu, yanda yakejin ƙuna acikin ransa harya zarce misali, wani  irin tafarfasa zuciyarsa keyi masa, harzuwa yanzu kalaman da su Zaleeha suka faɗa ga ɗan uwa kuma abokinsa basu daina yawo acikin kunnuwansa ba,  Ishaq ma zama yayi tare dayin shiru, tunda yake bai taɓa jin ɓacin rai irin na wannan ranan ba, sam shi bai ɗauki nakasarsu amatsayin kasawa ba, baitaɓa tunanin zasu fuskanci irin wannan tozarcin da cin fuska dalilin nakasarsu ba,  shin menene aibunsu? Menene aibun nakasarsu? Ashe Allah Bashine ke aiwatar da komai bisa abun daya so ba? haƙiƙa bawai don Allah Bayasonsu bane ya jarrabesu da nakasa, ƙaddara ce wacce yayi imani tanakan kowani bawa, babu wanda yafi ƙarfin nakasa kuma babu wanda ya isa ja da ikon Allah.
Shin ashe dama da gaskene Nakasassu na fuskantar iriren waɗan ƙalubalen yayin nemanaure da lafiyayyu, anya kuwa anayiwa nakassasu adalci? ace wai dole sai dai nakasasshe ya auri nakasasshiya ƴa uwarshi".
  Shi makoho ne bazai iyayin kukan cikin idanu ba, hakan yasa yakeyin na zuci wanda yafi na fili ciwo.
A hankali Ahmad ya ɗago jajayen idanunsa, cikin wani irin tururi da zuciyarsa keyi masa, ya dubi Saifuddeen,  hawayene suka sake gangarowa daga cikin idanunsa sakamakon wani irin tsananin tausayin Saifuddeen ɗin daya kamasa. Cikin muryarsa dake rawa  yace.
  "Sam ba matar aure bace Saifuddeen, wannan bata dace dakai ba, kabarta Saifuddeen, dan Allah ka ƙyaleta kasayawa zuri'armu mutumci, sannan ka sayawa ƴaƴanka tarbiya, Kabarta Saifuddeen ba irinta ya dace ka aura ba, sam batasan menene Ƙaddara ba, batasan me ake nufi da ƙudurar Allah Ba!". 

Idanu Saifuddeen ya lumshe tare da cije laɓɓansa, shikaɗai yasan me yakeji acikin zuciyarsa, shikaɗai yasan yanda ƙirjinsa ke duka,   ahankali ya ware idanunsa wanda suka ɗan sanja launi, hannayensa yasanya ya dafe dai-dai inda zuciyarsa take,  cikin nuna alama yace.
"Ina sonta Ahmad, Ina matuƙar sonta, sonta tamkar numfashi yake agareni, bazan iya rabuwa da ita ba, kasan so Ahmad!".
Hannayensa ya haɗe waje guda alaman ban haƙuri agaresu.

Tasowa Ahmad yayi tare da ƙarasowa har gaban keken Saifuddeen, cikin yanayi me ɗauke da tsananin tausayawa Ahmad ya rungume Saifuddeen, tare da sakin sabon kuka, tunda yake bai taɓajin zafi da ciwon Nakasar da ta samu Saifuddeen ɗinba sai yau.
Ummi datun shigowarsu ke tsaye abakin kitchine tana jinsu batare dasun kula ba, wani irin karyewa zuciyarta tayi, yayinda tsananin rauni ya bayyana akan fuskarta, idanunta ne suka cika tab da ƙwalla, cikin sanyin jiki ta tako ta ƙaraso cikin falon,   jin motsinta yasanya Ahmad sakin Saifuddeen ya juyo tare da kallonta, ganin yanda hawaye ke gudana akan idanun Ahmad ɗin yasanya hawayen dake cikin idanunta samun daman gangarowa, murya araunane tace.
"Kada ka ɓoyemin komai Ahmad, taƙisa ko? taƙisa saboda Nakasar dake tattare dashi ko?".
Wani murmushi mai ciwo Ummi tayi tare da duban Ahmad cikin rawar murya tace.
"Sanar dani gaskiya Ahmad kada ka ɓoyemin!".
Kuka Ahmad ya fashe dashi tare da zama akan kujera, ayanda yakejin zafi da tsanar Zaleeha acikin zuciyarsa bayajin zai iya rufe cin mutumcin da tayi musu, cikin muryar kuka yasanar da Ummi duk abun daya faru inda ya ƙarishe maganan  yana kuka sosai, don sosai abun keci masa rai.
Hawayene suka cigaba da fita daga cikin idanun Ummi.  Sosai hankalin Saifuddeen yakai ƙololuwa wajen tashi sakamakon ganin da yayi Umminsa na kuka, aduniya idan akwai abun da ya tsani gani to hawayen Umminsa ne, Yana matuƙar son mahaifiyarsa ta yanda bayason shiga damuwarta koda ta ƙwayar zarra ne, sam baiso ace sanadinsa Umminsa ke kuka ba, ahankali ya shiga murza kekansa har ya ƙaraso gareta, hannayensa yasanya yashiga share mata hawayen dake fuskarta, ɗago kai Ummi tayi tana kallonsa, Idanunsa wanda sukai ja ya lumshe tare da gigiza mata kansa,  wani irin sabon kukane ya zo mata, hakan yasa takawar da kanta gefe,  ji take kamar zuciyarta zata fashe saboda tsabar tsananin tausayin ɗan nata daya cika zuciyarta,  cikin dauriya haɗi da ƙoƙarin kauda rauninta ta juyo ta kallesa, hannunta tasanya ta shafi ƙuncinsa cikin son kwantar masa da hankali tace.
  "Kada  hakan yasanya rauni acikin zuciyarka Saifuddeen, idan ita taƙika balallai ne ace kowacce mace taƙi kaba, haƙiƙa nasan itama rashin sanin nagartan kace yasanyata ƙin amincewa, amma sam baƙinka take ba, babu macen da zata ƙin Saifuddeen, saidai taƙi aminta dakai abisa rashin sani nagartarka."
Lumshe kyawawan idanunsa yayi tare da ɗan sakin murmushi, haƙiƙa yaji daɗin ƙarfin guiwan da Ummin nasa ta basa, har acikin zuciyarsa yaɗanji sanyi.
Ahmad dake kallonsu tsananin tausayinsu ne yasake rufesa, hannayensa yasanya ya sharce hawayen dake kan fuskarsa. 
Ishaq kuwa kasa cewa komai yayi, raunin dake zuciyarsa yasanya gaba ɗaya jikinsa yayi weak, sosai kukan da Ummi tayi ya taɓa masa zuciya, sam baitaɓa tsammanin haka daga Zaleeha ba koda wasa, baitaɓa tunanin cewa ƙuruciyarta zai ruɗeta har takai gayi musu rashin mutumci ba, haƙiƙa zafafan kalaman da ta faɗamusu sun daki zuciyarsa sosai, sam bai damu da baƙaƙen maganganun da ƙawayenta suka faɗa musu ba, saboda koba komai sudama basaninsu sukayi ba, amma ita Zaleeha fa?."

Cikin son kwantar musu da hankali shida Ishaq Ummi tashiga basu baki, tare da yi musu nuni da cewa, ɗan Adam baya taɓa iya tsallake ƙaddaransa, ko ba gasu bama, mutanen da suke da cikakkiyar lafiya ma suna iya fuskantar irin haka, sannan taƙara da tausasa musu zuciya,  sam Ummi bata barsuba saida taga zuciyar kowannensu yayi sanyi, amatsayinta na Uwa ta gari, haka ta shanye gaba ɗaya damuwarta ta kwantar musu da ɓacin ransu, cikin ɗan nutsuwa da Ishaq ya samu, ya tashi tare dayiwa Ummi da Saifuddeen Sallama, Ahmad ne ya rakashi har waje, inda driver'n sa ke tsaye yana jiransa.  Koda Ahmad ya dawo daga rakiyan Ishaq kai tsaye ɓangarensu ya nufa.

lura da Raliya tayi cewa mijin nata yana cikin yanayi marar daÉ—i, yasanyata kwantar da murya tare da lafewa ajikinsa, cikin salo irin nata na Æ´a mace ta shiga kwantar masa da hankali tare da neman sama nutsuwa, lokaci guda ta fitar dashi acikin hayyacinsa, inda ya rungumi matar tasa tare da kawar da duk wata damuwa dake cikin ransa.

Cikin son samawa zuciyarsa nutsuwa ya sarrafa kekensa, inda ya nufi hanyar ɗakinsa,  yana shiga ya turo ƙofar ɗakin ya rufe,  ahankali ya tuƙa keken nasa tare da ƙarasowa cikin tsakiyan ɗaki, cikin hikima ya cire kayan jikinsa, inda ya rage dagashi sai boxer,  kaitsaye bathroom ya wuce, nan ya haɗawa kansa ruwan wanka, kamar yanda ya saba, cikin hikima yayi wankansa,, bai wani jima acikin banɗakin ba yafito sanye da bathrobe ajikinsa,   sama-sama yashafa body lotion ɗinsa, tare da feshe gaba ɗaya jikinsa da daddaɗan turarensa, sif ɗinsa ya buɗe tare da ciro wata farar short sleeve da kuma wani combat 3 guater jeans ya sanya, sosai kayan suka amshi jikinsa,   kasancewar akwai alwala ajikinsa, yasanya ya shumfuɗa sallaya tare da sauƙa daga kan kekensa, kamar kullum kuma koda yaushe azaune ya gabatar da sallan Magrib ɗinsa, bai tashi akan sallayan ba harsaida yayi sallan Isha, koda ya gabatar da addu'o'insa kamar yanda ya saba, yunƙurawa yayi ya hau kan kekensa, cikin nutsuwa ya shiga tura keken nasa har izuwa bakin haɗaɗɗen gadonsa wanda aka lailaye samansa da tattausan bedshet mai kyau,  cikin hikima ya sauƙo daga kan keken nasa tare da kama jikin gadon nasa ya hau,    kwanciya yayi luf akan gadon tare dakai hannunsa gefen gadon inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe,  bedsite lamb ya kunna, sai yanayin ɗakin yayi daɗi shiba duhu ba shikuma ba wadataccen haske ba.

Ɓangaren Zaleeha kuwa, ranta amatuƙar ɓace haka suka koma falon Mama, cikin rufewar ido Zaleeha na shiga cikin falon ta yaye mayafin kanta, saboda tsaban ɓacin rai da takeji, idanunta har rufewa suke, cikin ƙunan zuciya tace.
"Ni! wai ni! Zaleeha Kurma kuma Gurgu zaizo yace yanaso,
lallai mutanen nan sunfara ganin damata da yawa, chab lallaima nakasassunnan, wato shiga cikinsu da nakeyi ina murmushi shine abun dayasa harsuka rainani ko, waima wannan ɗan ruwan ni zaice yanaso na, ko nayi masa kama da kalan matar aurensa ne?, da sauri taƙarasa gaban ƙaton madubin dake jin k'ofar falon, tsayawa tayi tana me ƙarewa kekyawar surar jikinta kallo, wani irin kuka ta fashe dashi tare da kai dubanta ga su Balkisu waƴanda sukayi saƙare suna kallonta, cikin ƙunan rai da sheshsheƙan kuka tace.
"Shin nima akwai wata nakasa ajikina ne dahar wani banzan nakasashshe zaizo yace yana sona?".
Dariya Bilkisu ta kwashe dashi cikin tsananin shaƙiyaci tace.
"Kawai ganin dama ne irin nasa, hmmm amma wallahi wannan mutumin ya raina miki hankali, tayaya ma in ban da rashin tunani irin nasa da tsaurin ido zai dubi ajibon yarinya kamarki yace wai yanaso".
  Dariya ta ƙara kwashewa dashi tare da tafa hannunta, cikin son ƙara cusawa Zaleeha tsanan Saifuddeen tace.
"Kurma fa, kuma bayan haka ma wai gurgu, lallai kam aikuwa daki auri wannan gwara kin auri dutsi, donshi dama dutsi-dutsi ne bayako motsi, sai inke kika motsa shi, amma wannan kam banga dame zai amfaneki ba, saidai in kuma ko zaman jinyarsa zakiyi ba zaman aure ba!".

Rashida ce ta sauƙe ajiyar zuciya tare da duban Bilkisu dake ta dariyan mugunta, cikin ƙasa da murya tace "Haba Bilkisu dan Allah kibari hakanan, nifa Allah gayen yabani tausayi, sannan tsantsar kyawunsa ya tsoratani, koda farko Allah banso yin dariya ba kedaice kika sani, amma gaskia gayen sam bashida wata makusa, kunfasan wata nakasar bata zama kasawa, idan kikaga nakasashshe ya kasa, to tabbas ya kashe zuciyarsa ne, kuma kunsan nakasar zuciya tafi kowacce nakasa ciwo, sannan ayanda na fuskanci mutanen nan sam su awajensu.
Nakasarsu ba kasawa bace, don tabbas baƙaramin jahadi sukayi ba da sukazo miki da maganar Soyayya kuma ai komin yaya masoyi yafi mak'iyi".

Wata uwar harara Bilkisu ta aunawa Rashida cike da baƙin ciki tace.
"Tab amma dai Rashida baki da kai, me za'ayi da waƴannan nakasassun, kyawunsa na banza na wofi, idan kece suka zo gunki da batun soyayya na tabbata bazaki amince ba."   Tsagaitawa da maganan tayi tare da dafa duka kafaɗun Zaleeha cikin zugan hasada tace.
"Wallahi kada kiyarda ki kashe rayuwarki wajen zama da nakasasshe, me wannan zai yi miki wanna ai dashi da mace duk d'aya, saidai baƙin cikinsa yayi ajalinki,  da kyaunki da ƙuruciyarki da komai ki cuci kanki ki auri nakasasshen da bazai iya kauda miki budurcinki bama, ae wallahi Zaleeha kinci baya!".

Wani irin kuka Zaleeha ta sake tare da faÉ—awa jikin Bilkisu cikin aminta da kalaman nata tace.
"Bazan taɓa sauraransa ba Wallahi, koda ace duk duniya zasu taru akaina don na soshi, na kuma zauna dashi, bazan taɓa aminta ba, Wallahi na tsaneshi tsana me tsanani, danayi rayuwar aure dashi gwara na mutu, don bazan iya ɗaukar baƙin cikinsa ba!!".
Cikin kukan dayaci ƙarfinta ta juya da gudu ta wuce ɗakinta.
Wani irin munafukin killer smile Bilkisu tayi tare da bin Zaleehan da kallo.
Rashida kuwa ajiyar zuciya ta sauƙe tare da kwantar da kanta gefe, cikin sanyi tace "Amma Bilkisu dakin tausasa harshenki akan sa, saboda ƙaddara nakan kowa.....".

"Dakata Rashida ai nima nasan ƙaddara nakan kowa, amma wannan nakasashshen gurgunne dai Insha Allah Zaleeha bazata aureshi ba".

Ajiyar zucia Rashida ta sauƙe tare da ɗaukan jakarta, duban Bilkisu tayi tare da cewa. "Natafi sai gobe saduwar al'khairi".

Da sauri itama Bilkisu ta É—auki jakanta tabi bayan Rashidan, don sam bataso kowa yagane ainihin nufi dakuma abun dake ranta da zuciyarta, saboda ita tamkar mage take me kwanciyar É—aukan rai...

SAIFUDDEEN.

Gyara kwanciyarsa yayi tare da gyara zaman kansa dake bisa pillow, idanunsa ya lumshe tare da sauƙe ajiyar zuciya, filla-filla kalaman Zaleeha da ƙawayenta ke dawowa cikin idanunsa, inda idanunsa keyi masa imagine duk wani motsin bakinsu,  ƙam-ƙam haka ya kulle idanunsa tare da cije laɓɓansa, haƙiƙa yaji kalamanna Zaleeha har acikin zuciyarsa,  saidai kuma tsananin soyayyar da yakeyi mata yariga dayaci ƙarfinsa.
  Jin soyayyarta yake Tamkar zata zautar dashi, sake lumshe idanunsa wanda ke ɗauke da tsananin mayen sonta yayi, wani irin murmushi yayi wanda ya ƙawata fuskarsa,  cikin zuciyarsa yace. 
"Dakin sani da baki nemi cin zarafinmu ba, domin hakan da kikayi bazai taɓa sanyawa na janye batun aurenki ba, ko yasa muradinki ya fita araina ba, kin ƙaramin sonki sannan kuma kin ƙara min kwaɗayi da burin aurenki, bazai taɓa yiwuwaba, kowacce ƙaddara da sanadinta, kuma ni dai nasan Allah ne ya d'ora min sai daifa duk abinda ya sameni arayuwa ta sanadiyarkine, kece kikajamin komai, sannan kuma dole ke zan aura, kamar yanda ƙaddarata akanki take to dole kema saikin ɗanɗani ƙaddaranki dake kaina, zan aureki koda bakyaso!, zankuma shayar dake mmaki da zazzafar soyayyata irin wanda zata zautar dake batare dakin shiryawa hakan ba!".
sake muskutawa yayi tare da gyara kwanciyarsa,  tabbas ayanzu yaɗauki ɗamaran fuskantarta sam kuma bada wasa zaije mata ba, lallai al'ƙawarine sai ya shayar da ita ruwan mamaki, haka yadinga saƙa abubuwa da dama aransa har bacci ɓarawo ya ɗaukesa.

Ɓangaren Zaleeha ma da ƙyar ta iya bacci, ita kaɗai tasan irin suyan da ƙirjinta keyi mata, haƙiƙa sosai zuwan kurma kuma gurgun da ko son jin sunansa batayi ya ɓata mata ranta, babuma abun dake hassalata kamar irin kallon da taga yanayi mata tamkar wani tsohon maye bugu da k'ari kwarjinshi na sata rud'ewa, sannan kuma ta lura duk irin rashin mutumcin data surfa masa sam bai ɓata ransa ba, don bata ga alaman ɓacin rai akan wannan munafukar farar kyakkyawar fuskartasa ba, yau ko tunanin abincin ruhinta batayi sosai ba saboda baƙin ciki, haka tayi bacci cikin ƙuncin rai, wani abun mamaki kuwa fuskarsa ce tayita zuwa mata acikin baccinta.

Washegari.

Saboda yanda ranta ke ɓace sam ko shirin fita wajen aikima batayi ba, don gaba ɗaya jinta take wani irin kamar wata marar lafiya.

Saifuddeen kuwa yau da wani irin sabon tsarin plant ya wayi gari, harzuwa yau yanajin cewa shi nakasarsa ba kasawa bace agaresa, akan dinning table sukaci abinci su dukansu cike da ƙaunar juna,  inda Hayatuddeen keta damunsu da zancen Asma'u Ahmad Matawalle, zancen nasa ɗayane shine yanda yake faɗin takurawan da tayi masa da zancen hammansa, harma cewa tayi wai idan ayyuka sukai mata sauƙi zatazo Gombe'n ta dubashi.

Ummi ce taÉ—ago kai ta dubeshi cikin É—an mamaki tace.
"Au ma'aikaciya ce ma kenan to Allah ya taimaka."

"Ameen, ma'aikaciyace amma bata gomnati kota kamfani ba, jarumace ƴar film kuma mawaƙiya".
Hayatuddeen ya ƙare maganar yana mai sanya soyayyen chips abakinsa.

Baki Ummi ta taɓe tare dayin murmushi kawai ta girgiza kanta, tabbas tasan da ace Saifuddeen ɗinta macece to fa da ankwashi ƴan kallo don ba makawa maza asuke musu layin zance aƙofar gida. 
  Haka suka kammala breakfast ɗin cikin lumana, inda Saifuddeen ya tura kekensa har zuwa tsakiyan falon, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga internet don ɗebewa kansa kewa.

Sake muskutawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya, duk da ɓacin ran dake shumfuɗe aƙasan zuciyarta amma hakan baihanata jin cewa abun da tayiwa  Ishaq bata kyauta ba, sai yanzu kalaman da ta faɗawa Ishaq din ke dawowa cikin brain ɗinta, haƙiƙa tasan Ishaq kamilin mutum ne sannan kuma jajirtacce ne, sam abun da tayi masa bai dace ba, saidai kuma koma me yafaru shi ya jawo, sannan abun da tayiwa abokinsa kuwa ko kaɗan bata dana sanin hakan, don ko ayauma yace zaizo zatayi masa wanda ya ninka na jiya.
Wayarta ta ɗauka tare shiga contact ɗinta, number'n Ishaq ta zaƙalo, ɗan cije bakinta tayi cikin gamsuwa da zuciyarta ta dannawa number'n Ishaq ɗin ƙira, don tanaso taɗan bashi haƙuri akan abun daya faru, harsaida wayan ta kusa katsewa kafun akayi picking, cikin sassanyar muryarta tace.
"Assalamu Alaikum, Malam Ishaq barka da safiya."
Shiru taji anyi batare da anyi magana ba, hakan yasa taɗan ƙara duban screen ɗin wayar, ganin cewa eh da gaske an ɗaga wayanne yasanya cikin zazzaƙan muryarta tace.
"Dama haƙuri nakeso na baka akan......".
    ƙit taji ankashe wayar, da sauri ta cire wayar daga kan kunnenta, tare da duban screen ɗin wayar, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da sake dialing number'n.
Ishaq dake zaune akan table ɗinsa yanajin wayartasa na ringing amma ya share,  har yanzun baigama hucewa ba danko ɗaga wayar da yayi ɗazun ma rashin sanin cewa itace yasanyashi ɗagawa amma sam baida niyar ɗaga wayarta. 

Zaleeha kuwa jin wayar harta katse ba a ɗauka ba, yasanyata sake ƙiran number'n nanma har ya katse ba ayi picking ba, saida taƙira har sau uku amma no answer,  hakanne yasa tagane cewa Ishaq yayi fushi sosai, ɗan taƙaitaccen text message ta rubuta masa na bada haƙuri kana ta aje wayarta..

Cikin wata haɗaɗɗiyar boyel yellow colour wanda taji ɗinkin straight jumper ya shirya kansa, boyel ɗin irin mai tsadan nanne hakan yasa aka fesa haɗaɗɗen aikin ajikin wuyanta da coffee brown ɗin zare, sosai kayan yayi kyau, takalmine sau ciki mai kalan coffee brown sanye aƙafarsa yayinda ya ɗaura haɗaɗɗiyar hula akansa itama me kalan Coffe brown, sosai yayi kyau ba abun da jikinsa keyi sai tashin ƙamshi,    cikin nutsuwa yake tura whelchair ɗinsa har ya ƙaraso babban falon na Ummi.
Ummi dake zaune hannunta riƙe da carbi tanaja, tana ganinsa ta saki murmushi cikin kulawa ta dubesa tare da cewa.
"Sai ina kuma?."

Murmushin daya ƙara bayyana cikar kwarjini da haibansa yayi, cikin nutsuwa yayi ƙasa da kansa, sam ƙarya ba al'adarsa bace bata kuma daga cikin ɗabi'arsa, hakan yasa yaɗanyi jim kafun ya ɗago kansa ya kalleta, cikin body language ɗinsa yayi mata alama akan cewa gidansu Zaleeha zashi,  shiru Ummi tayi tare daɗan yin murmushi, wani irin fargaba ne taji yacika zuciyarta,  hakanan taji tsoron zuwansa gidan su Zaleehan ya kamata, saboda batasan wannan karon kuma me Zaleehan zata faɗa masa ba, cikin son nuna rashin damuwarta tace.
  "Masha Allah, amma dai ae zaka ƙira Ishaq ko Ahmad don su rakaka ko?."
Murmushi yayi tare daÉ—an lumshe idanunsa sarai ya fuskanci me Ummin ke gujemasa, amma dayake abun da zuciya ke so ne hakan yasa yayi mata alaman cewa.
"Insha Allah.Ba abun dazai faru."

Ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe tare dayi masa fatan dawowa lafiya, cikin body language ɗinsa ya amsa mata da "Ameen." 
Idanunta akansa harya fice daga cikin falon, ajiyar zuciya ta sauƙe, lokaci guda hawaye suka cika idanunta,  haƙiƙa tana tsananin jin tausayin ɗanta Saifuddeen, musamman ma yanzu da ta hango soyayyar Zaleeha kwance acikin ƙwayan idanunsa,  cikin dauriya ta maida hawayen nata tare da jingina bayanta da jikin kujera, ahankali take jan carbin tana me tasbihi ga Allah.

Shikuwa Saifuddeen yana fitowa daga falon Ummin kaitsaye inda Sule driver ɗinsa yake ya nufa, Sule dakansa ya buɗewa Saifuddeen ɗin murfin motar, cikin hikima kamar koda yaushe haka ya shiga gidan baya ya zauna, both ɗin motar Sule ya buɗe inda ya aje keken Saifuddeen aciki,  cikin ɗan hanzari ya shige wajen zaman driver tare dayiwa motar key. 

Fitowanta awanka kenan, gaba ɗaya fatar jikinta ɗauke yake da danshin ruwa,  towel ne ajikinta wanda iya karsa guiwarta, zama tayi akan kujeran gaban mirror tare da ɗaukan handrayer'n ta ta jona ajikin socket,  dashi tayi amfani wajen busar da dogon gashin kanta wanda ke jiƙe da ruwa, tana kammala busar da gashinnata ta shafawa gashin nata olive hair oil mai tsananin ƙamshin zaitun,  cikin nutsuwa ta shiga taje dogon gashinnata wanda tsawonsa ke taɓa har tsakiyar bayanta,  wani baby yellow ribbom tasanya akannata tare da tattara gashin tayi farkin nasa agefen wuyanta,  body lotion ɗinta mai daɗin ƙamshi ta shafa agaba ɗaya jikinta,  powder'nta wanda aƙalla kuɗinsa zaikai 8k ta shafa akan fuskarta,  wani light mochka colour lipstick ta shafa akan siraran pink lips ɗinta,  sosai lipstick ɗin ya amshi ɗan ƙaramin bakinta,  black eye pencil taɗauka tare da buɗe idanunta ta goga acikinsu, da water proof mascara tayi amfani wajen miƙar da zara zaran gashin idanunta, wanda suke ga cika ga kuma tsawo, kallon kanta tayi acikin madubi'n, murmushine ya bayyana akan fuskarta don ita kanta tayi na'am da kyawun da tayi, haƙiƙa sau da dama takan godewa Allah agame da baiwan kyau daya bata. 
Miƙewa tayi ahankali tare da ƙarasawa gaban ƙaton drawwer'n ta,  buɗe drawwer'n tayi tare da zaro wani tsadadden yadi mai kallan yellow light, sosai yadin ya haɗu yayinda aka ƙawatasa da ɗinkin riga da sket pieces,   koda ta sanya kayan baƙaramin kyau sukayi mata ba, sket ɗin ɗas ya zauna ajikinta yayinda ya bayyana faffaɗan ƙugunta wanda ke ɗauke da wani irin tsareren hips mai jan hankali, kasancewar sket ɗin yakamata hakan yasa tsararren hips ɗinta bayyana, kamar yanda sket ɗin yayi mata ɗas ajiki haka ma ƴar fitted ɗin rigan ta amshi jikinta sosai saboda irin yanda rigar ta kamata yasanya har kana iya hango beautiful breast ɗinta ta saman wuyan rigar saidai ba sosai ba,  wani ɗan manne'n ɗan kunne mai kyau ta saƙala akunnenta tare da sanya wata ƴar siririyar sarƙa awuyanta,  zama tayi agaban dressing mirror tare da tsantsara ɗaurin turban akanta,  masha Allah kyau kam Zaleeha tayishi harta gaji.

Tunda suka ɗauki hanyar G.R.A ɗin yakejin wani irin shauƙi aransa, babu abun da idanunsa ke ɗoki kamar ganin kyakkyawar fuskarta, baisan wani irin so yake mata ba, da tunani kala-kala acikin ransa harsuka iso gaban tangamemen gate ɗin gidan,  horn Sule driver yayi inda take maigadin gidansu Zaleehan ya wangale musu gate,  acikin compound ɗin gidan Sule driver yayi parking motar,  daidai lokacin Ya Aminu ya fito daga ɓangaren Mamy hango Saifuddeen dake ƙoƙarin fitowa amota da yayine yasanyashi ƙarasowa garesu.

Da turarenta mai azababben ƙamshi ta feshe gaba ɗaya jikinta, wani ɗan siririn mayafi mai kalan kayanta ta yafa daga kan wuyanta zuwa ƙugunta, yanayin yanda dogon baƙin gashinta ya kwanto akan gefen wuyanta shi ya matuƙar ƙara ƙawata ado da kuma kyawunta, wani takalmi mai uban tsini ta sanya aƙafafunta, cikin takunta mai nuna tsantsar aji, ƙasaita, wayewa, da kuma jinkai tafito zuwa falo, nan ta iske Mama da kuma Zahira suna hira, duban tsab Mama tayi mata fuska shafe da toka tace.
"Sai ina?."

Zama tayi akan hannun kujera tare da É—an turo bakinta gaba murya acushe tace.
"Makay zanjeni yin shooping".
Baki Mama ta taɓe tare da gyara zamanta ta fuskanci Zaleehan, fuskarnan tata sam babu alaman fara'a tace.
  "Ya kukayi da banzan gurgun da yazo wajenki jiyan?."

Lokaci guda yanayin fuskar Zaleeha ta sauya kala domin tunowa da baƙin cikinsa da tayi, cikin bayyana tsantsar tsanarsa da tayi tace.
  "Na musu bana sonshi." 
Ƙwafa tayi tare da ɗan gyara zamanta tacigaba da cewa.  "Wai harni wani banzan MUSAKI zaizo yace yana son ƴata hmm!."
Murmushin jin daɗi Mama tayi tare da ci gaba cewa. 
"Ae ni banga laifinsa bama, dama ni tuncan wannan ɗan iskan aikin naki na Babu maraya  ne, ko Nakasa ba kasawa bace ko mene yake da suna, sam ba ƙaunarsa nake ba, amma dayake ke uwar taurin kaine haka kike zuwa cikin nakasassu musakai kita washe haƙora kina naɗan muryarsu wai ke adole mai tausayi ƙaunarsu, to ai gashinan kin fara ganin sakamako tunda dai har Kurma kuma gurgu yasamu daman biyoki har gida da maganar soyayya.

Hannu Ya Aminu ya bawa Saifuddeen suka gaisa amutumce, nan Ya Aminu dakansa yayiwa Saifuddeen jagora zuwa BQ, shikam har acikin ransa ya yaba da nutsuwa da kuma haiba haɗi da kwarjini irinta Saifuddeen, koda Ya Aminu yayi masa jagora zuwa BQ cewa yayi dashi bari ya ƙira masa Zaleehan, cikin body language Saifuddeen yace "To."
Tare da yiwa Ya Aminu'n godiya.

Ɗan ƙaramin bakinta taƙara cunowa gaba, tare da gallawa Zahira dake ta dariya ƙasa ƙasa najin cewa wai kurma kuma gurgu yazo wajen yayartata da ƙoƙon barar soyayya, baki Zaleeha ta buɗe don kaftawa ƙanwartata rashin mutumci shigowan Ya Aminu ne yasanyata saurin haɗiye maganan dake ranta, dan da tayi niyan aunawa mayataccen gurgun zagine, kana daganan saita ci mutumcin Zahira dakeyi mata dariya.
Duban Zaleeha Aminu yayi fuskarnan tasa sam babu alaman annuri akanta, cikin tsare gida yace.  
"Ke Zaleeha kije kina da baƙo a Boys Quaters."

Wani irin faɗuwa gaban Zaleeha yayi, cikin sarƙewar murya tace.
"Ni...Ni kuma Ya Aminu?."
Harara Ya Aminu ya watsa mata cikin yanayinsa na rashin fara'a agaresu yace. "Da akwai wata Zaleehan agidannan ne bayan ke? ko kuma aduk gidannan akwai ƙatuwar gantsamemiyar budurwa sama dake? Maza tashi kije Saifuddeen ne yana jiranki banason shashanci!." 

Idanu Zaleeha ta zaro, lokaci guda jikinta yasoma ɓari kamar mai aljanu, sam ta manta da cewa Ya Aminu ne agabanta cikin tsananin ɓacin rai tace.
"What! Mayataccen gurgun nanne yaƙara dawowa, aikuwa saidai ya shekara don babu inda zanje!!".
Taƙirasa maganan cikin rufewar ido.

Cike da mamaki Ya Aminu ya matso inda take azafafe, cikin tsananin ɓacin rai yace "Me kikace? Maimaita nasakeji don banji da kyauba!".

Shiru Zaleeha tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, wani irin tafarfasa ranta keyi mata, ji take kamar ta kurma wani uban ihu ko zatasamu salama acikin rai da zuciyarta.

Jin tayi shiru batace komai bane yasanya Ya Aminu daka mata tsawa cikin faɗa yace "Kintashi kinjene ko saina ɓaɓɓallaki anan wajen shashashar yarinya da batasan ciwon kanta ba!!."

Jikin Zaleeha narawa ta-tashi da sauri har ƙafafunta na harɗewa haka ta nufi hanyar fita daga falon tuni wasu irin hawayen baƙin ciki sun cika idanunta, fuuuu haka Ya Aminu ya fice daga cikin falon,  tsuka mai ƙarfi Mama tayi cikin baƙin ciki da takaicin Mijin ƴartata Maryam wato Ya Aminu tace. "Wallahi indai akan Zaleeha ne babu wanda ya isa yayi mata dole, idan kuwa har dolennema za a mata tofa lallai saidai in akan Abdussalam, amma wallahi babu wani matsiyacin gurgu daya isa nahaifi ƴa kuma ya aure ta."
ƙwafa Mama tayi tare da cewa.
"Duk zanyi maganinku ne ae dani kuke zancen!."

Zaleeha kuwa ko gabanta bata gani da kyau saboda tsabar hawayen da suka cika idanunta, wani irin ɗaci na ɓacin rai takeji a maƙoshinta,  cikin ranta wata irin wutar masifa ne ke cinta, yayinda wutan tsanarsa ke ƙara ruruwa acikin zuciyarta,  tana kawowa bakin ƙofan da zai sadata da babban falon BQ ɗin ta tsaya cak,  ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi,  da wani irin ƙarfi ta bugi ƙofan falon, cikin takunta mai ɗauke da isa da kuma tsantsar rashin mutumci ta kutso kanta cikin falon.
Idanunsu ne suka sarƙe acikin najuna domin dama tuntuni idanunsa akan ƙofar shigowa falon suke.
Wata uwar harara mai ɗauke da tsantsar tsana, Zaleeha ta watsa masa, cikin takunta dake nuna tsantsar rashin mutumcin da takeji dashi ta ƙaraso cikin falon, ƙwas-ƙwas haka sautin takun takalminta ke amsa gaba ɗaya ilahirin falon, sam idanunta ya rufe da tsana, haɗi da masifar dake cinta arai, cike da son ƙuntata masa ta tsaya kusa dashi tare da sanya hannayenta ta kama ƙugunta,  amasifance tace.
  "Waikai wani irin maye ne? ina tunanin tun a jiya nasanar dakai cewa bana sonka na tsaneka!".
ɗan shiru tayi tare da dubansa sama da ƙasa da sauri ta janye idanunta daga nashi dan wani irin bugu da zuciyarta keyi a duk sanda suka had'a ido,
tabbas yayi kyau sosai acikin idanunta amma masifane kawai ke É—awainia da ita, cikin gatsali tace.
"Oho wato kazone don ka nunamin naci da kafiya irintaku ta kurame ko?  to bari kaji duk bala'in nacinka bazan taɓa sonka ba, na tsaneka wallahi natsani ganin fuskarka, waima shin kai bakasan cewa kai nakasashshshe bane? gurgu, kurma, sannan kuma maye" ɗan numfasawa tayi tare da sake matsowa kusa dashi cikin son ƙunsa masa baƙinciki tace.
  "Kakalleni da kyau koda a iya fuskata aka tsaya kai kasan niba matar yara bace, bare kuma irinka wanda bazai taɓa amfanata da komai ba, ginannen taɓo mai kama da dutsi!".
Taƙare maganar tana jujjuya masa idanu tare da murguɗa baki, wai ita ala dole hakan masifa takeyi.
Tunda tashigo cikin falon yake kallonta har kawo yanzu, wani irin sanyine yaji yana ratsa zuciyarsa, sosai abubuwan Zaleehan ke bashi dariya, duk acikin abubuwan da ta faÉ—a babu É—aya wanda bai fahimci me tace ba sai dai ya gane tana tsoron kwayar idanunshi, acikin ransa yace.
"Ginannen taɓo ko, hmmm zakisha mmki!."
Ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa,  cikin tsananin takaici Zaleeha ke kallonsa, zuwa yanzu kam yakaita bango don yagama ƙureta ahatsale tace. 
"Kayi dariya zama kayi kuka da waÆ´annan fitinannun idanun naka masu kama dana zuri'ar mayu, wallahi-wallahi, idan baka rabu dani ba nice nan ajalinka, me yasa bazaka gane cewa na tsaneka bane? Meyasa bazaka kalli wutar tsanarka dake ruruwa acikin idona ba? kaduba kaga na tsaneka nace, na tsaneka!!!".
Cikin tsananin ƙaraji take maganan yayinda hawaye suka cika idanunta, jitake kamar taje ta ɗauko wuƙa ta caccaka masa.
Dai-dai lokaci Sallaman Kaltume mai aikin gidan nasu ya ratsa kunnuwanta,  amatuƙar harzuƙe tajuyo tana kallon Kaltume,  ƙarasowa cikin falon Kaltume tayi hannunta ɗauke da wani babban tray wanda samansa ke ɗauke da bottle water dakuma kayan marmari dangin su Apple da Inibi, akan babban table ɗin dake tsakiyan ɗakin Kaltume ta ajiye tray ɗin, dubanta takai ga Saifuddeen wanda yake kallonta, aladafce tace dashi "Ina wuni ranka shi daɗe!".
Murmushin daya bayyana cikar haiba da ƙwarjininsa yayi inda ya gyaɗa mata kai alamar.
"Lafiya"
Nan Kaltume ta miƙe tafice daga cikin falon aranta tana me mamakin tsananin kyau irin nasa take cewa.
"Duk yanda akayi balarabe ne shiyasa banji ya amsa gaisuwata ba, dadukkan alama baisan ma menace ba, gsky Aunty Zaleeha tayi sa'an miji".

Kaltume na fita Zaleeha tasaki wani mugun murmushi tare da cije laɓɓanta, ahankali ta ƙarasa gaban table ɗin da tray ɗin kayan marmarin yake, ɗaukan tray ɗin tayi tare da juyowa ta kalli Saifuddeen turamasa tiran kusa dashi tayi, ranta aɓace tace.
"Dama nakasassu irinku sunfi buƙatar irin waƴannan abubuwan hala shiyasa kazo nan don kaci ko? Mayunwaci gasunan saikaci ae!".
TafaÉ—a tana me tura masa gaba É—aya tray É—in,
cikin wani irin yanayi ya rumtse idanunshi da azaban k'arfi, jin zuciyarsa na tafarfasa,
sai kuma ya bud'esu da sauri. Juyawa tayi daniyar barin falon, cikin zafin nama da tafasan zuciya Saifuddeen ya damƙo hannunta tare da hankaɗata kan kujeran dake kusa dashi,
mamaki ɗauke akan fuskar Zaleeha ta zaro idanu tana kallonsa cike da tsoro, domin sam ita batasan ya akayi ba sai jinta tayi akan kujera, cikin zafin nama ya ƙaraso dakekensa har gabanta, ƙafansa ɗaya yasanya ya tokare gefen kujeran yanda babu yanda za'ayi ta iya tashi.
Wani irin horo yashiga yi mata da idanunsa wanda duk rashin kunyarta take kasa kallon cikinsu,
da sauri ta sunkuyar da kanta yayinda k'irjinta ke duka uku-uku,  ga wani iri abu da taji ajikinta, cikin haɗe fuska da tattaro d'an guntun jarumtarta da ragwowar tsiwartata tace.
"Miye hakane dahalla Malam, ni ɗagamin ƙafanka na wuce idan ma maitan nakane yatashi kurwata kur kaci kanka!".
Tafaɗa tana me ƙoƙarin miƙewa tsaye,  da sauri Saifuddeen yasanya ƙafarshi ya tokari guiwanta, da tashi guiwar da azaban k'arfi.
da sauri ta yarfa hannu tare da cewa.
"Wayyo Allah na, mugu'azzalumi, karya min k'afa zakayi ka maidani gurguwa irinka ko?."
bai kulata ba sai k'ara datse mata guiwarta da yayi da tasa guiwar har takai suna iya jiyo hucin numfashin juna, yayinda daddaɗan ƙamshin turarensu ya cakuɗa waje ɗaya, ahankali yashiga yawo da idanunsa akan jikinta, wani irin yaaarrr haka yaji a jikinsa alokacin da idanunsa suka sauƙa kan tudun ƙirjinta, tuni tsikar jikinsa suka soma mimmiƙewa yayinda yaji wani irin feeling ya dirar masa alokaci guda,  idanunsa ya ɗauke daga kan ƙirjin nata tare da sauƙesu akan laɓɓanta, wani irin yawu ya haɗiya amaƙoshinsa tare da ɗan lumshe idanunsa, jiyake kamar ya jawota ta faɗa jikinsa,  yanajin kamar ya ladabtar da ita tahanyar bawa kyawawan laɓɓan  bakinta professional kiss, ahankali idanunsa suka ɗan sauya kala daga farare zuwa yanayin bacci, cikin wani irin salo yasanya hannayensa inda ya tallafo haɓarta, idanunsu ne suka dire acikin najuna da sauri tayi ƙasa da idanunta cikin faɗa tasanya hannunta ta buge hannun nasa daya taɓa haɓanta, cikin son koyan rashin kunya murgud'a mishi baki tace. 
"ÆŠan iska kawai!, ai bama sai ka gwadamin a zahirance nagani ba.
Duk wanda yaga waƴannan munafukan idanun naka yasan kai ɗan iskane!!". taƙare maganar tana murguɗa bakinta, wayarta dake hannunta ce takawo haske, cireta a key tayi tare da k'ok'arin duba waye mata flashing,
sam ba zato ba tsammani taji Saifuddeen ya wafce wayar daga hannunta, rai aɓace ta ɗago ta dubesa cikin gatsali tace.
"Bani wayata tunda bada kuÉ—in Nakasassun guragu na saya ba!".
Ƙin bata wayar yayi gashi gaba ɗaya yayi mata ƙawanya da jikinsa, sannan kwarjininsa ya cika mata ido.

Saifuddeen kuwa number'nsa ya sanya acikin wayan inda ya danna dialing, take wayarsa dake cikin al'jihun gaban rigarsa ta soma ƙara, ganin numbern ta yafito acikin wayarsa ne yasanyashi katse ƙiran kaitsaye wajen text messages ya nufa,  sannu ahankali ya rubuta kalamai masu hikima inda yayi sending zuwa phone ɗinsa, saida ya tabbatar da cewa saƙon yashiga wayarsa sannan ya maida idonshi kanta.

Itakuwa Zaleeha cikin ƙufula take binsa da harara, ganin yanda ya tsareta da idanune yasanya a hatsale ta wafce wayarta dake hannunsa, miƙewa tsaye tayi tare da watsa masa harara cikin yanayi na tsanarshi tace.
"Kada ka taɓa manta cewa bana sonka, sannan kuma na tsaneka tsana mafi mufi, cigaba da kusantata tamkar kusantan ajalinka ne!".
Tana kaiwa nan azancen nata ta tsallake ƙafarsa ta wuce.
Da kallo Saifuddeen ya bita harta ɓacewa ganinsa, murmushi yayi tare da cije laɓɓansa, cikin zuciyarsa yace.
"Kin gama naki daga yau É—in saura nawa Æ´an mata yanzu lokacina ya fara."
cikin nutsuwa ya shiga tura kekensa har ya fice daga cikin falon, koda ya kawo compound ɗin gidan nan ya iske Ya Aminu wanda fitowarsa kenan aɓangaren Baba Malam, ganin Saifuddeen yasanya Aminu cewa.
"Har zaku tafi?"
Kai Saifuddeen ya jinjina masa fuskarsa É—auke da murmushi alaman.
"Eh". kana cikin body language É—insa yace "Yanason gaisawa da Baba Malam idan yana gida."
Murmushi Aminu yayi don sam baigane me Saifuddeen É—in ke nufi ba, kasancewar ba sosai yake gane body language ba.
Ganin cewa Ya Aminun bai gane me yake nufi ba, yasanya shi zaro wayarsa daga al'jihu inda yayi rubutu ya miƙawa Ya Aminu'n, amsan wayan Ya Aminu yayi, koda ya karanta saƙon murmushi yayi, cikin yabawa da hankalin Saifuddeen ɗin yace.
"Masha Allah, aikuwa Baba Malam na ciki muje sai namaka jagora."

Ya Aminu ne yayiwa Saifuddeen jagora har zuwa cikin haÉ—aÉ—É—en falon na Baba Malam.

Ganin Saifuddeen yasanya fara'ar dake kan fuskar Baba Malam ƙara faɗaɗa, cikin farin ciki yace.
"A'a É—alibina Saifuddeen kaine ke tafe, Masha Allah sannunka da zuwa."
Murmushi Saifuddeen yayi cikin hikima da ladabi yagaishe da Baba Malam ɗin, fuska asake Baba Malam ya amsa tare da tambayansa ya bayan rabuwa, nan suka ɗan taɓa hira tsakanin Baba Malam da Saifuddeen, yayinda Ya Aminu ke sa musu baki, Ya Ahmad ne yashigo cikin falon na mahaifinsa, ganin Saifuddeen ya sanyashi faɗaɗa fara'arsa inda suka gaisa amutumce. Nan suka sake ɗan taɓa hira wanda Saifuddeen ke ɗansa baki ta hanyar body language ɗinsa.
Wayarsa yaciro inda ya miƙawa Ya Aminu, bayan yashiga text message saƙon da ya tura da kansa ta wayarta ya bayyana akan screen ɗin wayar tasa, koda Ya Aminu yakaranta saƙon murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa cikin jin daɗi ya miƙawa Ya Ahmad, Ya Ahmad ma yana karanta saƙon yasaki wata nannuyar ajiyar zuciya sosai hakan yayi masa daɗi, amincewa da auren Saifuddeen da Zaleeha tayi, abun farin ciki ne agaresu, domin samun nagartaccen namiji kamar Saifuddeen amatsayin suruki cikin zuri'arsu abun alfaharine sosai.
Miƙawa Baba Malam wayar Ya Ahmad yayi, koda Baba Malam yakaranta saƙon da aka rubuta kamar haka.
_"Ni ZALEEHA NA AMINCE DA AURENKA Hamma SAIFUDDEEN SABODA HAKA KATURO MAGABATANKA WAJEN BABANA DON ATSAIDA MAGANAR Aurenmu."_

Wani irin ingantaccen farin cikine ya cika zuciyar Baba Malam jin cewa Zaleeha ta amince da Saifuddeen takuma tsai dashi a matsayin gwaninta, cikin tsananin farin cikin daya kasa ɓoyuwa akan fuskar Baba Malam ya ɗago ya kalli Saifuddeen wanda ya sunkuyar da kansa ƙasa, cikin zuciyarsa yace.
"Nawa wasan ya soma Zaleeha daga gobe idanunki zasu fara kuka kamar yadda kikasa Ummina kuka, kuma Insha Allah ni da kika ƙira Ginannen taɓo kuma dutse, niɗin nanne zan-zamo mijinki!."

"Masha Allah, Haƙiƙa naji daɗin kasancewar haka sosai Saifuddeen, saboda haka ni mahaifin Zaleeha na baka Zaleeha sannan koda yaushe kashirya kana iya turo manyanka su kawo sadaki don atsaida ranar auren ku da ita!."

Wani irin tsananin farin cikine suka cika zuƙatan Ya Ahmad da kuma Ya Aminu, shikuwa Saifuddeen faɗan farin cikinsa ma ɓata lokaci ne, domin kallon fuskarsa kaɗai da ƙwayoyin idanunsa sun isa sanardakai farin cikinsa.

Cikin aminci da salama Saifuddeen ya miƙa godiyarsa ga Baba Malam harma dasu Ya Ahmad, nan sukayi sallama cikin mutumta juna har bakin mota Ya Ahmad da Ya Aminu suka raka Saifuddeen saida sukaga ficewar motarsa acikin gidan kana suka juya suka koma wajen Baba Malam don su tattauna yanda bikin zai kasance...

A cikin mota kuwa wani irin murmushi Saifuddeen yayi tare da sake jingina bayansa ajikin kujeran motar, lumshe idanunsa yayi yana me tunano haɗaɗɗiyar surar jikinta, tabbas yaƙudurta aransa cewa zai shayar da ita ruwan mamaki, aduk sanda ya aureta kuwa saiya nuna mata cewa NAKASA BA KASAWA BACE...!

By
*GARKUWAR FULANI*

             *NAKASA BA KASAWA BACE*

                            *PAGE 29*

                             *NA*
           *AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Daga Gidansu Zaleeha kai tsaye unguwar tudun wada suka nufa wato gidan Baba Bello,  aƙofar ɗan madaidaicin gidan na Baba Bello Sule driver yayi parking motar, both ya buɗe inda ya cirowa Saifuddeen kekensa, buɗe murfin motar Saifuddeen yayi, inda dakansa  ya yunƙuro ya hau kan keken nasa.
Yana gama dai-dai ta zamansa akan keken,  Jafar almajirin Baba bello yafito daga cikin gida, ganin Saifuddeen yasanya Jafar sakin murmushi cikin kulawa yaɗan rusuna tare da cewa. "Hamma Saifuddeen sannu da zuwa."
Murmushi Saifuddeen yayi masa tare da jinjina masa kai alaman.
"Yauwa."
Cikin sauri Jafar yajuya ya koma cikin gida, nan ya iske Baba Bello dake zaune yasanar dashi zuwan Saifuddeen,  cikin hanzari Baba Bello yazura takalma aƙafansa,  inda kai tsaye yanufi hanyar fita daga cikin gidan.
Fuska ɗauke da fara'a Baba Bello ya tarbi Saifuddeen,  nan yayiwa Saifudeen ɗin iso zuwa cikin ɗakinsa dake hanyar soro.
Bayan sun zauna ne Jafar ya kawowa Saifuddeen ɗin ruwa acikin wani babban plastic jug,   kofin ruwan Saifudeen ya ɗauka tare da kaiwa bakinsa, tuno da yanda Zaleeha ta turs masa kayan fruits gabanshi ga kuma tsoronshi cikin ƙwayar idanunta tono hakan ne yasa yayi,  yasanyashi sakin murmushi, ɗan kaɗan yasha ruwan gudun kada Baba Bello yaji ba daɗi, cikin kulawa Baba Bello ya dubeshi kana yace.
  "Sam ban tsammaci zuwanka ba Saifuddeen, ai da nasanya Innar ku (Matar Baba Bello) tayi maka kwaɗon zogale da tumatur, gashi kuma yanzu batanan taje kitso."
Murmushi Saifuddeen yayi tare  da sadda kansa ƙasa, cikin body language ɗinsa yayiwa Baba Bellon alamar cewa babu komai,  nan suka shiga ɗan taɓa hira da Baba Bellon, inda Baba Bellon ya nuna jin daɗin zuwan Saifuddeen ɗin, domin kuwa tun ranan da suka dawo daga zuwa dubasa da sukayi,  lokacin dawowarsa basu sake haɗuwa ba sai yau ɗin,  hira sukeyi tsakanin magana da kuma body language, inda sosai Baba Bello ke gane yaren Saifuddeen, wato body language, cikin girmamawa haɗi da kulawa Saifuddeen ya labartawa Baba Bello maganan aurensa, kama daga farkon tura masa tambaya har kawo yanzu, cikin hikima yanemi shawarar Baba Bello agame da bikin.
Cikin jin daɗin yanda Saifuddeen ɗin ya karramasa, yakuma maidashi uba, yasanya Baba Bello gyara zama, nan yashiga bawa Saifuddeen ɗin shawarwari masu kyau, sosai kuwa Saifuddeen ya aminta da shawaran, inda ya yanke cewa jibi jibinna za akai masa lefe da kuma sadaki,  sun ɗan jima suna hira daga bisani yayi wa Baba Bello sallama, kuɗi yaciro ƴan bandir ɗin ɗari biyar biyar sabbi ƙal ya ajewa Baba Bello agabansa, cikin dattako da halin kamala Baba Bello yace.
"Dan Allah Saifuddeen kada kasa kanka awahala, bayan ɗaukemin nauyin gidana da kayi gaba ɗaya kuma saika ƙara da sakanka a wata wahalan? kabar kuɗinka Saifuddeen nagode sosai bani da abinda zance maka sai dai addu'a, domin kuwa koda baka da lfy baka ƙasarma baka daina kulawa damu ba."
Fuska Saifuddeen ya kwaɓe cikin rashin jin daɗin dawo masa da kyautar tasa da Baba Bello yayi.
fuska  ya marairaice, cikin body language ɗinsa yace.
 
"Dan Allah Baba Bello ka karɓa, kaifa matsayin Uba kake agareni, kamar yanda zanyiwa mahaifina kaima haka zanyi maka.!"
Jikin Baba Bello ne yayi sanyi, haƙiƙa Saifuddeen yaron ƙwarai ne, samun irinsa na da matuƙar wahala, tabbas Ummi tayi sa'ar haihuwa, domin samun Saifuddeen amatsayin ɗa babban nasara ce ga rayuwa,   haka Baba Bello ya amshi kuɗin nan batare daya soba saidai sanin halin Saifuddeen yasanyashi karɓan kuɗin dole, nan ya rako Saifuddeen ɗin har bakin motarsa, saida Baba Bello yaga tashin motar tasu Saifuddeen kafun ya juya yakoma cikin gida.

Daga gidan Baba Bello kuwa kaitsaye ƙaramar kasuwa suka nufa, abakin kasuwan sule driver yayi parking motar, shida kansa ya buɗewa Saifuddeen murfin motar tare da gyara masa zaman kekensa,  haka Saifuddeen da Sule driver suka kutsa cikin kasuwa,  cikin nutsuwa Saifuddeen ke sarrafa kekensa, duk inda suka wuce  ido ne ke binsu, yayinda mutane da yawa ke yaba tsantsar kyau irin na Saifuddeen, saidai ganinsa akan keken guragu shine abun dake ɗaure musu kai, kowa kallon cikakken balarabe yake yi masa, sam koda wasa babu wanda ya shaida kamannin Saifuddeen, duk acikin mutanen dake kallonsa babu wanda yakawo aransa cewa shine wannan matashin saurayin dake gararanban yawon raba leda, yake kuma yawon raba omo, kana harma da tallan fiyo wata (pure water),  babu wanda zai gansa ayanzu yace shine wannan yaron da yasha gwagwarmayar rayuwa, yayi ta zagaye kasuwa koro-koro luggu da saƙo.
Fuskarsa ɗauke da annuri ya ƙarasa gaban wawakeken shagon wanda yake mallakinsu, Mudassir da Warisu naganinsa suka taso cikin tsananin farinciki suka tarbeshi,  sam basu tsammaci ganinsa ba don ya matuƙar shammace su,  yaɗan jima kaɗan ashagon nasu Warisu inda suka ɗan taɓa hira kaɗan,   duban Mudassir da Wareesu yayi cikin body language ɗinsa yace.
"Kufara shiri tun yanzu don nanda Æ´an sati kaÉ—an zakusha biki."
Mamakine ya bayyana akan fuskar Wareesu,  daɗan ƙarfi yace.
"Biki kuma na waye?."
Murmushi Saifuddeen yayi tare da nuna kansa.
Cikin alamun ban mamaki Wareesu yace.
"Wow Surprise kenan!  Kai amma naji daɗi sosai Allah yasa ayi damu, koya Mudassir, yakamata ne ma ai mufara gagarumin shiri."
Wareesu yafaÉ—a cike da farinciki.
Shiru Ahmad da ya shigo yanzu yayi tare da kafe Saifuddeen da idanu, kallonshi shima Saifuddeen ɗin yayi, yanayin yanda yaga fuskar Ahmad kaɗai yasayashi gane abun dake cikin zuciyarsa,  murmushin daya bayyana kyawawan dimples ɗinsa yayi, cikin son ganar da Ahmad irin yanayin dayake ciki ya lumshe idanunsa, hannunsa yaɗaura adai-dai saitin zuciyarsa wacce ke beating.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Ahmad ya sauƙe, tabbas ya gane hakan da Saufuddeen ɗin yayi me yake nufi, alamace dake nuna cewa Saifuddeen ɗin nasonta da duka zuciyarsa,  tabbas yana matuƙar jin tausayin Saifuddeen domin kuwa shi tuni yajima da gano cewa Zaleeha ba matar aure bace, ba irinta Saifuddeen ke buƙata ba, Saifuddeen yana buƙatar kamilalliyar mace, nutsatstsiya, wacce ta yarda da ƙaddara tayi imani mai kyau ko akasinsa daga Allah Ne, amma ya zaiyi dolensa zai haƙura da ƙin Zaleeha da yake, sahoda yaga gaba ɗaya soyayyarta ta rufe idanun Saifudeen, ya fahimci cewa Saifuddeen  Zaleeha kawai yake gani aciki da wajen idanunsa, saboda haka zaiyi ƙoƙari wajen manta abun da tayi musu, zai taya Saifuddeen ɗin ƙaunarta, nan yayiwa Saifuddeen ɗin Allah yasanya al'khairi, daga shagon nasu Warisu  kaitsaye Saifuddeen shagonsa ya nufa,  shida Ahmad masha Allah koda yaje yasamu nutane maƙil sun cika shagon, sayan kaya kawai suketayi, yayinda cikin shagon ke shaƙe da kaya tam na yara irin new designer ɗinnan masu kyau, Manyan Hajiyoyine keta business ɗinsu, wasu sayan dayawa sukazo wasu kuwa sayan ɗaɗɗaya , kasancewar shagon cike yake da mutane yasanya Saifuddeen baiwani zauna acikin shagon sosai ba ya tafi,  Kaitsaye shagon Ba mishkila ya nufa, nan ya iske Ba mishkila yau shida kansa ne acikin shagon, ba ƙaramin farin ciki ba mishkila ya yiba dayaga Saifuddeen, nan yashiga tambayarsa jikinsa,  inda ya amsa masa cewa "Dasauƙi sosai"
Daga shagon ba mishkila shagon Alhaji Ishaq baban abokinsa wato Ibrahim ya nufa, sosai Alhaji Ishaq yaji daɗin ganin Saifuddeen, shima sun ɗan taɓa hira inda yayi masa ƙarin ya jiki,  daga shagon Alhaji Ishaq shagon Alhaji Kabiru Saifuddeen ya nufa,  nan fa shima Alhaji Kabirun yacika da murnar ganin Saifuddeen, kasancewar hakan alamace dake nuna cewa sauƙi ya samu ga Saifuddeen ɗin.  Sosai Saifuddeen yaɗan jima acikin kasuwan yayinda ya tsaya yagabatar da sallan Magriba cikin masallacin dake gefen kasuwan, yana idarwa suka kama hanyar dawowa gida.

Ahankali yake tuk'a kekensa haryakawo cikin falon na ummi inda ya iske Raliya, Hayatuddeen, da kuma Ummi wacce ke zaune akan kujera, Hayatuddeen na zaune aɗan gefe da ita yana latsa wayarsa, Raliya kuwa tsugune take agaban Ummin tana mammatsa mata ƙafa,  murmushin dake kan fukar Ummi ne ya faɗaɗa sakamakon ganin yanda fuskar ɗan nata ke ɗauke da farin ciki,  cikin kulawa tace.
"Saifuddeen kadawo?"
Kansa ya jinjina mata tare dayi mata alama,  cikin body language ya sanar mata cewa daga kasuwa yake.
Murmushin jin daÉ—i Ummi tayi tare da cewa.
"Allah ya taimaka."
Duban Raliya tayi cikin kulawa tace.
"Bar matsamin ƙafannan haka jeki kawowa hamman naku ruwa mai ɗan sanyi yasha." 
"To."
Raliya tace tare da miƙewa tsaye ta nufi hanyar kitchine ɗin dake cikin falon.
Hayatuddeen ne ya É—ago kansa, inda ya kalli Hamman nasa, cikin tausasawa yace.
"Hamma barka da dawo, dama kamar kasan naƙosa ka dawo wallahi."

Murmushi Saifuddeen yayi tare dayi masa alaman meke faruwa?

Gyara zama Hayatuddeen yayi cikin zumuÉ—in labarin dake cinsa yace.
"Ina wannan kyakkyawar mawaƙiyan da muka haɗu da ita a jirgi,  lokacin da zamu dawo Nigeria, Hamma ka tuna ta  Asma'u Ahmad Matawalle?."
Yaƙare maganan yana me tsatstsare Hamman nasa da ido.

ÆŠan jim Saifuddeen yayi tare da É—an lumshe idanunsa, in few second ya hasasho fuskarta, duban Hayatuddeen yayi tare da gyaÉ—a masa kai alamar eh ya tunota.

Gyara zama Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Yauwa Hamma, wai kasan mene? tun ranan da takarb'i phone number na, kullum sai munyi chart, bata da wani labari sai naka, kullum maganarka take, shine yau tace nafaÉ—a maka wai tanasonka, zaka aureta?."

Baki Ummi ta buɗe tana kallon Hayatuddeen, shikuwa Saifuddeen fuska ya yamutsa tare da tab'e baki, wai harshi wata y'ar jagaliya mace mai rawa da wak'a data gama nunawa duniya sirrin jikinta babu hijabi zatace tanaso, bama wannan ba shi ayanda yakejinsa, ayanzu babu wata mace da zaiso, So d'ayane tak kuma Zaleeha yakeyiwa shi, sam bayajin cewa wata mace zata samu matsuguni ko muhallin zama, koda ko abaki-bakin zuciyarsa ne,   d'an madaidaicin glass cup ɗin da cikinsa ke d'auke da lemon exotic,  wanda Raihana ke mik'o masa ya amsa,   da kad'an-kad'an yake sipping exotic juice d'in,  saida yasha kusan rabin cup d'in kafun ya ajiye,  ahankali yatuƙa kekensa inda ya k'arasa har gaban Ummi, hannayensa ya d'aura akan nata tare da langwab'ar dakai.
Murmushi Ummi tayi don hakan da yayi yasa ta fahimci cewa magana me mahimmanci yakeso suyi.
Cikin sakin fuska Ummi tace.
"Faɗi  duk abun dake ranka Saifuddeen ni me mara maka baya ce akoda yaushe."
Murmushin jin daɗi yayi inda ya ciro wayarsa daga cikin al'jihun rigarsa,   duk wani abun dake cikin rai da zuciyarsa haɗi da duk wani ƙudirinsa saida ya rubuce shi cikin text message, miƙawa Ummi wayar yayi inda ya sunkuyar da kansa ƙasa, karɓan wayar Ummi tayi cikin nutsuwa ta shiga karanta abun da Saifuddeen ɗin ya rubuta,  wata irin sassanyar ajiyar zuciya Ummi ta sauƙe alokacin da ta gama karanta saƙon nasa, murmushine ya bayyana akan fuskarta take kuma sai ga hawaye sun cika idanunta, sosai rauninta ke ƙoƙarin fallasa sirrin zuciyarta, hannayenta tasanya ta ɗago haɓarsa, cikin son ƙarfafa masa guiwa ta shafi gefen fuskarsa, cikin yanayi na tausasa murya tace.
"Dama nasani ɗana bazai taɓa zama rago ba, haƙiƙa kai ɗin jarumine, haka kuma babu wata ƴa mace da zata so yin asararka."
Ɗan numfasawa tayi tare da sauƙe ajiyar zuciya akaro na barkatai.
"Nayi matuƙar farin ciki Saifuddeen, haƙiƙa ganin aurenka yana ɗaya daga cikin burukan rayuwata,  Allah Ubangiji yasanyawa tarayyarku albarka!."
Ummi tafaÉ—i haka cikin tsananin farin ciki, sosai takeson abun da Saifuddeen É—in ke so, saboda farin cikinsa itama shine nata.
Cikin samun nutsuwar zuciya Saifuddeen ya ɗaura kansa bisa kafaɗan mahaifiyar tasa, cike da ƙaunarta  yayi mata alaman godiya, ahankali tashiga shafa kansa, tana mejin farin ciki aranta, lallai dole ta-tayashi wajen ganin ta ƙawata bikin ɗan nata.
Hayatuddeen da Raihana kuwa idanu kawai suka zuba musu,  aƙalla Saifududdeen yaɗauki kusan 4 minute kansa na bisa kafaɗan Ummi, kafun daga bisani ya janye, cikin nuna alamun gajiya ajikinsa yace da Ummin nasa zaije yaɗan watsa ruwa. 

"To." Ummi ta amsa inda tace dashi Hayatuddeen zai kawo masa abinci.

Hayatuddeen naganin wucewar Hamman nasa É—aki ya zaburo, cikin tsananin gulman dake cinsa yace.
"Ummi wani abu ya farune naga kunata farin ciki keda Hamma?".

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Banason gulma fa Hayatuddeen."
Baki Hayatuddeen ya turo gaba.
Raliya ce ta gyara zama tare da cewa.
"Ummi ai ba Hayatuddeen kaÉ—ai bama nima ina son ji, dan Allah Ummi menene, ko akan maganan aurensa ne?"

Dariyan yaran nata ne ya kamata, cikin kulawa tace.
"Yarinyar da Hammanku yakeso ta amince dashi, harma ta bashi daman turo magabatansa don atsaida maganan aure,  yanzu haka mahaifinta ya amince, mu kawai ake jira mukai lefe da sadaki asaka ranar aure!."

Wani irin ihun daɗi Hayatuddeen yayi tare da miƙewa tsaye, cikin tsananin farinciki yace. "Yessss!! Lokacin yazo!."

Raliya ma tashi tsaye tayi cike da murna tabawa Hayatuddeen hannu suka tafa, cikin jin daÉ—i da farin ciki tace.
"Masha Allah, ae kuwa za ayi biki irin wanda ba'a taɓa yiban zaton mai nakasa zai yishiba acikin garin Gombe."
Sake tafawa da Hayatuddeen sukayi cikin jin daÉ—i Hayatuddeen yace.
"Yanzune jama'ar cikin garin Gombe zasu san cewa akwai manyan yara masu tasowa, na rantse Adda Raihana saina baku mamaki, saina nunawa Hammana cewa idan yana dani bashida damuwa a duniya!." 
Yaƙare maganar yana me jujjuyawa, tare da soma yin rawar shaku-shaku.
Dariya Ummi da Raihana suka saka, don abun na Hayatuddeen ya wuce tunaninsu, ganin hayaniyan su Hayatuddeen ɗin na ƙoƙarin damunta yasanya ta miƙewa ta koma ɗaki bayan tace da Hayatuddeen ya kaiwa Saifuddeen ɗin abincinsa,  tana shiga ɗaki ta dannawa number'n Adda Rahama ƙira, bugu biyu Adda Rahama dake kwance jikin Dr Adnan suna shan love ɗinsu ta ɗaga wayar, cikin son dai-dai-ta nutsuwarta tace.
"Ummi barka da dare."

Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"Barkanki dai, fatan kuna lafiya baki É—ayanku."
Da "Lafiya ƙalau." Adda Rahama ta amsa mata.
Gyara zama Ummi tayi,  take tashiga labartawa Adda Rahama maganan auren Saifuddeen ɗin da ta taso lokaci ɗaya.
Hmmm faɗar irin tsananin farin cikin da Adda Rahama tasamu kanta aciki ma ɓata lokaci ne, sosai taji daɗin labarin nan tace  zata tambayi Dr Adnan gobe idan yabarta zatazo gidan, da haka sukayi sallama ita da Ummin nata,  cikin ɗoki haɗi da marari ta rugume mijin nata ƙam-ƙam, fuskarta ɗauke da farin ciki tace.
"Yaya Adnan Saifuddeen zaiyi aure,  ina cikin tsananin farin ciki wallahi, nasan shima zai samu salihar mace wacce zata kawar masa da duk wata damuwarsa!."

Cikin jin daɗin labarin Dr. Adnan yasake hugging ɗinta,  dogon gashin kanta ya shafa, tare da sanya hannuwansa ya ɗago haɓanta,   ido cikin ido suke kallon juna cikin nuna jin daɗinsa yace.
"Alhamdulillah lallai zamusha biki, masha Allah mun kusa zama surukai!."
Murmushi Adda Rahama tayi tare da cewa.
"Farin cikina bazai faɗu ba Ya Adnan, akullum da tausayin Saifuddeen nake kwana nake tashi, raunin Saifuddeen raunina ne,  naji daɗi matuƙa saboda nasan shima ayanzu zai samu gamsuwa irinta aure!."
Murmushi Dr Adnan yayi tare da jan dogon hancinta cikin salon tsokana yace.

"Hmmm irin wato ke kinsan gamsuwar aure É—innan ko?"

Dariya suka sanya atare, cikin yanayi najin kunya ta ɓoye kanta acikin ƙirjinsa,   sake matseta yayi cikin raɗa yace.
"Dama kuma nima gashi yau inada buƙatar wata gamsuwar, ke ma kinsani bana taɓa gajiya dake!."  yafaɗi maganar yana me haɗe bakinsu waje ɗaya.

***
Fitowarsa daga wanka kenan, wata brown jallabiya yasanya ajikinsa, tattausan darduman sallansa ya shumfuɗa inda ya gabatar da sallan Isha, kana kuma ya gabatar da sallan shafa'i da wuturi, yajima zaune akan sallayan yana addu'o'i har Hayatuddeen yakawo masa abinci ya fita, bai idar ba,  cikin nutsuwa yajawo kekensa, cikin  yanayi na ɗan dabara daya saba ya zauna akan lafiyayyar keken nasa,  food flask d'in da Hayatuddeen yakawo yashiga bubbud'ewa,  kulan farko daya bud'e yam balls ne aciki wanda yaji kayan ƙamshi da kuma ƙwai, sai kuma sauce ɗin egg and onion da akayi musamman don cin yam balls ɗin dashi, ɗayar kulan kuwa pepper chicken ne aciki wanda yaji curry da kayan ƙamshi,  gaba ɗaya ƙamshin abincin ya cika ɗakin,  pepper chicken ɗin yaɗan ɗiba kaɗan a plate,  wani ɗan madaidaicin flask ya jawo wanda ke ɗauke da tafashashshen coffee,   ruwan coffee ɗin wanda yaji kayan ƙamshi ya zuba acikin wani ɗan madaidaicin cup,   bawani sosai yaci naman ba saidai ace ba laifi, coffee ɗin nema yasha sosai, minti 10 da gamawa Hayatuddeen yazo ya kwashe kwanukan yafita dasu,  kekensa ya tura inda ya nufi bathroom,  kaitsaye gaban ɗan madaidaicin sink ɗin dake cikin toilet ɗin wanda yake dai-dai tsawonsa ya nufa,  yana daga zaune akan keken nasa yayi brush, yayinda ya sake ɗaura sabuwar al'wala ajikinsa, don sam hakanan yake baya wasa indai wajen zama da alwala ne shi gwanine awannan fannin, domin yawan zama da alwala ma wata babban kariyace ga bawa.

Cikin hikima ya hau kan gadonsa tare da rage gudun AC'n dake ɗakin, luf yayi akan gadon nasa tare da fidda wani irin numfashi,    lumshe kyawawan idanunsa yayi yana me imagine kyakkyawar surarta acikin idanunsa,  kyakkyawan murmushine ya bayyana akan fuskarsa, sakamakon tunawa da yayi da yanda ɗan ƙaramin bakinta ke motsawa,  alokacin da take surfa masa ruwan masifa,  komai nata me kyau ne, haka kuma komai nata gwanin burgewa ne,  harshensa ya sanya yaɗan lashi laɓɓansa wanda suke cike da muradin jinsu akan nata laɓɓan, wani irin so yakewa Zaleeha wanda shikansa baisan iyakarsa ba,  yanason Zaleeha fiye da duk yanda wani zaiyi tunani,   sake gyara kwanciyarsa yayi tare da sakin wani killer smile, wani irin nishaɗine yakejin ya cika zuciyarsa,  kalmar
"Maye." da ta ƙirasa dashi shine abun daya dawo cikin brain ɗinsa.
cikin ƙasan zuciyarsa yace.
"Am so sorry My Beautyful Wife, dama kin sani da bakicemin maye ba, don kuwa gashi yanzu kinjawo dole saina nunamiki cewa eh da gaske niÉ—in maye ne."
Cikin wani irin azababben shauƙin sonta haka bacci ɓarawo ya ɗaukeshi.

Gaba ɗaya ko ina dake cikin gidan nasu ya ɗauki shiru,  a irin wannan lokacin mafi yawancin mutane kowa na kwance ne a makwancinsa, yayinda wasu ke gudanar da baccin nasu cikin yanayi mai daɗi, saɓanin wasu kuwa da sukeyinsa cikin rashin yanayi me daɗi, adai-dai wannan lokacin cikin waƴanda suke bacci cikin rashin jin daɗi hadda Zaleeha domin kuwa duk sanyin dake cikin ɗakin ita gumi ne ke fesowa daga jikinta.

Binsa takeyi cikin sauri ayayinda ko takalma babu aƙafanta, ƙoƙarin cimmasa take amma yana ƙara yi mata nisa, bayansa kawai take iya hangowa kasancewar ya bata baya, cikin ƙosawa haɗi da gajiyawa ta tsaya tare da sanya hannuwan ta duka biyu ta kama ƙugunta, cikin tsananin gajiys muryar dake bayyana rauninta tace.
"Dan  Allah katsaya, katsaya atare dani, barinka cikin rayuwata tamkar rabani da numfashina ne, tayaya zaka gane irin sonda nake maka? shin tayaya zaka gane cewa ina buƙatarka cikin rayuwata, Dan Allah kazo, katsaya nazo gareka!!."

Cak ya tsaya daga tafiyan da yakeyi, amma saidai ko motsawa baiyi ba balle tasa ran cewa zai juyo ta kalli fuskarsa.
Ahankali tashiga takawa zuwa garesa, taku biyu kacal ya rage taƙarasa garesa,  ahankali yaɗan juyo gareta,  idanunta ne suka sauƙa akan kyawawan laɓɓansa wanda ke ɗauke da kalar red, yayinda wasu kwantattun gargasa sukayiwa bakinnasa ƙawanya, wani irin sheƙi da shinnig gashin dake kwance akan fuskar tasa keyi, idanunta taɗaga daniyar kallon full face ɗinsa, kafun ta sauƙe ganinta akansa wani irin haske wanda batasan daga ina yafito ba ya cika gaba ɗaya idanunta.
Azabure ta-tashi daga baccin da takeyi, cikin ƙaraji tace "Dan Allah kada katafi pleaseee help me!!!."
Buɗe idanunta wanda suka kaɗa sukai jajur tayi, lokaci guda wani irin gumi ya shiga keto mata,  ƙirjinta ne yashiga bugawa da sauri sauri,    aƙalla taɗauki kusan 3 minute kafun taɗan soma dawowa cikin hayyacinta gane cewa mafarki take yasanyata sakin kuka mai ciwo, jikinta ta takure waje ɗaya tare da cusa kanta tsakankanun cinyoyinta, kuka take rerawa sosai mai ɗauke da tsanin ciwon so, cikin rufewar ido haɗi da sambatu tace.

"Shikenan katafi kabarni? yazanyi? shin tayaya kake tunanin zan iya jure rashinka? nazautu akan sonka, nakai ƙololuwa,  nazama kurma, makauniya,  har wasu suna mini kallon zautacciya duk akan sonka,  Ina sonka! Ina sonka! Ina tsananin sonka!!!."  Taƙare maganar tana me rushewa da kuka, sosai Zaleeha tayi kuka awannan dare har da shiɗewa,  daƙyar ta iya jan jikinta ta wuce toilet, wanke fuskarta tayi kana ta ɗauro alwala, sosai wani irin zazzafan zazzaɓi da ciwon kai suka rufeta asakamakon kukan da tayi, wata zumbuleliyar hijab ta sanya ajikinta, inda ta hau kan shunfuɗaɗɗen dardumanta, cikin tsananin ciwon da kanta keyi mata tagabatar da sallan Nafila raka'a huɗu,  zama tayi akan praymad  tare da jingina bayanta da jikin bango, idanunta ta lumshe, ahankali wasu zafafan hawaye suka shiga kwaranyowa daga cikin idanun nata, ji take kamar zuciarta zata fashe saboda soyayyarsa, ashe dama haka so yake? ada taɗauki batun so wasa sai gashi kuma yanzu yana shirin yi mata ɓarin kwan makauniya, haƙiƙa gangar jiki da zuciyarta na azabtuwa, Inama da ace yin so baizama ɗaya daga cikin Ƙaddarorinta ba,  kuka tacigaba dayi sannu ahankali wani wahalallen bacci ya samu nasaran ɗaukarta..

Kamar yanda ya ƙudurta aransa hakance ta kasance, zuwa yanzu yasanar dasu Baffa Ali gaba ɗaya abun dake faruwa.

5 million ya ware daga cikin ribarsa,  ayau yau yake da buƙatar haɗa kayan lefe, inda Baffa Ali yace ya ɗauke masa nauyin biyan sadaki.
Aunty  Kubra matar yayan Abokinsa Jabeer dakuma Adda Rahama sune suka shiga cikin babban kantin nan na San Hussain Super Market don haɗo masa kayan aure nagani na faɗa,  dayake Aunty Kubra cikakkiyar ƴar kasuwace kuma sana'anta kenan saida kayan mata, hakan yasanya sosai ta darje wajen zaɓo zafafan lesuka, atamfofi, shaddodi, materials,  dakuma tsadaddun yadukan boyels na mata, kaya sosai suka saya masu tsananin tsada don kuwa kaf cikin kayan nasu babu wanda kuɗinsa yayi ƙasa da dubu Hashirin talatin dai arba'in dai kana hamsin, ɓangaren jakakkuna da takalma kuwa ba acewa komai domin kuwa kaya suka saya masu kyau da inganci.
sashin yan kunnaye da awarwaro haɗi da saraƙa kuwa komai na gwal suka saya,   ɓangaren takalma da jaka kuwa ko wani takalmi da mayafinsa, kana kuma da kalan kayansa, materials, lace, atamfa ko boyel,   sashin ƙananan kaya kuwa abun ba'acewa komai, ɓangaren dogin riguna kuwa saida suka cika akwatuna biyu tam da dogin riguna masu kyau da tsada, domin kaf cikin rigunan babu ta ƙasa da 30k, kaya kam dai sun haɗu sosai, musamman ɓangaren kayan meckup sun kashe kuɗi sosai, musamman suka sayi meckup kit har guda uku,   masha Allah kaya ya haɗu sosai inda aka shirya kayan cikin akwatuna, tsab kayan suka ɗauke gaba ɗaya akwatuna 24 dozin biyu kenan sai guda shida da akasa kayan uwa da uba a akwati sauran ukun kuma akasa na dangi shine ya bada akwati 30 da suka saya.   Koda suka dawo gida kowa saida ya yaba kayan domin anyi abu wanda sam babu ƙaranta aciki, ko ƴar Gwomna aka kaiwa ba laifi. ya ware Million uku da rabi ya bawa Salisu, tare da cewa ya kawo mishi dan ƙareriyar mota mai kyau ta mata irin wacce ake yayi.

Shima Salisu nan yayi tasa bajintar, inda ya kawo haÉ—aÉ—É—iyar mota har ta million huÉ—u.

Can cikin gida kuwa tuni su Adda Rahama, Aunty Mina, Aunty Kubra, matar yayan Jabeer, da Goggo Dada, da  Hajia Rabi matar Alhaji kabiru duk suna cike a parlour Ummi, musamman sukazo don kai lefen Saifuddeen.

Hayatuddeen da abokanshi Imran da Sulaiman ne suka shigo da kayayyakin.
Wanda Ahmad yake matuk'ar jin takaici da bak'in cikin yawan kuɗaɗen da aka ɓatar akan yarinyar da ba mutunci ne da itaba.

Gaba ɗaya sun cika da mamakin irin Yanda Saifuddeen ya narka kuɗi wajen ƙawata kayan,
Hajia Rabi ce tace.
Sam baza'a kai kayan nan duka ba dole a rabashi biyu, ai wanna almobazzaranci ne.
Ita dai Ummi shiru tayi tare da danne ainihin abinda ke ranta wanda babu mahaluk'in da zai gane meke cikin ranta.
Aunty Kubra ce tace a a banda dai a raba biyu kam,
dan ita bata son harkan ƙaranta,
ita da tasoma a Dubai zasu haɗo lefen dan dai kawai abin yazo a ƙurarren lokaci ne, ta nace dole saida aka rarrage wasu abubuwan wasu kuma tama hana fir.

A gidan Baba malam kuwa tun jiya da yamma da Dirankadi ya shaida mishi gobe fa za'a kawo komai da komai kama daga gishiri goro da lefe da kayan rufi da sadaki,
duk zasu kawo a tare sai ya gayawa Mamy.
dan Mama yanzu ko Magana bata mishi, shiyasa shi kuma ya shareta dan ya bata iya matsayinta na uwa so yanzu dole ya nuna mata koda ita ko ba ita dole nefa zai aurar da yarsa ga wanda takeso, ya ga kuma ya dace da ita.

Daga nan ya ƙira ƙanwarshi Goggo Maryama ta kwarar Maryam yayar Zaleeha kenan.
Kana ya sanar da ita Maryam É—in.
sannan matar abokinshi Malam Adam itama tazo,
sai Maman Ya Aminu matar yayanshi kenan,
ga Lubna matar Ahmad nan fa Lubna da Maryam suka shiga kitchen tunda safe
suka fara shirya abin tarban baƙi, waƴanda za abawa ƴan kawo lefe da kuma abinda za'a basu su tafi dashi gida, kamar yanda al'adar Gombawa take.
Mommy matar malam Adam ƙawar Mamy mace mai sauƙin kai gata ta iya girki da kala-kala kasancewar shuwa arab ce. Tana matuƙar son Zaleeha haka itama Zaleeha duk cikin matan abokan Baba malam  da suke ƙawayen Mamy tafi sonta.

Sosai suka shirya komai cikin manya-manyan food flask masu azabar kyau,
yayinda tuni sun cika fridge da ƙawatattun drinks.

Mama kuwa dama yau tunda sanyin safiya ta tafi Doho gidan yayarta Ruda da takebi wacce itama arniya ce dan duk zuriyar Mama ita kaɗaice ta musulunta sai ƙanwarta mai binta,
wacce ta sauya suna daga Rebeka ta dawo Aisha.
tana nan cikin Gombe da mijinta da yaranta Aisha macece mai nitsuwa da kamala sau da dama tana dakatar da yayar tata daga aikata wasu mugayen É—abi'u da sukafi dacewa da masu aljihun baya.
Yayinda Ruda kuwa ke ingizata.

Ƙarfe uku da rabi  na yammaci dai-dai,
Salisu yazo da Matarsa Sadiya da zazzafar motarsa,
Kana Ahmad ya d'auki motar Saifuddeen,
sai kuma Aunty Kubra da Jabeer yazo ya amshi tuk'in haɗaɗɗiyar motarta ƙiran babbar vibe,
sai kuma Motar Ishaq da direbanshi. sai Motar ya Adnan. Sai dalleliyar mota kirar kia samfurin bugun 2019, wacce take baƙa mai Shek'i dan har an kawo fara Saifuddeen yace,
ai ita farar macece dan haka baƙa za'a kawo mata, don haka dole aka canzo aka kawo mata kalar da yake so ɗin.
Nan duk suka kwashi kayan suka shirgeshi cikin motar kana aka bawa Muddasir Key É—inta yaja.

A jere-a Jere suke tafiya yayinda,
Hayatuddeen ke cikin motar Aunty Kubra,
yana gaba gefen Ya Jabeer. Ita kuwa Aunty Kubra ita da Aunty Mina suna baya.
Imran kuwa motar ya Adnan ya shiga yana gaba kusa dashi baya kuma Adda Rahma ce da Goggo Dada.
Sai motar Saifudddeen da Ahmad ne  aciki,Raliyanshi na gefenshi,
tana ta son sama mishi farin ciki dan ta lura sam shi baya wani farin ciki da abun.

Sai Hajia Rabi dage gefenshi wacce itama sam bata farin ciki da abin sabida Hayatuddeen yana gaya mata komai.
sai motar ishaq wacce ba komai a ciki shiyasa shida Saifuddeen suka shiga baya direbanshi yaja,
suka nufi can k'ungiyar tasu.

Shima Ahmad sam baiso zuwaba to ya zaiyi dole yaje.

Su kuwa masu kai lefen.
Suna isa bakin Gate É—in gidan mai gadi ya wangale musu gate inda suka kutsa cikin gidan cikin nutsuwa,
bayan sun gama yin parking ne.
Ahmad ya fito ya nufi wurin mai gadin,
hannu ya bashi suka gaisa sannan yace mishi ya shiga cikin gida yace bak'in sun iso.
Cikin mutuntawa mai gadin yace to tare da juyawa ya shiga cikin gidan.

Jim kaÉ—an ya fito yace.
Ance su isa.

Nan duk matan suka shiga su kuma mazan duk suka zauna cikin motocin.

Suna shiga cikin gidan Maryam tayi musu jagora har babban parlour Mama duk da bata nan dole a bata matsayinta na uwa.
Bayan sun zazzauna, an gaisa cikin mutun taka, an kawo musu drinks da snacks, sun ɗan taɓa abin sha.
Hajia Rabi ce ta gyara zama tare da cewa.
"Raliya je kice Imran Suleiman da Hayatudeen su shigo da kayan."
A hankali ta mik'e tare da cewa.
"To."

A tare suka shigo duk suna riƙe da akwatuna harda ma'aikatan gidan,
haka suka dinga shigowa da haɗaɗɗun akwatunan cikin falon, saida suka ƙare
sannan suka juya suka fiti suna haki,  dan sosai akwatunan suke da nauyi kasancewar kowanne ashaƙe yake da kaya.
Aunty Kubra ce ta kalli Raliya dake riƙe da ɗan Maryam tana mishi wasa,
tace.
"Ke ƙanwar ango ai bakici ta zama tashi ki nuna musu kayan."
murmushi tayi tare da cewa.
"To Aunty Kubra amman dai a tayani."
Murmushi sukayi baki É—aya ganin yadda taketa kiciniyar bubbude akwatunan,
tare da cewa.
"Wannan turamene a ciki wannan laces, wannan shadda wanna boyel."
sai kuma ta fara jawo na ƙananun kaya dana kayan shafa wanda ta buɗe akwatuna biyu wanda suke cike maƙil da ababen shafawa na kwalliyar jiki irin na mata.
Da sauri Mommy matar Malam Adam tace.
"Masha Allah. Gsky ki huta kawai, wannan ai yafi ƙarfinki muma masu gani har mun gaji,
wani abun ai bazai ganuba,
sai dai muce Allah ya sanya al'khairi yasa al'barka a ciki."
Aunty Lubna kuwa kai kawai take jinjinawa domin idonta ya raina fata,
nakasasshen da ake zatawa riƙe ƙoƙon bara da bin kwararo lungu da saƙo yana allazi wahidin,
shine da wannan kayan lefe wanda ita dai a iya ganinta lefen Zahra buhari ne kawai ta taɓa gani wanda zatace yafi wannan, a dai gani da idonta.
Goggo Maryama kuwa tausayi suka bata ganin irin ruwan dukiya da suka binne a kan yarinyar da ta sani tabbas uwarta bazata barta ta zauna a gidan Saifuddeen ba.
Mamy ma tabbas tausayinsu taji ganin yadda sukayi ɓarin naira.
Maryam kuwa sai addu'a takeyi a ranta tana cewa.
"Ya Allah ka rufa mana asiri,
ka hana mahaifinmu jin kunya da tozarta,  ya Allah ka tausasa mana zuciyar wannan baiwar taka Zaleeha kasa tayiwa mahaifinmu biyayya ta zauna lfy da mijinta da yan uwanshi."
sosai Maryam ke jin tsoron abinda zai zubarwa mahaifinsu darajarsa da mutuncinsa.
Adda Rahamace ta ɗanyi dariya kana ta jawo ɗan kit ɗin  da saraƙuna suke ciki, ta buɗe  babban gwal ɗin da Saifuddeen ya saya  a India ta zaro ta miƙawa Mommy dake kusa da ita cikin sanyi tace.
"To ga wannan ko za'a adanashi da ban, duk da cewa sauran ma gwala gwalaine amma shi tsadansa dabanne."
sosai Mommy ta girgiza da girma da darajan gwal É—in, mai surki da ruwan farin zinari.
amsa tayi tare da miƙawa Mamy,
mamakinsu ya ƙaru ne lokacin da Aunty Kubra ta miƙawa Aunty Lubna car key ɗin kia d'innan tare da cewa.
"Ga wannan Key d'in motar amaryarmun ce,
motar tana nan waje.
zuwa yanzu fa Mamy abin ya fara zarta zatonta cikin dattaku da nitsuwarta da iliminta tace.
"Anya kuwa, gsky Malam zaiyi faɗa in muka karɓi abubuwan nan, ko lefen ma in ya gani zaiyi faɗa."
Da sauri Goggo Dada da Aunty Kubra sukace.
"Dan Allah da manzonsa kar muyi haka daku,
Saifuddeen bazaiji daÉ—iba tunda shi ya gani zai iya yiwa matarsa komai,
kuma abinda nanda wani É—an lokaci ta zama matarsa."
Murmushi Aunty Lubna tayi tare da cewa.
"Kuma shi za'ayiwa kolliyar ba."
Ta ƙarishe mgnar tana kallon Aunty Kubra wacce bazata wuce sa'arta ba.
da sauri Aunty Kubra tace.
"Ato kunga ai kanshi yayiwa tanadi, mutun da matarsa."
Goggo Maryama ne tace.
"To mu dai tunda kunce dan Allah da manzonsa to zamu amshi kayan,
saura mgna kuma tana wurin Yaya Malam."
Hajia Rabi ce tace.
"Shima anjima da dare za'a kawo sadaki fatanmu Allah yasa,
a saka bikin nanda mako É—aya."
Amin Amin sukace baki É—aya.
Maryam ce tace.
"ai kam naga alaman Saifuddeen ya zaƙu yana son matarsa nan kusa tunda gashi harda kayan rufi kuka kawo."
Cikin sakin fuska Adda Rahma tace.
"Sosai makuwa ,ai shi ko yau ya sameta yana so."
Daga nan suka ɗan taɓa hira sannan suma miƙe tare da cewa.
"To mu zamu tafi sai kuma in munzo É—aukan amaryarmu."
Da sauri Mommy ta kalli Maryam da Lubna ta musu alamun su ɗauko food flasks ɗin dake cike da ababen mƙulashe.

Ganin sunata cika musu kulolin a gabansu yasa,
Goggo Dada cewa.
"wannan abu yayi yawa ku barshi."
da Saudi Goggo Maryama tace.
"A a ai yaba kyauta tukuici, ku barmu muma muyi iya iyawarmu."
Hajia Rabi ce ta kalli Mommy matar Malam Adam dake miƙa mata damin kuɗin tukuicinsu rafa guda shida yan dubu daddaya.
A hankali tace.
"Hajia wannan kuÉ—in kuma na menene duka?."
Cikin salon girma ba batun ƙaramta Mommy tace.
"Yaba kyauta tukuici, ba ku muka bawa ba yaran da suka shigo da kayan muka bawa."
Akan dole su,suka karɓa, nan Aunty Lubna taƙira biyu daga cikin masu aikin gidan Baba Malam ɗin suka shiga jidan food flask ɗin suna kaiwa cikin motocin da su Adda Rahama suka zo dashi.

Har bakin gate suka rakosu baki d'ayan su,
aka rabu cikin mutunci da jin dadi.

Bayan sun koma cikin gida ne,
Aunty Lubna ta kalli Maryam tare da cewa.
"Ke zo muga kayannan da kyau,".
Dariya Maryam tayi kana ta matso ta fara bubbud'e akwatunan, Mommy, Mamy, goggo Dada kuwa suma zama sukayi suna kallon kayan d'aya bayan d'aya.
yayinda tuni Aunty Lubna keta viewing tana d'aukan komai a zazzafar wayarta.

Sune basu gama ba har aka kira sallan magrib, dole suka hak'ura suka k'arisa kallon a gaggauce kana suka rufe komai,
suka shirgeshi a cikin d'akin Mama,
kana duk sukayi al'wala dan gabatar da salla.

Bayan sunyi sallah harda na isha,
sukaci abinci,
sukaci gaba da hira,
dan Maryam jira take mijinta ne zaizo ya d'auketa hakama Mommy Malam Adam ne zaizo ya d'auketa,
Goggo Maryama kuwa Ya Ahmad ne zai maidata gida.

Baba Malam kuwa, tunda yamma yake gidan Malam  Adam,
dan amaryarshi bata zoba.
Ya Ahmad kuwa da Ya Aminu tunda safe suka tafi dukku kai ziyara dan Ya Ahmad ya kusa komawa Abuja.

Saida akayi sallan magriba suka dawo,
Kai tsaye parlour'n Baba Malam suka nufa,
nan Maryam ta kawo musu abinci,
bayan sun gama cine sukayi al'wala suka nufi masallaci a nan suka samu Baba malam da Malam Adam.
Koda aka idar da salla tare suka shigo cikin gida.

Suna shiga bada dad'ewa ba,
Dirankadi da Bappa Ali da Malam Ashiru suka iso harabar gidan.
Dirankadi ne ya kira Baba malam ya shaida masa isowarsu,
jin haka ya kalli Ahmad tare da cewa.
"Ahmad tashi kaje ka shigo da iyayen Saifuddeen."
Cikin tsananin girmamawa da sanin darajar mahaifa Ahmad yace.
"To." sannan ya miƙe tsaye ya fita.
Yana zuwa yayi musu jagora har zuwa parlour'n Baba Malam É—in, sunyi farin cikin ganin juna sosai.

Bayan sun gaisa ne tare da ɗan taɓa hira,
sai Bappa Ali ya É—an gyara zamanshi tare da yin gyaran murya kana ya fito da damin kuÉ—i kimanin dubu É—ari cas,
daga cikin aljihun babbar rigarshi,
miƙa kuɗin yayi wa Malam Adam tare da cewa.
"To ga aiken É—ana Saifuddeen ga sadakinshi."
cikin sakin fuska Malam Adam ya karɓa tare da cewa.
"Masha Allah. Allah ya sanya al'khairi. Yasa ayi damu."
"Amin Amin." suka amsa baki É—aya,
sai kuma suka kalli Dirankadi da yace.
"Tofa É—alibin naka yace yanzu sauran a saka masa rana kawai."
Murmushi mai kama da dariya sukayi baki É—ayansu, sannan
Malam Adam ya kalli amininshi Baba malam da yaketa murmushin jin daÉ—i yace.
"To Malam Bashir me kace kan batun saka ranan?."
Kanshi ya É—an rausayar ya kalli babban É—anshi mafi soyuwa a zuciyarshi, kana kuma É—ansa mai tsananin biyayya da kare mutuncinsa,
sannan ya kalli É—an É—an uwanshi kuma surkinshi mai kare daraja da martabar ahalinshi wato Ameenu kenan, yace.
"To ga yayun Zaleeha nan mu basu dama muga irin dattakunsu mana."
da sauri Ahmad ya ɗago kanshi ya kalli mahaifin nashi sai kuma yayi sauri yayi ƙasa da kannasa tare da cewa.
"Baba malam in dai kuna raye ai mu bamu da bakin mgn, sai abunda kukace."
sosai Ahmad ke burge su Bappa Ali yanayin biyayyarsa tamkar Saifuddeen.
malam Adam ne ya É—an kishin giÉ—a kana ya kalli Ahmad da Aminu yace.
"To Ahmad mu É—in tabbata zamuyi ne?."
A hankali ya jujjuya kanshi yana mai jin tsoron randa zai rasa iyayenshi.
Shikuwa Malam Adam cigaba yayi da cewa.
"To kaga shiyasa muke jawoku a jiki dan mu nuna muku yadda ake aiwatar da komai na jagoranci,
a matsayinku na manya wanda dole wata rana kune a madadinmu,
yanzu dole zamu so muga yanayin dattakunku,  tunda dai kusan komai kuma kunga an kawo ko wani abu na al'ada kama daga gishiri da goro da lefe da kayan rufi, kana yanzu kuma kunga sun gabatar da abinda shariya ta zantar sun kuma buƙaci a saka ranar biki,
to yanzu dattakunku muke son gani,
kai Aminu kaine Babba kan Ahmad yaushe nene kakega za'ayi bikin?."
A hankali Ya Aminu ya É—an rusunar da kanshi sai kuma ya kalli Ahmad,
kusan a tare suka haÉ—a baki wurin cewa.
"Ashirin da bakwai ga wata mai kamawa. Yayi ko?."
A hankali Baba malam ya fidda sassauƙan numfashi tare da cewa.
"Yayi kyau,  to Amman meyasa har wata ɗaya, baku shirya bane?."
Cikin nitsuwa Ahmad ya kalli mahaifin nashi tare da cewa.
"Eh to Baba malam mun shirya amman bamu gama shirin ba.
Nanda kwana biyar zan koma Abuja,
sannan inada zirga-zirga tsakanin ƙasashe da dama Dubai, India, US, Korea, Egypt. Yanzu dai in na fita zan ɗan kwana biyu kafin in karkato Nigeria, kuma inaso inyiwa Zaleeha kayan ɗaki mai kyau zan bata zabi kayan ƙasar da takeso,
zan gama saya mata komai a online sannan nasan cikin sati biyu jirgi zai iso dasu nan,
to shiyasa nake son ya kai wata É—aya."
murmushi Dirankadi yayi tare da cewa.
"Yaran zamani ku dai kunfi yarda da kayayyakin ƙasashen turawa, sam kun Kasa tsayuwa ku inganta mana na ƙasarmu yadda zamuci gaba muma, yanzu jihar gombe wanne irin kayane babu?.
Duk fa arewacin ƙasarnan babu jihar da ta kai jihar Gombawa yawan kafintoci da ci gaban kafintoci. Babu irin samfurin kayan ƙasar waje da basa iya sarrafawa,yanzu konan cikin Sahaja Ventures kuka shiga ae akwai kaya masu kyau da inganci, wasu ma harsun ɗarawa kayan waje kyau."
Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"Ahmad wannan zirga-zirga duk na menene?."
Aminu ne ya É—an kalleshi tare da cewa.
"Ai driver ne shiÉ—in shiyasa yana nan kamar farin wata yana ko ina."
Cikin mamaki Bappa Ali yace.
"Driver kuwa?."
Murmushi Malam Adam yayi tare da cewa.
"Eh shi pilot ne driver' n jirgin sama. Yana aiki da kamfanin Azman Air Land."
kai bappa Ali ya jinjina jin suna kamfanin ma aikatar Ahmad É—in.
Nan dai suka gama tsara komai da shirya komai na bikin yadda ya dace,
an dai bar batun É—aurin aure nan da wata É—aya mai zuwa.

Wai to ina Zaleeha ne, mun dai san Mama da Zahira kan suna Doho,
Ziyada da Zakariyya kuma mun san su dama gidan Hajja inna suke da zama tsohuwa mai boris.

A gidan su Saifuddeen kuwa su Adda Rahma suna dawowa,
duk suka zauna parlour'n Ummi suna hirar mutunci da karramawar mutanen, Hajia Rabi ce ta kalli Ummi cikin nitsuwa tace.
"Na É—an samu nitsuwa da naga gidansu yarinyar gidan mutunci ne, duk mutanen gidan sunada mutunci."
Kai Ummi ta jinjina tare da cewa.
"Masha Allah."
Aunty kubra ce tace,
"A gsky ba laifi sunada dattaku, sai godiya suketayi kamar kyauta muka basu kayan."
Hayatuddeen ne yayi dariya tare da cewa.
"Nan kuma wayo zamuyi musuba mu É—auke musu Æ´arsu kayan kuma gidanmu zai dawo da dalelliyar amaryar Hamma na."
Dariya sukayi baki ɗaya, Imran ne ya ɗan sosa ƙeya tare da cewa.
"Aunty Kubra zamu tafi fa."
cikin dariya tace.
"Yo to ku tafi mana."
Sulaiman ne ya É—an zaro ido tare da cewa.
"To kuÉ—in namufa da aka bamu?."
da sauri suka juyo suka kalli Isma'il da yayi dariyar ras Kamar ba kurma ba.
Hajia Rabi ce tace.
"Ohoho ni Rabi'atu wlh wata rana kuÉ—i zaisa Isma'il É—ina yayi magana, ji shewar da yake jin ance kuÉ—in nasu ne."
Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa.
"Yaseen kuwa Mom Isma'il in yaga kuÉ—i har harshenshi zakiga yana rawa."
Dariya yayi tare da kaucewa dukan da Isma'il ya kai mishi,
Ita kuwa Hajia Rabi kuÉ—in ta fidda cikin Jakarta irgasu tayi ganin dubu hamsin ne a rafar forko kuma duk girmansu É—aya,
shiyasa suka gane cewa dubu É—ari uku ne suka basu tukuici,
wanda a al'adan gombawa in an kai kayan lefe anasa kuɗi a ƙasan turame,
in dubu goma akasa to dangin amarya zasu ƙaro wasu dubu goman su ɗaura kan goman dake ƙasan turame sai su bawa wanda suka kawo kayan wannan nasune tukuicinsu kenan so su yasu zasu raba,
in dubu biyar akasa to biyar ɗin dangin amarya zasu ƙara,
In 20k nema to dole zasu ƙara in 30k ne ko 50k Ko 80k 100k nema dole su ninka,
to su dama dubu ɗari suka saka a ƙasan turamen,
su kuwa madadin su ƙara dubu ɗarin sai suka ƙara dubu ɗari biyu,
shiyasa suka samu dubu É—ari uku.
Rafan dubu hamsin Hajia Rabi ta miƙawa Hayatuddeen tare da cewa.
"To gashi ku karɓi wannan."
Da sauri suka amsa tare da É—aukan tiren da Adda Rahama ta cika musu pepper chicken dasu drinks akai, tace kuci abinci kafin ku raba kuÉ—in.
to sukace kana suka haura sama a parlour'n Hayatuddeen suka baje kolinsu,
Imran ne ya É—auki kuÉ—in ya irga 10k ya bawa Sulaiman kana ya bawa Isma'il ma 10k shima ya É—auki 10k kana ya bawa Hayatuddeen 10k, 40k kenan,
sai ya É—ago sauran 10k É—in kuma yace.
"To wannan 10k É—in kuma na Zakariyya ne.
kun san Zakari namu yaseen in mukaci kuÉ—in nan bamu bashi ba sai ya tsigemu.
dan baya nanne shiyasa bai samu zuwa ba."
dariya sukayi baki É—aya,
Hayatuddeen ne ya figi lallausan tsokan cinyar kaza tare da taunawa ido ya lumshe jin harshenshi na motsi dan daÉ—i, buÉ—e idon yayi tare da cewa.
"Yanzu ma yamin text wai wlh mu ajiye mishi naman rabonshi."
dariya Suleiman yayi tare da cewa.
"Wai ina yaje ne?  Ni tun jiya bamuyi mgna da shiba?."
Hayatuddeen ne yayi gyatsa tare da cewa.
"Dad'in kowa sukaje da Hajja inna tamu, da wannan fitinenniyar yayar tashi wai sunje gidan ƙanin Hajja inna tamun sai gobe zasu dawo."
dariya sukayi ganin Isma'il fa baya tare dasu sai harraƙawa yakeyi.
Nan sukayi ta hirarsu irinta sabbin matasa masu jin da rawan kan gigin balaga.

A parlour kuwa Adda Rahma da Raliyya sam ƙin karɓan kuɗin sukayi.
Ummi ta kalli Hajia Rabi tace.
"Ku rabasu, ki É—auki dubu hamsin Kubra hamsin sai Goggo Dada itama a bata hamsin Aunty Mina ku bata hamsin Sadiyan Salisu hamsin.
Su kuma Rahma da Raliya angon zaizo ya basu tukuicin."
Dariya sukayi duka ganin karamci da kima da dottakun Ummi sannan tasa Aunty Mina ta raba musu kayan ciye-ciyen da suka dawo dasu.

Ganin magriba ta karato yasa  duk suka miƙe suka sallami juna suka tafi.

Hakama abokan Hayatuddeen duk sun tafi.

Bayan an idar da sallan magriba ya Adnan ya shigo har parlour'n Ummi in da ya samu suna zaune gaba É—ayansu ga Aunty Mina da Goggo Dada,
cikin sakin fuska ya kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"Eye ƙanin ango me ka samu hakane naga sai murna kakeyi?."
kai ya jinjina tare da cewa.
"Ji nake kamar dai na jawo bikin nan."
kafaÉ—anshi ya É—an buga tare da cewa.
"kamar yau ne."
Sai ya kuma kalli su Ummi tare da cewa.
"To Ummi mu zamu wuce gida,
tun É—azu Faroq keta kirana wai muyi sauri mu koma."
kai ta jinjina tare da cewa.
"To Allah ya kiyaye hanya."
"Amin Amin".
yace tare da miƙewa ya amshi Akih dake hannun Raliya,
sannan ya juya ga matar tasa tare da cewa.
"Rahma taso mu tafi ko."
to tace kana ta miƙe ta zari hijabinta tabi bayanshi.

Ƙarfe tara na dare dai-dai su bappa Ali suna parlour'n Ummi.
suna shiga da kamar 15 minutes Saifuddeen ya shigo bisa wani zazzafan wheelchair É—insa red colour da gani kasan sabone.
ganinshi ne yasa su murmusawa gaba É—ayansu,
Ahmad dake biye dashi a baya wanda shine daya maida Imran sai ya É—aukoshi dan shi tunda yamma yana gidansu Ishaq .
Cikin girmamawa ya gaidasu,
kana shima Ahmad yazo ya zauna gefen kawun nashi tare yin gyaran murya yace.
"Kawu Ali kun jene?."

"Eh munje yanzu ma daga can muke?."

"Masha Allah, to ya batun saka ranan?."

Malam Ashiru ne ya amshi zancen da cewa.
"Alhamdulillah an tsaida ranar É—aurin auren."
Cikin zumuÉ—i Hayatuddeen yace.
"Yaushe ne auren?."
murmushi bappa Ali yayi tare da cewa.
"Yau saura kwana ashirin da takwas yadda lissafi ya nuna."
Wani irin zabura Hayatuddeen yayi tare da sakin sauti,
sai kuma yasa hannu ya rufe bakinshi tare da komawa ya zauna ganin wani irin kallon da Saifuddeen ke mishi alamun ya nitsu.
Zumbura baki yayi tare da karkaÉ—a kai.
Shi kuwa Saifuddeen wani irin yalwataccen murmushi yayi a cikin zuciyarshi yana mai jin wani irin zazzafan farin ciki na ratsa mishi jiki jini jijiya harma da ɓargo,
a fakaice ya kalli Hayatuddeen tare da yin mganar zuciya.
"Hmmmm am so sorry Hayatuddeen, duk farin cikin da kakeji baka kai niba, da kunsan yadda nakeji tabbas da kunsha mamaki,.
lumshe idanunsa yayi tare da ci gaba da batun zuci.
"Badan kunya da nakasar da Allah ya minba da nashayar daku mamaki, Wallahi ina É—agowa daga sujjadar godiya ga mahaliccina sai inyi ta tsalle ina kurma ihu da kururuwa duniya tasan cewa ban taba samun irin farin cikin dana samu a yau ba."
a hankali ya buÉ—e idanunshi ya kalli,
Ahmad da fuskarsa ba yabo ba fallasa inda yace.
"Masha Allah, Allah ya kaimu lokacin bisa rai da lafiya."
Amin Amin suka amsa baki É—aya.
Shi kuwa Saifuddeen sai godiya yayi musu kana ya kalli Umminshi da yake hango abubuwa biyu a kwayar idanunta farin ciki da fargaba mai tattare da tsoro,
ita kuwa Ummi zallan farin ciki dake cikin kwayar idanun gudan jinin nata take hangowa hakane yasa kaso 50 cikin 100 na fargabanta ya gushe.
kauda idonta tayi daga gareshi ganin alamun yana son keɓewa da ita,
cikin kula ta miƙawa Hayayuddeen Key ɗin BQ ɗinsu tare da cewa.
"Tashi kaje ka buɗewa su bappa Ali masauƙinsu kazo ka kai musu abinci."
Amsa yayi ya fita kana suma su bappa Ali dake son hutawa sukabi bayanshi.

Goggo Dada da Aunty Mina kuwa É—akin budurcin su Raihana suka shiga dan duk sun gaji,
Ahmad ma miƙewa yayi tare da kamo hannun Raliya yace.
"Ke mu tafi bacci nakeji."
cikin jin kunya ta miƙe tabi bayanshi,
shi kuwa Saifuddeen ko inda suke bai kuma kallo ba.
Kai tsaye side É—inshi ya nufa.

Yana shiga ratsetsen parlour'n shi yayi wani irin sassanyan a jiyan zuciya,
tare da lumshe manyan idanunshi,
murza masarrafin wheelchair d'in nashi yayi tare zaro harshen sa ya karkad'a a rashi yace.
"Kaddararki ce aurena Zaleeha, insha Allah sai kin amsa sunan matar wanna gurgun kurma nakasasshe ginennen tabon nan zai shayar dake zallan ruwan madarar da zata tsastsafo daka gareshi,
sai kin zama inuwar ni'imata,
wannan ginennen tabon sai ya zautar da kwanyarki."
A hankali ya fara zare rigar jikinshi yanayi yana shiga bedroom É—inshi,
cire kayan jikinshi yayi can ya rage dagashi sai boxer d'inshi mai zanen fari da ja,
Bathroom ya shige cikin tsananin shauk'i da farin cikin cin nasara yake komai da kuzarinshi.
yana cikin bathtube É—in wankan shi ya kalli surarshi tare da lumshe ido kana ya fara zancen zuci.
"Am sorry Baby zakisha bulalar nan da kika tab'o lafiyarta tsawon shekaru talin bata tab'a tashi tsayeba bare ta harba saida kika tab'a sashinta,
kuma daga ranar duk sanda zuciyata ta tunaki sai ta harba,
wannan shine yak'inin gidanta a jikinki yake."
A hankali dai yayi wanka yana fitowa yayi shirin baccinsa.

Bakin gadonshi ya zauna tare da mik'e k'afafunshi sannan ya d'aura system d'inshi a kan cinyoyinshi bisa dukkan alamu,
aiki mai mahimmanci yakeyi, wanda kuma fuskarsa cike take da farin ciki,

Yana cikin haka yaga Umminshi ta shigo bisa dukkan alamu itama ta gama shirin baccinta,
ganinta ya sashi muskutawa ya É—an bata wuri,
ganin haka ta zauna gefenshi,
cikin tsananin jin daÉ—i ya ture system É—in kana ya matsota a hankali ya raba jikinta kanshi ya kontar a kafaÉ—unta,
ganin haka alamune na yana cikin tsantsar farin ciki, ko tarin gajiya,
sabida Saifuddeen baya da juriyar hawala ko kaÉ—an in dai Umminshi na kusa to tana gane rauninshi shiyasa baya ma boye mata.
hannunta tasa ta shafa kanshi,
sannan ta matso da system É—in cikin rashin kwarewa tayi rubutu a hankali.
"Gajiya ne ko farin ciki?."
ganin abinda ta rubutane ya sashi lumshe ido tare narkewa jikinta a hankali ya rubuta mata.
"Daɗi farin ciki kwanciyar hankali salama da annashuwa, Ummi yau ina cikin farin cikin da ban taɓa jin irinsa ba."
ya ƙarishe rubutun yana kallonta dan sam bai iya mata ƙarya."
murmushi tayi tare da cewa.
"Allah ya cika rayuwar auren naku da farin ciki."
A saman lips inshi ya amsa da Amin.
Sai kuma tasa hannu bisa bedside ta ɗauko cup mai ɗauke da zazzafan tea mai ganyen Na'a-na'a, ta miƙa masa.
karɓa yayi tare da ɗan zuƙa a hankali,
idonshi ya lumshe dan jin ƙamshin da tea ɗin keyi.
Ita kuwa Ummi a hankali tace.
"Sai da safe ko."
Kai ya gyadÉ—a mata alamun "To."
tana fita ta wuce bedroom d'inta,
kwanciya tayi amman baccinta yak'i zuwa nazari sosai takeyi tana tsoron duk wani abu da zaizo ya cutar mata da É—anta.

Hayatuddeen kuwa a d'akinshi yana konce yayi É—ai-É—ai yana shan dadÉ—an sanyin A.C kana yana chatting da yan uwa da abokan arziki inda yaketa sanar musu date É—in auren Hammanshi.
musamman a dandalinshi na Instagram wanda yakeda mabiya sama da dubu 9 wanda kuma yawanci sabida pictures É—in Saifuddeen ne da yake sawa, da kuma son jin ainihin waye shi,
tarin tambayoyin da ake mishi bazai iya amsarsu ba,
sabida da yawama a zatonsu Saifuddeen bazai iya aureba.

Ganin tambayoyin sun mishi yawane ya rufe datan Instagram yana niyar buÉ—e WhatsApp sai ga kiran Amina ya shigo wayarshi video call.
yana É—agawa yayi dariya ganin yadda ta haÉ—e fuska,
A ƙufule tace.
"Dariya ma na baka kenan?."
Cikin dariyar yace.
"Hmmm to ni me nayi miki naga sai hararata kikeyi?."
ajiyan zuciya ta É—anyi tare da cewa.
"Yau kwana biyar kenan ina kiranka baka É—aga waya meyasa."
da sauri yace.
"Sabida nasan zakice in bawa Hamma Saifuddeen wayar,
kuma duk sanda kike kira baya kusa shiyasa bana É—agawa."
baki ta ɗan taɓe tare da cewa.
"Ai dai yanzu kam yana gida ko?."
Miƙewa zaune yayi tare da cewa.
"To amman ya shiga fa."
Da sauri tace.
"Please karkace komai ka kai mishi wayar. Dan Allah karkace a a."
jin haka ya miƙe tsaye ya nufi ƙasa.

Kai tsaye Side ɗinshi ya nufa inda Ummi ta rufeshi ta baya dan haka a sauƙaƙe ya shiga parlourn,
a hankali yace.
"Ni dai duk in da akace nawane sai ya koma kamar tirken doki,
kalli yanzu parlour nan ko sarkin makka zai zauna a nan komai tsab-tsab sai ƙamshi tamkar da turare ake mishi mopping,
kalli can kuma sama yadda banzayen nan su Imran suka wancakalarmin da parlour haka aka barminshi kamar wani maraya,
to yaseen yau a nan zan kwana."
Ya k'arishe mgnar lokacin da yake shiga bedroom d'in.

Ita kuwa Amina sai dariya takeyi dan duk taji me yake faÉ—in.
Yana shiga kai tsaye ya nufi kan gadon inda ya hango Hamman nashi na zaune wayar ya miƙa mishi cikin zumbura baki ya haura kan gadon ya konta gefen ɗan uwan nashi tare da rufe idanunshi wai shi yayi bacci.
Murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara mushi rufuwan da yayi dan yasan bazai iya jure kwana cikin sanyin dashi yake kwana ba,
sai ya kuma juyo ya kalli fuskar wayar tashi daya miƙa mishi,
da sauri ya rage idanun nashi ganin fuskar Amina ita kuwa,
girarta É—aya ta É—aga mishi alamun ya dai.
sai ta kuma kalleshi cikin lunshe ido tace.
"Ya jikin ka?." bata tsumayi amsaba dan tasan ba samu zatayi ba shiyasa taci gaba da cewa.
"In zo har garinku har gidanku in dubaka da jiki,
in dawo Amman ko ka kira kaji mun dawo lfy ko?."
a hankali ya zaro harshenshi ya lashi jajayan labbanshi hakan yasa suka ƙara fitar da sheƙi,
Lumshe idonshi yayi tare ds longoɓar da kanshi bisa kafaɗarshi tare da narke fuska, haka nan yaji wani guntun murmushi ya suɓuce mishi,
ido ta lumshe tare da cewa.
"Bakinka yana min kyau, gashin girarka mai kyau, idanunka masu  tarin   kyau,  sajenka yana min  kyau sosai Hamma, ina son komai naka surarka, yan uwanka, abokanka ina son duk wani abu naka,
bayan Ya Amir kaine mutun na forko da nake bege da so."
shiru yayi ya zuba mata idanu, yana karantar lafuzanta,
ita kuwa cikin zazzafar soyayyarshi dake sarƙe mata zuciya da ruhi tace.
"Ina sonka Hamma Saifuddeen zaka aureni?  Kayi haƙuri kunya nakeji bazan iya rubuta makaba, kuma inajin kunyan in gayawa Hayatuddeen, gashi kai kuma baka jina to ta yaya zan shaida maka soyayyata,
ina sonka ka zamo mijina uban Æ´aÆ´ana, ina addu'ar Allah ya azurtamu da samun yara masu kama da kai."
sai kuma ta kalleshi ganin ya tsareta da ido haka nan yake jin kalaman nata har cikin zuciyarsa,
to amman wai meyasa ita bata kunyan faÉ—i mishi wasu abin ne, ita kuwa ganin yayi shiru ya kuma rage girmam idanunshi ne ya sata cewa.
"Ka gaji ko? bacci kakeji ko?, naga idonka yayi limshi, bari in kashe wayar sai da safe."
Tana kaiwa nan ta katse kiran,
shi kuwa Saifudddeen dariya yayi a ranshi yace.
"Sokuwa kawai mai tunanin yara wato kina sona, hmmm ke dai faÉ—i gsky bani kike wani soba, kinada dai abinda kikeso daga gareni."
daga nan yayi ta aikinshi.
sai kusan ƙarfe ɗaya,
ya sauƙo ya shimfid'a sallaya kana yaje yayi al'wala sannan yazo yayi nafilfilinshi sai d'aya da rabi ya konta.

Washe gari ranar Jummu'a tun da safe su Zaleeha suka dawo,
daga gidan Hajja inna tayi wanka ta wuce Billiri dan hira da nakassusun wancan yankin wanda k'arfe biyar na yammacin ranar jumma'ar ne zata gabatar da shirin, tun randa ta had'u da Saifudden a Jonapwd, bata sake zuwa canba,
kuma tunda ta turawa ishaq text ɗin ban haƙuri bai kulataba itama bata sake bin ta kanshi ba,
shi kuwa Ishaq shida Saifuddeen bakinsu a had'e a cewarshi ita da kanshi zata nemeshi har mazauninshi...

K'arfe uku ta dawo daga billiri kai tsaye gidan radio nasu ta nufa,
a nan tayi sallan la'asar, sannan ta zauna jiran lokacinta,
tana zaune anan Bilkisu ta shigo ita da Manager d'insu tana ganin Zaleeha ta kwashe da dariyar shak'iyanci cikin ingizarwa tace.
"Hajiyar nakasassu ina mutanen naki ne? Koda yake amaryar nakasashen gurgu kurma zance ko."
cikin tsananin takaici Zaleeha ta watsa mata harara tare da cewa.
"A a uwar nakasashe zakice ba amryar nakasashe ba wlh mai gado bana so ki daina had'ani da wannan musakin."
cikin Shek'iyanci bilkisu ta iso gareta tare da cewa.
"Sorry baza k'araba,  amman mutanen nakine da abin dariya."
juyawa tayi ta fita tabi bayan Manager ita kuwa Zaleeha Raveel ta kalla wanda yake mik'o mata sweet amsa tayi tare da cewa.
"Ngd."
kai ya gyad'a mata tare da cewa.
"Kada ki sake aibata nakasassu dan duk wanda bai mutuba ba'a gama mishi halittaba.
da kullum haka kike gaya min to meyasa kawai dan nakasasshe yace yana sonki sai ki juye daga Mai kakkyawar alaƙa i zuwa mummunar ɗabi'a, kada ki bari imaninki ya samu rauni."
kai ta gyaÉ—a mishi sannan ta juya ta nufi É—akin gabatar da shirin nata ganin lokacinta yayi.

Mama kuwa da Zahira sosai zugar Ruda yayi tasiri a kwanyarsu da yake dama zuciyar ba inganci.

Ƙarfe huɗu dai-dai suka dawo daga doho,
suna shiga gidan kai tsaye side d'in Baba malam suka nupa,
a parlour suka sameshi shida Ya Ahmad da Ya Habu, sai Mamy dake haÉ—a musu tea a kofuna.
sannu da hanya sukayi musu, fuskarnan kamar zatayi ruwan jini Mama ta amsa musu kana ta gaida Baba malam,
sannan Ahmad da Habu suka gaidata,
Zahira kuma duk ta gaidasu sannan ta wuce cikin gidan tayi shashin maman.
Ita kuwa Mama a hankali ta mik'e ta fita ganin duk basubi ta kantaba,
to wazai kulata yadda taketa harare-harare,
tana fita ta nufi Side d'inta da yake tsab Maryam da Aunty Lubna sun gyarashi jiya da dare.
A parlour ta zauna,
dai-dai lokacin kuma Zahira ta fito daga bedroom d'in Maman a guje,
ganin Maman a parlour yasata tsayuwa cikin rawan jiki da halin fitina tace.
"Mama zo zo zo kiga wani abu a bedroom naki."
tsaki ta d'an ja tare da cewa.
"Menene kike wani zaro idanu haka?."
hannun uwar ta kamo tare da cewa.
"Mama zo ki gani mana an cika miki d'aki da akwatuna dasu buhunan gishiri dasu goro."
ido ta zaro gaba d'aya tare da cewa.
"Akwa tuna kuma to na meye."
cikin hatsabibanci tace.
"To waya sani ko lefen Anty Zaleeha aka kawo."
ai kafin ta rufe bakima Mama ta kutsa kai cikin bedroom É—in.
wani irin wawan birki taja tare da cewa.
"To wanna kuma daga ina, to ko Abdussalam ne da tace mishi a turo komanshi Zaleeha ta yarda dashi, tuni ya turo É—in,
sai kuma ta girgiza kai ina sam ba shi bane ai in shine zai gaya mata, shida kuma É—azu suka gama mgna,
cikin tafasan bala'i tace to waye.
Sai kuma ta dawo parlour da sauri cikin karad'i da kware murya baki d'aya ta fara rabkawa Habu kira.
"Habu! Habu!! Habu!!! Habuuuu!."
da sauri ya iso cikin parlourn a tsorace yace.
"Na'am Mama ganifa nazo."
A hatsale tace.
"To dan ubanka meyasa bazaka amsa da kyau ba."
cikin had'e fuska yace, "Na'am." cikin yamutsa fuska tace.
"Wancan kayan fa na meye ne."
Kai tsaye yace.
"Lefen Zaleeha aka kawo jiya."
cikin É—aga sauti tace waye kawo lefen?."
A dake yace.
"Wasu mata ne."
zaburowa tayi kanshi tare da cewa.
"Dan ubanka ba wanda suka kawo nake tambaya ba wanda aka kawowa nake nufi."
cikin kauda kai yace.
"Zaleeha aka kawowa."
wani dogon tsaki taja tare da jawo hannunshi tace.
"Kai mahaukacin inane wanne saurayin ne ya aiko lefen."
Cikin dakiya da rashin tsoro yace.
"Saifuddeen."
wani irin zabura tayi tare da buga tsalle tace.
"Inji uban waye ya basu damar kawo banzayen lefen wanna musakin d'an nasu?."
Yana fita yace.
"Inji Baba Malam mana Baban Zaleeha shine ya basu dama."
wani irin kware murya tayi tare da yin sauri ta nufi parlour Baba malam tana shiga parlour tare da masifa murya a hargitse tace.
"Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya....!

*Dan Allah da manzonsa ku dena fitarmin da littafi,*

                                  By
                     *GARKUWAR FULANI*
8/

              *NAKASA BA KASAWA BACE*

                            *PAGE 30*

                                  NA
               *AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

"Lallai yau za'a sabunta yaƙin duniya na biyu".
Fuska ta ƙara haɗewa tamkar wacce akayiwa bushara da mummunan al'kaba'in rayuwar duniya.
Ido suka zuba mata baki É—ayansu, tare da maida hankalinsu gareta.
Cikin takaici da tashin hankali tace.
"Meyasa!  Meyasa haka ne malam? Ina dalilin kullum sai an sani baƙin ciki kan aurar da ƴaƴana?."
Kauda kanshi yayi daga kallon mummunar fuskarta tare da maida dubanshi ga al'ƙiblah, a hankali yaci gaba da tasbihi da yakeyi.
"Subahallahi, walhamdulillahi, wa la'ilahalillahu, wallahu akhbar."
haka yaketa mai-maitawa tare da motsa yatsun hannunshi na dama, kana yana ɗan karkaɗa ƙafafunshi dake miƙe bisa table ɗin dake gabanshi a hankali a hankali.
idonshi ya rumtse da ƙarfi jin Mama na cewa.
"Wallahi-Wallahi bazan taɓa yarda a zalumunci Zaleeha irin yadda aka zalumci Maryam ba, akan wani dalili zai sa baza'a sakarmin rayuwar yarana ba, suma su auri wanda sukeso sai ayi ta musu cushe da auren dole ina dalili? to Wallahi  muddin ina raye, Wallahi bazan taɓa lamunta Zaleeha ta zauna da wannan banzan nakasasshen kurma kuma gurgun, da kuka yayibo zaku liƙa mata ku kashe mata rayuwa ba,
haka kawai dan an iya min kisan mummuƙe, shine za'a nunamin wariyar launin fata, a nuna min ni bare ce to Wallahi ban amince ba!."
Cikin gajiya da ihu da hayagagar da take musu Ya Ahmad ya ɗan tanƙwashe sawunshi tare da cewa.
"Mama ai Zaleeha ita ta kawo shi, zaɓinta ne ita ta amince dashi babu wanda ya mata dole,
itace ta amince tasa ya turo iyayenshi."
Cikin tsawa tace.
"Rufe min baki, kaima ae munafuki ne, ban nemi jin ta bakinka ba, da ubanka nake magana,
karka wani karkace kace zaka meda laifin kan Zaleeha, munafurcin banza kawai."
Rumtse idanu Ya Ahmad yayi, cikin takaicin abinda Mama'n kewa mahaifin nashi yace.
"Allah ya huci zuciyarki."
A hasale tace.
"Wannan karon dai zuciyar tawa ba zata huce ba, Wallahi bazan taɓa lamunta da batun ƴata ta auri musakiba,
dan rainin hankalin yarinya da kyawunta da ƙimarta tanada masoya gabas da yamma kudu da arewa amman a rasa wanda za'a zaɓa mata sai nakasasshe, wulaƙantacce wanda ko magana bayaji!."
Tafaɗa ranta amatuƙar ɓace domin sosai zuciyarta ke tafasa.

Duk ihu da hargowan da takeyi Baba Malam bai sake ɗaga  ido ya kalleta ba, sai ma tasbihi da yakeyi ga mahaliccinsa da ya jarabceshi da auran wanna mata mai munanan al'adu.
Mamy kuwa wayarta ta jawo kana ta fara karanta  Dua Azkar.
Ganin haka shima Ahmad sai yasa hannu ya ɗauki ɗan madai-daicin Qur'Ani'n  dake gefenshi ya buɗe ya fara karatu ahankali cikin suratul. Kahf kasan cewar yammacin Jummu'a ne.

Habu ne ya shigo parlour'n a hankali ya nufi gefen mahaifin nasu ya zauna kusa da É—an uwan shi Ahmad,
ido ya rumtse da ƙarfi yana mai jin takaicin hali irin na mahaifiyar tashi,
cikin sanyin sauti yace.
"Ya salam! Dan Allah Mama kiyi haƙuri ki bar yin ihun nan, kowa yanayin abinda zai samar mishi lada ke kuma kinzo kina tarawa kanki zunubi kina ɗaga harshenki sama dana mijink..."
Da sauri ya haÉ—iye rogowar maganar tashi, sakamakon jin Maman ta kai mishi wani uban bugu kan bakinshi.
"Habu kayi asara Wallahi, kai dai ka banunka da baka da kishin mahaifiyarka!." Takuma faÉ—a a hasale.

Baba Malam ne ya miƙe tsaye, tare da kallon yaran nashi cikin kamala da cikar haiba yace.
"Kuyi al'awala mu tafi masalaci lokacin sallah ya gabato."
Da sauri suka mimmiƙe tare da cewa.
"To."
Haka duk sukaje suka sabunta al'wala kana suka tafi zuwa masallaci.

Mamy ma tuni tayi side ɗinta,  inda ta samu Aunty Lubna a parlour tana sawa ƴarta hijabi alamun zatayi salla ne.
"Barka da shigowa Mamy."
cikin nitsuwa da mutuntaka Mamy tace.
"Barka dai Lubna ya gajiyar kitchen? na tafi na barki ke ɗaya da aiki niƙi niƙi ko."
Kai ta rausayar tare da cewa.
"Tun É—azu na gama ai Mamy aikin ba yawa."
"Masha Allah!  Allah Ya saka da al'khairi, ya baki surkai masu miki fiye da abinda kike min."
"Amin Amin"  Aunty Lubna  ta amsa cikin jin daɗi, kana tayi side ɗin da nanne masauƙinsu duk lokacin da sukazo Gombe dan ita da Mamy tamkar uwa da ƴarta haka  suke.

Ita kuwa Mama ta cika tayi tam sai ihu da haushi takeyi ita kaÉ—ai kamar karya.

"Watoma mahaukaciya suka medani? sun watse sun barni wato inyi ta haushi ni ɗaya ko, tam zanyi maganinku, Wallahi gaba ɗaya saikunji aranku cewa inama da ace bakuyi ganganci ƙulla wannan haɗin ba, saina sanya baƙinciki acikin zuciyoyinku, kuma sannan saina saku danasani marar yankewa, badai dani kuke wasan ba, hmmm Wallahi zakusan kun taɓo cikakkiyar ƙaɓila Batangali da surkin bateriya, akan auren nan babu wanda zan ɗagawa ƙafa!!."
Tana gama faÉ—in haka ta juya fuuuuu kamar kububuwa tafice daga cikin falon na Baba Malam.

Tana shigowa falonta ta soma afkawa Zahira ƙira,
da sauri Zahira ta fito daga cikin É—akinsu tana cewa.
"Na'am Mama."

A harzuƙe tace.
"Zo zonan mu kwashi Æ´an iskan kayayyakin nan mu watsasu waje, Wallahi bazasu kwanar min a É—aki ba gayyar tsiya!."

Da sauri Zahira  tace "To."

Nan suka shiga cikin ɗakin, haka suka dinga ibo akwatunan nan masu kyaun gaske,  suna watsasu a tsakiyar farfajiyar gidan,
wai don ma kasancewar Mama ƙaƙƙarfar  mace ce shiyasa kab ta iya jidon manyan akwatunan, tanayin waje dasu harda su gishiri da goron bata bari ba, ranta yakai ƙololuwa wajen tafasa, jin kanta take dai-dai da uban kowa, jira take wani yace mata cass tuni zata sullesa tas.

Saida ta gama watsasu a tsakiyar gidan, sannan ta koma cikin É—akinta tana haki tamkar wacce tayi dambe ta gaji.
Al'wala tayi sannan tazo ta kabbara niyar sallan magriba, wanda tuni lokaci ya ƙure mata, don  har an riga da anƙirayi sallan isha.

Zaleeha kuwa daga ma'aikatan nasu gidan kakar tasu ta koma,
don dama kwana uku ta roƙi Baba Malam  daya barta tayi, kuma da yake gidan mahaifiyarshi ce sai bai hanata ba.

Kafin ma ta dawo tuni Ziyada ta gama haÉ—a musu komai na girki,
tuwon É—anyar shinkafa da miyar kase,
tana ganin haka tace.
"Ziyada ina Zakariyya kuma da tsohuwar nan sukaje, suka barki ke É—aya a gida?."
Cikin yanayin nutsuwarta irin na Maryam sak tace.
"Sun tafi gidansu abokinshi Hayatuddeen."

Tana warware naÉ—in gyalen hijabin dake jikinta tace.
"Sun daÉ—e da tafiya ne?."
Kai ta gyaɗa mata  tare da cewa.
"Eh tun da akayi sallan la'asar suka tafi."
kai ta jinjina kana ta zaro wayarta ta danna ƙiran number'n Zakariyya.

Shi kuwa Zakariyya lokacin suna parlour'n Ummi shida Hayatuddeen da Raliya, sunata tsiya wa Hajja Inna, ita kuwa Hajja inna
sai surfa musu boris takeyi,
Ummi kuwa sai nan-nan takeyi da hajja Inna dan taji dad'in zuwan kakar abokin autan nata, sosai takejin son tsohuwar a ranta, musamman yadda ta nuna tana masifar son Saifuddeen É—inta.
Ta tasashi gaba tana yabo harda kukanta tana.
"Allah sarki bawan Allah, yaro kyakkyawa, Allah ya jarabceshi da nakasa,
ganshi kuwa kamar balarabe."
Sai kuma ta juyo ta kalli Ummy tare da cewa.
"Wannan yaron naki abin sone da tausayawa ga ko wanne mutum É—an Adam me imani, ki godewa Allah daya azurtaki da samunsa a matsayin É—a,
wasu suna can sun haifi lafi yayyun yara amman sai ki samu yaran munanane kamar kashin dare,
kinga ko gwara miki kyakkyawa fari ƙal nakasasshen."
Hayatuddeen ne yayi dariya sosai tare da cewa.
"Kai tsohuwar nan munana sun boni a wajenki."
Zakariyya ne ya zaro wayarshi dake suwa, wacce take cikin aljihun wondonshi yana cewa.
"Itafa sam bata son mummunan mutum, in taga kyakkyawan mutun kuma wai ji take kamar ta dawo dashi É—anta."
Dariya sukayi baki É—aya,
kana shiko Zakariyya ya amsa kiran Zaleeha tare da cewa.
"Hello Adda Zalees ya akayi ne?."
Sai ya kuma yafito Hayatuddeen tare da mishi alamun ga mutuniyarshi fa.
amsar wayar yayi ya kara a kunne tare da cewa.
"Adda Zalees nayi fushi dake muka dawo ko kizo ki duba kyakkyawan hammana da jiki ko."

Murmushi tayi tare da cewa.
"Afwan autan gidansu."
da sauri yace.
"No autan Ummi dai zakice, gidanmu kam ai kwanannan ma Hamma na zai fara ƙenƙesa mana yara sabbin zubi, ƴan yayi kuma kyawawa, irin yaran da Hajja inna ke masifar so."
Ƴar dariya tayi tare da cewa.
"To aku sarkin zance, please ka cewa Zakariyya su biya Abba bakery ya saya min  pizza dan Allah."
Da sauri yace.
"To ba matsala karki damu zan bashi abin daÉ—i ma ya kawo miki, cikin na Hamma na zan É—iba miki."
Da sauri tace.
"A a ni dai pizza kawai nake so."
Bai kulataba ya katse ƙiran.
sannan ya amshi kular da Raliya ta haÉ—a musu tsarabar Kai kayan lefen jiya."
Daga nan suka miƙe  zasu tafi,  har sun kusa fita daga parlour Hajja Inna ta juyo ta kalli Saifuddeen murmushi ya mata, haka itama murmushin tayi mishi sannan ta kalli Ummi cikin halin tsufa tace.
"Kin ga Æ´ata kada ki yarda ki bari wannan kyakkyawan É—an naki ya auro miki mummunar surka,
in kuwa kika bari ya auro miki mummunar surka,  to shike nan ya ɓata miki wannan kyakkyawar zuriyar taki,  dan tabbas dole wata rana sai ta haifo muku mai kama da ita,
dan ni dai anmin na gani, yanzu in kika kalli Zahira zakice ba jinin ahlina bane dan ita kamannin dangin uwarsu tayi yo."
Zakariyya ne ya tura baki tare da cewa.
"Kefa kince baki da goni a duniya sai mai kyau, to sam gigin tsufarki baya gaya miki gsk,  ya zaki rinƙa sarata ina ji, aikin kawai."
Dariya sukayi dukansu ganin yadda ta kamo hannun Zakariyya tana cewa.
"A a kada kaji haushi shalelena, ai kai sak da kakanka baban babanka kakeyi,  shiyasa kai da Ahmad kuke tsananin kama,
Zaleeha da Ziyada kuwa dani suke kama, bakaga Zaleeha ko gashi irin nawa ta gado ba?."
Janye hannunshi yayi tare da kunna machine ɗinsa, kana ya amshi kular da Hayatuddeen ke miƙo mishi ya saka a cikin ɗan kondon dake gaban machine ɗin.
Sai ya kuma kallon Hayatuddeen dake miƙo mishi 10k kana yace.
"Ga tukuicinmu na jiya."
Dariya Zakariyya yayi tare da cewa.
"Kace abin namu ne babu ƙaranci, ashe ko zamuyi casu a bikinga."
Sosai Ummi ke murmushi dan Zakariyya sak autan tane da shirmensa.
Sosai hajja Inna ta ɗale saman machine ɗin na Zakariyya,  kamar ba tsohuwa ba,
da sauri Ummi ta riƙe kai ganin yadda Zakariyya ya figi machine ɗin ya fita a guje.
Hayatuddeen ne ya kece da dariya tare da cewa.
"Hege Zakary namu, wata rana zai ɓarar da hagwaran tsohuwar nan a titi yaseen."
Dariya Raliya tayi tare da cewa.
"Ai harda karya mata ƙafa."
Daƙuwa Ummi tayi musu tare da juyawa tayi cikin gida sannan suma sukabita a baya.

Su kuwa Zakariyya na isa ya miƙawa Zaleeha kular da Hayatuddeen yabasa yayi,  dan tuni shi yaci a can yayi haniƙan,
ita kuwa Zaleeha kamar bazata buɗe kularba sai ta kuma buɗe,  ganin abinda ke cikine ya sata yin murmushi sannan ta miƙe tsaye, lemon exotic ta ɗauko acikin fridge kana ta dawo ta zauna, haka  ta fara cin pepper chicken ɗin dayaji onion,  tanaci tana latsa wayarta,
Ziyada kuwa tuni tabi bayan Hajja inna da ta kirata wai tazo ta cire mata sarkan da ta sanya awuyanta, kasancewar idanun tsufa gareta bazata iya cirewa kanta ba.

Ƙarfe tara dai-dai Zaliha Ziyada da Zakariyya dukansu suna zaune parlour'n  Hajja ina sunata hirarsu irin ta ƴan uwan juna,
yayinda kakarsu ke tsakiyarsu,
tana kallon kyawawan jikokinta da take matuƙar so arayuwa, dan 
duk cikin  jikokinta tafi son Ahmad da kuma Zakariyya.
Sam bata shiri da Habu a cewarta wai shi baya dariya.

A can New G.R.A kuwa kasan cewar yau girkin Mamane dan Mamy yau ta ƙare kwana biyunta.

Suna dawowa sallan isha Ahmad da Habu sukayi cikin gida.
Da sauri Habu ya tsaya, cikin mamaki yace.
"Ya Ahmad kalli can."
Da sauri Ahmad ya isa wurin da Habu ke nuna mishi, ganin
kayan  lefen Zaleeha ne da aka kawo jiya watse aƙasa, setin gaba ɗaya akwatuna 30  dasu  tarkacen gishiri da goro duk an watsosu waje, 
cikin tsananin Al'ajabin halin Mama da tsaurin ido irin nata yace.
"Innalillahi! Habu tayani mu kwashesu, tunkan Baba Malam yazo yagani, nasan bazaiji daÉ—i ba aransa ba."
Da sauri suka fara tattara kayan, sai kuma duk suka tsaya tare dayin shiru, sakamakon jin muryar mahaifinsu ta window parlour'n shi.

"Ku barsu a wurin ko tsinke kada ku É—aga, ku wuce ku bar wurin."

Shiru sukayi cikin tsananin tarin damuwa dan dagajin muryar Baba malam yana cikin tsananin baƙin ciki, muryarshin ce ta katse musu tunanin da sukeyi.
"Ku bar wurin ko nace!." ya ƙarishe maganar cikin bada umarni irin na fusata.
Da sauri sukace.
"Toh".
sannan suka juya, kowa ya nufi É—akin mahaifiyarshi.

Gefen Mamy Ahmad ya zauna cikin ƙunan rai yace.
"Please Mamy kije ki bawa Baba malam haƙuri, naga ranshi ya matuƙar ɓaci, kice  yayi haƙuri ya barmu mu kwashi kayan, in yaso mushigo dashi nan ɗakinki."

Murmushi Mamy tayi tare da cewa.
"Hmmm Ahmad ai wannan ba hurumi na bane,
ku bar kayan kamar yadda ya umarceku,
Mamanku ta zauna da Malam kusan tsawon shekaru 30 kenan yau, amman har yau bata san waye Malam ba, bata taɓa ƙureshi ba,
amman da dukkan alama yau zata san kaɗan daga cikin halaiyarsa,  idan ransa ya ɓaci,
shi acikin ruwan sanyi zai dafata."

Jin haka yasanya Ahmad cewa.
"Hmmm kai Mama tanada matsala Wallahi, mutum duk haƙurinshi sai ta ƙureshi."

"Kaje kaci abinci ka dena zama da yunwa."
Mamy ta umarceshi cikin son kauda zancen, kasancewar bata son tayi mgnar kishiyarta, dan wannan shi ke ɓata alaƙar zuciyar yaro da matar ubanshi.

Ƙarfe tara dai-dai Mama ta shiga parlour'n  Baba Malam,  tare da yin sallama can ƙasan maƙoshi, ta yadda shi baima jitaba.
A kan kujera ta sameshi zaune ya zubawa TV idanu yana kallon BBC News.
Kan dinning table ta kai dubanta, gani tayi  yanda ta ajiye abinci, yana nan ayanda yake, da alama babu wanda ya taɓa ko food flask ɗin bare akai ga ci,
juyowa tayi ta maida kallonta kan fuskarshi da ta ɓoye ɓacin ransa,
ta sani koda bazaici abinciba to tabbas zaisha tea,
dan haka  taku uku zuwa biyar ne yakaita gaban dinning area, 
cup ta É—auka sannan ta haÉ—a mishi tea kamar yadda ta saba,
a hankali tazo ta ajiye mishi cup ɗin a kan table ɗin dake gabanshi, wanda yawanci nan yake miƙe sawunshi idan yana zaune akan kujera.
danne ɓacin ranta tayi dan yanzu so take ta gwada kirsa tunda taga hayagagar bata kamashi,
gefenshi ta zauna tare da cewa.
"Ga tea É—inka nan nahaÉ—a ma kada yayi sanyi."
shiru yayi  baice ƙala ba, ganin yadda yayi kamar babu wani mahaluƙin dake kusa dashi, yasanya
cikin tsareshi da ido taƙira sunanshi.
"Malam!."
Baima juyo ya kalleta ba bare tayi zaton ko zai amsa mata,
saima kaɗa ƙafafunshi da ya farayi a hankali.
shi kuwa wani irin tafarfasa zuciyarsa keyi,
yadda tazo tayi ta mishi ihu da haushi a kanshi gaban yaranshi da uwar gidanshi, shine ke ƙara ɓata masa rai, sam bata sa hankali da nutsuwa cikin lamuranta.
Kusa dashi ta kuma matsowa tare da cewa.
"Malam magana nake so muyi da kai fa."
Bai bi ta kantaba bare ya saurareta saima ƙara volume ɗin TV da yayi.
Cikin takaicin abin tace.
"Ya kamata muyi magana ta fahimtar juna,
a bani matsayina da damata a matsayina na uwar yarinya,
ni nasan Zaleeha bata son wannan nakasasshen, ta tsaida gwaninta, harma ta bashi daman ya turo komai na aure, tunda dama iyayenshi kam sun zo kuma ka sansu ba baƙin fuska bane,
d'an manya ne gaba da bayansa."

Gum yayi mata tamkar dutse,
ita kuwa sai surutai takeyi uwa aku,
ganin an gama labaran ne ya sashi,
miƙewa tare da kashe TV sannan ya nufi bedroom ɗinsa,
da sauri tabi bayanshi tana Magana, bai kulata ba, haka ya shiga bathroom,
ruwa ya watsa sannan yayi al'wala kana ya fito.
A bakin gado ya sameta tana zaune,
shi kuwa shirin bacci yayi kana yazo ya tsaya gefenta, da  hannu ya nuna mata hanyar fita alamun ta fice mishi daga ɗaki,
fuska a tsuke tace.
"Muyi maganar tukun!."
Fuska ya kuma tsukewa wanda saida taji gabanta ya ɗan faɗi, yayinda zuciyarta kuwa ta buga da ƙarfi,
hanyar fita ya kuma nuna mata,
da sauri tace.
"Dan Allah, dan darajar ma'aiki kayi haƙuri ka buɗi baki muyi magana."
Ido ya rumtse dan ya rigada ta haÉ—ashi da Allah.
Itama sanin in dai ta haÉ—ashi da Allah zai saurareta ne ya sata yin hakan.
cikin kaushin murya da haÉ—e fuska zuciya na tafasa murya a zafafe yace.
"Kije ki kwashi kayan da kika watsar É—in ki maidasu É—akinki ki ajiyesu yadda kika samesu."
da sauri tace.
"Dare yayi fa."
A kausashe yace.
"Baza kuma su kwana a waje ba."
Cikin sanyin jiki tace.
"To bari in ƙira Habu yazo ya kwashesu."
A ƙufule yace.
"Waya fito dasu?."
Kai ta juya tare da cewa.
"Ni ce."
Cikin bada umarni yace.
"To kije ki maidasu kizo muyi maganar."
Bata da zaɓi dan ta san kaɗan kenan daga halinshi dole taje a daren ta kwashi kayan,
ta maidasu cikin É—akinta,
tana gamawa a gajiye ta koma ɗakin nashi,  a kwance ta sameshi cikin maida numfashi tace.
"Na maidasu. Ka tashi muyi maganar."
Kai ya jujjuya tare cikar haiba da isa da gidanshi yace.
"Maganar ai na gamata babu wani wanda zan aurawa ɗiyata Zaleeha sai Saifuddeen,  kuma babu wani mahaluƙin da ya isa  hanani sai ubangijin daya halicceni!."
Yana faÉ—in haka ya gyara kwanciyarshi tare da rufe ido alamun bacci zaiyi.

Cikin tsananin takaici haɗi da ƙunci tace.
"Ni kuwa Wallahi ƴata bazata auri gurgu kuma kurma ba, ɗiyata bazataje ta zama majinyaciya ina kallo da idona ba, sannan bazan taɓa bari takashe rayuwarta wajen kula da nakasasshe ƙaskantacce ba, Allah ya sauwaƙa ma, ni dai ajinina ban haifawa nakasashshe matar da zai aura ba ehe!!."
Tana gama faÉ—in haka ta juya ta fita a fusace.
Gyara kwanciya Baba Malam yayi tare da rufe idanunsa, sunayen Allah Kawai yake ambata acikin ransa.
***

Washe gari kuwa Zaleeha daga gidan hajja Inna ma'aikatarsu ta nufa, bayan ta gabatar da shirinta na mushaƙata kai tsaye gidansu kuma ta nufa.

A harabar gidan tayi kiciɓis  da ya Ahmad,
cikin shaƙuwarsu ta nufi inda yake, da alamun cewa shima yanzu shigowarsa cikin gidan.
hannunshi ta kamo tare da cewa.
"Ya Ahmad nayi kewarku kwana biyu bana nan ko kuyi cikiyata."
murmushi yayi tare da cewa.
"Muma munyi kewarki, kin san inata shirin tafiyarmu ne,
naso in wuce da Lubna amman Mamy tace wai in bar miki ita."
tsalle tayi cikin jin daÉ—i tace.
"Yessss! My mamy kai amman ko naji daÉ—i sosai!!."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Ato ai dama amare yan jin daÉ—ine."
Sam bata kawo komai a rantaba da jin furucinsa,
sai sakin hannunshi da tayi lokacin da sukazo dab da ƙofar Mama,  cikin alamun gajiya da kuma yunwa dake damunta tace.
"Yauwa Ya Ahmad bari inje inyi wanka sai inzo muyi hira,  ka cewa Aunty Lubna ta gasa min abin daɗi yunwa nakeji, please  ko roasted fish nema nasamu idan nazo."

"To." Kawai yace tare da juyawa yayi side É—in Mamy.

Ita kuwa Zaleeha da sallama ta shiga,
da sauri ta kutsa kanta cikin parlour'n,  saboda hango Mamanta na zaune fuskar nan a kumbure alamun tsananin fushi,
da sauri ta durƙusa agabanta cikin tsoro tace.
"Lafiya kuwa Mama? Meya sameki? baki da lfy ne?." Duk tayi mata tambayar cikin kulawa, irin wacce ke tsakanin Ƴa da Uwa.

Cikin tsananin takaici Mama ta watsa mata harara tare da cewa.
"Ae naji ke har dariya ma kike ko? yayinda ni kika barni ina nan baƙin ciki da ɓacin ranki zasu haɗu su kasheni!."

Cikin zaro ido haÉ—i da tsoro tace.

"Na shiga uku Mama me nayi miki?."

A hasale Mama tace.
" kikamin ko kikayiwa kanki."
Sai kuma ta miƙe tsaye tare da watsawa Zaleeha wani  irin mugun kallo.
Sannan tayi cikin bedroom ɗinta, wanda idan  ba doleba, sam  bata son shigarsa, saboda idan taga wannan kayan ji takeyi kamar ta faɗi ta mutu, tsabar baƙincikin dake cika zuciyarta.

Da sauri Zaleeha ta bita,
a gaban Maman  ta tsaya, cikin raunin murya tace.
"Mama kiyi haƙuri in na miki laifine ki gaya min Wallahi bazan sakeba!."

Azafafe ta nuna mata tarin akwatunan wanda ita sam bata gansuba sai yanzu cikin kakkausan murya tace.
"Kinyi asara Zaleeha, Wallahi kinyiwa kanki sakiyar da ba ruwa, ki rasa wanda zaki zaɓa duk cikin masoyanki sai wannan banzan nakasasshen da baya ji baya magana, uwa uba kuma baya tafiya, ki zaɓeshi matsayin miji har zaki bashi dama ya turo iyayenshi su kawo tarkacensu harda su sadaki,
wato kin maidani shasha naje inata haushi ashema ban saniba kece kika amince mishi sai É—azu Habu yake sanar min."
Mama fa bata tsagaita da masifaba bare tasan halin da Zaleeha ke ciki.
sai Zahira ne ta zaro ido da ƙarfi ganin yadda Zaleeha tasa hannu da tsananin ƙarfi ta kama kanta,
yayinda tuni kunnuwanta sun toshe tun lokacin da Mama tace mata an kawo sadakinta kuma wai ga kayan aurenta a gabanta,
sannan wai da yardarta uwa uba kuma wai da wancan ginannen taɓon ne da Allah ya ƙawatashi da kyan sura,
daga nan bata kuma jin zancen Mama ba, sai rumtse idanunta da tayi tare da  cilla wani irin gigitaccen ƙara mai tsananin ƙarfi, haɗe  da cewa.
"Ƙarya ne banice na turo shiba, bana sonshi! bazanyi aureba Wallahi, bazan zauna da kowaba sai wanda ya taimakeni!!." 
Sai ta kuma buɗe idanunta, wanda sukayi jazir ta kalli tarin akwatunan, wani irin gigitaccen ƙara ta saki wanda yasa,
Ahmad, Habu,Aunty Lubna da suka nufo parlour'n  maman tun ihunta da sukaji na  forko  ya sasu shigowa a guje,
suna shiga ita kuwa zaliha ta yanki jiki ta faÉ—i sumemmiya.

Da sauri Ahmad ya tarota ta faÉ—a jikinshi,
cikin rawan jiki murya a hargitse yake É—an jijjigata tare da marin kumatunta yana faÉ—in.
"Zaleeha!  Zaleeha!! Ki tashi Zaleehaaa!!!."
Sai ya kuma kalli Zahira daketa kuka tana cewa.
"Shike nan ta mutu, tace muku bata son auren ba wanda take so ku barta ta jira wanda takeso anƙi gashi yanzu baƙin ciki zai kasheta.
Mama kuwa da sauri ta juya ta nufi falon Baba malam tana shiga tasa kuka tare da cewa.
"Shike nan baƙin ciki zai kashe min ƴata,
in ta mutu ai kowa ya huta sai a kaiwa shashashan musakin gawanta."

Shiru Baba malam yayi sai murmushin da yakeyi, Mamy kuwa da sauri ta miƙe zata nufi side ɗin Maman,
dan da fari da suka jiyo ihun Zaleeha sunyi zaton ko uwarce ke dukanta, shiyasa data yunƙura zata je Baba malam ya dakatar da ita.

A can É—akin Mama kuwa a kiÉ—ime Lubna ke cewa Ahmad.
"Hubby a sume take fa,  ko dai da gaske al'jani ne ya taima keta shine yau zasu baiyana kansu? Hubby mu kaita wurin Baba Malam!." Tafaɗi maganan cikin tsananin ruɗewa.

Yunƙurawa  Ahmad yayi da ita a jikinshi,  fita yayi da matsanancin sauri ya nufi parlour'n Baba Malam,
a bakin ƙofa sukayi karo da Mamy.
Cikin tsoro da firgitan ganin Zaleeha kamar gawa Mamy tace.
"Malam da gaske Zaleeha ba lfy."
Shi kuwa Ahmad a gaban mahaifin nasu ya direta tare da cewa.
"Baba malam al'janine fa a jikin Zaleeha da gaske danfa kawai taji batun auren ne yasa ta suma."
Habu ne yaja wani dogon tsaki tare da cewa.
"Ya Ahmad meyasa kake yarda wai Zaleeha iska gareta?."
Cikin tsawa yace da Habu.
"To in ban yarda tanada iskaba meya sumar da ita?
please Baba malam ayi mata ruƙiyya ko al'janin zaiyi magana."

Cikin takaici Habu ya juya gaban fridge ɗin dake gefenshi, buɗewa yayi tare da ɗaukan goran bottle water  mai ɗan karen sanyi,
kana ya juyo marfin gorar ya murÉ—a kana ya ziraro da bakin gorar dai-dai saitin fuskar Zaleeha ya fara tsula mata ruwan sanyin.
Wani irin wawan ajiyan zuciya taja, me ɗauke da azaban ƙarfi kana ta fizgo numfashinta da wani zazzafan kuka,
cikin kuka mai cin rai ƙuna da kuma tsananin tsoro take cewa.
"Bana sonshi Ya Ahmad ka gayawa Baba malam wallahi bana sonshi na tsaneshi!."
Sai ta kuma kamo hannun Ya Ahmad É—inta da tuni ya fara zubda hawaye, cikin kuka taci gaba da cewa.
"Ya Ahmad ka gayawa Baba malam mana,
ka faÉ—a mishi cewa gurgu nefa haka kuma kurma ne, kace mishi bana sonshi na tsaneshi,
wallahi in aka aura min shi zan mutu wlh ya Ahmad mutuwa zanyi!!!." Taƙare maganar cikin wani irin kukan fitar hayyaci.

Habu ne ya watsa mata wani zazzafan harara tare da cewa.
"To ki mutu mana! In kin mutun sai me? Ko kina zaton mutuwarki zaisa muma mu mutu ne?."
Faɗawa  jikin Aunty Lubna dake raɓe agefe  tana zubda hawaye tayi, cikin kuka da raunin murya tace.
"Wayyo Allah na Aunty Lubna ki taimaka min ki faÉ—a musu inada wanda nake so, kice musu wlh bana son musakin can."
Cikin rauni Ahmad ya kalleta murya  a tausashe yace.
"To meyasa kika ce mishi kin amince dashi ya turo iyayenshi tunda kin san bakya sonshi?."
cikin kiÉ—ima da gigita tace.
"Wallahi ban faɗaba wlh ƙarya yake min, to shida kurmane ta inama zaiji abinda zance mishi?."
cikin hatsala Habu yace.
"Ba text messages kika tura mishi ba, da wayarki."
Miƙewa tayi a hargitse ta kalli Mahaifinsu da ya zuba musu ido, yana murmushin ganin ƙuruciyar yaran nashi, ba abinda ke sashi murmushi kamar yadda Ahmad yake taya Zaleeha kuka kamar yaro,
yana jin daÉ—in zafin Habu dan yasan Habu Baban ya Aminu ya gado yayan Baba malam kenan,
cikin kuka Zaleeha tace.
"Wallahi ƙarya yake min ni bani da number shi ma."
Mama ce tayi kaffa tare da jan dogon tsuka.
Habu kuwa falon Mama ya koma,
jim kaɗan sai gashi da wayar Zaleeha riƙe a hannunshi,
cikin takaici ya cire wayar a key dan yasan komai na wayar,  hakan kuma tsarinshine dan bincikar woyoyin ƙannenshi yasa su duk yasan komai na wayarsu.
kai tsaye inbox nata ya shiga ai kuwa text biyar ya duba, ana shida sai ga text É—in gama number shi da Saifuddeen yayi seven da My happiness.
Cikin zafin rai ya nuna mata wayar tare da cewa.
"Meye wannan?".
Ido ta zaro gaba ɗaya, ganin abinda ke rubuce da kuma haƙiƙa ita ta rubuta, kuma ta turawa number da aka sawa suna da my happiness, sai kawai ta miƙe ta koma can gefe nesa da mahaifin nasu ta fara buga tsalle tare da yarfa hannu tare da kurma ihu kana tana cewa.
"Sharri! Sharri!! Sharri!!! Sharrine yayi min wallahi ƙarya ne ni bana sonshi!!!."

Ganin yanda takeyifa yasa Baba malam yin wani murmushi mai kama da dariya.
Saura kuma gaba É—aya ido suka zuba mata.
Habu kuwa belt ɗin ƙugunshi ya zaro tare da yin kanta.
ai fa tana ganin haka ta juya a guje tayi cikin gidan, shi kuma ya mara mata baya a guje,
radadada kake jinsu a guje.
ganin yadda Habu ya bita yasa Ahmad binsu da gudu hakama Aunty Lubna da Zahira.

Zaleeha kuwa gudu take da iya ƙarfinta dan tasan Habu ba mutunci ne dashi ba. In ya kama duka kamar mara imani.
Kai tsaye ɗakinta ta shiga cikin sa'a ta samu ta maida ƙofar garam ta rufe,
tun kafin ya iso,
ganin haka yayi kwaffa ya juya tare da cewa.
"Yar iska kawai da ki tsaya mana."
Ita kuwa a cikin ɗakin wani irin fitininan nen kuka tasa da iya ƙarfinta, tana kuka da surutai cewa.
Ita dai bata sonshi ta tsaneshi zata mutu in an aura mata shi.
Ahmad kuwa da Lubna rarrashinta sukayi tayi da bata baki amman ina.
ranar haka ta kwana a rufe tana kuka da al'washin ciwa Saifuddeen zarafi.

Mama kuwa sosai taji daÉ—in abinda Zaleeha tayi,
ta kuma yi niyar yaƙi da wannan auren.

Ƙarfe takwas dai-dai na safiyar ranar asabar Zaleeha fito cikin d'akinta inanun ta a kumbure tayi ja alamu tayi kukan  mai yawa.
gefen Mamanta ta zauna cikin sanyi tace.
"Ina kwana Mama".
"Lfy."
ta bata amsa a tak'aice.
kai ta d'an sunkuyar ida nunta cike da hawaye tace.
"Mama wlh k'arya yake min sharri ne, ni bance ina sonshi ba." kai Mama ta gyad'a mata cikin alamun gamsuwa tace.
"To yanzu ya zakiyi?."
cikin k'arifin hali tace.
"Zan yi mgnin abun in sha Allah shida kanshi zai dawo yace ya fasa."
Cikin jin dad'in Mama tace.
"Ke dai ki kafa ki tsare cewa bakya sonshi ni kuwa zan san abinda zanyi a kai."
To tace kana ta kira Zahira tare da cewa.
"Je parlour Baba Malam ki d'auko min wayata".
Juyawa tayi ta nufi bedroom d'in Mama tare da cewa.
"Gashi nan na d'aukoshi tun jiyan ai."
Amsar wayar tayi kana ta koma d'aakinta.
Ita kuwa Mama murmushin jin k'arfin guiwa tayi tare da cewa.
"Bazaki auri gurgu ba kam ko kina sonshi zan hana kuma wlh bazan bari kiyababanki boyayya kan arennamba dole zanyiwa boka bayanin yadda nake son yasa ki bijirewa wannaɓin da BAban naki ya miki, don ko sama zata had'e da k'asa zaki auri Abdussalam dan shine dai-dai dake."
Tana kaiwa nan ta kira wayar Abdussalam yana d'agawa suka gaisa kana tace mishi,
ya had'o komi da komai na aure ya turo iyayenshi Zaleeha ta yarda dashi.

Jin haka yasa Abdussalam jin k'arfin guiwa nanfa yaci gaba da shirya lefenshi dai-dai da matsayinshi.

Ita kuwa Zaleeha konciya tayi kan gadonta sannan ta fara rubuta text kamar haka.

```Kai baka cancanci inyi makasa sallama ba, domin ita sallama ta masu amincine ba mak'aryata azzalumai irinka ba. nace maka bana sonka na tsaneka bazan soka ba har abadan,
dan haka kayi maza ka turo wad'anda ka aiko suka kawo wannan tarkacen suyi maza su zo su kwashe gaiyar dukiyarka```
murmushi tayi lokacin da ta tura text d'in a ganinta ta k'unsa mishi bak'ak'en maganganu.

Saifuddeen kuwa yana zaune bisa kujerar wheelchair d'inshi Amman a dinning table,
Ummi na had'a mishi tea yayinda yake cin soyayyan doya da kwai,
jin wayarshi dake cikin al'jihunshi ta bashi wani alamun sak'o ya shigo kamar bazai duba ba,
sai ya kuma zaro wayar ganin number tane ya sashi yin murmushin mugunta dan yasan,
Kwanan zancen.
ganin yanata murmushi Ummi yin murmushi dan farin cikinsa shine nata.
Raliya kuwa da Hayatuddeen suma murmushin suke tayasu.

Bai bud'e text d'inba saida ya koma side d'inshi sannan ya bud'e ganin abinda ta rubuta ne yasashi yin maganar zuci.
"Hmmmm wasa farin girki, yarinya kinga ta kanki." a zahiri kuwa yi yayi kamar baiga text d'inta ba bare ya bata amsa.

Ita kuwa ganin shiru-shuru bai maida mata martini bane yasa da azahar ta sake tura mishi wani text d'in wanda yafi na safe zafi.

Shiru ba amsa har dare, ganin haka ta kuma tura mishi wani text d'in.

Har kusan k'arfe d'ayan dare tana jiran amsa amman cib ba amsa.

Washe gari haka da asuban fari ta kuma tura mishi wani zazzafan text ,
Still ba amsa.

Abu fa ya isha Zaleeha yau kusan kwana uku kenan ba amsa,
kuma bata fasa tura mishi bak'ak'en maganganu ba.

A gidan kuwa babu wanda ya sake mgnar auren Baba malam kuwa duk nacin Mama bata jin ta bakinsa.

Habu kuwa shida Zaleeha hararace a tsakaninsu.

Zahira kuwa munafuka yar koren Mama ce.

Aunty Lubna kuwa ita ke hillace Zaleeha,
har take mantar da ita batun wani aure.

Ita kam Zaleeha ta fara sakewa dan ganin baya maida mata amsa sai take zaton yayi mubaya'a ne,
koda wasa bata shiga d'akin Mama dan bata son ganin jerin akwatunan.

Ya Ahmad yanata shirin gobe zai tafi.

Suna cikin hira ya kalli Zaleeha da ta d'an sake a hankali yace.
"Ke Zaleeha kayan d'aki dana kitchen na wanne k'asane kikafi so kikega sunada ink'anci.
cikin rashin fahimtar mgnar tashi tace.
Gada je dai da kujeru Dubai komansu nada ink'anci da tsari.
Kayan kitchen kuwa na Chaina sunfi kyau." murmushi yayi tare da salonta yadda gaba d'aya hankalin ta na kan wak'ar da takeji a wayar Lubna, har tana cewa.
"Yauwa Aunty Lubna tura min wannan wak'ar mana ina sonta tamin dad'i."
To Lubna tace tare da yiwa mijinta signal alamun sam fa Zaleeha bata gane komai ba.

Mama kuwa a sashinta ta kira yayarta Ruda ta shaida mata abinda ke faruwa,
Jin haka yasa Ruda cewa cikin satin nan zata shigo gombe.

Maryam kuwa duk abinda akeyi bata saniba.
shiyasa har ta kira Anty Aisha k'anwar mama ta shaida mata an kawo lefen Zaleeha biki kuma 27 next month.
Itama tace zata zo ganin lefe.

Saifuddeen kuwa Ishaq kadai ya gayawa abinda Zaleeha ke rubuto mishi nan Ishaq yace mishi ya barta sai tazo har inda suke,
dan yasan zata zo.

Ya  Ahmad ya tafi harkan aikinsa, tunima ya bar k'asar.
in da ya bud'a bakin aljihunshi yake kashewa Zaleeha mahaukatan kud'ad'e na ban mmki wurin saya mata dukkan abin buk'atan amare.

Tafiya dai ta mik'a a lissafin yau saura mako d'aya ne auren.
tuni shirye-shirye sun kankama ta gefen ango da amarya.

Da hantsi misalin k'arfe 11:15 Am Zaleeha ta shigo d'akin Mama wanda lokacin kenan ta fito daga d'akinta da shirin zata wuce wurin aikita, jin
muryar Yayarta Maryam da Anty Aisha da Ruda yasa ta nufi d'akin a hankali ta shiga bakinta d'auke da sallama.
sai kuma tayi turus a baki k'ofar ta tanya cikin tsananin kad'uwa da firgita,
ido ta zubawa Maryam dake tsakiyar akwatunan ta bubbud'esu gaba d'aya tana nunawa Any Aisha kayan,
Yayinda Mama kuwa da yayarta Ruda suke kan gado fuskokin nan nasu tamkar suyi ruwan jini kuma tuni sun barbaɗe ƙofar falon Mama da maganin da Ruda ta kawo wanda aka basu tabbacin in dai Zaleeha ta tsallakashi tofa bazata lamunci zaɓin mahaifin nataba zata tashi hankalin kowa har sai an janye batun auren.
cikin sanyin murya Anty Aisha take cewa.
"Allah ya sanya al'khairi yasa gidan zamanta kenan iya rai da mutuwa."
Maryam ce tace Amin Amin.
sai kuma suka juyo suka kalli Ruda dake cewa.
"Tir da addu'arki Aisha bakinki ya sari guntun kashi,
kifa kalli wannan zuk'ek'iyar budurwa ki fasalta zamanta da gurgu kuma kurma musaki mara amfani kice Allah yasa gidan zaman tane.
Ke kuma Maryam da yake baki da hankalin da kishin yar uwarki harda wani cewa Amin."
ita kam Zaleeha tamkar an dasa tane a wurin ta kasa tantance abinda kunnuwanta ke jiye mata daga bakin Maryam dake cewa.
"Addu'a ita ta dace da Zaleeha tunda dai wannan abun yin Allah ne,
ko ana so ko ba'a so in Allah yayi ita matar Saifuddeen ne dole taje gidanshi,
kuma ke Mama kin san halin Baba malam me amfanin bad'i babu rai,
yak'in da babu nasara ai gwara yin mubaya'a du du dufa auren nan saura sati d'aya ne rak."
Da sauri Zaleeha tasa tafin hannunta ta dafe k'ahon zuciyarta dake gab da tarwatsewa,
idanunta ta rumtse da azabar k'arfi kanta ta fara jujjuyawa tare da zamewa ta durk'usa gaban Mamansu murya a hargitse tace.
"Bana sonshi, bazan zauna da shiba, wlh mutuwa zanyi in aka had'ani dashi please Mama kiyi wani abu a kai."
Maryam ce ta d'an kalleta a tausashe dan tasan irin abinda Zaleeha keji a ranta tunda itama a dole aka had'ata da Ya Aminu amman gashi yanzu da tayi biyayya tabi umarnin iyayenta tana ganin ribar haka,
duk da zafin zuciya irin na ya Aminu zama yake kamar bawa a gareta,
baya son duk wani abinda zai sata zubda hawaye.
shiyasa a hankali tace.
"Zaleeha kiji tsoron Allah kiyi biyayya ga mahaifinmu zakiga ribar hakan kada ki bari rud'in duniya ya Kaiki ya baroki.
Ku dena yakice Saifuddeen dan nakasarsa dan babu wanda yasan k'arshensa, kuma in baka mutuba to ba'a k'are maka halitta ba,
shimafa bada larurarnan aka haifeshi ba, kaso 95 cikin 100 ba haihuwarsu ake da nakasaba a duniya suke samu. Kaso 5 ne na cikin 100 ake haifarsu da nakasa,
because muma bamu da yak'inin a haka zamu k'are rayuwarmu."
Cikin tsawa da masifa Mama tace.
"Rufe min baki hegiya mara zuciya,
mai mugun fata mu nan in sha Allah lfy lau zamu k'are rayuwarmu.
Kuma wlh wlh muddin ina raye Zaleeha bazata zauna da wannan gurgunba.
Dan ke kinada macecciyar zuciya sun tankwaraki kin zauna a dole to banda Zaleeha."
Cikin sanyi Maryam tace.
"Kiyi hak'uri Mama ki gafarceni in furucina ya sosa miki zuciya."
ita kuwa Zaleeha mik'ewa tayi ganin sunk'i su sarara bare su saurareta,
ficewa tayi daga gidan a guje.

A Cikin gidan kuwa, Anty Aisha ce ta kalli yayun nata cikin kafiya da fad'in gsky tacewa Mama.
"Da hankalinki da tunaninki kike biyewa zugar wacce kin san batayi imani da Allah da manzonsa ba, bare ta yarda da k'addara mai kyau ko sab'aninta."
A zafafe Ruda tace.
"Ke Rebeka ni kike gayawa haka?."
cikin tsuke fuska da tsawa tace.
"An gaya mikin! K'arya nayi ne, imanin gareki tunda har yanzu baki samu tsarkin zuciyaba, kina kafura,
mara lissafi zata zauna tana bin zugarki,
lallai ke yar uwata ce kuma yayata Amman baki da hurimin kirana da Rebeka call me Aisha in bazaki iya ki bari."
A zafafe tace.
"don't call me Rebeka again."
Sai kuma ta juya ta kalli Maryam tace.
"Maryam tashi mu tafi, ni dai ina bayan Baba Malam daga yau kuma zamu fara shirye-shiryen auren nan."
A hankali Maryam ta maida akwatunan duk wurin zamansu,
sannan ta mik'e tabi bayan Anty Shatu kamar yadda suke kiranta kenan...

Mama kuwa da kafurar Yayarta Ruda,
nan sukaci gaba da tubka da warwara,
suna tubke yadda auren Zaleeha da Abdussalam, kana suna warware auren Saifuddeen.

Ita kuwa Zaleeha tana fita kai tsaye (Jonapwd)  ta nufa tuk'in takeyi tamkar wacce zata bar garin.
tana shiga harabar wurin tayi parking, cikin sauri ta fito gaba d'aya ida nunta dishi-dishi suke mata,
kai tsaye office d'in Ishaq ta kutsa kanta sam bata iya amsawa mutanen nata gaisuwar da suke mata.
shi kuwa Ishaq tun tana babban parlour yajiyo mgnar Sani na mata sannu da zuwa so koda aka turo k'ofar office nashi aka shiga yasan itane.
Tana ganinshi kawai sai rauni ya rufe masifarta dan iya tsawon zamanta da ishaq a matsayin yayanta Ahmad take kallonshi ishaq yanada mutunci a ida nunta gashi last time ta surfa musu rashin É—a'a kuma daga nan yake fushi da ita,
a hankali taja kujerar dake fuskantar wacce yake zaune a kai ta zauna.
sunkuyowa tayi ta kifa kanta bisa glass table dake tsakiyarsu kawai sai ta saki wani irin mawuyacin kuka mai cike da rauni da tarin k'uncin rayuwa.
cikin tsananin mmki Ishaq ya zubawa saitin inda yakejin kukan idanu tamkar yana ganinta.
sai kuma yayi shiru kamar baya wurin yana jin sautin kukanta na ratsa kunnuwanshi.
Kusan tsawon 10 minutes tana kuka,
bai kulata ba, ita kuma bata bariba,
har 20 minutes har ta zarta rabin awa tana kukan bil hak'k'i da gsky.
daga jin kukan kasan daga cikin zuciyarta yake fitowa kukane mai tattare da k'una da tsoro,
sosai Ishaq ya fara jin tausayinta na kamashi ai ko ba komai ita macece kuma mai rauni.
cikin sanyin sauti yace.
"Ya isa, ya isa haka Zaleeha kada ki cutar da kanki."
jin haka sai kukanta ya k'aru cikin kukan murya a raunace tace.
"Malam Ishaq bana sonshi, wlh bana sonshi, na tsaneshi, inada wanda nakeso wanda ya bada ranshi da lfyarshi domin kare mutun cina pleaseeee Ya Ishaq kace mishi ya janye batun aure a tsaka ninmu, wlh muddin akayi auren nan cikin mu biyu dole d'aya zai rasu."
Sosai ya nitsu yana jin kala manta sai ya kuma ji alamun tazo tana durk'ushe a gabanshi a hankali tace.
"Dan Allah Ya Ishaq ka zame min Garkuwa na mana a karo d'aya dai a rayuwa ta,
dana rok'eka abu dan Allah dan annabi kaji tausayi na mana ka rabani dashi kar in rasa raina please ya Ishaq kada ka bari ayi min auren dole."
Sai ta kuma kife kanta bisa d'aya kujerar taci gaba da kuka.
Sosai raunin ishaq ya halarto kan zuciyarshi,
me zai hana ya taimaketa, to amman bari yaji meyasa bata son Saifuddeen, a hankali yace.
"To waye kike son?." murya a raunane tace.
"Ban sanshi ba?."
fuska cike da mmki yace.
"Ina yake to me sunanshi?."
A hankali tace.
"Duk ban saniba sau d'aya muka tab'a had'uwa shiyasa a gidanmu ake cewa wai ba mutun bane al'janine."
Da sauri yace.
"Yes al'janine mana nima haka zance, tunda shi gaibune."
kuka ta kuma sakewa, sai kuwa ta d'ago kanta jin yana cewa.
"To meyasa baki son Saifuddeen?. "
Rashin sani yafi dare duhu shiyasa Zaleeha tacewa Ishaq.
"Nakasasshe nefa shi gurgune kurma ne ta yaya zan aureshi da lfyata gurgunefa ananfa kuke cemin irinsu basa aure."
da sauri ta mik'e tsaye jiki na rawa ta koma gefe dan jin yadda ishaq ya buga table dake gabanshi tare da buga mata tsawa.
"To sai me!? Shi nakasasshe ba mutun bane!? Ko shi nakasasshe baida ikon auran lafiyayyiyar mace!? To wlh Zaleeha kinyi ganganci wannan furucin naki, ni babu taimakonki da zanyi in sha Allah sai Saifuddeen ya aureki ko zaki mutu ne.
Get out of my office!."
Ya k'areshe mgnar da k'arfi tare da mik'ewa tsaye.
wanda saida mutanen cikin babban parlour nan suka jiyosu.
Ita kuwa Zaleeha cikin tafasan zuciya ta juya ta fita dan yanayinshi ya bata tsoro.

Daga nan gidansu Rashida ta nufa,
nan ta tasa Rashida a gaba tana kuka.
Murmushi Rashida tayi tare da cewa.
"Hmmmm Zaleeha kenan to ni mai zance miki,
kin dai san bazan baki goyon bayan ki bijirewa iyayeki ba, in dai k'awancenmu na gsky ne,
sannan da kiketa mai-maita shi nakasasshe ne ke kinada tabbacin a haka zaki k'arene.
Zaleeha kifa farga ki dawo nitsuwarki kin gani ko wlh wlh dani Saifuddeen yace yana so na rantse miki da zatin Allah da hannu bibbiyu zan amshi soyayyarsa,
Zaleeha inafa gaya miki kada kiyiwa kanki sakiyar da babu ruwa, kibi umarnin iyayemu ki samu rabauta duniya da k'iyama in zaki farga ki farga Ki daina wanna yarintar."
Cikin tsananin takaici ta ture Rashida da tasa hannunta tana share mata hawayenta a hatsale tace.
"Sai yau na gane asalinki Rashida, ke farin cikima kikeyi da wannan abun har dariya kikeyi ko?."
Da sauri Rashida tace.
"Tabbas farin ciki nakeyi abinda baki saniba,
ko jiya muna tare da abokan ango, d'azuma na dawo daga can anguwar tasu federal law cos, layin Sabana hospital, wurin shagon Bash wani tela ne.
Can suka kai kayayyakin d'inkinmu na biki naki da namu na k'awaye kuma komai yayi kyau,
anjima kuma zasu zo batun shagulgulan da za'ayi."
Cikin mmki da tarin takaici Zaleeha tace.
"Shegiya yar iska a ina kika sansu?."
Dariya Rashida tayi tare da cewa.
"A wayar wani É—an kawuna Jabeer naga hoton Saifuddeen sai yake cemin abokinshi,
harma an kai lefe.
to nan nake ce mishi ai mune k'awayen amarya,
kinga daga nan komai yazo da sauk'i mu yanzu shirin bikin mukeyi babu kama hannun yaro.
nice nan na kaiwa telan kayanki yadda zai d'inka komai dai-dai dake."
bazata fa juri jin tatsuniyar Rashida da É—an kawunta Jabeer da sauran abokan Saifuddeen ba don haka ta zari car key d'inta ta bar gidan.

Ita ko Rashida murmushi tayi tare da cewa.
"Ayyah Zaleeha zuk'ar zuciya da rud'in shaid'an na d'awainiya da ke sun hanaki ganin nagartan Saifuddeen.
Fatana Allah ya sanya al'khairi a aurenku."

Ishaq kuwa Zaleeha na fita ya biyo bayanta ranshi a matuk'ar b'ace,
parking lot ya nufa ganin haka Ado drivarnshi ya biyu bayanshi bud'e mishi marfin motar yayi.
Bayan ya shiga ya maida marfin ya rufe,
sannan ya shiga yaja motar suka fita,
suna hawa kan titin da kyau Ado ya juyo ya kalli uban gidan nashi cikin girmamawa yace.
"Ina zamu je?."
A takaice yace.
"Gidan Saufuddeen."

A parlour'n Ummi ya samu Saifuddeen shi kad'ai,
kamar babu kowa a gidan.
bayan sun gaisa ne da salon yadda suke mgna,
Ishaq ya rubutawa Saifuddeen duk yadda sukayi da Zaleeha yanzu,
yana gama karanta text d'in ya gyara zamanshi kana ya fuskanci abokin nashi cikin lumshe ido yayi wani tattausan murmushi tare da rubuta mishi.
"Cool down my friend.
kada ka damu da duk abinda zatayi."
cikin jin haushi Ishaq fuskaci abokin nashi da kyau kana yace.
"Saifuddeen ka hak'ura da Zaleeha mana tunda ba ita kad'ai bace d'iya mace,
ita mafa macece kamar kowa ya za'ayi wasu na binka kai kana binta tana ci maka zarafi, na gaji Ka rabu da yarinyar nan,
yarinyar da ikirari zata mutu in ka aureta kayi zuciya ka barta mana."
A hankali Ummi ta zame ta zauna a kujerar da Saifuddeen ya baiwa baya, ishaq kuma ba ganinta zaiba.
Gaba d'aya jikinta rawa yakeyi.
Tsoronto d'aya kada k'iyayya tasa Zaleeha ta cutar mata da d'anta, ya zatayi in wani abu ya kuma samun Saifuddeen d'inta d'a mafi soyuwa a zuciyarta d'an da yake k'arar da lokutanshi wurin sama mata farin ciki da kare martabarsu. tuni hawaye na zirya a kumatunta dan tana tausayawa zuciyar d'an nata da Allah ya jarbaceshi da son matar da bata sonshi.

Shi kuwa Saifuddeen kanshi ya jujjuya kana ya fara rubutawa ishaq mgna kamar haka.
"Uhmmm Ishaq ai duk cikekken masoyi zai jure karan tsana.
Zai jure kai kawo da zirga-zirga ako ina.
Kuma bazai nufi masoyinshi da hatsala ba.
Kuma ai ba'a son fushi a so sai dai hak'uri da juriya
domin yin fushi a so alamun rashin nasara ne, in sha Allah
dole ne fa sai Zaleeha ta shigo gidane dolen-dolenta sai taga aikin ginennen tab'on nan da tace sai na shayar da ita ruwan mmki, barni da ita zata gane kurenta!."
cikin mmki Ummi ta zuba musu ido ganin sun tafa kuma ishaq ya saki wani irin shak'iyin dariya.
"Saifuddeen kenan ya iya sarrafa harshe gashi daga fushi yasa ishaq dariya ko meye ya rubuta mishi sai Allah."
Ummi Ke fad'i a ranta lokacin data mik'e ta nufi bedroom nata dan bata son Saifuddeen ya gane taji zancensu.

Ita kuwa Zaleeha daga gidansu Rashida  gidan Hajja inna nufa,
tana shiga kawai ta tasa hajja inna a gaba ta bud'e wani sabon shafin kuka.
Zakariyya ne dake gugun kayanshi dana Ziyada ya ajiye dutsen gugan tare da cewa.
"To yau kuma me aka miki?."
cikin kuka take cewa hajja inna.
"Wallahi bana sonshi dan Allah ki cewa Baba malam yayi hak'uri kada ya min auren dole."
shiru tayi jin hajja Inna ta ja wani dogon tsaki,
kana ta b'alli tsallin goro ta afa a bakinta tare da taunashi,
kai ta karkace tare da cewa.
"To me ruwana a ciki, aure ne dai dole fa sai an aurar dake,
na gaji da zamanki a gidan d'ana."
Dariya sosai Zakariyya da Ziyada keyi sabida abin na hajja Inna ba mutunci.
suna cikin dariyar suka jiyo muryar Hayatuddeen da sauri Zakariyya ya tarbeshi cikin murna suka ruggume juna irin yar ruggumarnan ta gefe.
kana suka zauna bisa 2 sitter.
Bayan sun gaisa da Hajja Inna ne Ziyada ta gaida Hayatuddeen cikin mmki Hayatuddeen yake tambayar meyasa Zaleeha kuka,
Zakariyya ne yayi dariya tare da cewa.
"Wai kuka take dan za'a mata aure."
Dariyar shak'iyanci sukayi mata cikin dariyar Hayatuddeen yace.
"Ato yarinya da kin san kina tsoron auren mai yasa zakisa gaye ya turo iyayenshi."
Ziyada ce ta d'an kalleshi cikin yanayin d'an sabonta dashi tace.
"Ya Hayatuddeen ai bata son mijin ne shiyasa take kuka auren dole za'ayi mata."
da sauri ya matso kusa da Zaleeha wacce keta kuka hajja Inna kuwa nata aikin auna mata harara, cikin sanyi yace.
"Allah sarki Adda Zalee gsky ba'ayi miki adalciba a dai wannan zamanin mace kekyawa big girl kamarki ace an miki auren dole,
gsky dole kiyi kuka."
jin haka yasa Zaleeha fuskantarshi cikin kukan tace.
"Kuma ina da wanda nakeso sannan su had'ani da wani can banza ginennen tab'o."
kai ya jinjina mata tare da cewa.
"To meyasa bazakuyi mgna ta fahimtar junaba keda shi,
ki gaya mishi kinada wanda kikeso, kice mishi koda ya aureki bazai ji dad'in zama da keba,
in ya amince ya hak'ura shine nan kin huta in ya kafe ya nace kuma kiyi hak'uri kibi umarnin iyayenki."
Cikin kuka tace.
"Na tsaneshi bana sonshi ta yaya zan auri nakasasshe alhalin da lfyta."
shiru tayi ganin yadda a take fuskar Hayatuddeen ta canza launi da yanayi cikin had'e girar sama da k'asa mik'ewa yayi ya matsa gefenta tare da cewa.
"Zancen banza kenan, ashema baki da hujja, shi nakasasshe ba halittar Allah bane, ko a zatonki Nakasa kasawa ce,
aikin banza d'an adam da bai san k'arshenshiba yace yana kyaran larurar wani."
Gaba d'aya ran Hayatuddeen ya b'aci sosai sai yake tuno wata k'ilfa wata ran ayiwa Hamma Saifuddeen d'inshi irin wannan cin zarafin, haka kawai kalamanta sukayi masifar tayar mishi da hankali,
Hajja Inna ce tayi dariya tare da cewa.
"Ato ai duk mai bin bayan Zaleeha zai shak'i takaici, yo wani nakasasshen ma ai yafi mai cikar halitta haiba."
Ita kuwa Zaleeha cikin kuka tace.
"Bazaku gane bane. Gurgu nefa akan wheelchair yake rayuwa, kuma kurmane bayaji baya mgna."
Dam-dam zuciyar Hayatuddeen ya bada wasu tagwayen tarnaki mai cike da fargaba cikin zargin kai anya kuwa wannan bada Hammanshi take ba, cikin tsananin fargaba baki na rawa yace.
"Uhmmm me sunan shi ne!?."
cikin tarin tsanar tsuna taja wani dogon tsaki tare da mik'ewa kana tace.
"Wai Saifuddeen n!!!."
da sauri Zakariyya ya mik'e tsaye tare da cewa.
"Hamma Saifuddeen.
Shi kuwa Hayatuddeen cikin k'arfi ya fizgo hannunta tare da zaro idanunshi da sukayi jazir tuni hawaye na shatata a kumatunshi har kan gemunshi cikin rawan murya yace.
"K'arya ne wallahi Hamma na ba nakasasshe bane, domin nakasarsa bata zame mishi kasawa ba,
Ke da kike zagin nakasarsa kinada tabbacin naki lafiyar ne, da har kike inkarin ke da lafiyarki, to wlh yanzu kika fara kuka ko zaki mutu sai kin zama matar kurma kuma gurgun nan,
D'an uwane shine jigon rayuwar ahlinmu."
Sai kuma ya sake mata hannu ya koma ya zauna, Zakariyya ma tuni hawaye yake zubdawa, dan sai yanzu ya gane ashe Hamma Saifuddeen ne wanda yayarshi Zaleeha keta ƙi.
hakama Ziyada hawaye take zubdawa,
Hajja Inna kuwa cikin mmki tace.
"Hayatu, ashe ma Saifuddeen kyakkyawa ne ta samu har take rigima.
Wlh ni ban saniba."
Cikin zubda kwalla shima Hayatuddeen yace.
"Wlh Hajja Inna nima sai yanzu na gane data kira sunanshi da yanayin nakasarsa kuma,
na tuna ance min sunan matar da aka bashi Zaleeha ne."
ita kam Zaleeha juyawa tayi ta fita jin ƙaninta Zakariyya na cewa.
"Wlh nima ban san akan Hamma Saifuddeen bane take wannan haukan da ko inda take bazanma kallaba."

Hajja Inna ce ta katsesu da cewa.
"Ai kuwa ko mutuwa zatayi sai ta aureshi."
Sai ta kuma kalli Hayatuddeen cikin rarrashi tace.
"Kayi haƙuri kaji ko Hayatu, dan Allah kada ka gayawa Umminku da yayunka wannan batun in sha Allah Zaleeha zata tanƙwaru."
Kai ya gyaÉ—a mata alamar to,
sai ya kuma Kalli Zakariyya tare da cewa.
"Dama nazo nefa muje gidansu Imran muyi batun dinner ɗin da za'ayi a bikin ne, ina son mu tsara fita ta musamman a wurin," cikin bada ƙarfin guiwa Zakariyya yace.
"To muje, danko abu namune maganin a kwaɓemu."

Daga nan suka tafi gidansu Imran ƙanin ishaq.

Ita kuwa Zaleeha abu ya cakuÉ—e mata komai ya birkice mata,
Yanzu ba mai bin ta kanta ta lura Aunty Lubna da Zakariyya basu damu da dmuwar tata ba

Haka yasa dole ta ƙudurci son haɗuwa dashi ido da ido ayita ta ƙare.

A lissafi dai yau saura kwana biyar ne auren.
ganin har danginsu na Dukku sun fara zuwane ya ƙara tayar mata da hankalin.
Gashi haka nan take jin kamar ana ingzata da zugata kan tayi wani mummunan abu.
Shiyasa yau tunda safe taketa tura mishi text akan yazo gidansu zasuyi mgna mai mahimmanci ganin har yamma ba amsa ne yasa ta kira Ishaq bayan ta tuttura mishi saƙo dan Allah ya amsa kiranta,
Yana d'agawa cikin rawan murya alamun zata fara kuka tace.
"Dan Allah Malam Ishaq na rok'eka da manzon rahma kace yazo gidanmu inada mgna dashi."
cikin danne dariyarshi da sai yanzu kalamanta na wai sun ce mata irin larrarshi basa iya aure dariyar ya É—an danne kana yace.
"Yaushe kike son yazo?."
Da sauri tace .
"Dan Allah yazo yau. Ban san in da zan sameshi ba da naje na sameshi."
wani munafukin murmushi ishaq yayi sannan yace.
"Ki duba hanyarshi zuwa bayan sallan isha."
Da sauri tace to kana ta katse kiran,
a take ta kira Bilkisu dan tasan itace zata tayata ci musu zarafi ta yadda sai sun tsani kawunansu ma, aiko Bilkisu najin shirin Zaleeha tace gata nan zuwa.

Bayan sallan isha, Saifuddeen ne zaune bisa wheelchair ɗin shi kalar ruwan toka mai azabar kyau da sheƙi, a zahiri yadda yake caccanza sutura da ɗaukan wanka to hakama mota da wheelchair ɗinshi suma masu kyau da tsada ajin forko yake hawa hakama huluna da takalma,
Sanye yake cikin wani d'anyen yadin voyel mai kalar shud'in sararin samaniya, sai kuma ratsin fari fari tamkar gajumare,
an ƙyanƙyasawa rigar aiki da surfani mai ruwan garai-garai,
hannun rigar guntu ne masu zagayen zaren garai-garai d'in daga bakinsu, hannun yayi cib damatsan hannunsa da suke farare k'al-k'al masu yalwar gargasa mai tsawo da shek'in bak'i mai d'aukar hankalin duk wanda ya gansu sun zauna cib,
hular damanga ya kafa a kanshi irin kafin nan da ake cewa baruwanka da duniya bi ma'ana ya d'an tura hular tayi baya,
hular farace sai ratsin shud'in zare, sajen nan nashi ya kwanta lib-lib a kyakkyawar fuskarshi mai suturce da farar fata da kan sura jajayen labbansa sai Sheƙi sukeyi a cikin zagayen gashin bakinsa.
hakama takalmanshi farare ne k'al sai layi biyu da akaja mai kalar shuÉ—in daga samansu,
sai wani zazzafan agogon fata na Gucci mai kalar garai da manna a tsintsiyar hannunshi na dama,
sai farin ring É—in azurfa dake É—auke da É—igon diamond a tsakiyarshi daketa wal-wal,
wayarshi samfarin iPhone daya zura cikin al'jihun gaban rigarsa, wanda kana iya ganin kusan rabin wayar ma a sarari.
Hayatuddeen ne ya lumshe ido tare da ƙara zuƙan numfashi dan shaƙan ƙamshin turaren Hamman nashi.
Ummi kuwa ido ta zuba mishi cikin yin hamdala da godiya wa ubangijinta da azurtata da wannan kyakkyawan matashi a matsayin É—anta.
Murmushi yayi tare da mishi fatan a dawo lfy bayan ya mata alamun zai fita.
Hayatuddeen kuwa har bakin mota ya rakashi inda suka samu Ishaq da Sule direba suna jiran fitowarshi.
Mota suka shiga sannan suka nufi New G.R.A.

Suna isa cikin gidan kuwa sukayi kicibis da Ya Aminu shi yayi musu jagora har cikin parlourn BQ kana yaje ya turo Zaleeha wacce,
take tare da bilkeesu.
kusan a tare suka fito yana gabansu.
suna bayanshi suna tafe zuƙatansu fal farin cikin zasuci zarafinsu

A harabar wajen suka samu  Ya Aminun da Ishaq suna mgna da alamun mai mahimmanci ce.

Suna shiga cikin parlour'n. Zaleeha tayi wani irin taku me tattare da izza ta isa gabanshi kujerar dake gefenshi ta zauna tare da ɗaura ƙafanta ɗaya kan ɗaya, a hankali take karkaɗa ƙafafun nata cikin tsaurin ido ta ɗago fuska tare da harba mishi ida nunta cikin nashi idanun.
A hankali ya muskuta ya gyara zamanshi tare da sarƙe manyan idanunshi cikin nata idanun, kana yayi wani irin makirin murmushi tare da ɗaga mata girarshi ɗaya, alamun.
"Baby ya dai ya akayi ne?."
Wani irin yam taji tsikar jikinta duka na amsawa, hatta gashin kanta saida taji ya amsa,
wani irin azabebben kwarjini fuskarshi tayi mata tsoronshi da shakkarshi suka cika mata idanu.
A gigice ta janye ƙwayar idanunta daga nasa, tare da rumtse idanun Nata, jiki na rawa murya a sarƙafe cikin zato da yaƙinin wannan ba mutun bane tace.
"WA innahu Sulaiman...!".

Yau dai ba editing

                             By
                 *GARKUWAR FULANI*
8/22/20, 5:15 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BAKASAWA BACE*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.