Complete Hausa Novels

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: NAKASA BA KASAWA BACE PART 1.txt

Chapter 24 of 27

*PAGE 24*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Da taga ya juyo fuskarsa ya fuskanci Hayatuddeen,
ba zato ba tsammani taji bakinta ya furta.
"Masha Allah. Allah tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai da yayi wannan hallitar kana ya wanzar da kwarjini a kanta."
gashin girarshi ta zubawa idanu ji takeyi tamkar ta kai yatsarta manuniya kan zirin girar nashi.
Shi kuwa Hayatuddeen cikin sangarcin da yake zubawa d'an uwan nashi ya kwab'e fuska tare da cewa.
"Hamma na gaji, wlh tafiyar nan tayi tsawo da yawa."
a hankali ya lumshe idanunshi wanda hakan ya basu damar hade gashinsu ya kwanta lib bisa kwarminsu,
harshenshi ya d'an zaro a hankali ya lashi jajayen labbanshi,
damshi yawun daya shafa musu ne ya basu damar Shek'i.
Hannun shi yasa ya jawo Hayayuddeen ya mannashi da k'afad'arshi kana ya fara d'an bubbugawa alamun ya huta.
Duk abinda sukeyi idanunta na kansu.
sam bata luraba da wayarta dake zamewa sai da taji sautin fad'uwan wayar,
wanda ya jawo hankali Hayatuddeen har ya rigata sunkuyowa ya d'auki wayar da ta fad'o a d'an zirin tsakiyar hanyar da ake wucewa.

Wanni lallausan murmushi tayiwa mishi lokacin daya mik'a mata wayar tare da cewa.
"Kud'in ki million d'aya!."
amsar wayar tayi tare da cewa.
"Kud'in me fa?".
Cikin yanayinshi na calikanci dayin wasa da kowa yace.
"Kud'in kalle min kekyawar fuskar Hamma na mana."
Itama dariya tayi cikin jin dad'i tace.
"A a kune dai zaku biya kud'in darajar idanuna da suka kalleshi,
ladan jamin hankali da yayi da kekyawan sajenshi."
ta k'arishe mgnar da d'an k'arfi wai dan ya jita ya juyo.
murmushi Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Hayatuddeen Muhammad Ahmad Dukku."
kai ta jinjina tare da yin fari da ido kana tace.
"Sunan babba ake fara gabatarwa."
gane nufinta ya sashi gyara zama tare da cewa.
"Darajar mai sunan da sunan yafi k'arfin a badashi kyauta har sai in anyi baranshi, to nan muna badawa sadakanshi."
Sosai take matuk'ar jin dad'in hirarta da yaron mai d'an karen surutu da iya sarrafa harshe.
Fuska ta kwabe tare da cewa.
"To ina bara, duk da nasan shima da kanshi ai zai al'fahari da hakan."
cikin tab'e baki yace.
"No shi ba kamar kowa bane, na tabbatar baki taba haduwa da irinshi ba kuma bazaki tab'aba ,
tsadar muryarshi yafi farashin tsadar ruwan sanyi a zazzafar sahara."
hannu tasa ta dake kanta tare da kai kallonta jikin windows d'in jirgin tana ganin yadda suke ratsa gajumare,
a hankali tace.
"Kana ji da Yayankan nan, ji yadda kake rowar sunanshi."
murmushi yayi mai kama da dariya kana yace.
"Saifuddeen Muhammad Ahmad Dukku."
wata sassanyar ajiyar zuciya ta fesar tare da cewa.
"Saifuddeeeeeeeeeeen sunan ya dace da kekyawar halitta."
kai ya gyad'a mata alamun yasan haka.
juyawa tayi ta d'an kalleshi kana tace.
"Asma'u Ahmad Matawalle."
gyad'a kai Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Na sani, ai ko ledan pure water yafi sunanki tsada da, da buya."
ido ta zuba mishi cikin wani yanayi mai wuyar fassara,
sai kuma tace.
"Yaushe kuka shiga India?."
ba tare da ya kalleta ba yace.
"Last year."
da sauri tace.
"Karatu kukeyi a can ne?."
Kai ya jujjuya mata tare da manna kanshi a kafad'an yayan nashi kana yace.
"Jinya dai mukaje."
cikin sanyi tace.
"Ayyah waye mara lfyan."
da hannu ya nuna mata Saifuddeen wanda hankalin shi ke kan jaridar hannunshi.
ita kuwa cikin mmki ta tambayi meke damunshi,
Hayatuddeen aku sarkin zance tuni ya fesa mata labarin ciwon Hamman nashi.
Tuni hawaye ke kwaranyowa bisa fuskarta, harda ɗan sheshesƙa
Da sauri Hayatuddeen ya d'ago kanshi tare da cewa.
"Gsky dole kiyi tacin kud'i a fims da wanna saurin hawayen naki haka."
ina Hayatuddeen fa bazai gane bane, bazai san ya taji Saifuddeen a rantaba.
A hankali dai sukaci gaba da hira har sukayi musayen phone number,
ta kafa ta tsare tana son ta kalli fuskar Saifudddeen Amman ina domin hankalinshi baya kansu.

Abuja
Amina kuwa bakin da tayine ya hanata damar sake kiran Hayatuddeen.

Gombe
Bayan ta tashi daga baccin, sai ta d'ora daga inda ta tsaya.
Tayi kukan mai isarta tanayi Maryam na tayata,
Zahira kuwa itace ta shiga kitchen da Mamansu.
Bayan sun gama aikin lunch Zahira ta kai na Baba malam dasu Ya Ahmad da ya Aminu,
sai kuma tazo ta d'auki na Mamy ta kai mata.

Ita kuwa Mama tana fitowa kitchen kai tsaye d'akin Zaleeha ta shiga.

A bakin gado ta zauna tare da juyawa ta fuskanci yaran nata cikin sanyi tace.
"Zaleeha!." kanta ta d'ago kana ta zuba mata jajayen idanunta,
hannunta ta kamo cikin yanayinta na fuskar bosawa tace.
"Meyasa kika zabi ki azabtar da kanki a kan gaibu, abinda baki da tabbaci a kai?
Menene nak'asun Abdussalam? Meyasa bazaki zabi inda zakije ki hutaba Meyasa kike son tayarmin da hankalin? Kinfa san halin Babanku da kafiyar tsiya,
kinga dai yadda ya min a auren Maryam? Kin kuwa sani bazan lamunci ayi miki auren doleba koda ko hakan na nufin zan rabu da mahaifinku,
meyasa zaki tasani gaba kina kuka?
kiga yadda kikasa Maryam shiga tashin hankali."
a hankali ta mik'e zaune kana ta share hawayenta sannan tace.
"Please Mama kiyi wani abu mana, a barni in fito da zabina a hankali,
ni bana son Abdussalam,
yana da k'afafa da al'fahari da kud'i yana jin kanshi shi wanine."
kai ta jinjina tare da cewa.
"A a Zaleeha ki ma bar kushe Abdussalam, kadafa ki mance k'anin aminiyata ce."
A hankali Maryam tace.
"To menene aibun Raveel?."
da sauri Mama ta had'e fuska tare da cewa.
"Me kuma Raveel waye shi wannan yaro mai kama da gurgu yana tafiya yana d'ink'isa kafa,
Surkina musaki ina ai Raveel bayama cikin layi,
Yaronda shine gatan danginsu babu wani ficeccen mai kud'i a ahlinsu."
cikin jin dad'i an yakice Raveel Zaleeha ta gyara zamanta,
ita kuwa Maryam cikin sanyin sauti tace.
"Sanya getzner rik'e babbar waya, yin karatu a kasar waje,
shiga manyan motoci. duk basu ake bincikawa a neman aureba a musulunce,
Addininshi da asalinshi sana'arsa nasabarsa.
sune abin bincika Mama."
wani dogon tsaki taja tare da hararan Maryam kana tace.
"Kin san ai ni tubebbiya ce, gwara kimin nasiha yar malamai."
Da sauri ta fara jujjuya kanta cikin tattausan lafazi da biyayya tace.
"Afwan Mama ba haka nake nufiba ki gafarceni in furucina ya b'ata miki rai na tuba ki yafe min."
kai ta gyad'a tare da cewa.
"Na yafe miki."
dan tabbas tasani Maryam d'iyace irin wanda ko wacce uwa ke fatan samu,
matsalarta komai sai tace zata mata wa'azi shike had'asu.
Daga nan tasa Zahira ta kawo musu abinci suka ci.
suna zaune a wurin suka jiyo muryar Zakariyya yana cewa.
"Mama! Mama!!."
bata kulashi ba har saida ya shigo cikin had'e fuska tace.
"Sai shegen yawan kira kamar mafarauci ko tsohon makaho."
Murmushi yayi kana yasa hannu ya amshi spoon d'in hannun Zaleeha tare fara cikin abincin saida ya had'iyi lomar da yasa a baki sannan yace.
"Da Hajja Inna mukazo shine Baba malam yace inzo in gaya miki kije ku gaisa."
Tsaki ta d'an ja kana ta gyara zamanta tare da cewa.
"Ziyada fa bada ita kuka zo bane?."
kai ya gyad'a mata alamar eh sannan ya kalli Zaleeha cikin tsokana yace.
"Amaryar watan gobe har kin fara tunanin auren ne haka?."
duka ta kai mishi tare tura baki.
Shi kuwa ganin yadda Zahira ta zuba mishi idone ya sashi danna mata tsawa.
"Ke me haka kike ta kallona kamar tsohuwar mayya, muna fuka kawai."
tura baki tayi kana ta kauda kanta sam shi baya shiri da ita.

Sunan zaune suka jiyo muryar ya Ameenu yana cewa.
"Kai Zakariyya fito ku tafi."
Da sauri ya mik'e ya fita.
Jin haka yasa Mama mik'ewa tabi bayanshi hakama, Maryam da Zaleeha.

Suna shiga parlour Baba malam suka sameshi zaune gaban mahaifiyar tashi tamkar yaro k'arami shi kuwa Ahmad na zaune a gabanshi,
bisa dukkan alum farce yake yankewa kakar tasu
Habu kuwa na gefensu.

Suna shiga ta kalli Maryam cikin son jikar tata tace
"Ah Maryama dama kina cikine?."
cikin nitsuwa tace.
"Eh Hajja inna ina ciki salla nakeyi sanda Zakariyya yaje kiran Mama."
"Ayyah." tace da ita tare da kallon Zaleeha cikin yar tsamarsu tace.
"Rasa kunya berar tanka uwar kid'e-kid'e, ke ba abinda kika iya sai rawa da wak'a da kid'a ko."
Baki ta murguda mata tare da watsa mata harara.
cikin zaro ido tace.
"Iye ni kikewa wannan kallo lallai wannan yarinya in ba'a aurar da keba to tabbas zaki tashi gari,
hegiya mai zubin nasara."
Sai ta kuma juyo ta kalli Mama data tab'e fuska ko gaisheta batayi.
kwaffa tayi kana ta kalli d'an nata sannan tace.
"Kai Bashiru wlh infa kana son tsira da mutuncinka to ka aurar da wannan fitinenniyar yarinyar.
In ba haka zataci gaba da worwore maka tubkar da kakeyi.
Kullum kana kan hanyar zuwa gidan radio kana shirin tafarkin tsira al'ummar musulmai na k'aruwa da kai.
Abin takaici ana gama shirinka sai a sako shirin wannan dujaliyar yar taka wai mushak'ata,
haka zatayi ta zubawa wak'ok'i ka jita tanabin waken tamkar zabiya."
duk shiru parlour sukayi sai Zakariyya dake cewa.
"Ni dai da zata amshi shawarata ta dena bin wak'ok'in tana hanamu jin abu d'aya. Mu jita ko muji radio."
Da sauri ta gyad'a kai tare da cewa.
"Uhun ai dai kunji ko?."
shi kam Ahmad da Habu sai murmushin sukewa inna boris.
Ya Ameenu kuwa sai harara yake watsawa Zaleeha.
cikin muryar jin haushi Mama tace.
"Inna an wuni lfy?."
A hatsale Inna tace.
"Lau na wuni! gsky ce dai sai na fad'i ehe!."
Dariya sosai Ahmad yayi yayinda Baba malam ya murmusa.
ita kam Zaleeha ficewa tayi abinta,
ita kuwa inna sai cewa tayi.
"Dama iyayen yara sunfi son marasaji,
shiyasa take son Zaleeha kamar ranta bata son laifinta.
Kuma dole in fad'i dan ba yadda za'ayi in haifi d'ana malami ke kuma kizo ki haifa mishi zabiya, amara k'irjin biki."
Su duk dai ba wanda ya kuma mgn,
shigowa Mamy ne da kulan soyayyun kaji yasata washe baki tare da cewa.
"Allah dai ya miki al'barka Mamyn Ahmad."
Cikin sanyi Mamy tace.
" Amin Amin ." dan ita dai bata fiye son abinda inna kewa Zaleeha ba,
dan ita tana matuk'ar son Zaleeha kuma itama Zaleeha tana matuk'ar sonta.
Ido suka zuba mata ganin ta mik'e tare da cewa Zakariyya.
"Shalele na maza tashi mu tafi."
da sauri ya amshi kular sannan Suka fito,
suna zuwa parking lot nasu Baba malam yace.
"Inna muje in maidaki."
da sauri tace.
"Lalala bari a machine d'in Shalele na mukazo,
kuma a kanshi zamu koma."
Cikin tsoro baba malam yace.
"Inna a machine kuwa, to Ahmad ya maidaki ko Ameenu."
Kama hannun Zakariyya tayi tare da cewa.
"Muje ko Shalele yaro yana jin dad'in yau na hau machine d'insa kuma shine zaku hana."
Habu ne yayi dariya tare da cewa.
"Allah sarki watarana sunan hak'oranta babu."
Mamy ne tayi mushi dak'uwa su kuwa jikoki suka k'elk'ele da dariya.

Koda suka koma cikin gida Baba Malam da Ameenu da Ahmad da Habu mgnar Zaleeha sukaci gaba da d'an tattaunawa inda shi Ahmad yaje jaddada musu wai al'janine.

Jirgunsu na sauk'a a Abuja.
Ya Rabi'u da kanshi yazo ya d'aukeshi dan acan zasu kwana sai da safe zasu samu jirgin Gombe.

Sosai suka samu kulawa da karramawa ta musamman a wurin Aunty Mami.

Inda tayi tayiwa Hayatuddeen tsiya wai ya zama ba'indiye.

Washe gari k'arfe tara na safe jirginsu zai tashi.
So tun bakwai da rabi suka fito kai tsaye asibitin su Dr Aliyu sukaje.

Sosai fa Dr Aliyu yaji dad'in ganin Saifuddeen ya fara samun lfy,
Dr Batulu kuwa saida akayi mata kwatancenshi sannan ta tunoshi dan da fari tayi zaton ko ba indiye ne yazowa Dr Aliyu ziyara.

Karfe tara dai-dai jirginsu ya d'aga zuwa Gombe doma.

A hankali Hayatuddeen ke tura weelchair d'in da Saifuddeen ke zaune a kai,
cikin shiga ta alfarma,
wani dakekken yadine mai tsananin azabar kyau blue irin blue mai hasken nan sai ratsin d'igo-d'igo yellow irin yellow mai d'an duhun da za'a iya cemai ruwan k'asa.
Sai wata dakkeyar hukar damanga mai azabar kyau shina irin kalan kayanshin sai kuma takalminshi sau ciki suma kalar yellow mai d'an duhuwa,
sai agogon Gucci na fata shima kalan takalmansa,
ya kafa hular tayi ras a kanshi,
Sajenshi ya konta lib wanda hakan ya k'ara k'awata kekkyawar fuskarsa farar fatarshi ta k'ara baiyana red lips É—insa suka kara yin kyau cikin zagayen saje da kota million dake fuskarshi.
Shi kuwa Hayatuddeen wasu k'ananun kaya yasaka masu azabar kyau.
Tura weelchair d'in yakeyi a hankali da hannu d'aya,
yayinda d'aya hannun kuma ke janye da trollinsu.
a d'aya sashi kuwa ma'aikatan jirginne ke turo sauran kayan nasu wanda yake hade da wani weelchair d'in a ciki da dai sauran abun buk'a tunsu.

A hankali iska mai sanyi ke ratsa jiki da zuciyar Saifuddeen.
Tasbihi yakeyi ga ubangijin talikai daya sake nufarsa da dawowa k'asarsa jiharsa ta haihuwa wacce lokacin d'aya barta baisan inda yake bama tsawon shekara d'aya kenan dayawuce.

Isakar ya kuma shak'a tare da lumshe idanunshi yana maijin wani yanayi mai kashe jiki.

Suna isowa inda masu tarbarsu suke,
Kamar daga sana Hayatuddeen yaji an ruggumeshi ta baya,
da sauri ya juyo tare da sakin weelchair d'in ,
ganin Raliyya da Faruq ne ya sashi hadesu da jikinshi cikin tsananin jin dad'i,
jin sun sakeshi ne yasashi binsu da ido ganin inda suka nufa,
Adda Rahma ne sunkuye a gaban Saifuddeen dayi mishi wata iriyar rugguma ta yan uwa na jini,
madadin tayi mgna ina sai murmushi takeyi ga kuma hawaye nata kwaranya a idanunta.

Hakama Rainaha sarkin kuka tuni ta kasa isowa inda suke sai wani irin sark'ekk'en kuka da takeyi.
Ahmad kuwa wayarshi ya zaro yanata yi musu hoto a cikin duk motsin da sukayi,
ganin yadda Raihana ke kuka yasa Saifuddeen mik'o mata hannu,
aifa da gudu ta iso inda yake kawai sai ta durkusa dirsham har k'asa ta kafa guiwowinta kana ta kifa kanta bisa cinyarshi tare da yin zazzafan kuka,
kawai duk sai suka had'e kai a wurin.
Suna kukan farin ciki da tausayawa d'an uwansu.

Salisu ne yayi saurin isa inda suke ya janye Hayatuddeen da Faruq,
yayinda Ahmad kuwa ya janye Raliyya,
Ya Adnan kuwa ya gaza ce musu komai,
Ishaq kuwa, yana zuwa ya ruggume abokin nashi,
ganin airport d'in yayi musu kad'an wurin farin cikinsu yasa suka,
shiga motocin suka tafi,
Adda Rahma kam fir taki yin nesa da k'aninta a motar ya Adnan suke ita da Saifuddeen suna baya,
Ishaq kuma na gaba.

Hayatuddeen kuwa da Faruq da Raliya motar ya Ahmad suka shiga.

Salisu kuwa kuwa shi ya kwashi kayansu shida Raihana.

Daga airport zuwa cikin gombe akwai yar tazara,
so tafe suke suna hirarsu ta yan uwa shak'ik'ai.

Cikin tsananin mmki Hayatuddeen yake baza ido lokacin da suka shigo cikin gari sabida,
Sosai yaga sauye-sauye a garin.
Hakama da suka iso gida Saifuddeen da kanshi yayi mmkin ganin zubi da tsaruwar gidan,
Komai yayi shar tsirran da shuke-shuke sunyi lip-lip gwanin sha'awa.

Anayin parking Hayatuddeen ya fita da sauri, kai tsaye cikin gidan ya nufa a guje.
Ya Adnan kuwa yana fitowa ya bud'ewa Saifuddeen k'ofa kana ya bude but d'in motar ya fito da weelchair d'in.
A gab da kofar motar ya ajiye kujerar, yayinda tuni Adda Rahma da da Ishaq suka fito.
Hakama su Raihana ganin duk sun zagayeshi sun mishi zobene,
yasashi lumshe ido kana ya zuro k'afafunshi wojen tare dasa hannunshi ya dafa gefen motar sannan ya yunk'ura ya taso cid'ak cikin azama da jarumta da zafin nama ya zauna bisa weelchair d'in.
Wani irin nannauyan ajiyan zuciya Adda Rahma ta sauk'e da tsananin k'arfi dan da gani take kamar bazai iyaba.
Faruq kuwa da sauri ya tsuguna ya saita matakalar kujerar,
wani lallausan murmushi Saifuddeen yayi kana da taimakon Ahmad ya d'aura fararen sawunshi kan abin takawan.
Salisu kuwa tuni ya firfito da kayayyakinsu ya nufi cikin gida dasu.

Shiko Saifuddeen girarshi d'aya ya d'agawa Ahmad alamun tammayar ya dai ganin duk sun tsaya a kanshi.
Cikin tsananin tausayi da k'aunar d'an uwan nashi yace.
"Ai kaine jagoran."
lip inshi na k'asa ya d'an tauna ta gefe kana yasa hannunshi ya share hawayen dake bin fuskar Raihana sannan yasa d'aya hannunshi dai-dai wurin masarrafin weelchair d'in ya d'an daddana wasu madannai sai ga keken ya fara tafiya a hankali.
da sauri sukabi bayanshi.

Da sauri ya danna wani pin d'in sabida ganin Baba Ado mai gadinsu da Sule direbanshi sun rusuna gabanshi.
Sam sule ya gaza tsaida ruwan hawayenshi dan kamar yau yana tuna randa sukayi fitarsu ta k'arshe in da uban gidan nashi ya taka da sawunshi,
sai gashi cikin shekara d'aya ya zama bashi da damar tsayuwa.
kai ya d'an jujjuya musu alamun suyi hak'uri su bar kuka.
da kyar suka iya tsaida hawayensu kana suka mushi sannu da hanya da fatan samun lfy.

Hayatuddeen kuwa yana shiga parlour yayi tsalle ya fad'a kan kujera 3 str gefen Umminshi sai ya kuma ruggumota ta baya tare da cewa.
"Wayyo dad'i yau gani ga Ummi na."
Sosai Ummi ta ruggume autan nata tana maijin son yaran da begenshi.
Goggo Dada ce ta kalleshi cikin son yaran d'an uwan nata tace.
"Wato Umminka kawai ka gani ko?."
Da sauri ya juya zuwa gareta.
Dai-dai lokacin kuwa su Saifuddeen suka shigo,
wani irin farin cikine mara misaltuwa ya rufe Ummi wanda ta kasa koda motsa yar yatsarta,
sai bugawa da zuciyarta keyi da k'arfi-k'arfi.
Shikuwa Saifuddeen k'ara gudun weelchair d'inshi yayi ya saitata gaban Ummi.

Yana isa inda take gab da ita tayi saurin mik'o mishi hannu,
da sauri ya kamo hannun nata duka biyu kana ya tallabe fuskarshi dasu,
haka nan rauni zuciya suka rintsa mishi zuciya bai taba zubda k'walla akan wannan larura tashiba sai yau.
Kawai sai yaji wasu zafafan hawaye suna kwaranyo mishi,
da sauri ta mik'e tsaye ta matso gab dashi hakan ya bashi damar sahannunshi duka biyu ya ruggumeta tare da manna kanshi a cikinta,
wani sautin kuka mai cike da raunin d'a a gaban mahaifinshi ya sake.

Tuni itama Ummi kukan takeyi tamkar zata shid'e,
Raihana kuwa kife kai tayi bisa cinyar goggo dadansu tana kuka da majina.
Yau Adda Rahama mai dauriyarma kuka takeyi wi-wi.
Raliya kuwa jikin mijinta ta fad'a cikin rauni take cewa.
"Ya Ahmad kace suyi shiru, ya zamuyi da k'addararmu da munada dama da tuni mun canza k'addarar Hamma Saifuddeen."
ina shima kanshi Ahmad hawaye yakeyi.
Ya Adnan ne yayi k'arfin hali cikin d'an d'aga sauti yace.
"Kiyi hak'uri Ummi, addu'a shi ya dace da Saifuddeen ba kukaba,
da ace kuka na mgni ai da tun kan yau Saifuddeen ya worke."
A hankali Ummi ta gyad'a kai kana tasa hannu ta d'ago kan Saifuddeen.
murmushi tayi mai had'e da hawaye hannu tasa ta share mishi hawayenta.
cikin rawan murya tace.
"Baba kada ka mance furucin yayanku, koda ya mutu baya raye ai furucinsa bai mutuba."
rimtse idanunshi yayi da k'arfi kana ya bud'esu a hankali.
kafad'unshi ta dafa cikin tausasa lafazi tace.
"Ae ita Nakasa ba kasawa bace.
Da nakasarma ka zame mana jigo garkuwa gata a garemu, ka meyewa k'annenka gurbin uba ni ka zame min uwa uba yaya k'ani d'a kuma abokin kukana."
kai ya jinjina mata alamun gamsuwa,
Goggo Dada kuwa Raihana ta lallasa kana Ya Adnan yayi musu nasiha mai ratsa jiki,
daga bisani yayi addu'ar samun lfy ga Saifuddeen sannan shida Salisu suka fita suka tafi.

Ummi kuwa da kanta ta mik'e taje kawowa Saifuddeen ruwan sanyi,

Bayan yasha ruwan ne duk sun gaggaisa,
tare da mishi sannu da hanya,
sukaje Dinning table sukayi breakfast dan suma gidan duk babu wanda yayi karin kumallo.
Sosai suka cika musu gaba da abubuwan ci da sha namusammam.
Ummi da kanta ta zubawa Saifuddeen tuwon farar d'anyan shinkafa,
miyar zogale wanda yasha man shanu da kifi da busasshen nama,
cikin kula Ummi tace.
"Nida kaina nayi maka girkin dan nasan kayi begen miyar da ita kafi so."
murmushi yayi tare mata alamun godiya da jin dadi kana ya fara cin abincin da yayi begenshi sosai.

Hayatuddeen kuwa couscous da miyar hanta Adda Rahma ta sa mishi.

Ummi kam ji takeyi kamar ta bawa Saifuddeen abinci a baki sabida yadda yakeci wanda dama halittarsa kenan rabin malmalan yaci,
kana ya cire hannunshi tare da jawo jug d'in damemmiyar fura da nono mai sanyi da zuma,
da Sauri Goggo Dada ta tsiyaya mishi a kofi ta mik'a mishi.
Hayatuddeen kuwa kular pepper chicken ya jawo kamar kura yayi ta yagan cinyoyin kaji saida yayi hanik'an sannan ya mik'e ya koma tsakar parlour.

Su kuwa su Ummi babu wanda ya iya cin komai saida sukaga Saifuddeen ya k'oshi,
sannan sukaci,
suna gama duk suka dawo parlour akaci gaba da hira.

Suna cikin hirar Bappa Ali da Malam Ashiru da Baba Hamisu suka iso.

Nan kuma aka gaggaisa tare da yiwa juna barka,
karshe dai su Ummi d'akinta suka koma d'akinta.
Dan Su Mudassir, Jabeer, Hisham, Kabiru, Salisu, Ishaq, Ahmad.
Kusan duk nan suka wuni yayinda Saifuddeen ke zaune a tsakiyarsu bisa weelchair d'inshi da system nashi a cinyarshi wanda dashi yake bawa kowa amsar mgnar da zai mishi.

Sune basu tafiba saida akayi sallan azahar.

Bayan sallan la'asar Salisu da Ahmad suka meda Goggo Dada da Aunty Nina dasu Bappa har cikin Dukku sannan suka dawo.

Suna isa ana kiran sallan margin.
Bayan anyi sallane duk suka cika a parlour Ummi,
nan sukayi dinner,
kana suka dawo tsakiyan parlour suna d'an tab'a hira, ganin isha ya kusa ne Salisu ya mik'e ya tafi da Salima kana Ahmad kuma ya maida Adda Rahma da yaranta.

Koda kuwa suka tafi ci gaba da hira dasu Rahma,
cikin kula Hayatuddeen ya kalli Hamman nashi a hankali yace.
"Hamma Saifuddeen lokacin baccinka yayi fa."
Kanshi ya gyad'a alamun to.
Kana ya kalli Umminshi da k'annen nashi kana yace.
"Bari inje in d'anyi wonka kana inyi bacci."
Duk cikin body language yayi mgnar fahimtar hakanne yasa sukace to.
Ganin ya juya akalar weelchair d'inshi ya nufi side d'inshi da aka gyara mishi kuma aka nuna mishi tun kafin ya dawo.
Dan haka kai tsaye ya nufi parlour.
Ummi ce ta kalli Hayatuddeen tare da cewa.
"To kuma kana zaune?."
Gyara konciyarshi yayi tare da cewa.
"Ummi ai da kanshi yakeyiwa kanshi komai ba, ruwan wonka kuma Adda Rahma ta had'a mishi."
kusan a tare sukace.
"Har wonkan?."
Kai ya gyad'a musu tare da cewa.
"Harda canza kaya da shirya kanshi da komi da komai yanawa kanshi."
wannan labarin yayi matuk'ar sasu cikin tsananin farin ciki.

Shi kuwa Saifuddeeen yana shiga parlour nashi,
wani sassanyan ajiyan zuciya ya dire dan daddad'an sanyi da k'amshin da yaji yana ratsashi.
a tsakiyar parlour ya d'an tsaya ya karewa komai na parlour kallo,.
"Da kyau." yace a ransa kana ya wuce cikin bedroom yana shiga kai tsaye bakin gadon ya nufa,
ido ya dan lumshe tare da yin luuu dasu,
dan ya fara jin bacci,
rigarshi ya fara cirewa iska ya fesar a hankali jin daddad'an sanyi da k'amshi, k'afafunshi ya dire bissa tattausan carpet dake gaban gadon,
singlet d'inshi ya zare tare da ajeshi kan gadon a hankali ya ja ta zugen shi ya kunceshi soko-soko hannunshi d'aya yasa ya d'an danne bakin gadon yadda ya samu ya d'an d'aga mazaunanshi kana yasa d'aya hannun yayi kasa da dogon wondon saida ya kawoshi har guiwanshi sannan ya zauna, tare da sunkuyowa ya cire wondon baki d'aya.
Ya rage boxer ne kadai a jikinshi,
A hankali yayi mik'a mai cike da sak'onni a jikinshi,
"Hoooohhh." ya bada sautin tare da sunkuyar da kanshi murmushi yayi ganin yadda bananarshi ta harba tayi sama sam b'al...!

To Gafa Saifuddeen ys dawo ga Zaleeha ga Amina ga Mama gasu Raveel da Abdussalam ƙaƙa tsara ƙaƙa wadin Zaleeha saura kaɗanfa hmmm

By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:53 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

        *NAKASA BA KASAWA BACE*

                           *PAGE 25*

                   *NA*
*AISHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Ahankali weellchair ɗin nasa ke tafiya har zuwa bakin bathroom, hannayensa ya sanya ya tura ƙofar bathroom ɗin, tare da ɗan sake danna wani madanni dake jikin wellchair ɗin, take yaci gaba da tafiya.
   Saida ya ƙaraso har tsakiyan bathroom ɗin sannan ya tsaida  keken nasa, ahankali ya ɗaga idanunsa yana me ƙarewa cikin bathroom ɗin kallo, sosai aka ƙawata bathroom ɗin, komai tsab-tsab yayinda aka sauƙaƙa masa komai ta yanda zaiyi amfani da komai cikin sauƙi batare da ya sha wahala ba, inda akayi masa wani ɗan igiya kusa da toilet ɗinsa yanda koda zai zauna akai basai yasha wahala ba, haka wajen da zaiyi wanka ma anƙawata masa shi inda akayi masa komai asauƙaƙe,       Madannin kekensa ya danna tare da ƙarasawa wajen da zaiyi wanka inda aka kewaye wajen da wani haɗaɗɗen glass,  cikin nutsuwa ya zare boxer ɗin dake jikinsa tare da yunƙurawa ya sauƙa akan kekensa cikin tsananin shauk'i ya zauna acikin bathtube ɗin wanka, wanda cikinsa ke cike da tsabtataccen ruwa,  ahankali yazame yaɗan kwantar da jikinsa acikin bathtube ɗin yayinda gaba ɗaya ruwa ya haura saman jikinsa, iya kai da ƙirjinsa kawai ake gani,  kansa ya jingina da jikin bathtube ɗin tare da lumshe kyawawan idanunsa, wani irin abune yaji yana sauƙa ajikinsa mai kama da kasala,  sannu ahankali tunaninta ke ɗauke duk wata nutsuwarsa, idanunsa cike suke da ɗoki da kuma son sake ganin kyakkyawar fuskarta,  har yanzu yakasa manta yanda tattausan hannunta daya taɓa jikinsa, sannan kuma har yanzu  ya kasa manta kyakkyawan hug ɗin da ta bashi alokacin da take roƙonsa da yazo su gudu lokacin da yaran Dalla ke shirin cim musu,  wani irin abune yaji ya taso masa daga kansa har zuwa ƙasan ƙafarsa, ahankali yasake gyara kwanciyarsa acikin ruwan yana mejin wani irin fitinanniyar sha'awarta na taso masa, yayinda joystick ɗinsa dake cikin ruwa ta tashi tayi tsaye,  shikansa yana mamakin halitta irin nasa.
Ido ya lumshe a hankali ya tuno,
abinda yake faruwa dashi na sha'awa tun randa ta ruggumeshi.
Abinda bai tab'a jiba a tsawon rayuwarshi kafin had'uwa da ita lokacin Yanada shekaru 30 a duniya amman bai taba ji ko ganin gabanshi ya tashi ba, asalima in yaji wuya kad'an gaba d'aya ma gabanshi ke komawa ya lafe ya b'uya yayi lakwas,
musamman in yayi azumi. To amman tun randa suka had'u ya fuskanci cewa yana da wata irin fitinanniyar jaraba mai tada hankali,
  jikinsa ɗin ne yasake harbawa sakamakon tunowa da tausasan laɓɓanta da yayi wanda yaji tamkar alokacinne take motsasu, harshenshi ya d'an turo woje cike da shauƙi yaɗan lashi laɓɓan bakinsa kana ya ɗan buɗe idanunsa wanda suka ƙanƙance kuma sukayi ja, sakamakon wutar sha'awarta dake cinsa arai, 
coming ransa yace.
"Name dawo gareki Zaleeha ina nan tafe, Allah yana sona tunda bai k'addara aurenki cikin shekara d'aya da nayi bana nan d'inba, ya kuma bani damar sanin duk wani motsinki da shiga da fitanki ta sanadin aminine, shiyasa na rayu a india ba fargaba sabida ina jin labarinki wurin aminin da samun kamarshi ke wuya a duniya". Ishaq kensn.
Akasalance yashiga wanke jikinsa domin gaba ɗaya yayi weak, yayinda Saifuddeen ɗinsa kuwa har yanzun taƙi kwanciya, cikin nutsuwa yayi wankansa inda ya wanke jikinsa tsab, daddaɗan ƙamshin sabulun da yayi wankan da shine ke tashi ajikinsa.  Yana kammala wankan nasa yayi alwala, kamar yanda yasaka karsashi wajen shigar da kansa bathtube ɗin wankan haka yanzuma ya saka karsashin wajen ganin ya fito da kansa, wata farar rigan wanka irin ta maza dake rataye ajikin wani ɗan ƙarfe ya ɗauka tare da sanyawa ajikinsa, yana gama dai-dai-ta zamansa akan kekensa ya danna madannin da zai sanya keken tafiya batare daya wahalar da hannayensa ba,  koda yafito daga cikin bathroom ɗin  kaitsaye gaban dressing mirror ya nufa inda ke cike da tsadaddun mayukan jiki da kuma na gashi,  ɗan ƙaramin towel ya ɗauka tare da soma goge jiƙaƙƙen gashin kansa, yana gama tsane ruwan ya ɗauki handrayer tare da jonawa ajikin socket yashiga busar da gashin kansa, mintuna kaɗan kuwa gashin nasa ya bushe yayi wasar kamar ma ba'a samasa ruwa ba, wani body lotion ɗinsa me daɗin ƙamshi ya shafa tare da ɗaukan oil body spray me matuƙar ƙamshi ya kuma shafawa ajikinsa,  cumb ɗinsa ya ɗauka ahankali yashiga gyara haɗaɗɗiyar sajensa wanda tayi matuƙar ƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini dan yadda ya cika yayi lip-lip a farar fatarshi tayiwa fuskar tasa k'awanya, yana kammalawa,
yashafawa kansa wani hair oil me ƙamshi, kekensa ya tura har zuwa gaban tangamemen sif ɗinsa, inda aka jere masa gaba ɗaya kayan sawansa a hawa na ƙasa dana tsakiya wani long jeans black colour ya zaro tare da kai dubansa ɓangaren da t-shirt's ɗinsa ke jere reras, gaba ɗaya kayan sawansa sabine ƙal ƙal, wata white polo shirt ya ciro me kyau,  cikin dabara yasanya wandon ajikinsa tare da zura farar t-shirt ɗin ajikinsa, masha Allah sosai yayi kyau yayinda gashin kansa keta faman ƙyalli, rufe sif ɗinnasa yayi tare da sake tura kekensa ya ƙarasa gaban mirror, farfumed ya fesa ajikin kayan nasa tare da ɗaukan wayarsa,
  tura kekensa yayi ya ƙarasa gaban bedsite carbinate inda anan aka aje masa sallayan yin sallan sa, ɗaukan sallayan yayi tare da shimfuɗawa kasancewar lokacin har ansoma ƙiraye ƙirayen sallan Isha,  cikin hikima ya sauƙo daga kan kekennasa tare da zama akan sallayan,  azaune ya gabatar da sallan isha'ɗinsa yayinda daga ƙarshe ya haɗa da shafa'i da wuturi, akan ƙafafunsa ya zauna inda yajima yana tasbihi,   hannunsa ya sanya ya ɗauko al'ƙur'anin dake aje kan bedsite,  ɗaura ƙur'anin yayi akan cinyansa tare da buɗe suratul Ma'idah ahankali cikin nutsuwa yashiga rera karatun yayinda zazzaƙar muryarsa ke ratsa mishi zuciyarshi, aƙalla ya ɗauki wasu mintuna kafun ya kammala karatun addu'a yayi tare da shafawa kana ya rufe Al'Qur'anin, gadonsa yaɗan dafa tare da jawo wellchair ɗinsa ya yunƙura tare da komawa kai ya zauna, laptop ɗinsa ya ɗauka yashiga duba harkan kasuwancin su, daga nanne kuma yashiga duba labaran halin da duniya take ciki.
Hayatuddeen ne yaturo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama yayinda hannunsa ke ɗauke da ɗan ƙaramin tray wanda samansa ke ɗauke da yankakkun fruits masu sanyi sai goran ruwa mai sanyi kana d'aya hannunshi rik'e da robar magunguna,
ƙarasowa cikin ɗakin yayi tare da duban hamman nasa da gaba ɗaya hankalinsa ke kan laptop ɗinsa, cikin kulawa ya aje tray ɗin akan table d'in glasses dake gaban gadon hamman nasa tare da cewa.
"Hamma kasha fruit inji Ummi,
ga kuma magungunan ka"
ido ya d'an lumshe tare da ƙaɗa kansa alamar to, ɗaukan green apple wanda yake ba'a yanke ba yaɗan gutsura, lumshe idanunsa ya kuma yi tare da soma tauna apple ɗin ahankali,  ganin haka yasanya Hayatuddeen sakin murmushi tare da ɗan matsowa kusa da hamman nashi,  wayars ƙiran Samsung galaxy S10 ya ciro tare da shiga camera, hannayensa ya sanya akan kafaɗun Hamman nasa ya ɗaukesu  hoto selfie wanda dukansu murmushine ɗauke akan fuskarsu, sosai sukayi kyau a hoton bama kamar Saifuddeen,  komawa gefe Hayatuddeen yayi inda ya shiga Whatsapp ɗinsa ya ɗaura hoton nasu da sukayi a status ɗinshi.
Shikuwa Saifuddeen sosai yasha kayan fruits dan shi yafi ta'ammali da yayan itatuwa fiye da abinci, bare kuma yanzu da likitocin suka umarceshi da yawanta cinsu.
Maganinshi ya sha.
ya gamawa sauƙa yayi daga kan wellchair ɗin ya kwanta akan lallusan gadonsa wanda yaji tattausan katifa, luf yakwanta tare da ɗaura kansa akan pillow kana yaja blanket ya rufe rabin jikinsa, ganin haka yasanya Hayatuddeen ɗaukan ragowan kayan marmarin yafice daga cikin ɗakin, ganin fitan Hayatuddeen yasanya Saifuddeen yakai hanunsa saman gadonsa inda anan makunnin wutan ɗakin yake ya kashe, bedsite lamb wanda ke bata light blue ɗin haske ya kunna tare da sake gyara kwanciyarsa, wani irin sha'awane yasake taso masa wanda yasanya ya kasa bacci sai juyi yaketayi akan makeken gadonnasa.

A hankalin Umminshi ta shigo,
taku takeyi a hankali dan ganin alamun yayi bacci,
kanshi ta iso tare da zuba mishi ido,
sai kuma tayi saurin sunkoyowa kanshi jin ya kamo hannunta,
murmushi tayi mishi mai cike da k'aunan gudan jinin nata,
sannan tasa hannunta na dama ta shafa kanshi tare da cewa.
"Ka gaji da yawa kayi bacci ka huta, ko Babana."
kai ya gyad'a mata tare da sumbatar hannunta kana ya maida idanunshi ya lumshe a hankali.
Ganin hakan yasa Ummi gyara mishi blanket d'in daya rife iya k'ugunshi sannan ta fita,
tare da ja mishi k'ofa.
A parlour ta samu Ahmad yanzu ya dawo daga meda Rahma gidanta,
Ganin kamar yana buk'atar matarshi ne yasa Ummi cewa Raliya.
"Ke Raliya dare yayi ni zanyi bacci tashi ku tafi."
cikin gajiya dan yau kusan wuni tayi hidima,
mik'ewa tayi kana tabi bayan Ahmad da tuni ya fita cikin jin dad'i.

Ita kuwa Ummi ita da Raihana ne sukaci gaba da hirar.

Hayatuddeen kuwa yana maida plate ɗin kayan marmarin kitchine direct sama ya haura inda ɗakinsa yake, yana shiga ya faɗa kan gado tare da shiga cikin Whatsapp ɗinsa don yaga anturo masa new messages da yawa, sunan Asma'u Ahmad Matawalle ce a sama tayi masa comment akan hoton nasu daya sanya a status ɗinsa inda tayi rubutu kamar haka.
"Tsarki ya tabbata ga Ubangijin talikai da ya halicci Saifuddeen cikin wannan halitta mai d'aukan hankali"  murmushi mai kama da dariya Hayatuddeen yayi tare da yi mata reply inda yace. "Kuɗin ganin status yawane dashi ina fatan zaki iya biya?".
Itama dariya tayi kana tace "Zan iya bada gaba É—aya dukiyata indai zanke ganin wannan kyakkyawar fuskar É—an uwannaka ako da yaushe".
Yanzu kam dariya Hayatuddeen yayi sosai yayinda ya rubuta cewa.
"Sai kiyi ta addu'a dan samun Hammana sai mai tsananin rabo, dan sai ya zaɓa kuma saiya darje, kuma shi mijin mace d'aya ne d'aya tak"
Itama dariya tayi sosai don tasan Alhamdulillahi itama tana da nata kyaun yanda bakowani ɗa namiji bane zai ƙita, haka dai suka ɗan taɓa hira kaɗan da ita duk kuma zancennata akan Saifuddeen ne, don sosai ya tsaya mata arai.

Saifuddeen kuwa yasha juyi kafun yasamu da ƙyar bacci ya ɗaukesa, ko acikin baccin nasa kyakkyawan fuskar Zaleeha itace keta zuwar masa, inda yayi bacci cikin wani irin shauƙi.

Washegari.
Ƙarfe tara tuni yagama shirya kansa inda yayi kyau cikin riga da wandon jeans ɗin dake jikinsa, ahankali yake tafiya da keken nasa harya kawo bakin ƙofar fita daga ɗakin, hannunsa yakai jikin handle ɗin ƙofan ya buɗe,  yanzukam da kansa yake tuƙa keken nasa cikin nitsuwa da salonsa na k'in wahala inda ya dumfaro babban falonnasu.
Ummi, Hayatuddeen, da kuma Raihana su ya tarar zaune acikin falon,yayinda Raliya ke ta kaikawo tsakanin dinning area da kitchine tana shirya musu breakfast, shigowarsa cikin falon shi yabayyana murmushi akan gaba ɗaya fuskokin ƴan uwan nasa, ƙarasowa tsakiyan falon yayi tare da kai dubansa ga mahaifiyarsa wanda takasa ɗauke idanunta akansa, murmushi zallan ƙaunarsa ne kwance akan fuskarta,  murmushin daya bayyana kyawunsa yayi tare dayi mata alaman.
"Ina kwana"
"Lafiya ƙalau Saifuddeen ya jikin naka?".
Ummi tafaÉ—a cikin kulawa.
Da body language yayi mata alaman.
"Da sauƙi" nan Raihana ta gaidashi tare da tambayar jikinsa,  itama da body language ya amsa mata  fuskarsa ɗauke da murmushi tare da mik'o hannu ya shafan kan Affan dake kwance bisa jikin Ummi. Raliya da Hayatuddeen ne suka gaidashi, suɗinma amsa musu yayi cike da ƙaunar ƴan uwannasa.
 Raliya na gama shirya musu break fast shida kansa ya sarrafa kekensa har zuwa kan dinning table ɗin,  kujera ɗaya ya matsar gefe kana ya turo kekensa har wajen,  kasancewarsa bamai cin abinci da yawa bane hakan yasa tea kawai yasha sai kuma chips dayake ɗan tsakala yana sawa abakinsa kaɗan kaɗan, sosai zuciyar ƴan uwansa da Umminsa ke wanke fari ƙal, babu abun dake ɗawainiya dasu face farin ciki da jin daɗi, kasancewarsu da Saifuddeen awaje guda baƙaramin ƙara musu kuzari da karsashi yakeyi ba, basu jima da fara breakfast ɗinba Ahmad da  Saminu suka shigo, nan suma suka zauna aka shiga cin abincin tare dasu,  duk da cewa suɗin surukaine ga Ummi, amma su jin kansu suke matsayin ƴaƴa awajenta, don sunajin kamar yanda su Hayatuddeen ke ƴaƴa awajenta haka suma suke saboda haka babu batun wani nuƙu-nuƙu agabanta don mahaifiyace garesu a gabanta suka girma tun suna yara har zuwa samartansu sukanci abinci a gabanta a matsayinta na uwa a garesu shiyasa kuma, koda suka auri yaranta tafiyar bata sauya zani ba.
Suna kammala cin abincin ne dukansu suka koma falo suka zauna,  hira sosai sukeyi yayinda Saifuddeen ke binsu da idanu yana me karantar abun da kowannensu ke cewa, idan na dariyane yakan ɗan murmusawa, ana haka ne Ishaq da tawagar ƙungiyarsu ta Joint National  association of persons with disabilities (Jonapwd) Gombe State Chapter. All the best! Suka ƙaraso, nanfa falon Ummi yacika tam da mutane, makafi, guragu, kurame, duk zuƙatansu suka cika da murnar ganin Saifuddeen,  Ishaq kam ji yake kamar yamaida abokin nasa ciki saboda daɗi, duk da cewa baya gani amma zuciyarsa ta gamsar masa da cewa Saifuddeen ɗinsa aboki kuma ɗan'uwansa ya samu lafiya, haka Ummi tasa su Raihana suka ajiye abunci da abunsha ga kowanne daga cikinsu, baƙaramin daɗi Saifuddeen yaji azuciyarsa na ganinsu da yayi ba, haka suka kwashe tsawon awanni suna tare da juna, saida akayi Azahar ne Ishaq ya tattarasu duk suka koma.
Adda Rahama da Dr Adnan da Baba Bello haɗi da goggo mahaifiyarsa ne suka zo,  suna zuwa babu jimawa kuwa saiga mutanen dukku wanda suka kusa cika mota suma sunzo don duba jikin Saifuddeen ɗin da kuma taya Ummi murnar dawowarsa,  nanfa gida ya ƙara ɗinkewa da jama'a.

  Da yamma kuwa Alhaji Sani da Alhaji Kabiru da kuma Alhaji Sulaiman mahaifin Hisham da Alhaji Adamu yayan Jabeer sukazo duba jikin Saifuddeen ɗin, sosai ƙwarai yaji daɗin ganinsu, suma sunji daɗi sosai da suka tararda jikin nasa da sauƙi, nan suka ɗan taɓa hira inda kowanni magana da body language sukeyi idan basu gane ba kuma yakan rubuta musu awayansa sai ya basu su karanta, sosai suka ɗansha hira kafun daga bisani sukayi masa sallama, koda sukazo tafiya al'khairi me yawa suka bawa Ummi don sunsan idan suka bawa Saifuddeen to ko sama da ƙasa zasu haɗe bazai amsa ba,  awajen Ummin ma kuwa ba tsira sukayi ba don kafewa tayi tace bazasu amsa ba, da ƙyar Alhaji Sani yasanya Ummi ta amsa, inda yayi mata tuni da cewa bakyau maida hannun kyauta baya.  Badon Ummi tasoba haka ta amsa kana tayi musu godiya.  

Wayar Hayatuddeen dake aje kan kujeran falonne kete tsuwa alaman shigowar ƙira saidai hartayi ta katse ba'a ɗauka ba, wani ƙiranne ya kuma shigowa, Hayatuddeen dake cikin kitchine ne yafito da gudu hannunsa ɗauke da wani dogon tsinke wanda jikinsa ke saƙale da gasashshen nama sai tiriri yake da'alama yanzu aka gasa naman,  saura ƙiris wayan ta tsinke ya ɗauka tare da karawa akan kunnensa, cikin yanayi na ɗan faɗa tace.
"Saikuma kaga dama ne kafun ka amsa wayana?"
Dariya Hayatuddeen yayi  tare da cewa.
"Yi haƙuri Likita ina kitchine ne".

Murmushi Amina dake zaune akan kujera tayi tare da gyara zamanta cike da kulawa tace "KwaÉ—ayayye kawai, meya kaika kitchen?."
hyyy yayi dan zafin da yaji lokacin da ya kai bakinshi kan sokan nama daketa tiriri,
jin tana mishi dariya ne ya sashi cewa.
"Nama ne Ummina ta gasa min,
shine nake d'an tab'i."
Kwaffa tayi tare da cewa.
"Ni bawannan ba yajikin Hamma Saifuddeen?".

"Eh dai naji, jikin Hamma Saifuddeen da sauƙi sosai, don yanzu haka ma muna gida, da jiya kika ƙira ma wataƙila da kinzo kin dubashi don muna Abuja" 

Idanu Amina tazaro tare da cewa.
"Wai kana nufin ya tabbata kun dawo Nigeria? kuma ma wai har jiya kun sauƙa Abuja shine baka ƙirani kasanar dani ba?" 

Dariya Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Ga zahiri kuwa muna mgna da number ta na Nigeria."
Cikin jin haushi tace.
"Tun shekaran jiyan can nake kiran number ka ta Indian bata shiga,
sai kawai yanzu kamar da wasa nace bari in gwada mtn naka.
kuma sai ya shiga, gsky Hayatuddeen baka kyauta min ba wlh."
cikin tauna naman yace
"Tuba nake Likita, ai bansan kina da buƙatar ganin kyakkyawan Hamman nawa ba!"
Cikin haushin rashin sanin dawowarsu da batayi ba tace "Harsai na faÉ—a mane sannan zaka sani, nidai ba wani nan munyi faÉ—a".
Dariya sosai Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Kiyi haƙuri bokan turai!".
"Nidai ai nace maka munyi faÉ—a ko".
tana gama faɗan haka ta kashe wayarta, dariya sosai Hayatuddeen yayi, Ummi dake tsaye abayansa ne ta ƙaraso cikin falon, dubansa tayi tare da cewa.
"Kai kuma kaida waye kake waya haka?"
Murmushi yayi tare da cewa "Amina ce fa Ummi wannan nurse ɗin da ta kula da Hamma Saifuddeen lokacin da muke Abuja, to shinefa yanzu da ta ƙira nake shaida mata dawowar mu shine wai ita tayi fushi da har jiya muka sauƙa a Abuja ban gaya mata ba taje ta duba jikinshi".
Murmushi tayi cikin tsananin jin dad'i tana matuk'ar son duk wani maison Saifuddeen d'inta,
murmushin kawai Ummi ta kumayi tare da zama akan kujera kana ta maida hankalinta ga TV inda sunna tv ke haska wa'azin Malam Isah Ali Pantami.

Yau tunda tazo wajen aikin nasu fuskanta aɗaure yake tamau, sam takasa sakin fuska ga kowa wanda hakan ya matuƙar bawa abokan aikinta mamaki, don kuwa sunsan bahaka take ba ita takowace sannan itaɗin me yawan fara'a ce saɓanin yau da suka ga ta tsuke fuska, fitowarta daga ɗakin gabatar da shirye-shirye kenan inda ta gabatar da shirinta na mushaƙata, kaitsaye ɗakin hutawansu ta nufa inda anan tabar jakarta harma da wayarta.
Koda ta shiga cikin ɗakin kan wata kujera ta zauna tare da ɗaukan jakarta, zip ɗin ta zuge kana ta ciro wayarta, 4 missed call ta iske acikin wayar wanda kuma duk daga Abdussalam ne, tsuka tayi tare da kunna data'n wayarta ta shiga Instagram, Raveel ne ya turo ƙofar ɗakin ya shigo bakinsa ɗauke da sallama, can ƙasan maƙoshi ta amsa masa sallaman batare da ta ɗago kanta ta kalleshi ba,
asanyaye ya tako ya ƙaraso zuwa inda take, kan wata baƙar kujera dake facing wanda take ya zauna murya asanyaye yaƙira sunanta "Zaleeha!"

Bata amsashi ba haka kuma bata ɗago kai ta kalleshi ba, ganin haka yasanyashi sauƙe ajiyar zuciya, kansa ya ɗan langwaɓar gefe guda cike da tsananin shauƙin mayen soyayyarta yace.
"Dan Allah M B S Dukku ki saurareni mana, ashe shikenan don zuciyata ta kamu da soyayyarki tayi laifi? Dan Allah Zaleeha kiyi haƙuri ki fahimci irin sonda nake miki, wallahi inasonki ina miki son da nikaina bansan adadinsa ba, rasaki dai-dai yake da daiɗaicewar tunanina Inasonki Zaleeha, dan Allah ki Amshi soyayyata!!"
Tsananin rauni da damuwar dayake cikine ya bayyana ƙarara akan muryarsa.

Idanunta ta lumshe tare da cizon laɓɓanta wanda suka sha pink lipstick, jin kalaman nasa take tamkar sauƙan ruwan zafi afatar jikinta, waye zai fahimceta? wanene zai gane me takeji azuciyarta? tabbas da ace mazan dake kawo kansu gareta da sunan soyayya sun san metakeji acikin ranta tabbas da zuwa yanzu sun ƙyaleta hakanan ta huta, tana matuƙar ganin ƙiman Raveel saboda koba komai abokin aikinta kuma suna shiri sosai dan yanada abin dariya tamkar abokin wasanta haka suke kodan kasan cewarshi babarbare ne, amma ayanzu furta mata kalman so da yayi yasanya taji gaba ɗaya batako son ganinsa, burinta ayanzu shine kowa yafahimci halin da take ciki na tsananin soyayyar dake cinta azuciya.
Ganin yanda ta rumtse idanunta ne yasanya Raveel ƙiran sunanta murya atausashe yace.
"Balaifina bane Zaleeha don Allah Karki tsaneni, laifin zuciya da ruhina ne da suka matuƙar kamuwa da soyayyarki, najima ina dakon soyayyarki araina Zaleeha, please and please ki amshi soyayyata ki amshi soyayyata kozan samu sauƙin abun danakeji azuciyata!!".
tuni idanun Raveel suncika tab da ƙwalla, ji yake kamar yajawota jikinsa yayi hugging ɗinta sannan yasata ta amsa masa soyayyarsa.
Idanunta da suka kaɗa sukai jajur ta buɗe tare da watsa masa su, saida yaji wani yaarr acikin jikinsa, cikin dakiya tare da ƙunan zuciya ta dube shi murya asarƙafe tace.
"Please Raveel i say leave me alone!, dan Allah kabarni na huta, kana ta faÉ—in kana sona! kana sona! na tausaya maka, kai kasan ni me nakeji acikin tawa zuciyar kuwa! to ji nake tamkar zan mutu in bar duniya in ban sameshi ba? har yanzu ina mutuntaka amatsayinka na abokin aikina,saboda haka kana da sauran daman da zaka janye batun soyayya agareni, bana sonka Raveel bana kuma tunanin zan soka ko anan gaba!!".
miƙewa tsaye tayi tare da ɗaukan jakarta ta nufi hanyar fita daga ɗakin, Sunanta Raveel yashiga ƙira amma sam bata tsayaba balle ta waiwayo ta kalleshi haka ta fice daga cikin ɗakin.
Idanu Raveel ya rumtse take saiga hawaye sun biyo kan ƙuncinsa, ya zaiyi da matsanancin son Zaleeha da yakeyi? Tayaya zai soma rarrashin zuciyarsa akan ta haƙura da Zaleeha? Kansa ya kifa akan ɗan madaidaicin table ɗin dake gabansa yana mejin wutar soyayyarta na ƙara kunnuwa acikin zuciyarsa.

Itakuwa Zaleeha kai tsaye motarta ta nufa tana shiga tayi mata key tare dayin reverse, maigadi ne ya wangale mata gate ɗin fita daga cikin gidan redi'on nasu na vission FM. gudu takeyi sosai akan titi gaba ɗaya komai ya cakuɗe mata waje ɗaya, ko ina tasanya kanta batajin daɗi, gida babu daɗi haka wajen aiki ma babu daɗi ko ina ta kutsa zancen aure akeyi mata kamar ita d'aya ce budurwa a duniya, hannunta tasanya ta bugi steering motar tata da ƙarfi tare da ɗan sake sautin kukanta, kuka takeyi ƙasa-ƙasa hadda sheshsheƙa, kai tsaye unguwar sarki tanufa hanyar da zai sadata da shagon A.A ALIYU PHARMACY a dai-dai wajen a dai-dai lokacin kamar wannan ranan anan ta tsaida motarta tare da zubawa ƙofar shagon A.A ALIYU PHARMACY ɗin ido, dai-dai inda tafara ganinsa ta sauƙe idanunta, sannu ahankali tasoma ganin tamkar alokacinne abubuwan da suka wakana tsakaninsu ke faruwa, lumshe idanunta tayi tare da sakin sautin kukanta ya fito fili, cikin magagin soyayyarsa da ta rufe mata ido tace.
"Inakake? Inakatafi kabar zuciyata cikin tsananin kewa da begenka? Kaine mafarkina haka kuma Kaine Zahirina, Koba danni ba kodan zuciyar da ka dasawa soyayyarka acikinta dan Allah kabayyana agareni na ganka, kowa yanamin kallon zautacciya wacce take son gaibu, wasu suna faɗin cewa kai ba mutum bane, kafito ka nuna musu cewa kai mutum ne kamar kowa, kazo gareni Ina Tsananin buƙatarka ayanzu fiye da wancan ranan, Dan Allah kazo gareni!!!".
Kuka take sosai tare da kifa kanta ajikin steering motar, wani irin zogi zuciyarta keyi mata yayinda idanunta ke ƙoƙarin rufewa, kuka tayi sosai harsaida wani irin azababben ciwon kai ya rufeta kafun ta zaro wani baby pink colour handkerchief daga cikin jakanta tashiga share fuskarta wacce tayi dama dama da hawaye, sake duban ƙofar shagon tayi, sai kuma ga wasu hawayen na sake sauƙowa daga cikin idanunta, dai-dai lokacinne wani matashin saurayi ya shiga kukkulle ƙofofin shagunan yana samusu kwaɗo kasancewar anata ƙiraye ƙirayen sallan magriba saboda haka zasuje sallah, ganin cewa sun rufe shagonnasu ne sannan da ɗai ɗai da ɗaiɗai jama'an dake wajen ke tafiya izuwa masallaci hakan yasa cikin rashin kuzari ta tada motar tata, ayanzukam ahankali take tafiya da motar kasancewar gaba ɗaya jikinta yayi weak ga wani irin zazzaɓi da ciwon kai da suka kawo mata cabka lokaci guda.
Agaban tankamemen gate ɗin gidansu dake cikin New G.R.A ta tsaya da motartata tare da danna wani ɗan siririn horn, Malam Kalla me gadi ne ya wangale mata gate ɗin, yayinda ta tura hancin motar tata cikin gidan, ko parking mai kyau yau batayi ba haka ta fito daga cikin motar, kai tsaye ɓangaren Mamy ta nufa, don acanne kaɗai take da yaƙinin samun nutsuwa, cikin muryarta da ta dashe ta yi sallama, Unaisa da Unaid yaran Yaya Ahmad ne keta wasa acikin tsakiyar falon, suna ganinta suka taho da gudu cikin ƙaunarta su duka sukace.
"Oyoyo Aunty Zaleeha!"
cikin yanayin sanyi daya rusketa haɗi da rashin kuzari tashafa kayinsu kana ta zuge zip ɗin jakarta, kasancewarta uwar mak'ulashe da shan zaƙi hakan yasa sam bata rabo da abubuwan zaƙi dangin su chocolate's da sweet's, chocolate ta basu sannan ta nufi ɗakin Mamy nan tabarsu sunata murna.

Sallama É—auke abakinta tashiga É—akin Mamy'n,
Mamy dake zaune abakin gado tana ninke kaya ta amsa mata cike da kulawa tana me dubanta.
"Sannu da hutawa Mamy!" tafaÉ—a tana me ajiye jakan hannunta kana ta sanya hannu ta zare mayafin dake jikinta.

"Yauwa Zaleeha sannu da dawowa ya aikin?".
cewar Mamy tana mebinta da kallo.

"Lafiya". tafaɗa ataƙaice kana ta faɗa kan gadon Mamyn blanket taja ta rufe jikinta dashi.
Cikin damuwa haÉ—i da kulawa Mamy tace .
"Yadai Zaleeha bakida lafiya ne?"
cikin muryarta dake neman sarƙewa tace.
"Mamy kaina ke ciwo, sannan zazzaɓi na damuna!"

"Subahannallah! kinsha magani kuwa?".
Mamy tafaɗa aɗan rikice tana mai taɓa jikin Zaleeha'n, aikuwa nan taji jikin yaɗau zafi zau.
Kai Zaleeha ta girgiza alaman batasha ba, tashi Mamy tayi tare da cewa.
"Bari naje na kawo miki abinci da magani kisha inyaso idan yayanku Ahmad yashigo sai ya kaiki asibiti"
Mamy na fita Aunty Lubna matar Ya Ahmad tafito daga cikin toilet ɗin dake ɗakin Mamyn, jikinta duk ruwa da'alama alwala tayi, ganin Zaleeha akwance lulluɓe da bargo yasanyata cewa.
"Lafiya kike kuwa Zaleeha duk wannan uban zafin shine ke hadda lulluɓuwa".
Zaleeha da zazzaɓi yasake cin ƙarfinta ta ɗago idanunta ta kalli Aunty Lubna'n sai kuma ga hawaye shaaa sun kwaranyo daga cikin idanunta.
Ganin hawaye na fita daga idon Zaleeha yasanya jikin Aunty Lubna yin sanyi, zama tayi akusa da Zaleehan tare da sanya hannu ta dafa kanta cikin kulawa tace.
"Kuka kuma Zaleeha? share hawayenki kinji komai yayi tsanani yana tare da sauƙi ki sawa ranki jarumtar yadda zaki fuskanci k'addararki!"
Kai Zaleeha ta girgiza mata tare da kife kanta akan cinyan Aunty Lubna'n cikin dasashshiyar muryarta tace "Menene laifina Aunty Lubna? meyasa kowa agidannan bazai yarda cewa inada wanda nakeso ba, sannan kuma ba aljani bane kamar yanda suke tunani, mutum ne shifa kamar kowa, Inasonsa! Aunty Lubna Inasonsa!, bansan meyasa kowa yaƙi fahimtan hakan ba hatta Ya Ahmad ɗina ma fa shima kallon bansan me nakeyi ba yakeyi mini gani yake wai ba mutum nake soba aljan ne!".
shiru tayi da maganan tare da ƙara sautin kukanta.
Cikin lallashi haÉ—i da tsananin tausayinta Aunty Lubna ta sanya hannunta ahankali take shafa bayan Zaleehan, cikin son kwantarwa da Zaleeha hankali tace.
"Kiyi haƙuri Zaleeha ki kuma kwantar da hankalinki, nafahimci yanda kikeji kuma insha Allah zaki gansa harma kuyi aure dashi kidaina kukannan kinji shalelen Ya Ahmad ɗinta!".
Wani irin sanyi kalaman Aunty Lubna suka sauƙarwa Zaleeha acikin zuciyarta, take taji son matar Yayan nata ya ƙara shiga ranta, nan tasoma ƙoƙarin share hawayenta harma da sakin murmushi, Mamy ce ta dawo cikin ɗakin hannunta ɗauke da plate ɗin abinci da kuma magani, kasancewar taji sanyi acikin ranta bisa kalaman da Auntyn nata tayi mata hakan yasanya ta ci abincin saidai ba sosai ba magani tasha inda tayi alwala tayi sallah bata bar kan sallayan ba saida tayi sallan isha, anan ɗakin Mamy ta kwanta, mintuna kaɗan bacci ya ɗauketa, ana idar da sallan Isha kuwa saiga Abdussalam yayiwa gidan dirar mikiya, koda Mama taji zuwan Abdussalam nan tashiga zazzaga masifa wai Zaleeha batajin magana tayi baƙo me mahimmanci kuma taje ɗakin uwarta tabiyu tayi zamanta, koda akaje ɓangaren Mamy ƙiran Zaleeha nan aka iske tana bacci, inda Mamy ta shaida cewa bata da lafiya ne, haka Abdussalam ya koma gida batare daya samu ganin Zaleeha ba, Mama kuwa ba irin faɗa da maganganun da bata faɗa ba ita kaɗai taketa ɓaɓatun ta harda cewa wai Mamy ce ke zuga Zaleeha akan kada taso Abdussalam, haka tayita aikin baƙin ranta ita kaɗai awannan daren dai Zaliha aɗakin Mamy ta kwana.

***

Alhamdulillahi yau kwanan su Saifuddeen uku da dawowa Nigeria, inda acikin kwanaki Ukunnan sauƙi kullum ƙara samuwa yake ga Saifuddeen yana mai ci gaba da shan sabbin magungunan da aka loda mishi.
sannan kuma acikin kwanakin kullum gidan nasu cikin karɓan baƙuncin mutanen dake zuwa gaisuwa yake,ciki kuwa hadda matar Alhji Sani, da kuma Matar Alhaji Kabiri da Mommyn Hisham.da kuma matar Alhaji Adamu Hajia Kingi damn k'anwarta Aunty Kubra yar kasuwa ce mai zuwa Dubai sari kayan k'awa na mata, time to time da ita Ahmad ke zuwa sari, suma sunzo sun duba jikin Saifuddeen inda Ummi taji daɗi sosai.

Ranan yau takasance laraba kuma yaune ranan da Ishaq ya sanar da Saifuddeen cewa Zaleeha zatazo gidan nasu na nakasassu don gudanar da shirinta mai suna BABU NAKASASHE SAI RAGO, hakan yasa tun safe yau Saifuddeen yatashi yanajin kansa cikin wani irin shauƙi yayinda yakejin zuciyarsa wasai.

Ɓangaren Zaliha kuwa kwana biyu kenan yau bataje aiki ba sakamakon ɗan jinyan da tayi, amma yanzu Alhamdulillah jikin nata yayi sauƙi sosai, yayinda kullum Aunty Lubna ke ƙara kwantar mata da hankali, hakanan yau tatashi tana mejin faɗuwar gaba yayinda takejin zuciyarta na tsinkewa akai akai haka dai ta kawar da duk wani abu da takeji ta shiga shirya kanta don zuwa gabatar da shirinta.

Fitowarsa daga wanka kenan lafiyayyar skin ɗinsa sai fidda daddaɗan ƙamshin tsadadden sabulun wankansa, zaune yake agaban mirror yana shafawa jikinsa mai, yana kammalawa ya shiga gyara ƙawataccen sajen dake kwance akan fuskarsa, wanda ta sauya gaba ɗaya kamanninsa na da, taƙarawa fuskarsa kyau da kwarjini. Wata dakakkiyar shadda me kyau da tsadan gaske wacce take da kalan skay blue ya sanya, sosai shaddar ta amshi jikinsa inda tayi bala'in da cewa da white skin ɗinsa, wata haɗaɗɗiyar hulan zanna bukar wacce jikinta ke ɗauke da ratsin sky blue yasanya, yayinda aƙafansa kuwa yasanya lafiyayyun takalma sau ciki ƙiran kamfanin bally suma kalar sky blue garesu hakan yasanya haɗuwar tasa ta ƙara bayyana, bakaɗan ba Saifuddeen yayi kyau yayinda kyakkyawan sajensa keta ƙyalli, tsadadden turarensa me daɗin ƙamshi ya fesa ajikinsa take ɗakin ya gauraye da ƙamshinsa, agogonsa ƙiran kamfanin rolex ya ɗaura akan tsintsiyar hannunsa na dama, wayarsa ƙirar iphone ya tura acikin aljihunsa tare da sarrafa kekensa ya nufi hanyar fita daga cikin ɗakin.
Daddaɗan ƙamshin turarensa shiya ja hankalin su Ummi da Hayatuddeen da kuma Raihana dake falon suka dawo da kallonsu garesa, "Wow Hamma Saifuddeen ka ganka kuwa? Wallahi Hamma na baka taɓa yin kyau irin na yau ba!!".
Hayatuddeen yafaÉ—a cikin santin kyawun da yaga hamman nasa yayi.
Murmushine ya bayyana akan fuskar Saifuddeen tare da duban Ummi cikin body language É—insa yayi mata alama akan wai maganan da Hayatuddeen yafaÉ—a gaskiya ne?
Dariya Ummi tayi tare da cewa.
"A kullum a koda yaushe kai kekyawa ne koda bakayi wonkaba bare kolliya.
to ya kake zato idan kayi kwalliya to sai kayi kyau tamkar balarabe.
kaga kenan sharrin Hayatuddeen ne kawai dama tuncan kai kyakkyawane!"
Dariya gaba É—ayansu suka sanya banda Saifuddeen wanda shidai saidai yayi murmushi.
Cikin yabawa da kyawun da yayi Raihana tace.
"Hammana wallahi kayi kyau sosai".
murmushi yayi mata tare da yi mata alama kan cewa ya gode, Hayatuddeen kuwa cikin azarɓaɓi ya ciro wayarsa hoto yashiga ɗaukan Hammannasa yana me cewa ya samu na sawa a status da kuma Instagram.
jin haka Raihana ta amshi wayar tare da yi musu hoto shida Ummi da Raliya data shigo yanzu. Sunyi kyau matuk'a duk suna murmushi Ummi ta d'an roggofo kanshi.

Cikin body language É—insa yayiwa Ummi bayanin inda zaije, fatan Alkhairi Ummi tayi masa tare da cewa.
"Adawo lafiya".

Har bakin mota Hayatuddeen ya raka hamman nasa yayinda da kansa ya sauƙa akan kujeransa ya shiga cikin tsaleliyar motarsa ƙiran mercedes benz, agidan baya ya zauna sannan Hayatuddeen ya sa mishi weelchair d'insa a but yayinda Sule driver ke tuƙasa...

Tana gama shafa mai ta ɗauki tsadaddiyar hodan ta ta goga akan fuskarta, tana gama shafa hodan ta ɗauki black eye pencil ɗinta ta goga acikin manya manyan idanunta dake matuƙar gigita masu kallonsu, pink lipstick ta goga akan ƴan ƙananun laɓɓanta, yayinda tayi amfani da Mascara wajen miƙar da tulin eye lashes ɗinta, ita ba mace bace wanda take da yawan cika meckup akan fuskarta hakan yasa bata ƙara komai akan fuskarta ba bayan wannan ɗan kwallian da tayi.
Wani haɗaɗɗen lace wanda yaji dinkin riga da sket maroon colour wanda keda ratsin golding ash ta sanya, sosai kayan suka amshi jikinta inda sket ɗin ya bayyana haɗaɗɗiyar surar jikinta da kuma cikakkun hips ɗinta, parking dogon gashinta tayi atsakiyan kanta tare da zama akan stull ɗin mirror tashiga tsantsarawa kanta ɗaurin ɗan kwali, wani irin haɗaɗɗen ɗauri tayiwa kanta wanda yaƙara bayyana kyawun shigar nata, wata ƴar siririyar sarƙa golding ash ta sanya awuyanta tare da liƙa ɗan kunnensa me kamar manne akunnenta, wani takalmi me tsananin tsini da kyau wanda keda kalan lace ɗinta ta sanya aƙafafunta tare da ɗaukan wani vail shima maroon colour ta yafa ajikinta, baƙaramin kyau Zaleeha tayi ba ita kanta yau kyawunta ya ɗauki hankalinta, turarenta dake rikita maza ta fesa tare da ɗaukan haɗaɗɗiyar hand bag ɗinta me kalan kayanta ta riƙe ahannunta, wayarta tariƙe aɗayan hannun nata tare da car key ɗinta kana ta nufi hanyar fita daga cikin ɗakin, cikin nutsuwa take taku ƙwas-ƙwas hartakawo cikin falon mahaifiyartata, Mama dake zaune ta haɗe fuska tana ganin Zaleeha taji ranta ya sake, kallon Zaleehan tashigayi tana me godewa Allah daya bata wannan kyakkyawar yarinyar, lallai Zaleeha nada kyau irin nagaban kwatance, cikin nutsuwa Zaleeha tadubi Maman nata tare da cewa "Mama ni zanje (Jonapwd) saina dawo".
Tsuka Mama tayi tare da sake duban Zaleehan zata iya rantsuwa kyawun da Zaleeha tayi yau na dabanne amma abun haushin wai ba wajen wani hamshaƙin billionaire zataje ba wai gidan Nakasassu zata cike da ɓacin rai Mama tace.
"Yanzu akan zuwa wajen waƴancan Makafi da guragunne zaki wani caɓa ado kamar wata mezuwa gasan kyau na duniya?".
Baki Zaleeha taturo gaba tare da shagwaɓe fuska zatayi magana kenan Mama tace "Da halla ni ɓacemin da gani, ai dai indai wannan banzan aikin nakine kin kusa dainashi, don kuwa natabbata Abdussalam bazai bari kici gaba da wannan aikin ba don shi nasan awajensa aikinnan ƙasƙantacce ne".
Murmushi kawai Zaleeha tayi tare da sakai ta fice daga cikin falon, da kallo Maman nata ta bita aranta tana mejin wani sabon buri na ƙara ɗarsuwa acikin zuciyarta, don ayanzu tunaninta ya fara haurawa sama don kuwa har Abdussalam ɗinma tanaga Zaleeha ta zarce ajinsa.

Ita kuwa Zaleeha tana fita, tayi kicibis da Ya Habu,
cikin had'e fuska yace.
"Kina dai sane haramunne in mace baliga zata fita ta zabga irin wanna turaren naki mai shegen k'amshi, na hanaki yafi a k'irga amman da yake kunnen k'ashi gareki kink'i ki bari ko?."
ya k'arishe mgnar cikin zaro mata ido.
cikin yin rau-rau da ido tace.
"Ya Habu bazan sake ba."
kwaffa yayi kana ya wuce yayi cikin gida.
Motarta ta shige, maigadi na buɗe mata gate ɗin gidan ta cilla motarta kan titi. Cikin nutsuwa take murza steering motar tata yayinda daddaɗan ƙamshin turarenta ya cika gaba ɗaya motan.

Hancin motartane ta kunno kai cikin gidan nakasassun inda ta tsaida motar a parking lot, daga can wani babban falo kuwa nakasassune acike sun shirya tsab suna me jiran zuwanta.
Cikin nutsuwa take takunta ƙwas-ƙwas yayinda takun takalminta ke bada wani sauti, saura bai wuce taku biyu ta samu kanta acikin babban falon ba taji wani irin faɗuwar gaba ya rusketa, take taji wani irin iska na shiga jikinta, addu'a ɗauke abakinta ta sanya ƙafanta acikin falon, mutanen dake zaune da waƴanda ke gani da waƴanda basa gani tuni sun shaida da zuwanta saboda jin sallamarta da sukayi, waƴanda basaji kuwa hancinsu ne yasanar musu da zuwanta tahanyar shaƙan daddaɗan ƙamshinta, cikin mutumtawa haɗi da rashin ƙyama Zaleeha ta gaishe da kowannensu, Ishaq ne yashigo cikin falon fuskarsa ɗauke da murmushi yace "Sannunki da zuwa Hajiya Zaleeha!".
Murmushine yafaÉ—aÉ—a akan fuskar Zaleeha cike da kulawa tace.
"Yauwa Malam Ishaq ya fama da jama'a?".
Da. "Alhamdulillah ya amsa mata alokacin dayake ƙoƙarin zama akan kujera tare da gyara rik'on da yayiwa system d'inshi da wayarshi. Sosai ƙwazon Ishaq ke burgeta saboda yana aiwatar da komai nasa tamkar wanda yake gani.

Yau da wani Gurgu zata gudanar da shirin nata don haka tuni ta tafara ƙoƙarin soma yi masa tambayoyi kamar yanda tsarin shirin nata yazo dashi, ko mintu 10 ba ayi da fara shirinba a hankali taji wani irin ni'imtaccen iska na ratsa ko ina dake jikinta yayinda bugun zuciyarta ya tsananta,
lumshe idanunta tayi sakamakon wani irin daddaɗan ƙamshi da taji ya ratsa cikin hancinta ya kuma cakuɗa da numfashinta, wani irin mimmiƙewa taji tsikar jikinta nayi, wani irin sanyi me daɗine taji yana kusanto ta tamkar wanda ake hurosa, hakan yasanya akasalance ta kai dubanta ga inda takejin kamar tanan sanyin ke fitowa, dai-dai lokacin shikuma ya shigo cikin wajen, zaune yake akan kekensa fuskarsa na fitar da annuri haɗi da ƙyallin kyau sajenshi yayiwa fuskar k'awanya mai jan hankali.
Wani irin duka da harbawa zuciyar Zaleeha tayi, yayinda ta kafesa da idanunta masu rikita maza, cikin nutsuwa yake sarrafa kekennasa wanda kuɗinta kaɗai ya isa yasai wani gida, sam ya kasa ɗauke kyawawan idanunsa daga kan kyakkyawar fuskar da yajima yana bege dason gani, wani irin yawu Zaleeha ta haɗiye wanda ya tsaya mata amaƙoshi, zata iya rantsewa bayan mutumin daya taimaketa bata taɓa ganin wani kyakkyawa aduniya ba bayan wannan mutumin dake zaune akan kekensa in dai ido da idone, cikin tsananin dauriya da kama ajinta bawai don ta ƙoshi da kallonsa ba ta kawar da idanunta gefe, ƙarasowa cikin babban falon yayi tare da tsayawa adai dai inda Ishaq ke zaune,
A fakaice ta D'angelo kalle fararen yatsun hannunshi da yaketa musabaha da mutanen nasu da suka kewayeshi tamkar sarki a fadarsa,
ƙamshinsa kaɗai yasanya Ishaq ganesa, nan ya ɗauki wayarsa ya rubuta masa saƙo kamar haka.
"Gafa Zaleeha nan tana gudanar da shirinta wani sati dakai za ayi".
Murmushi kawai Saifuddeen yayi tare da yiwa abokin nasa rubutu inda yace.
"Allah ya kaimu,"
kana shiko Ishaq ya gyara zama tare da cewa.
"Zaleeha ga aboki na kurman da na tab'a gaya miki naje Indian dubashi da jiki."
ba tare da ta kalleshi ba tace.
"Ayyah."
Shiru yayi tare da kafeta da idanunsa kowani motsi da zatayi tare da bugun zuciyarsa yake tafiya amman da yake ya iya sarrafa kanshi babu mai ganewa sai ita da takejin kwayar kekyawan idanunshi na yawa a surar jikinta.
Hakan yasa gaba ɗaya nutsuwarta ce tayi ƙaura daga jikinta, cikin rashin kuzarin dayazo ya lulluɓeta haka take gudanar da shirin, ɗan ɗago da mayan idanunta tayi da niyar satan kallonshi karab idanunsu suka haɗe dana juna, da sauri tayi ƙasa da kanta, sakamakon wani irin shock da taji acikin jikinta, gaba d'aya taji wani abu na dark'efe kwayan idanunta,
bayan kamar minti 7 tasake ɗago da kanta don ta dubesa still idanunsu ne ya sake sarƙewa acikin najuna, sake yin ƙasa da kanta tayi aranta tana cewa.
"Na shiga uku waye wannan kuma ne wai da yazo ya hanani sukuni, irin wannan kallo saikace maye hegen gurgu mai jajayen kunnuwa, dama ai ance gurgu yafi mai k'afa iya shege!".
bayan kamar 8 minutes a hankali tasake ɗago kanta, har yanzu dai kallonta yake baya ko ƙiftawa sai dai ya rage girman idanun nashi, ɗan jim tayi tare da yin mgnar zuci.
"OK tsaurin ido ko tam zanyi mgninka yanzu".
kana itama ta tattaro tsaurin idonta da jarumta ta tsaida kwayar idanunta cikin nashi kwayar idanun,
dib-dib taji zuciyarta na bugawa da k'arfi-k'arfi kuma da sauri,
wani irin kwarjini da haibar fuskarsa da surarshi suka cika mata idani cikin one second ta janye idanunta cikin idanunshi da sauri ta maidasu akan surar kansa zuwa gefen sajenshi, ganin bai ɗauke nasa idanun daga cikin nata ba yasanya ta sakar masa harara tare da murguɗa masa baki, wani irin dariyane ya kama Saifuddeen don sosai hakan da tayi ya ƙarawa fuskarta kyau, lumshe idanunsa yayi yana mejin wani abu ya dark'afe ƙahon zuciyarsa.
Adaddafe haka Zaleeha tagama gabatar da shirinta inda gaba d'aya kallon da Saifuddeen ke mata ya dagula mata lissafi, ita sam batason yawan kallo musamman ma shida ya kafeta da ido kamar zai cinyeta kuma idanun nashi wani haiba suke dashi na musammam.
a hankali taja gajeren tsaki tare, kallonshi a fakaice kana tace.
"Maye kaci Kanka!."
ido ya lumshe a hankali dan ya gane me ta fad'i mishi,
ita kuwa hararanshi ta kumayi kana taci gaba da aikinta.
Shi kuwa Saifuddeen cikin lumshe ido da shak'ar sassanyar iskar AC mai cike da k'amshi a ranshi yace.
"Uhummmm bazan ci kaina ba in sha Allah ke d'in dai zan c...!

Duk fa masu bin labarin nan kunsan sashi sashi muke binshi, to da ganin yanzu kun san mun shigo wani sashi na musamman kuma. Wasan yanzu zai fara.
Dan Allah da darajar iyayenmu da girman Al'arshi Kada ki fitarmin da littafi na, in kin fitarba ba sai nace Allah ya isaba ko inyi zagi da tashanci ba damn tijar maguzawa ba, No da Allah isasshene kuma shi yana sane daku in ni bana sane daku, kuma shine zai mana hisabi. Dan haka ni bazan zageku ba bare in zagi iyayenku, dan nasan darajar nawa iyayen ko k'abilata bana so a zaga bare iyayena shiyasa bazan zagi iyayen wasuba🤗🤗🤗

BY

*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:56 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.