Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel
Reading file: NAKASA BA KASAWA BACE PART 1.txt
Chapter 25 of 27
*Page 26*
*NA*
*AISHA ALIYU GARKUWA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
Lumshe ido yayi tare da yin magana a cikin zuciyarshi.
"Uhmmm bazanci kaina ba insha Allah keÉ—in dai zan ci!".
Sake É—ago idanunsa yayi ya watsa mata su, ita kuwa Zaleeha daketa Æ™oÆ™arin tattara kayan aikinta ta turo É—an Æ™aramin bakinta gaba, duk da cewa ba kallonsa takeyi ba amma tabbas tanajin idanunsa na yawo ajikinta, tana gama haÉ—a kayan aikin nata taÉ—an É—ago da kanta,aikuwa idanunsu ne ya sake sarÆ™efe acikin na juna,Â
"Anya wannan ba maye bane!".
ta kuma faɗa cikin ƙasa-ƙasa da murya tana me wurga masa harara da kyawawan idanunta.
Lumshe idanunsa yayi tare da dafe saitin zuciyarsa dake beating, tabbas yau yasamu nutsuwa irin wacce yajima bai samu ba, bakomai ke tafiya da hankalinsa ba face yanda take kaɗa idanunta wajen hararansa, harshe yasanya ya ɗan lashi red lips ɗinsa, yanaji ajikinsa inama da yana da damar da zai kusan tota garesa, tabbas daya jawota jikinsa yayiwa wannan bakin tsiwannanta shan tom-tom.
 hand bag ɗinta ta rayata abisa kafaɗanta tare dakai dubanta ga jama'an dake gabanta, sallama tayi musu akan cewa zata wuce, cikin takunta dake matuƙar ɗaukar hankalin maza ta tako harzuwa inda Ishaq yake, ƙarasowanta garesu yayi dai-dai da kusan ɗaukewar numfashinsa sakamakon daddaɗan ƙamshinta daya samu cakuɗa da numfashinsa, cikin wani irin kasala ya lumshe beautyful eyes ɗinsa.
Saura bai wuce taku huɗu ba ta ƙaraso garesu ta tsaya cak tare dayin ƙasa da kanta, sam batajin zata iya kallon cikin idanun Saifuddeen dan wata azababbiyar fitina take hangowa cikin kwayar idanshi mai kama da maganad'isu haiba da kwarjinshi yana sa zuciyarta cikin wani yanayi, hakanan ƙarasowarta garesu ya haifar mata da faɗuwar gaba yayinda ƙirjinta ke duka da sauri-sauri.
Cikin tausasa murya ta dubi Ishaq daketa faman murmushi kamar yana ganinta,
 "Malam Ishaq nizan wuce sai kuma idan munsake haɗuwa wani sati Idan Allah yakaimu!"
Murmushin dake kan fuskar Ishaq ne ya faɗaɗa, inda ya sanya hannunsa ya dafa kafaɗan Saifuddeen cike da ƙaunar Saifuddeen ɗin yace "To bari nai miki rakiya Malama Zaleeha, amma fa wani sati kishirya don kuwa baƙonki na musammanne, abokina Saifuddeen kenan!".
Wani irin ƙululun baƙin ciki ne ya daki zuciyar Zaleeha cike da haushinsa ta ɗago fararen idanunta ta watsa masa harara, inda still ta kamasa yana kallonta, "Nasani ae dama kallona kake maye kawai!".
tafaÉ—a cikin Æ™asan maÆ™oshi tana me mulan-mulan da bakinta,Â
Murmushin daya ƙara bayyana zallan kyau da kwarjininsa yayi, sarai ya fahimci me take faɗa cikin ransa yace.
"Zakisan kuwa ni maye ne na gaske duk randa kika shigo hannuna!".
Sake gayara zaman jakarta akan kafaÉ—arta tayi inda ta juya cikin takunta me É—auke da nutsuwa ta nufi hanayar da zai fitar da ita daga cikin falon, tare da Ishaq suka jera suna tafiya, suna É—an hira sam idan kaga Ishaq bazakayi tunanin makaho bane.
Da wani irin kallon So, haɗi da shauƙi tare da zallan k'auna Saifuddeen ya bita, komai nata abun burgewane, idanunsa ne suka sauƙa akan tsararren hips ɗinta da cikin salo suke juyawa, saurin lumshe idanunsa yayi tare da cije laɓɓansa, don kuwa wani irin harbawa yaji jikinshi da zuciyarshi sa nayi, wata irin sassanyar ajiyar zuciya ya sauƙe, tare da buɗe idanunsa, dai-dai lokacin ita da Ishaq suka fice daga cikin falon,  murmushi yayi tare da ɗan sanya hannu ya shafi lafiyayyen sajen dake kwance akan fuskarsa.
Sannu ahankali gaba É—aya mutanen dake cikin falon suka soma watsewa kowa ya kama gabansa.
Har bakin motarta Ishaq ya rakata, inda sosai taji daÉ—in rakiyar tasa, cikin muryarta dake nuna jin daÉ—in rakiyar tasa tace.
"Godiya dubu Malam Ishaq!".
Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.
"To Malama Zaleeha kigaida mutanen gida!"
Da "To" ta amsa masa, kana ya juya yakoma inda yabar Abokinsa Saifuddeen.
Murfin motar ta buɗe ta shiga tare da murza mata key, dai-dai-ta tsayuwar motar tata tayi, cikin tuƙinta me ɗauke da nutsuwa ta fice daga cikin harabar ofishin ƙungiyar ta (Jonapwd), cikin salo take murza kan steering motar tata, tunaninsa ne ya faɗo cikin ranta, hakan yasa ta saki wata ƴar siririn tsuka tare dayin ƙwafa, cike da haushin irin kallon daya dinga yi mata ta murguɗa baki tare da yin guna-guni acikin ranta inda tace "Mutum gurgu sannan kurma amma sai shegen sa'ido, no wonder akace gurgu kafi me ƙafa iya shege!".
tafaÉ—i haka adai-dai lokacin da take shan wata kwana.
Ishaq na dawowa cikin falon, ya iske Saifuddeen wanda ke zaune cikin matsanancin shauƙinta.
Hannayen Saifuddeen ɗin Ishaq ya riƙo cikin nutsuwa yace.
"Saifuddeen kaga Zaleeha ko, tana da kirki sosai sannan akwai nutsuwa atattare da ita, sam kyawunta baisakata yin É—agawa ba".
Murmushi Saifuddeen yayi tare da zaro wayarsa daga cikin aljihu, inda ya rubutawa Ishaq saƙo kamar haka.
"Nayaba da hankalinta matuƙa ishaq, saboda hakane ma na zaɓeta a matsayi. Matar aurena uwar ƴaƴana in Allah ya yarda,
ba dama nace maka nasamu matar aure!".
Waro idanun Ishaq yayi bayan yagama sauraran wayarsa inda ta karanta masa gaba É—aya abun da Saifuddeen É—in ya rubuta, cikin tsananin mamaki yace.
"Wai kana nufin Zaleeha?"
Still murmushi Saifuddeen yayi inda ya rubata cewa.
"Inasonta Ishaq, haƙiƙa ina tsananin sonta, harma inajin kowani bugu na zuciyata tare da zallan soyayyarta yake tafiya, Inaso na Aureta! Ishaq tun randa na fara ganinta sonta ya zame min abokin rayuwa,
shiyasa kullum mukayi mgna da kai sai na tambayeka ita da lfyarta".
Koda Ishaq yagama sauraran batun wani irin tsananin farin ciki ne ya lulluɓesa, haƙiƙa baya gani da ido amma yana gani da zuciya, kuma tuni zuciyarsa ta gama karanta masa kyawawan halayya da kuma nagarta irin na Zaleeha, tabbas zaisowa abokinsa Saifuddeen samun mace irin Zaleeha amatsayin mata, cikin jin daɗi tare da son ƙarfafawa Saifuddeen ɗin guiwa Ishaq yace.
"Naji daɗi Saifuddeen, kuma zanfi kowa so da muradin kasantuwar aurenku da Zaleeha, saidai kuma baza muyi gaban kanmu ba, zaifi kyau mu fara sanar da manya don baza muje haka kawai ba sai da ƙarfin mu, ma'ana sai munsamu amincewar manyanta, tabbas ayanda nasan Zaleeha nasan tanada nagarta, kuma zata soka".
Ya k'arishe mgnar cikin karsashi domin su basu sawa ransu cewa nakasarsu zata zame musu kasawa ba, bare ta hanasu neman duk wani abinda mai cikar halitta zai nema kuma ishaq bai san dakon son dake ran Zaleeha ba.
Wani irin Æ™warin guiwa kalaman Ishaq suka Æ™arawa Saifuddeen, nan suka cigaba da tattauna hira atsakaninsu ta hanyar gudanar da text message. Â
Zaleeha kuwa daga Jomapwd kai tsaye gidan redionsu na vission FM. ta nufa, tundaga fitowarta acikin motarta gaba ɗaya kallo ya dawo kanta, haƙiƙa Zaleeha cikakkiyar mace ce dake iya ɗaukar hankalin kowani ɗa na miji, cikin takunta me ɗauke da nutsuwa ta ƙarasa babban ɗakin da suke tantance shirye shiryensu kafun su turashi izuwa ɗakin watsa shirye-shirye, saida aka tantance shirin nata na wannan rana kafun aka watsashi tayanda kowa zaijisa raɗau batare da wata matsala ba.
 Zama tayi akan wata kujera wanda keda ƙafafun taya, ahankali take jujjuyawa yayinda ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya, wayarta ta ciro tare da saƙala earpiece acikin kunnenta, cool music na Edsheeran ne ke tashi acikin earpiece ɗin nata, ahankali take jujjuya kanta alaman waƙan na taɓa zuciyarta sosai, luf tayi ajikin kujeran tare da kwantar da bayanta kana ta lumshe kyawawan idanunta, tunaninsa ne yayi mata tsaye acikin ranta, wani irin ƙauna haɗi da begensa ne suka cika zuciyarta, bazata taɓa cire rai da rabo ba akansa saba, haƙiƙa ita mai raunice hakanne ma yasanya soyayyarsa ke wahalar da zuciyarta, inama da ace wani zaiji abun da takeji, inama da ace ƴan uwanta zasu fuskanci mai takeji tabbas tasan da kowa sai ya jinjinawa girman soyayyar da takeyi masa, tanajin sonsa har cikin ƙashi da bargo, haka kuma tanajin soyayyarsa tamkar jinine dake gudana ajikinta ako yaushe, hawayene suka cika idanunta sakamakon rauni irin nata.
Ajiyar zuciya Raveel yasauƙe, wanda tun ɗazun yake tsaye yana kallonta, ayayinda tayi nisa cikin begen masoyinta, shikuma alokacin yakejin kamar zuciyarsa zata tarwatse saboda ƙaunarta, son Zaleeha yake da duka zuciyarsa, hawayene suka cika idanunsa, hango manager dake ƙoƙarin tahowa garesu da yayi yasanyashi saurin shanye hawayensa, tare da komawa cikin wani ɗan balcony ya tsaya don sam bayason manager ɗin ya gansa, saboda rauninsa ya bayyana sosai ta yanda bazai iya ɓoyewa ba.
Yana sako ƙafarsa cikin babban falon wanda yakasance kamar ɗakin hutu ga ma'aikata gidan radio'n vission FM ɗin wani irin walagigin ƙaunarta ne ya daki ƙahon zuciyarsa, yayinda ya lumshe idanunsa tare da shaƙan daddaɗan ƙamshin ta da ya cika ɗakin, ahankali ya buɗe idanunsa tare da sauƙesu akanta, sam batasan da zuwansa ba kasancewar haryanzu idanunta arufe suke, sannan zuciya da ƙwaƙwalwarta sunyi nisa wajen tunanin abincin ruhinta, ahankali yatako ya ƙaraso gareta, cikin kulawa yaƙira sunanta, sam bata jisaba don tayi nisa atunanin da takeyi, kujera yajawo tare da zama yana facing ɗinta, hannunsa yakai ya zare earpice ɗin dake kunnenta, da sauri ta ware idanunta da sukayi ja ta sauƙesu akansa, cikin mamakin ganinsa da kuma yanda ya cire mata earpiece ɗin kunnenta taɗa kallesa kana tayi ƙasa da idanunta.
Murmushi Manager yayi tare da cewa.
"Barkanki da hutawa gimbiyar mata".
Cikin takura ta amsa masa da yauwa acan ƙasan maƙoshinta, hakanan ganinsa yasanya taji ba daɗi acikin ranta, itafa yanzu hakanan ta tsani duk wani mahluƙin da zaizo mata da zancen soyayya, ayanzu mutum ɗaya kawai take muradi kuma tana nan tana jira ya taho mata da soyayyarsa,
"Zaleeha!" Manager yaƙira sunanta murya asanyaye.
Bata amsa masa ba bata kuma ɗago kanta ta kallesa ba, sam ayanzu batason damuwa, hutu da nutsuwa kawai take da buƙata.
Ganin cewa bata amsa shibane yasanyashi cewa "Kiyi haƙuri Zaleeha, bansan da yaushene kuma tayaya bane nakamu da sonki, amma tabbas inasonki sosai, ina fatan zamo warki mata agareni Zaleeha, nasan kina ganin girma ƙima da kuma mutumci na, amma banda yanda zanyi akan soyayyarki Zaleeha, inajin kaina tamkar ƙaramin yaro akan soyayyarki, bazan gaji da fallasa miki sirrin zuciyata ba, don ina fatan samun nasara agareki!".
Sai alokacin Zaleeha ta ɗago idanunta ta kalleshi, inama da ace shine zaune agabanta haka yake furta mata daɗaɗan kalaman soyayya? inama da ace zata kasance da masoyinta kasantuwa tahar abada, ajiyar zuciya ta sauƙe, tabbas tana ganin girman Manager acikin idanunta, saboda hakane ma batajin zata iya tafka masa yayyafin rashin mutumci, don ko bakomai shiɗin babban mutum ne, kanta ta kawar gefe cikin dauriya tace. "Tabbas kamar yanda kafaɗa ina ganin girma da ƙimarka acikin idanuna, saidai dan Allah naroƙeka Manager daka janye soyayyar da kakemin, inada wanda nakeso araina, banajin dagashi zanso wani aduniyar nan, dan Allah karabu dani naji da damuwar dake raina!". taƙare maganar tana me haɗe hannayenta biyu waje guda alaman roƙo.
Ajiyar zuciya manager ya sauƙe tare da ɗan rumtse idanunsa, idan yaji tana ambatan cewa tana da wanda takeso, ji yake tamkar kifiya take caka masa aƙahon zuciyarsa, cikin raunin daya bayyana akan fuskarsa yace. "Kamar yanda kike jinsa acikin zuciyarki haka nima nake jinki acikin tawa zuciyar, bansan taya zan fasalta miki irin tarin ƙaunar danakeyi miki ba Zaliha, dan Allah ki tausayawa zuciyar da ta jima tana dakon soyayyarki!"
Idanunta ta rumtse tare da cije laɓɓanta tana mejin kanta na wani irin sarawa tamkar zai fashe, sam bazata iya jurewa ba hakan yasa ta ɗauki hand bag ɗinta, tare da wayarta, ko kallon inda Manager yake bata sakeyi ba ta nufi hanyar fita daga cikin falo, da sauri Raveel dake tsaye yanajin duk abun da suke faɗa ya koma jikin gini ya tsaya, don sam bayaso sugansa harsusan yaji abun da ya wakana atsakaninsu, "Zaleeha! "Zaleeha!!" haka manager keta ƙiran sunanta, ko tsayawa batayi ba balle yasa ran zata juyo ta kallesa, hannayensa ya sanya ya dafe kansa, yayinda soyayyarta ke ƙara ninkuwa acikin zuciyarsa, itakuwa Zaleeha tuni hawaye sun cika idanunta, kaitsaye wajen motarta ta nufa, tanakai hannunta jikin murfin motar muryar Raveel ya daki dodon kunnenta.
Inda yaƙira sunanta, ƙoƙarin shanye hawayen dake cikin idanunta tayi tare da tsayawa cak, saidai bata juyo ba,  ajiyar zuciya Raveel dake bayanta ya sauƙe tare da cewa.
"Dan Allah kijuyo ki fuskanceni!"
"Kafaɗi abun da kakeson faɗa danni sauri nakeyi!" Zaleeha ta faɗa cikin ƙosawa, don gaba ɗaya komai bayayi mata daɗi.
"Maganace akan SO Zaleeha, dan Allah Zaleeha ki bani dama, ashirye nake dana zama GARKUWA agareki, zan baki ingantaccen farin ciki me É—orewa, sannan zan....."
"Ya isa haka Raveel, wai me kuka ɗaukenine kowa so! so!! So!!! maikuka maidani ne? shin wai ni kaɗaice mace aduniya? Dan Allah Raveel kafita arayuwata, ka tsaya amatsayinka na abokin aikina kadaina wannan ƙoƙarin na tura kanka inda baka da muhalli awajen!!". Zaleeha ta katseshi tare da faɗin maganan aɗan tsawace.
Bata jirayi me Raveel ɗin zai ƙara faɗi ba ta shige cikin motarta, azafafe ta murzawa motar key yayinda ta jata da wani irin speed, ko gama wangale mata gate ɗin bata bari maigadi yayi ba ta danna hancin motar tata waje ranta amatuƙar ɓace.
Raveel kuwa idanunsa da ke cike da hawaye ya rumtse tare da juyawa jiki asaluɓe shima yanufi wajen da motarsa take, don yanda yakejin ciwo azuciyarsa bayajin zai iya komawa cikin office ɗinnasu.
Ahankali take rage gudun da takeyi, kantane ke mata wani irin ciwo, gaba É—aya damuwa yayi mata yawa,  ɗan lumshe idanunta tayi tare da dafe saitin zuciyarta dakeyi mata zafi, kaitsaye Havilla tanufa, don ayanda takejin zuciyarta dole tana da buÆ™atar abun da zai sanyaya mata rai,  tana shiga cikin wajen ta lumshe idanunta sakamakon wani irin daddaÉ—an sanyi daya ratsa jikinta, wani irin ni'imtaccen Æ™amshin korayen shuke shuke dake wajenne ke ratsa cikin hancinta, sosai yanayin wajen yayi mata, cikin takunta mai É—uke da nutsuwa taÆ™arasa can ciki, ƴan mata da samari ne suka kusa cika wajen, waÆ´anda kallo É—aya zakayi musu batare da sai anfaÉ—a maka ba zaka gane cewa masoya ne, don kowanne dake cikin wajen fuskarsa É—auke take da shauÆ™i, dayawan mazan dake wajen kallonsu ne ya dawo gareta, musamman wani kekyawan gaye dake zaune shi kaÉ—ai akan table,  cikin ajinta da sanin darajar kanta ta Æ™arasa ga ma'aikatan dake cikin Havilla'n, nan ta basu order'n irin haÉ—in ice cream É—in da takeso ayi mata, mintuna kaÉ—an wani saurayi ya kawo mata ice cream É—in,zip É—in hand bag É—inta ta zuge inda ta ciro kuÉ—i ta bashi kana ta karÉ“i ice cream É—in, cikin takunta mai É—auke da nutsuwa ta juya ta fice, da sauri wannan saurayin ya rufa mata baya, don bayajin zai iya jure kasa furta mata soyayyarta da ta kamasa alokaci guda. Â
Harta kusa kai bakin motarta da sauri yasha gabanta, cikin yanayi naɗan mamaki taja baya, tana me ƙare masa kallo, murmushine ɗauke akan fuskar saurayin me suna Saleem, cikin da-ida-ita nutsuwarsa yace.
"Amincin Allah ya tabbata agareki yake wannan ma'abocian kyakkyawar halitta"
Idanunta taÉ—an juya tare da kafesa da ido.
ÆŠan lumshe idanunsa yayi ganin yanda kwawawan idanunta ke yawo ajikinsa, cikin nutsuwa yace.
"Saleem Sa'ad Turaki,
fatan banyi laifiba dana tsaida ki, naga kamar sauri kike".
Baki ta taɓe tare da buɗe murfin motarta ta shige, ƙoƙarin rufe murfin motar take, Saleem yayi saurin riƙewa, cikin sanya fuskar tausayi yace.
"Nasan dacewa shawo kan kyakkyawar mace sarauniyar mata kamarki abune mai matuƙar wahala, amma please ko phone number ɗin kine ki bani hakan zai taimakamin sosai"
Hannunta tasanya taɗan dafe goshinta, cike da ƙosawa ta ɗago ta dubesa, shiɗinma kallonta yake wani murmushin k'eta tayi tare da bashi number Raveel kana ta gaya mishi sunanta,
murfin motarta ta rufe tare da data motar tatafi tabarshi tsaye awajen, murmushi ɗauke akan fuskarsa yabi motarta da kallo, harta ɓacewa ganinsa, cike da fatan sake ganinta anan gaba ya juya yakoma cikin havilla. Itakuwa Zaleeha tana tuƙi tanashan ice cream ɗinta, hakan kuwa sosai ya haifar mata da nutsuwa.
Ransa fari ƙal fuskarsa ɗauke da farin ciki yake sarrafa keken nasa har yakawo cikin falon, Ummi da Hayatuddeen ne zaune, carbi ne riƙe ahannun Ummi yayinda Hayatuddeen kuma ke zaune akan sofa, yana riƙe da plate ɗin dambun nama ahannunsa, ahankali ya turo keken nasa zuwa gaban Ummi dake zaune akan kujera, wanda ganinsa da tayi yasanyata sakin murmushi, ƙarasowa gab da ita yayi tare da ɗaura kansa akan kafaɗanta, cikin tsananin ƙaunar da takeyi masa tasanya hannu ta shafa lallausan gashin kansa tare da cewa.
 "Da'alama wannan fitar taka al'khairi zata haifar mana don naga kafita cikin farin ciki, ka kuma dawo cikin farin ciki". Murmushine ya faɗaɗa akan fuskarsa tare da sake gyara zaman kansa dake kafaɗanta, shikaɗai yasan irin farin cikin da yake ciki ayau ɗin.
  Hayatuddeen dake ta faman cin dambunsa yana jijjiga kai alaman daɗin dambun na ratsashi, dubansa ya kai ga Hammannsa cikin santin dambun nasa yace "Hamma nine fa auta kowa ya sani".
Hararansa Saifuddeen yayi cikin body language yayi masa alama da cewa.
"Idan kaine auta saime, shikenan sai kada Ummina tanuna min ƙauna?"
Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ai dai ƙaunar dake tsakanina da Ummi na ta musammance, naɗan baka aronta ne naƴan wasu kwanaki"
Murmushi Ummi dake jinsu tayi, shiɗin ma Saifuddeen murmushi kawai yayi don ya fuskanci cewa dambun naman da Hayatuddeen ɗin ke cine yasasa santi. Dubansa Ummi tayi cike da kulawa tace.
"Akawoma abinci ne?".
Cikin body language É—insa yayi mata alama da bayanzu ba, ahankali ya tura kekensa inda ya nufi É—akinsa don so yake yayi wanka kana yaÉ—an huta,Â
Shida kansa ya haɗawa kansa ruwan wanka acikin bathtube, inda yacika turaren wanka me daɗin ƙamshi aciki, kwanciya yayi luf acikin bathtube ɗin tare da lumshe idanunsa, ba'a iya jikinsa kaɗai yakejin sanyin ruwan ba har acikin zuciyarsa, wani irin ƙawataccen murmushine ya bayyana akan fuskarsa sakamakon tunowa da irin yanda take murguɗa masa baki dayayi, tausasan lips ɗinsa yaɗan ciza tare da sanya hannunsa ya riƙe dai- dai saitin heart ɗinsa, wani irin tarin soyayyarta ne yasake ɗarsuwa acikin ransa, sake gyara kwanciyarsa acikin bathtube ɗin yayi tare da sakin wani sabon murmushi, sannu ahankali yakejin sabon so da ƙaunarta na huda gaba ɗaya jijiyoyin dake jikinsa, aƙalla ya ɗauki kusan sama da 30 minute yana tunaninta yayinda wata irin ƙaƙƙarfan begenta ke neman zautar dashi, adaddafe haka yayi wanka, koda yafito daga cikin toilet ɗin wata brown ɗin jallabiya me kyau yasanya ajikinsa inda ya feshe jikinsa da daddaɗan turarensa mai sanya nutsuwa,
kwanciya yayi luf akan gadonsa tare da jawo laptop ɗinsa, ya kunna, kyakkyawan hoton fuskarsa ne ya bayyana akan screen na laptop ɗin, cikin nutsuwa yake danna laptop ɗin inda ya kasa aiwatar da komai gaba ɗaya tunanin kyakkyawar fuskarta da zazzaƙan muryarta ya hana masa sukuni.
ya dade haka daga bisani ya turawa Ahmad text.
"Na samu matar aurefa yaro ka shirya shan biki."
Ahmad dake kwance bisa gado, yayi.da Raliya ke baccin gajiya a kan k'irjinshi.
dariya yayi tare rubuta mishi
"Eye-eye kace ka kusa shiga dausayin jin dad'in duniya yaro."
Tsaki ya tura mishi tare tura mishi nifa surkinka ne.
daga bisa ni dai yayiwa Ahmad d'an bayani,
sosai Ahmad yaji dad'i.
Washegari, yau tunsafe yatashi da wani irin ƙwarin guiwa nason mallakarta, wayarsa ya ɗauka ya turawa Ishaq text message inda yace shirya zuwa ƙarfe d'aya na gobe zai rakasa Dukku, koda Ishaq yaga saƙon abokin nasa murmushi kawai yayi don yasan kwanan zancen har acikin ransa kuma yaji daɗin hakan.
Zaune suke su dukansu akan dinning table suna break fast, surutun Hayatuddeen da Raliya ne ke tashi inda suke ta musu, Ummi dai jinsu kawai take yayinda Saifuddeen ya zaro wayarsa dake cikin aljihunsa, saƙon tafiyarsa Dukku ya rubuta kana ya miƙawa Ummi, amsan wayan Ummi tayi tare da karanta saƙon, ajiyar zuciya ta sauƙe tare da duban Saifuddeen ɗin da kyau, tabbas taji daɗin cewa da yayi zaije dukku'n saboda hakanma wani ƙarin karsashi ne dake nuna samun lafiyarsa, saidai kuma tayi mamaki don yau kwata kwata-kwata kwana biyar ne da dawowarsa Nigeria, sanin da tayi cewa koma mene zaije yi a Dukku'n tana da yaƙinin cewa al'khairi ne hakan yasa, tayi masa fatan zuwa lafiya da kuma dawowa lafiya, Hayatuddeen ne ya dubi hamman nasa jin Ummi nayi masa fatan alkhairi yace "Hamma tafiya zakayine?"
Kai Saifuddeen ya jinjina masa alamar eh tare dayi masa alaman.
"Ko zaka rakani?"
Baki Hayatuddeen ya washe tare da kaÉ—a kansa cikin sauri yace.
"Ƙafata ƙafarka ae Hammana!"
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To É—an sarkin son yawo tunda dai kanason yawo ae sai kabisa Dukku zashi".
Take Hayatuddeen ya kwaɓe fuska tare da girgiza kansa cikin halinsa na shagwaɓa yace.
"Dukku kuma? chab wallahi na haƙura dama wasa nake ba binsa zanyi ba".
Gaba ɗayansu suka sanya dariya don dama sunsan rashin sanin inda Saifuddeen ɗin yace zaije shiyasa cikin karaɗi yace zai bisa, suna kammala cin abincin, Saifuddeen ya wuce ɗakinsa, wanka ya ƙarayi inda ya shirya kansa cikin wata tsadaddiyar shadda Milk colour ɗinkin half jumper wanda taji coffee colour'n aiki a wuyanta, sosai shaddan ta sake fidda sihirtaccen kyaunsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar ya kafa akansa wanda gaba ɗayanta kalar coffee gareta saidai tana da ratsin milk colour ajikinta, hatta takalman dake ƙafansa kalan coffee garesu, inda farar fatarsa tafito tayi ɗas acikinsu, tsadadden agogo ya ɗaura ahannunsa inda ya feshe gaba ɗaya jikinsa da turare, masha Allah Saifuddeen baƙaramin kyau yayi ba, sai ayanzune ma nake lura da cewa ba kayanne sukeyi masa kyau ba shine keyiwa kayan kyau, don kuwa kowani irin kaya yasaka sai yayi musu kyau, haƙiƙa Allah mabuwayine ayayin daya tauye Saifuddeen da tawaya irin ta rashin jin magana da takawa da k'afaffunshi sai ya basa wani irin ɗanɗareren kyau haɗi da kwarjini yakuma sa ya zamto abunso azuƙatan mafi yawancin mutane, haƙiƙa kyawun Saifuddeen madubi ne wanda ko wacce cikakkiyar ƴa mace zataso fuskanta don ganin kanta acikin sa.
falon ya fito cikin kamala ya zauna gefen Ummi yayinda Raliya da Hayatuddeen ke gefe sunata hirar zasuyi kewar Raihana da itama gobe zata koma KD da mijinta.
nan suka d'anci gaba da hira, cikin hirar Ummi tace.
Raliya tare da cewa.
"Rana tayifa tashi ki shiga kitchen ki hada mana lunch kinga yau Hammanku wunin gida zaiyi yace yau lokacinsa namu ne."
dato ta amsa kwana ta mik'e ta shiga kitchen.
Raihana ce ta mik'e da sauri taje bakin k'ofar falon nasu jin ana d'an bubbugawa.
cikin fara'arta da sakin fuska ta kalli Mom d'in Amina tare da cewa.
"Sannu da zuwa shigo ciki."
cikin mmki ta kalli Amina dake bayan Mom da sauri ta k'ara matsawa ta basu hanya tare da cewa.
"La kamar na ganeki, ku ise."
murmushi sukayi baki d'aya kana suka kutsa kai cikin falon bakinsu d'auke da sallama.
Hayatuddeen ne ya mik'e da sauri tare d'an yin tsalle yayi gaban Amina tare da cewa.
"La likita bokan turai? Yaushe kika zo gombe? waya kwatanta miki gidanmu?."
Ummi ce ta mik'e cikin kamala take cewa Mom.
"Lale marhabin maraba lale ga wurin zama."
cikin sakin fuska Mom tace.
"Yauwa."
ita kuwa Ummi dak'uwa tayiwa Hayatuddeen tare da cewa.
"Kai auta me haka zaka tsareta da tambayoyi?."
kanshi ya fasha tare da nuna mata kujera kana yace.
"Kai naji dad'in zuwanki, zauna mana."
murmushi tayi tare d'an hararanshi k'asa-k'asa kana tace.
"Ba nace maka munyi fad'aba?."
dariya yayi sosai kana yace.
"Karki damu zan rarrasheki da dambun naman da Ummina tayimin."
Ummi kuwa cikin rashin saninsu ta gaisa da Mom.
kana ta juyo ta kalli Amina dake durk'ushe a k'asan carpet kusa da k'afafun Ummi tare da cewa.
"Ummi ina wuni."
cikin sakin fuska Ummi tace.
"Lafiya lau Alhamdulillahi."
kanta ta d'an d'ago ta kalli Saifuddeen dake can gefe kan weelchair d'inshi da system nashi bisa cinyarshi yana sarrafa cikin gwarewa, a hankali tace.
"Ya jikin Hamma Saifuddeen?."
zuba mata ido Ummi tayi tare da cewa.
"Alhamdulillahi jiki kam da sauk'i sosai."
a kunyace tace.
"Allah ya k'ara sauk'i ya bashi lfy rabbi ya sa yanada rabon sake takawa da sawunshi."
cikin wani irin tsananin jin dad'in addu'arta ga Saifuddeeen Ummi da yaranta duka suka amsa da. "Amin Amin Ameeen ya rabbil izzati".
cikin nitsuwa Ummi ta kalli Mom daketa kallon Saifuddeeen kana tace.
"Sai dai har yanzu ban ganeku ba?."
da sauri Hayatuddeen yace.
"Ummi baki gane Amina ba itacefa wanna nurse d'in dake kula da Hamma a Abuja kafin mu tafi Indian."
cikin mmki Ummi tace.
"Allah sarki Amina kai ngd ngd matuk'a Allah bar zumunci."
cikin tsananin jin dad'i Amina tace.
"Amin."
Raihana ce tayi sauri cewa.
"La wlh kuwa nima saida ka fad'a na tunata, yaudin tayi kyau da yawane shiyasa bamu ganeta ba."
dariya sukayi baki d'aya,
yayinda Raliya kuwa take ta kawo musu ababen sha dana motsa baki.
ita kuwa Ummi da kanta ta kalli Saifuddeen lokacin da Amina ta kallonshi.
tab'ashi tayi tare da nuna mishi Amina da mom sannan tace.
"Nurse d'inka ta Abuja ne da mamanta ko?."
ta k'arishe mgnar da kallon Amina alamun tambaya, cikin nitsuwa ta gyad'a kanta alamun eh.
shi kuwa Saifuddeen cikin d'an sassauta had'e fuskarsa ya gaida Mom tare da mata godiya duk cikin body language.
sosai Mom ke kallonshi,
shi kuwa kauda kanshi yayi daga kallonsu sam yak'i yarda ya kalli Amina.
shi kuwa Hayatuddeen sai jan Amina da hira yakeyi hakama Raihana.
Ummi kuwa da Mom hirar ciwon Saifuddeen suke d'an tabawa.
Raliya kuwa tuni ta koma kitchen.
Mom ce ta kalli Amina tare da cewa.
"Mu tafi ko Amina lokaci ya tafi."
cikin son bak'i Ummi tace.
"A a ai kwa tsaya kuci abinci."
da sauri Mom ta girgiza kai tare da cewa.
"A a kai Alhamdulillahi ai a k'oshe muke, jiya muka shigo gombe bikin yar k'awata a nan unguwartaku,
to shine fa Amina na zancen Saifuddeen sai aka samu wanda ta sanshi da gidan naku har ta kwatanta mana,
shinefa fir Amina tace sai munzo, ashe ba nisama layi biyu tsakani."
cikin jin dad'i Ummi tace aiko na gode matuk'a wlh naji dad'i.
Amman dai kuyi salla kafin ku fita tunda an kira sallan azahar."
sam Mom bata soba amman dole Ummi tasata suka shiga bedroom ta nuna mata k'ofar bathroom kana ta shimfid'a mata sallaya.
Hayatuddee kuwa kitchen yabi Raliya tare da cewa Amina.
"Bari inje in kawo miki abin dad'i."
murmushi tayi tare da kallon Raihana da ta nufi corridor d'in dasu Ummi suka shiga.
ido ta juya kudu da arewa gabas da yamma, ganin ba kowa a falon daga ita sai Saifuddeen da yaketa saurin ya k'arisa aikinsa ya shiga side d'inshi.
da sauri ta d'auki goran ruwan Faro ta garashi har zuwa gaban Saifuddeen d'in. Da sauri ya d'ago kanshi ya kalli ta inda yaga an turo goran,
fuska ya kuma had'ewa ganin ta zuba mishi sosai ya haɗe girar sama data ƙasa.
ita kuwa Amina, murmushi tayi tare da d'aga mishi gira kana tace.
"Eye kayi kyau, k'asar Indian ta amsheka ji yadda kayi wani fresh da kai kamar ba kaiba."
baki ta tura ganin ya k'ara had'e fuska a hankali taci gaba da cewa.
"Bafa zaginka nayiba kake wani had'emin kekyawar fuskarnan taka,
ko dai baka son in kalli wannan kekyawan sajen nakane."
dib yayi dan baya son yayi abinda zata gane yana gane abinda take fad'an.
ganin haka ita kuma ta lumshe ido kana ta bud'esu a kanshi a hankali tace.
"Wai kai baka gane mai sonka ne?
to in ma baka ganewa ni dai ina sonka, dan kana min kyau."
da sauri tasa tafin hannunta ta rufe ido dan ganin Raihana a tsaye a gefeta tanata dariya.
dai-dai lokacin Hayatuddeen da Raliya suka fito kitchen,
wanda suma suke dariya dan sunji mgnarta ta k'arshe inda take cewa dan kana min kyau.
wayyo ai ji tayi kamar ta nitse cikin k'asa ganin hakane Raliya ta jata suka tafi side d'inta inda acan tayi salla.
shi kuwa Saifuddeen baibi ta kansuba ya wuce side d'inshi.
Koda su Ummi sukayi salla suka fito ba yadda Ummi batayi akan suci abinci fir sukak'i,
dole Ummi ta hak'uri kana sukayi musu rakiya har bakin motarsu inda dama direbansu na nan yana jiransu.
saida suka tafi kafin su Ummi suka koma cikin gidan.
Washe gari kuwa stab Saifuddeen ya shirya cikin shiga ta al'farma sai k'amshi yake zubawa cikin shirinshi na tafiya Dukku.
Yana ƙoƙarin ɗaukar wayarsa dake aje kan gado, yaji anturo ƙofar ɗakin anshigo, Ishaq ne yashigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda shima yasha ado cikin yadin getzner me ruwan toka sosai shima yayi kyau.
Tamkar wanda ke gani ya lumshe idanunsa tare da faÉ—in.
"Kayi kyau sosai Saifuddeen!"
Murmushi Saifuddeen yayi yana me ƙoƙarin ɗaukar wayarsa don ya rubutawa Ishaq din saƙo, maganar Ishaq ta sake dakatar dashi inda yace.
"Bama sai ka sha wahala wajen rubutu ba nasan me zaka tambaya, cewa zakayi dawani idon nasan kayi kyau, bayan kuma nasha faɗa maka cewa masu ido abu ƙalilan zasu nunamin donni ma inaganin komai da zuciyata, zuciyata itace idanuna!"
Murmushi Saifuddeen yasakeyi aransa yana mejin ƙarin ƙaunar abokin nasa, cikin kulawa ya turawa Ishaq saƙo awayarsa kamar haka inda yace.
"Nikam nagaji da wannan surutun naka ni yanzu burina shine naganni a Dukku inda zan faÉ—i abun dake raina".
Ishaq na gama jin saƙon yasaki murmushi abayyane yace.
"Lallai Zaleeha tacika mai sa'a dahar ta iya sace zuciyar mutum ɗaya wanda yazama tamkar da dubu, jajirtaccen Namiji wanda samun irinsa keda matuƙar wahala"
Murmushi kawai Saifuddeen yayi inda ya danna madannin kekensa nan yafara tafiya, yana gaba Ishaq na biye dashi abaya haka suka fito daga cikin É—akin, Ummi dake tsaye tana ganinsu ta saki murmushi cike da so da kuma tsananin tausayinsu tace.
"Har kun fito, amma dai kafun kutafi ai dai zaku tsaya kuci abinci, musamman ma kai Ishaq musamman na aje maka ragowar dambun nama don nasan kanaso"
Murmushi Ishaq yayi tare da cewa.
"Shiyasa nake sonki Ummi na, yanzu dai abani dambun natafi dashi sai naci acikin mota don naga wannan abokin nawa sauri yake kamar wanda zai tashi sama burinsa kawai shine ya gansa a Dukku"
Murmushi Ummi tayi tare da cewa.
"To bari kawo maka sai katafi dashi amma dai inkun dawo kabiyo tanan zanyi abincin dare harda kai!"
Murmushin jin daÉ—i Ishaq yayi inda yace.
"Insha Allah!"
Nan Ummi ta kawo masa dambun naman, har bakin mota ta rakasu inda tayi musu adawo lafiya, Hayatuddeen kuwa É—an kalen baki hadda cewa Hamma Saifuddeen É—in nasa wai yakawo masa tsaraba.
Ƙarfe Biyu daidai suka samu isowa cikin garin na Dukku, gari me ɗauke da tarin al'barka da shuke shuken tsirrai masu kyau da ƙawatarwa, agidan Baffa Ali suka sauƙa inda yacika da tsananin mamakin ganinsu da yayi don sam Saifuddeen baisanar masa cewa yana zuwa ba.
A falon Baffa Ali'n suka zauna inda Aunty Nina takawo musu ruwa tare daɗan abun motsa baki, gyara zama Baffa Ali yayi tare da duban Saifuddeen cikin kulawa yace "Kashammace ni Saifuddeen nida jibi nake shirin tahowa Gombe'n sai kuma gashi kazo batare da kasanar dani ba, ai da kafaɗamin kanada buƙatar ganina to tabbas da har gida zanzo nasameka".
Murmushi Saifuddeen yayi tare da duban Baffan nasa, saƙo ya rubuta awayarsa kamar haka, kana ya miƙawa Baffa Ali'n.
"Kagafarceni Baffa Ali, magana me mahimmanci ne ta kawoni, naƙi sanar dakai zuwana ne kuma saboda nasan idan kaji cewa zakayi nabari zaka zo".
Ɗan murmusawa Baffa Ali yayi bayan yagama karanta saƙon inda yace.
"Shikenan Saifuddeen ina sauraranka, tabbas nasan baƙaramar magana bace zata tasoka daga Gombe zuwa nan".
Ajiyar zuciya Saifuddeen yayi tare da sunkuyar da kansa ƙasa, Ishaq ne yaɗan gyara zamansa tare da yin gyaran murya cikin nutsuwa yace "Saifuddeen yaga mata kuma yana fatan aurenta wannan dalili shiyasa mukazo don musanar dakai, saboda yana da buƙatar anemamasa izinin fara zuwa zance daga wajen manyanta kamar yanda addini ya koyar!"
Wani irin murmushin farin ciki ne ya bayyana akan fuskar Baffa Ali, cike da tsananin jin daɗi yace "Alhamdulillah masha Allah, Allah Abun godiya, haƙiƙa kun zomin da labari mai daɗi Ishaq, na kuma yi murna ƙwarai matuƙa, tabbas yanzu naƙara yarda dacewa NAKASA BA KASAWA BACE, haka kuma nakasar Saifuddeen bata tauye masa zamowa cikakken ɗa Namiji ba, Allah Abun godiya".
Duban Saifuddeen wanda kansa ke ƙasa Baffa Ali yayi cike dajin daɗi yace .
"To ita yarinyar a inane take sannan wanene mahaifinta?"
Ishaq ne yace.
"Anan Gombe take cikin G.R.A sannan mahaifinta babban Malami ne wanda ƙasa gaba ɗaya ke alfahari dashi Malam Bashir!"
Cikin jin daÉ—i Baffa Ali yace "Alhamdulillah mungodewa Allah, Insha Allahu yau yau É—innan zan sanar da aminin mahaifinka Malam Ashiru, don kuwa gobe zamu dira acikin garin Gombe, bazamuyi k'asa a guiwaba don ba'a wasa a lamarin aure".
Sosai daÉ—i ya cika zuciyar Saifuddeen wani irin farin ciki yakeji, yayinda zuciyarsa ta cika da annuri, kasancewar tanaji ajikinta cewa takusa samun muradin ta.
Anan cikin Dukku su Saifuddeen suka wuni inda suka zazzaga ƴan uwa da kuma abokan arziki a gidan Goggo Dada ma sun dad'e. har gidan Malam Ashiru sukaje da Baffa Ali, nan Baffa Ali yayi masa bayani, sosai yaji daɗi shima kuma yayi na'am tare da nuna farin cikinsa, inda suka tsayar akan cewa gobe insha Allah zasu sauƙa acikin garin na Gombe. Anan cikin Dukku su Saifuddeen sukayi sallan Magriba daganan suka kama hanyan dawowa cikin Gombe.
Zaleeha ce zaune acikin falon Mahaifiyarta yayinda ta tanƙwashe ƙafafunta washe guda, kayan ciye ciyene zube agabanta dangin su snacks da chocolates, sanye take da wata ƴar riga marar nauyi wanda taɗan kama jikinta, idanunta ta lumshe akaro na barkatai tare da jingina bayanta da jikin kujera, damuwane ke ƙoƙarin hallaka nutsuwarta, yayinda wutar ƙaunarsa ke tsananin ruruwa acikin zuciyarta, gaba ki ɗaya kwana biyunnan sam bata da nutsuwa, ko abinci bata wani ci sosai, sam batajin daɗin zaman gidan nasu ayanzu, don kuwa akowacce rana sake hura mata wuta ake akan fitarda gwaninta, sam idanunta sun rufe, bataji bata gani akan soyayyarsa, akullum akuma koda yaushe, duk bayan shuɗewar wasu mintuna soyayyarsa ƙara ninkuwa take azuciyarta, yayinda abun ke ƙara girmama akowacce rana, don yanzu hartakai ta kawo hatta numfashin da zata shaƙa da Soyayyarsa yake tafiya, zuciyarta tuni ta narke akan tsantsar ƙaunarsa, takanyi kuka sosai akan soyayyarsa amma babu me rarrashi,, ahankali take fitar da numfashi tana mejin tsananin kewa da begensa.
Zakariyya da tun ɗazu ke tsaye akanta batare da ta sani ba ya gyara tsayuwarsa, duk da cewa suna yawan faɗa atsakaninsu, amma duk da haka yana matuƙar son yayartasa, haka kuma yanajin duk wata damuwa tata shima damuwarsa ce, cikin tausayawa yace.
"Adda Zaleeha!"
Jin muryan Zakariyya acikin kunnuwanta yasanyata buÉ—e idanunta wanda sukayi ja.
Ganin yanda idanunta sukai ja, yasanya Zakariyya zama akusa da'ita cike da kulawa ya kamo hannunta, cikin ƙaunar ƴar uwartasa kuma yayarsa yace.
"Wace damuwace haka take neman rabaki da nutsuwarki? wace damuwace haka ta sauya gaba É—aya yanayinki? Dan Allah Adda Zaleeha kidawo kamar yanda kike da, banason wannan damuwar taki, kiduba fa kiga yanzu ko Æ´ar faÉ—annan bamayi banajin daÉ—in hakan wlh nafi son muna fad'a abinmu a shiga tsakaninmu aji kunya!".
Idanunta ne sukayi rau rau, yayinda hawaye ya cika cikinsu, cikin sassanyar muryar dake bayyana zallan damuwan da take ciki tace "Yazanyi Zakariyya? Yazanyi da soyayyarsa? inajin zafi acikin ƙirji da zuciyata, inajin idan bansamesa ba bazan taɓa samun cikar farin ciki ba, Ina sonsa! Ina matuƙar son sa!!". Ta ƙare maganar hawaye suna me gangara akan ƙuncinta.
Ajiyar zuciya Zakariyya ya sauƙe, duk da cewa shi yarone sannan baisan komai agame da soyayyaba, amma tabbas yaji ajikinsa cewa ƴar uwar tasa tana cikin wani hali, cikin son kwantar mata da hankali yace.
"Kiyi haƙuri Adda Zaleeha Insha Allah Zaki gansa, kuma shida kansa zai zo ya furta miki kalman Soyayya, nasan shima yanacan yanata tunaninki, yana kuma taso ya ganki, nasan shima yana can yana kuka akanki, yana cewa wayyo Zaleeha na, idan bake ba zan faɗa rijiya!".
Duk da cewa tana cikin halin damuwa sosai maganan Zakariyya ya bata dariya wanda har batasan sanda tayi ɗan murmushi ba, wani irin sanyi kalaman ƙanin nata suka sanya mata azuciya, cikin jin daɗin ganin murmushin Yayartasa yace . "Yauwa ko kefa Adda Zaleeha kinsan idan kina dariya ƙara kyau kike, sannan kuma idan kina dariya maza suna ganinki kamar tauraruwa ne, to waima wayeshi da zaice tunanin ƴar uwata bai kama masa zuciya ba? dagaske nake kiyarda dani shima yanacan yanata tunaninki, harma da inda zai sake ganinki, wataƙila ma yanacan soyayyarki ta kwantar dashi jinya, wata ƙilama baya iya bacci saboda ke, burinsa kawai shine ganinki, tabbas zaki ganshi zakuma ku haɗu nan bada jimawa ba, sannan har ƙasa zai tsugunna miki yace, wayyo Zaleeha na kibani soyayyarki dan Allah!!".
Yanzu kam dariya sosai Zaliha keyi inda har fararen haƙwaranta saida suka bayyana, wani irin farin cikine ya lulluɓeta, jin kalaman ƙanin nata takeyi tamkar dagaske, ganin tana dariya ne yasanya Zakariyya ɓare chocolate ɗaya yakai bakinta cikin kulawa yace.
"Yauwa to kici chocolate É—inki, kuma kiyi farin ciki yananan yana zuwa Insha Allah!".
Babu musu ta amshi chocolate É—in taci, wani irin sanyin daÉ—i takeji azuciyarta.
Wani dogon tsuka sukaji yafito daga bayansu hakan yasasu waiwayawa da sauri, Mama dake tsaye tun É—azu gaba É—aya taji kome suka tattauna, harara ta watso musu su duka biyun cikin takaici tace.
"Ae dama batun yauba nasan cewa daga ke har Zakariyyan baƙananan shashashai bane, kina kuka harkina cewa bazakiyi farin ciki ba idan babu wani wanda baimasan kinayi ba, wataƙila ma yanacan duniyarsu ta aljanu, waya sani ma ko yashiga jikin wata anƙonesa da ayar Allah zuwa yanzu babuma labarinsa, Wallahi Zaleeha kidawo cikin hankali da nutsuwarki, nagama fahimtar cewa tunaninki ne ke neman gushewa, saboda haka ko kinaso ko bakyaso Abdussalam shine wanda zai zamo miji agareki, kai kuma kada ka sake nasake dawowa cikin falonnan na iske ka azaune, baka da aiki sai hauka, har wai kana kwaɗaita mata cewa zaizo gareta".
Ƙwafa tayi tare da juyawa ta koma ɗaki.
Fuska Zaliha ta kwaɓe tare da duban Zakariyya, murmushi Zakariyya yayi mata tare da yin ƙasa da murya cikin kulawa yace.
"Kar maganan Mama ya dameki, ae dai bakyason Abdussalam ko?".
Kamar ƙaramar yarinya haka ta kaɗa masa kai alamar "Eh".
Murmushi yayi tare da cewa "Insha Allah Bazaki auresa ba, wanda kikeso shi zaki aura, kuma zaizo kamar yanda na faÉ—a miki, sannan baki dace da kowa ba saishi shi kaÉ—ai!"
Murmushi tayi tare da lumshe idanunta, sosai tasamu gamsuwa acikin kalaman ƙanin nata, hannunta yakama tare da cewa takoma ɗakinta, anjima zaizo su buga game a laptop ɗinta, bata musa shiba ta tattare kayan snacks ɗinta inda Zakariyya ya ɗauki cake guda ɗaya, haka ya fita yanaci itakuwa ɗakinta ta wuce tana mejin sauƙin damuwarta, don acikin kashi ɗari yanzu babu kashi 80..
Su Saifuddeen kuwa ƙarfe 7:30 pm dai-dai suka shigo cikin garin Gombe, kamar yanda Ummi ta buƙaci da Ishaq yadawo, baiyi ƙasa aguiwaba wajen biyo Saifuddeen suka dawo gidan, Raliya ce ta cika musu gaba da kayan ciye ciye inda Ummi da kanta ta dafa musu fried rice mai rai da lafiya wanda yaji haɗin kayan lambu da hanta, gefe guda kuwa hadda haɗaɗɗen coslow wanda yaji madara da bama tayi musu, dayake Saifuddeen bawani maicin abinci sosai bane hakan yasa baiwani ci da yawa ba, Ishaq ne kam yaci sosai, don dama yana matuƙar son fried rice sosai, koda suka kammala hira ne ta ɓarke tsakanin Ishaq da Ummi inda sukayi hira sosai, har dare yayi sosai batare da sun ankara ba, ƙarfe 11 Ishaq yatashi daniyar tafiya, nan Saifuddeen yakafe kai da fata akan cewa dole lallai saidai ya kwana idan yaso gobe sai ya koma gida, Ummi ce tasa baki anan cewa Ishaq ɗin ya kwana kawai tunda dare yayi, hakan kuwa akayi ranan agidan Ishaq ya kwana tare da Saifuddeen, haka yasha baccinsa yayinda yabar Saifuddeen nata faman juyi, sam yakasa bacci sakamakon wata irin fitinannennen tunaninta da ta addabesa, haka yayita faman juyi akan gadon da ƙyar bacci ɓarawo ya iya ɗaukarsa, ko acikin baccin haka yadinga mafarkai kala kala da Zaleeha, wacce gaba ɗaya ta riƙe masa zuciya.
Washe gari.
Kamar yanda su Baffa Ali suka alƙawarta masa hakance takasance don ƙarfe takwas dai-dai sai gasu acikin garin Gombe, tarba ta mutumci Ummi tayi musu, inda aranta take me mamakin ganinsu, bayan sun gama gaisawa ne Baffa Ali ya gyara zama tare da sanar da'ita abun al'khairin dake shirin tunkararsu.
Wani irin tsananin farin ciki ne yakama Ummi har batasan sanda wasu ƙwalla suka gangaro daga cikin idanunta ba, cikin jin daɗi tace.
"Alhamdulillah! Allah Abun godiya, naji daɗin wannan labarin matuƙa Allah kuma yasa matarsace!".
Da "Ameen ya Allah ". Su Baffa Ali suka amsa, nan suka ɗan tattauna akan batun daga bisani Ishaq yazo tare da mahaifinsa, saboda tare zasuje, dan sosai mahaifin Ishaq ɗin yasan Baba Malam, mahaifin Zaleeha kenan, dan harma yaƙirasa yasanar dashi batun zuwansu, kai tsaye suka wuce G.R.A.
Atare Raliya da Hayatuddeen sukayi Wani irin Tsalle, cikin tsananin farin cikin jin kalaman Ummin nasu suka rungume juna, cike da zumuÉ—i Hayatuddeen yace "Yesss! Allah Nagode maka Hammana zaiyi aure zan samu Aunty!!"
Itama Raliya wani irin farin cikine ya lulluɓe mata zuciya cikin jin daɗi tace.
"Insha Allah auren Hamman mu sai yazama abun kwatance aduk Nigeria, zamusha shagali irin wanda wasu basu taɓa yi ba!".
Hannu Hayatuddeen ya bata suka tafa cike da murna yace "Dan Allah Ummina asa lokacin bikin nan kusa!"
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"Amma kai dai Hayatuddeen Allah ya shiryeka, bafa sadaki nace maka ankai masa ba, neman izinin hirafa akaje nema masa!"
Baki Hayatudden ya turo gaba tare da cewa.
"Duk da haka dai, ai nasan Hammana JARUMI ne Insha Allah bazai taɓa zama LOSER ba, shi zaiyi nasara akan komai!".
Murmushi kawai Ummi tayi tare da fita sha'aninsu, nan suka cigaba da murnarsu shida Raliya suna shewansu, Ummi kuwa Adda Rahama taƙira ta sanar mata, sosai Adda Rahama taji daɗin zancen na Ummi, don itama tana da burin ganin auren ƙanin nata, haka Raihana ma tacika da murna alokacin da Ummi ta sanar da'ita.
Acan G.R.A kuwa su Baffa Ali sun samu isa babban gidan na Baba Malam bisa jagorancin mahaifin Ishaq, suna isa cikin gidan, Wani matashi mai kamala Ya Aminu kenan ya ƙaraso garesu, cike da girmamawa ya basu hannu suka gaisa, nan yayi musu jagora zuwa babban falon Baba Malam ɗin, da sallama ɗauke abakinsu suka kutsa kansu cikin falon....!
By
*GARKUWAR FULANI*
8/19/20, 11:30 AM - Ummi Tandama: ðŸ“ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*NAKASA BA KASAWA BACE*
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.