Complete Hausa Novels

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: NAKASA BA KASAWA BACE PART 1.txt

Chapter 12 of 27

*PAGE 12*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Cikin d'an d'aga murya take cewa.
"Zakariyya! Zakariyya!! Zakariyya!!! wlh bana son raini kazo ka bani wayata."
cikin d'aga murya Zakariyya yace.
"Ank'i a bada d'in uwar masifa k'arfinki ya kwata miki aikin kawai ke ba dama mutun ya tab'a woyarki sai kiyi ta rashin mutunci."
dariya Imran yayi tare da cewa.
"Yaseen yau sai mun zuk'e cajinki."
dai-dai lokacin ta fito daga ganinta yayar Zakariyya ne dan suna d'an kama kekyawace ajin forko tanada cikar sura,
idanu ta zubawa Hayatuddeen da yake kallonta tare da cewa.
"Wannan itama irin Raliya ce ko sai hegen masifa."
Zakariyya ne yayi dariya tare da cewa.
"Haka suke dan sun samu sun fimu da sharu uku zuwa hud'u kacal sai sukeji kamar sune suka haifemu."
da sauri ta iso ta wabce wayarta dake hannun Imran kana tace.
"Hegu kawai masu jajayen fuskoki."
cikin tsiya Zakariyya yace.
"Shima samune kina bak'in cikin jar fatanmu."
tsaki taja tare da cewa.
"Hauka kawai me abin jin haushi duk kunyi kalar zabiya kuma dai baku fini fari ba."
dariya Imran yayi sannan yace.
"Ke dai dama kina bak'in ciki ace Zakariyya ya fiki kyau."
juyawa tayi tana cewa.
"A ina ka tab'a ganin namiji yafi macce kyau."
cikin sauri Hayatuddeen yasha gabanta tare da cewa.
"Yaseen na miji nafin mace kyau kin ganki duk da kyanki Hamma Saifuddeen d'ina ya fiki kyau, in kin ganshi keda kanki zaki shaida hakan."
bata bi ta kansuba ta shiga cikin parlour inda kakarsu ke kwance tanata raki,
bayanta sukabi da saurinsu suna shiga suka gaida Kaka sannan suka zauna gefen ta. Cikin kula tace.
"Imarana ya gida?."
ba tare da ya juyo ya kalletaba yace.
"Lfy lau Alhamdulillahi Mama tace in gaidaki da jiki."
"Ina amsawa." ta bashi amsa tare da juyawa tana kallon Hayatuddeen da yake nunawa Zakariyya abu a wayarshi tace.
"Kai Hayatu hankalin ka duk yana kan waya, Umminka tana lfy ko."
still idanunshi na kan wayar yace.
"Nace miki ki dena cemin Hayatu, ki cika min sunana Hayatuddeen ko kuma kice min Deen in kuwa Hayatun kike son fad'i to kice Hayat."
dariya budurwannan tayi ganin yadda Tsohuwar taketa buga mishi harara,
Isma'il ma da babu bakin mgna sai murmushi yakeyi
Imran ma dariyar yayi dan da yaji dariyar Budurwar ne yasashi kallon inda take kallo,
d'ago kansu sukayi suma suka kallesu jin dariyar tayi yawa,
Zakariyya ne ya kad'a baki yace.
"Haba dai Inna ai wannan kallo sai ya razanamu, dan Allah ki rage idanunki."
sai ya kuma kalli yayar tashi cikin tsigar tsokana yace.
"Ke ashe ga wacca ta b'ataki da k'uru-k'urun idanu bamu ankara ba."
jin haka ai yasa ta haiyayak'o kanshi wai ya zageta mai k'uru-k'urun idanu,
ita kuwa Inna baki ta tab'e tare da cewa.
"Wannan dokoki na kiran sunanka ai sai 'yan boko ni ba abinda ya shamin kai Hayatu zan kiraka."
dariya yayi sosai jin Imran na ce mata.
"To inna ba sai mu shigar dake makarantarba mu samu ki haddace sunan ba Dukke."
shi kuwa Zakariyya sanin bayanshi Inna takebi yasa ya mik'e yana tarfawa yayar tashi tsiya,
ganin Inna tak'i ta kulashi yasa ta sunkuyo ta zari hand bag nata tare da car key d'inta dake gefen jakar cikin jin haushin tace.
"Yaseen bazan zauna a gidan nan ba,
zan koma gida haka kawai a turoni dan inzo in taimaka miki tunda kin gurd'e kuma kina ganin jikanki ya rainani da yake kin fi sonshi bazaki mishi fad'aba."
cikin sababi irin na tsofaffi masu zafi tace.
"Ki tafi mana kada Allah yasa ki zauna dan ubanki! ai bani na kirakiba ni dama Zahira nace a turo min dan itace mai mutunci,
amman tunda kikace bazaki zaunan ba ni kuwa yanzu zan kira Babanku kina komawa zaki dawo kiyi asaran man motarki kawai."
bata bi ta kan magar tsohuwar ba ta fice abinta,
su kuwa duk bayanta sukabi,
suna fitawa tana figin motarta ta tana shirin barin harabar d'an k'aramin gidan,
Hayatuddeen ne yayi sauri d'aga murya tare da cewa.
"Kadafa ki manta kinada tambarin *L* yaseen ki kula kada kije kiyi ta tambola a titi."
k'ura ta bud'esu dashi kana tayi ficewarta daga gidan.

Su kuwa nan sukayi ta sabgoginsu sai gab da magrib suka fito suka nufi gida duk da akwai 'yar tazara tsakaninsu amman haka suke tattakawa da k'afafunsu har zuwa gida a cewarsu Hayatuddeen yaga garin da kyau,
suna isa gab da gidansu Isma'il ne Imran ya tare machine ya tafi,
shi kuwa Hayatuddeen jan hannun isma'il yayi a kan dole sai suje gidansu a dole ya bishi.

Sannu-sannu su Ummi sun saba da bak'otansu da iyayen abokansu Saifuddeen da Hayatuddeen.

Yau jumma'a shiyasa Saifuddeen bai fita da wuriba,
sai h'ar k'arfe tara ya tashi daga baccin daya koma bayan sallan asuba,
a hankali ya mik'e mik'a yayi tare da yin salati a zuciyarshi,
bathroom ya nufa,
wonka yayi mai rai da lfy kana yayi al'wala sannan ya fito d'aure da towel a k'ugunshi sai d'an k'aramin dake hannunshi bisa bakin gado ya zauna ya fara tsane ruwan jikinshi,
mik'ewa ya kumayi bisa kujerar dressing mirror ya zauna mai ya fara shafawa sannan ya gyara suman kanshi,
mik'ewa yayi zuwa gaban durowar bud'ewa yayi ya zaro wani tattausan yadi mai taushi yadin bak'i ne mai shek'i yanada zanen gidan dara-dara,
sai kuma ya zaro boxer and vest farare k'al-k'al,
a bakin gado ya ajiyesu,
sannan ya kuma dawowa gefen durowar inda takalmanshi ke jere bisa wani kekyawan abin aje takalma wasu fararen takalma ya zaro,
sai ya kuma bud'e d'aya sashin na durowar inda hulunanshi ke jere,
hula zanna bukar ya zaro fara mai ratsin bak'i-bak'i,
kimtsawa yayi cikin kayan da ya fidda d'in,
bayan ya gama sawane ya dawo gaban mirror yana dai'daita zaman hularshi a kanshi,
murmushi yayi wanda har saida dimples nashi suka lotsa shida kanshi yasan yana kama da Abbansu,
ya kuma san Abbansu kekyawane na nunawa sa'a sosai bak'in kayan ya k'ara fito da farin fatarshi ras,
in ka ganshi tamkar balarabe suman kanshi a konce lib-lib a k'eyanshi da gefen sajenshi,
turare ya d'auka ya feshe jikinshi dashi lungu da sak'o,
ido ya lumshe a hankali tare da shak'an numfashi dan jin sassanyan k'amshin turaren dake ratsa mishi jiki da zuciya.
Towel d'in daya ciren ne ya d'auka ya shiga bathroom ya
shanyashi sannan ya fito,
ya nufi parlour.

Ummi kuwa da yaranta duk suna parlour suna tab'a hira,
Ummi na bisa 3 str Hayatuddeen kuma na konce kusa da ita yayi !!! kan tv,
da sauri Ummi ta d'ago kanta ido ta zubawa steps d'in sauk'owa k'asan dan jin takun d'an nata,
murmushi tayi tare lumshe ido kana tana godewa Allah daya azurtata da wannan kekyawa halitta a matsayin d'anta cikin sanyin sauti tace.
"Masha Allah, babana yayi kyau matuk'a gaya."
murmushi yayi shima dan idanunshi na kanta a hankali yaci gaba da tako steps d'in cikin takunshi mai d'arka hankali har ya sauk'o,
gabab da ita yazo ya zauna cikin kurma-kurma ya gaidata.
"Lfy lau Babana ka tashi lfy ko?."
hannunta ya kamo ya manna a habarshi alamun lfy lau Alhamdulillahi.
cikin girmamawa Raliya ta kalleshi tare da cewa.
"Ina kwana Hamma Saifuddeen."
kai ya jinjina mata ta lamun lfy lau,
sai ya kuma kallin Hayatuddeen dake kallonshi yana mirmushi cikin k'aunar d'an uwan nashi, murya a sake yace.
"Barka da jumma'a Hamma." bai jira amsarshi ba yaci gaba da cewa.
"Kayi kyau sosai Hamma na."
murmushi yayi kana ya shafa fuskar k'anin nashi.
Ummi kuwa mik'ewa tayi ta nufi dinning table tare da yafitoshi tai mishi alamar yazo yayi breakfast."
mik'ewa yayi yabi bayanta,

Zama yayi a kujerar dake dab da ita yana kallon yadda taken had'a mishi tea,
tana gamawa ta mik'a mishi sannan ta zubo mishi soyayyan dankali da kwai sai kuma ta jawo wani filet d'in da alamun wani abun zata kuma zuba mishi,
da sauri ya jujjuya mata kai,
tare da mata alamun sauri yakeyi tea d'in kawai zaisha da d'ankalin,
sanin halinshi da halittarshi ta rashin cin abinci da yawane yasata meda filet d'in sannan ta zauna gefenshi yana d'anci suna kuma d'an tab'a hira sauri-sauri ya gama ya sallameta ya fita ya tafi.

Ita kuwa Ummi ta haura sama kai tsaye bedroom nashi ta nufa ita da kanta ta gyara mishi d'akinshi da bathroom da parlour nashi duka ta sassake mishi labuye sannan ta feffesa turaren d'aki mai suna touch me sannan ta rege mishi gudun AC kana ta fito.

Tana sauk'owa taci karo da Hayatuddeen a tsakiyar parlour yanata kiciniyar kwance bel d'in k'ugunshi,
ido ta zura mishi ba tare da ta k'arisa sauk'owanba hakama Raliya ido ta zura mishi,
shi kuwa baima san sunayi ba yana zare bel d'in yayi k'asa da dogon wondon Blue Jeans dake jikinshi ya rage dagashi sai d'an gajeren wondo dake jikinshi, sawunshi ya zare kana ya tsallake wondon inda ya sab'uleshi ya nufi hanyar d'akinshi tare da cilla bel d'in a tsakiyar parlour,
sai kuma ya fara kiciniyar cire rigarshi tare da cewa.
"Nima bari inje inyi wonka dan yau a masallacin fad'ar jiha zamuyi salla dasu Imran dasu Sulaiman Zakariyya shi yace yama je tun d'azu."
tsayawa yayi tare da juyawa da sauri jin Raliya na mishi mgna cikin tsawa take ce mishi.
"Wai kai kam Hayatuddeen wanne irin yarone mara kan gado,
kalli yadda ka watsa mana parlour dan tsabar sakarci da sakalci inda ka cire wondonka nan kake bar mana shi wato kai gaka auta mai buhun sakalci uwar wa zata tattara maka kwamutsan naka to da ka barshi?."
wani dogon tsaki yaja tare da cewa.
"Uwata mana ce miki akayi bani da gatane banza kawai uwar sa ido."
yana fad'in haka yayi shigewarsa d'an k'aramin side inshi,
ita kuwa Raliya taita zumbura baki dan Ummi ta sata tattaramishi kayanshi daya watsar.

Saifuddeen kuwa yana fita yaci karo da Salisu wanda shine ya d'aukeshi suka nufi hanyarsu da zata sadasu da titin tutun wada,
mik'ewa sukayi direct har kusa da mashigar G.S.U cikin nitsuwa Salisu ke draving suna gab da shiga gate d'in.
Jonapwd k'ungiyar nakasassu ta jihar kenan Salisu ya juyo cikin nitsuwa da kula ya kalli Saifuddeen tare da cewa.
"Motocin nan da mukayi mgnarsu last week sun iso jiya,
shiyasa nazo da nufin muje ka gansu ka zab'i kalan da kakeso a ciki,
dan gsky zamanka ba mota baiyiba,
tunda ko bazaka yi tuk'iba zamu iya samar maka amintaccen direba da zai rink'a kaika duk inda kakeso da kai da Ummi kafin Hayatuddeen ya k'ara girma."
murmushi Saifuddeen yayi tare da gyara zamanshi duk da yaga Salisun yayi parking kai ya jinjina tare da rubuta mishi.
"Bank'i shawararku bafa sai dai kuda kanku kunsan cewa yanzu bani da kud'in a k'asa dan na yashe duk asusuna nayi hidimar k'aurannan to kuma bani son abu da bashi."
a take fuskar Salisu ta sauya yanayi,
cikin sanyin sauti yace.
"Bashi kuma! Saifuddeen yanzu ashe dama kayana ba naka bane,
ashe dan ka d'auki mota d'aya rak cikin jerin motoci kusan takwas wanda kaine silar samar min jarinsu sai ya zama wani abu?."
Kai ya rink'a jujjuyawa cikin nuna alamun ba haka bane,
ganin haka yasa Salisu cewa.
"To kada ka sake kiramin kalmar bashi a tsakaninmu kuma ko bakaje ka zab'i kalar da kake soba ni zan zab'a maka da kaina gobe zan kawo maka ita har gida,
kuma in ba matsala a cikin yaran da suke wonke mana motocin akwai wani yaro Sule yanada nitsuwa ya kuma iya tuk'i na mutunci sai ya dawo nan ya rink'a kaiku duk inda kuke buk'ata zai kuma iya kula da shuke-shuken gidan in yaso duk wata ka rink'a biyanshi abinda nake biyanshi,
to dama kullum ina bashi kud'in abinci,
to kaga kai ba sai kayi ta bashi kud'in abinciba sai Ummi ta rink'a zuba mishi shida baba maigadi ko?." ya k'arishe mgnar cikin yanayin tambaya.
kai ya jinjina mishi tare da rubuta mishi.
"To ba matsala kayi yadda kaga ya dace."
cikin jin dad'in amincewar Saifuddeen d'in yace.
"To ba matsala."

Daga nan suka fito suka shiga cikin harabar wurin,
kai tsaye office d'in Ishaq suka nufa,
jin motsin bud'e k'ofarne yasa Ishaq juyawa da sauri sai ya kuma mik'e da sauri jin muryar Salisu,
numfashi ya shak'a tare da cewa.
"Lalle marhabin da manyan bak'i."
jin Saifuddeen ya rik'e hannunshi ya sashi juyawa gareshi tare da cewa.
"Kai amman naji haushi wlh kaga da kazo awa uku da suka wuce da ka had'u da Zaleeha sabuwar ma'akaciyar gidan radio vision FM gombe wacce take gabatar da shirin *Babu nakasasshe sai rago* yau dani mukayi hira na d'an bata tarihin rayuwata ka ko san dole zaka shiga ciki."
shiru yayi jin Saifuddeen ya rufe mishi baki da hannu tare da zaro wayarshi da hannunshi d'aya kana ya rubuta mishi text.
"Kai dan Allah ka huta mana wai bakinka bai gajiya da surutune? to ni ka bani ruwan sha tukun."
da sauri ya zaro wayarshi jin shigowar sak'o yasan Saifuddeen ne ya mishi mgn,
dariya yayi sanda ya karanta kana yace.
"To sarkin k'warafi ga wuri ku zauna."
sai kuma ya d'anyi taku biyu zuwa uku ya isa gaban firiji ruwan sanyi ya d'auko musu sannan yazo kusa dasu,
Salisu kam har yau bai dena mamakin yadda abota ta kasance tsakanin makaho da kurmaba suna kuma fahimtar juna over,
amsar ruwan sukayi saida suka d'an sha sannan suka ci gaba da hira amman banda Saifuddeen dan TV yake kallon tashar Farin wata wanda duk had'e suke da vision sosai ya zubawa TV idanu yana karanta rubutun daya bayyana a fuskar tv inda aka rubuta Babu nakasasshe sai rago, sosai Saifuddeen ya maida hankalin shi kan tv ganin sun hasko fuskar wata kekyawar budurwa mai cikar haiba,
lips d'inta ya zubawa idanu dan yana son gane abinda zata fad'a da kyau,
wani irin sassanyan ajiyan zuciya yayi jin wani abu na yana zirta cikin zuciyarshi har zuwa kwanyar kanshi ganin yadda take motso labb'anta wani sassanyar ajiyan zuciya ya kuma yaja a hankali ya sauk'e jin zuciyarshi na bugawa da sauri-sauri,
wani irin shauk'i ne mai cike da farin ciki ya ziyarci zuciyarshi da gangar jikinshi,
ina ya kasa kauda idanunshi a kanta,
da kyar ya juyo a fizge ya kalli Ishaq da yake tab'ashi yana ce mishi.
"Yauwa Saifuddeen juya ka kalli tv kaga sun fara haska hirar da tayi damu yau da safen,
kaga wannan itace Zaleeha sabuwar mai gabatar da shirin babu nakasashe sai ragon."
da sauri ya maida kanshi ga tv ganin an d'auke fuskarta an haska fuskar Ishaq ya sashi jan dogon tsaki tare da yin mgnar zuci.
"Yauwa kaga wannan surutaccen ya janye min hankali da d'an banzai surutunshi kafin in juyo sukuma sarakan azarbab'i sun cire fuskarta sun hasko min sufkar wannan gardin,
sai ya kuma ja tsaki tare da buge k'eyar Ishaq da yaketa murmushin jin dad'in shirin.
sai kusan 4to5 minutes kafin suka sake nuno fuskarta inda take cewa.
"Eh lallai kam na yarda Nakasa ba kasawa bace, tunda gashi kunayin komai kamar sauran masu cikekkiyar halitta."
tsaki ya kuma ja ganin an kuma nuno fuskar Ishaq,
Salisu kuwa gaba d'aya hankalin shi na kan Saifuddeen d'in dan ya fahimci ya bawa kallon tv mahimmanci a ranshi yace.
"Kamar yana jin me suke fad'i."
sai ya kuma yi murmushi ganin yadda Saifuddeen keta lumshe idanu da sauk'e sassanyar ajiyan zuciya."
a haka dai har aka gama shirin,
sannan suka salami Ishaq suka tafi.

Washe gari kuwa kamar yadda Salisu ya fad'in haka yayi ya kawowa Saifuddeen motar da tayi matuk'ar bawa kowa mamki dan motace ta kud'i kimanin million uku da rabi,
ga kuma Sule direba.

Sosai darajar Salisu ta kuma k'aruwa a idanun makusanta Saifuddeen.

Daga ranar Ahmad kuwa ya kasa ya tsare akan ala dole Saifuddeen ya daina tallan leda,
ruwa da omo kuwa maiso yazo shagonsu ya saya,
haka tasa dole Saifuddeen ya dena yawo a kasuwa yana gararamba,
sai dai ya ajiye yaro d'aya mai wul baro,
wanda yake cika baronshi da leda ya rink'a kaiwa duk costumes d'in Saifuddeen shago-shago suna bashi kud'in ya kawowa Saifuddeen inda shi kuwa yake sallaman yaron da dubu biyu kullum,
haka yayiwa Ado dad'i sosai dan cikin awa uku yake gama raba ledan sannan ya dawo yaci gaba da dakon kayan mutane.

A kwana a tashi asarar mai rai.
Lokacin yaci gaba da tafiya,
tuni Saifuddeen harkalla taci gaba ya gama biyan bashin daya amsa a shagonsu wanda ya cikata ya sayi gidanshi,
ya kuma k'ara sayan wata dalleliyar mota mai d'an karen kyau da tsada.
Ya kuma jonawa Hayatuddeen da Faruq makarantar da suke son,
ya sayawa Hayatuddeen mashin d'in U.D sabuwa dal a leda.
Hayatuddeen kuwa rawan kai sai abinda ya k'aru ya k'ara sabawa da abokanshi su Zakariyya sosai tunda yanzu makarantarsu d'aya kuma duk su hud'u sunada U.D

Sosai Sule direba ya saba da Saifuddeen yana gane body language d'inshi sosai,
duk inda zaije Sule ke kaishi a sabuwar motarshi,
inda ya b'ar d'ayar kuma wa Ummi.

Salisu da Warisu duk sunyi aure,
Ahmad ma an aura mishi Raliya,
kuma suna nan cikin gidan da yake Ahmad bai k'arisa ginin gidanshi ba shiyasa,
Saifuddeen yace to yazo ya zauna a cikin d'aya daga cikin part d'in nan dake sashin daman gidan suna zamansu lami lafiya sai tsananin son haihuwa da Ahmad keyi musamman d'iya mace shiyasa yasa Raliya dole ta rink'a kiranshi Abban Farida kamar da wasa sai sunanshi ya koma haka dan sai ya zama su Ummi dasu Rahma duk haka suke kiranshi.

Salisu kuwa tuni ya d'auko kakarshi Iya shatu ta bar Dukku.

Mudassir kuwa bunsurune na Mamajo fir yak'i maida hankali kan batun aure sai tara buhun 'yan mata.

Ishaq kuwa shima har yau baiyi aureba da zaran an mishi mgnar aure sai yace wai baiga matar data mishi bane,
duk sanda ya fad'i haka Saifuddeen kan ce mishi to wai da wanne idon zaiga matar da zata mishin,
yakanyi dariya yace da idon zuciya zai ganta.

To uban gayya Saifuddeen kuwa tun randa ya fara ganin fuskar Zaleeha a tv Allah ya jarabci zuciyarshi da wata zazzafar k'aunarta mai kashe zuciya da jiki,
Allah da ikonshi kuwa bai tab'a ganinta eyes to eyes ba duk da yanzu yana yawan zuwa k'ungiyar tasu wai ko Allah zaisa su had'u amman ina,
ko dan yawanci Zaleeha k'auyuka takebi tana hira da nakasassunne shiyasa basu fiye had'uwa ba,
amman fa duk ran jumma'a shabiyu da rabi nayi zai kunna tv tashar Farin wata ya kalli program d'inta da take gabatarwa.

Ya kuma ci gaba da sirranta soyayyarshi dagashi sai zuciyarshi.
Duk da a wani sashi na zuciyarshi na tuna mishi irin wahala ko k'alubale da nakasassun kan fuskanta yayin neman aure,
to amman shifa yanada yak'ini a kan kanshi.

Sai dai tun randa ya fara ganinta yanayin rayuwarshi ta canza,
ya zama fitinenne da zaran ya tunata jikinshi ke harbawa shiyasa dole ya fara azumin Mondays and Thursdays, dan rage k'arfin abinda ke addabarsa kamar yadda shariyarmu ta musulunci ta koyar mana.

Raihana Ta Haifi d'anta na miji suna kiranshi Affan.

Adda Rahma kuwa sai yanzu Allah ya bata ciki tun tsowon shekarun da tayi aure,
tuni kuma Ya Adnan ya sayi wani gida a nan layin tudun wada kusa da babban titin da zai ratsa ta gaban babban pharmacy nan na A. A Aliyu pharmacy,
wanda gidan yake gab da gidan da Baba bello ya k'auro.

Ya Adnan kuwa ya k'arbi yar k'anwarshi ya had'a da Adam sun rik'e sun samu yara masu d'ebewa Mamasu kewa tunda dama can mahaifinsu baya raye.

Ganin aikin gidan zaiwa Raliya yawa tayi nata ta dawo tayi na Ummi ne yasa Saifuddeen yasa Adda Rahma ta nema musu mai aiki,
tana taya Ummi aikace-aikacen gidan.

*****
Soisa kasuwancinsu yaci gaba yanzu Ahmad na yawan zuwa legos dasu Onitsha kalaba dan yanzu harda harkan manja sukeyi sosai, yamzu hakama baya garin Gombe tun last week ya tafi Lagos shida Salisu shi kuma ya wuce Cotonou dan dubo wasu sabbin motocin da aka tallata musu,

Bappa Ali da Mudasssir da Warusu kuwa duk sun tafi umrah,
yanzu Bello da sabbin yaran shagon guda biyu da Ahmad ya nemane suke kula da shagon, duk da aiyukan shagon yana musu yawa,
shiyasa time to time Saifuddeen na zuwa ya d'an zauna a shagon.

Su Hayatuddeen kuwa sunata fama da karatun Waec sai gigi da rawan kan sun kusa shiga jami'a.

Raihana ma tazo da ziyara Affan d'inta dan tafi shekara bata zoba sai yanzu.

Yau Alhamis tunda safe Saifuddeen ya shirya ya taho office d'in Ishaq koda yaje lokacin ma Ishaqn baya nan ya shiga cikin G. S. U dan koyar da d'alibanshi, nan ya zauna shi d'aya dan Ishaq ya shaida mishi yau Zaleeha zata zo zatayi hira da masu matsalar spinal cord injury,
shiyasa ya bugo sammako,
koda ya samu Ishaq baya nan bai damuba wayarshi da tv suna d'ebe mishi kewa ganin zaman yayi yawane yasa ya mik'e ya ciro laptop d'inshi da yasa a carji tun zuwanshi, bisa kujerar ya dawo ya zauna ya jingina da jikin kujerar sannan ya mik'e k'afafunshi kan glass stoll dake ganshi, a hankali ya bud'e laptop d'in nashi ya fara duba sak'onnin da Ahmad ya turo mishi kasan cewar a rubuce suke komai ta yanar gizo-gizo tunda baya Magna shiyasa yafi gane yin harkar kasuwancinsa a na'ura sosai ya nitsu ya meda hankalin shi wurin tantance gamayyar kasuwancin shi.

Sai kusan azahar Ishaq ya shigo,
bayan sunyi salla ne sukaci gaba da hira,
ganin har sunyi la'asar bata zo bane yasa ya mik'e yacewa,
Ishaq zaije ya duba baba bello da jiki,
amman zai biyo ta nan wurinshi da haka suka sallami juna,
yana fita Sule na isowa dan ya mishi text akan yazo ya kaishi gidan Baba Bellon.

Motarsu na fita da kamar 5 minutes Zaleeha ta iso harabar wurin.

Direct gidan Adda Rahma ya fara shiga suka d'anyi hira har tana mishi batun aure dariya yayi yace mata auren ya kusa ta shirya.

Daga gidanta gidan Baba Bello ya shiga ya jima suna hira sannan ya amshi takardar maganin da ya Adnan ya rubutawa Baba Bellon ya nufi Kemis d'in A. A Aliyu pharmacyn
yana isa bakin pharmacy d'in yaji an rik'e mishi hannu,
da sauri ya sunkuyo ganin Zeenat ce d'iyar k'anwar Ya Adnan wacce take gaban Adda Rahma,
hannuta yaja suka shiga cikin kemis d'in,
bayan ya karb'in ledan magunguna ya basu kud'insu,
sai yayiwa Zeenat alamun da ta kaiwa Baba Bello mgnin ta kira mishi Sule kuma yazo su tafi,
da sauri ya rusuna gaban Zeenat ganin bata gane body language da ya mataba sai ya rubuta mata a wayarshi ya nuna mata,
murmushi tayi tare da gyad'a mishi kai alamun ta gane.

Daga can bakin Gate d'in Gombe State University kuwa,
a dai-dai lokacin mutanen dake bakin gate d'in duk suka fara kaucewa da sauri dan kauda kansu su tsira da ransu da lfyarsu daga sharrin Dalla...!

Wasa farin girki, wannan shine ma somin lbrin mun gama shimfid'an lbrin sai kuma shiga cikin ainin zaren lbrin kada ki/ka sake a baki/ka lbri, kada ayi babu ku!!

By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 26/2 2020...! 8:06 PM

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.