Complete Hausa Novels

Nakasa Ba Kasawa Bace Part 1 Complete Hausa Novel

Reading file: NAKASA BA KASAWA BACE PART 1.txt

Chapter 13 of 27

*PAGE 13*

NA
*AYSHA ALIYU GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

~28 February 2020/ 9:10 Am~

*Godiya ta musammam ga k'ungiyar nakasasu ta Jihar GOMBE, (JONAPWD) ina godiya da goyon bayanku*

_Gombawa d'iban fari ba'a kwana da kuba a tashi daku har cikin al'jannatul firdausi. Duk sammakonka to bagombe a tafe ya kwan, Gombe hamadan sarki Sulaimanu Gombawa masu kyawawan shatale-shatale da tsabtattun tituna, wannan shafi nakune al'ummar gombe_

A cikin babban birnin Gombe!.

Yauwa Monday da misalin 6:02 pm wannan lokaci yayi dai-dai da lokacin da mafi akasarin bani adam dake woje ke neman hanyar kowa gidanshi kama daga yan kasuwa da ma aikata maza da mata manya da yara da dai sairansu.
Musamman maza da matan musulmai don kowa na k'ok'arin ganin ya yasamu yin sallanan magrib kan lokacinta kamar dai yadda Saifuddeen yake saurin ya samu Sule ya fito su wuce gida direct bazama su biya wurin Ishap ba dan ganin ana gab da kiran salla shiyasa yake son ya koma gida ya samu yayi bud'a baki yasha ruwa a nitse.

A irin ya wannan lokacin duk mazauna gombe sunsan yadda ababen hawa ke cika titinuna especially wuraren da fitilun bada hannu suke haka yakesa cunkoson ababen hawa ke yauwaita tamkar a birnin Lagos.

Hakan ce ta kasance a wannan babban titi daya ratsa daga gaban babban gate d'in Gombe State University (G.S.U) wanda titin zai ratsa gaban k'ofar babbar fadar masarautar jihar ta. Gombawa kana daga hannun dama kuwa Gate d'in babban ofishin k'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe mai taken joint national association of persons with disabilities. (jonapwd) Gombe state chapter. All the best! ne wanda yake fuskantar ratsestsen ginin G.S.U kana daga gefen (jonopwd) d'in akwai wata yar kasuwar Tudu wato kasuwan mata,
in ka mik'a titin kad'an kuwa akwai fitilar bada hannu, wacce gefen titin wurin akwai shaguna a cikin jerin shagunan kuwa a nan babban shago na saye da sayarwan magunguna wato A.A Aliyu pharmacy d'in yake wurinda Saifuddeen yake a yanzu haka kenan!.

Wasu jerin ayarin tsala-tsalan motocine suka ratso harabar gate d'in G.S.U moto cin sun sun kai guda 5 ,
kai da gani kasan yara ne suke jan motocin dan yadda suke tsula gudu tamkar zasu tashi sama, sai gilmawarsu kawai zakaji fiw-fiw suna gibtawa. Da sauri mutane suka rink'a kaucewa sanin rashin mutuncin shugaban ayarin, *Dalla*
haka yasa akabi ayarin motocin da ido,
dukansu kyawawan motocine amman,
akwai guda d'aya daga cikinsu duk ta fisu tsada da sabunta,
bisa dukkan alamu bugun 2019 ce motar dalliyace mai azabar kyau sai shek'i da k'elli takeyi,
hatta tayoyinta tamkar ka lashe, koda yake haka baya rasa nasaba ne da yanayin tsabtace titunan birnin Gombe da akeyi ne a ko wanne safiya wannan yasa gombawa sukayiwa sauran jihohi zarra a fagen tsabta dan daga bakin gate din G.S.U. zaka iya cilla ganinka har kan shatale-talen dake k'ofar fadar jiha baza kaga koda tsinkeba a bisa titinunan ba,,
motar ruwan tokace sai gilashenta da suka kasance masu duhu,
yadda na ciki na iya ganin na woje na woje kuwa bashi da damar ganin na ciki,
motoci biyu dake gaban wannan motar sun wuce kenan sai kuma ita motar da tafisu kyau d'in tana biye dasu,
yayinda biyu ke bayanta gudu sukeyi tamkar titin dan su kad'ai akayishi .

Sun zo dai-dai bakin gate d'in K'ungiyar nakasassu ta jihar Gombe, Joint national association of persons with disabilities, (jonapwd) d'in kenan, sai kuma ga ratsetsiyar motar Zaleehs ta fito daga cikin harabar (jonopwd) d'in kai tsaye ta danna hancin motarta bisa titin kana ta ratsa tsakiyar ayarin motocin nan, inda ta shiga tsakanin motar nan mai kalar toka da saura biyun nan masu biyoshi a baya,
Zaleeha kekyawar budurwace a cikin motar wacce da ka ganta kasan tana cikin ganiyar k'uruciyarta iska na kad'a igiyar budurcinta, tutarta na karkakad'a zuk'atan maza tauraronta na d'auke idon dukkan lafiyayya namiji ganin fuskarta kawai kansa duk lafiyayyan namiji yayita yayyafi,
taka motar takeyi tamkar zatabi takan motarnan dake gabanta,
dole tasa saura biyun nan suka biyo bayanta,
kasan cewa gudu sukeyi cikin abinda bai gaza 58 seconds ba suka isa madakatar fitilar bada hannun dake tsakiyar titin, dole tasa suka d'an tattaka birki tare da tsagaita tafiyar tasu,
a hankali ta lumshe idonta tare da bud'esu kana ta shak'i sassanyar iskar hunturu dake ratsa jikin mutane,
kanta ta d'an juya ta kalli gefen gabas inda taga nanma cike yake mak'il da ababen hawa, wani d'an gajeren tsaki taja tare da d'an juyawa ta kalli gefen yamma inda nanne dai-dai bakin babban kemis d'in A.A Aliyu pharmacy yake,
ido ta kuma lumshewa kana ta kuma bud'esu a hankali, ido ta tsurawa fuskar Saifuddeen mai tsananin kyau dake gefen pharmacy d'in,
a hankali ta fesar da sassanyar iska daga bakinta kana ta kuma bud'e kekyawan idanunta a hankali ta zubasu kan surar Saifuddeen da ya gama zama cikekken matashi d'an 30 years kekyawa ne mai cikar zati da haiba wanda Allah yayi mishi cikar halitta,
farine k'al tamkar balarabe sumar kanshi tamkar ba indiye, yanada tsawo dai-dai misali, kana yanada halittar gwanji duk da suturar dake jikinshi yana son b'oye asalin halittarsa ta k'ak'k'arfan namiji mai zarra, fuskarshi mai kyau da haiba ce gashin girarshi kad'ai abin ganine fuskar ras babu saje,
a hankali ta kai idonta kan yarinya dake tsaye a gabanshi wacce bazata wuce 7 years ba, da alamun tsantsar so da k'aunan yarinyar a fuskarshi, sunkuyowa yayi d'ai-dai tsawon yarinyar kanta ya shafa tare da mik'a mata ledar hannunshi cikin d'an yin d'igirgire yarinyar ta manna mishi kiss a kumatunshi murmushi yayi tare da juya yarinyar alamun ta tafi.

Matashin dake cikin motar nan kalar toka kuwa,
shine ya d'an gyara zamanshi tare tsurawa motar dake bayanshi ido ta cikin madubi motarshi yaga sai matsoshi takeyi kuma yaga ba motocin shi bane,
bai gama nazartar ya akayiba,
sai kawai yaji gib-gib motarnan ta iso gareshi ta bugi wannan motar tashi da yakeji tamkar k'ok'on ranshi motar da aka binne miliyoyi aka saya mishi ita kuma du-du-du yau ya fara hawanta,
idanunshi ya rumtse da k'arfi bala'i ji yakeyi ko uban waye ya tab'a mishi motar nan sai ya illatashi.
ita kuwa Zaleeha gaba d'aya ta shagala da kallon Saifuddeen da babyn nan sam bata ankare da cewar motartafa na tafiyaba kuma sam ta mance cewa a madakata suke, bata dawo haiyacintaba saida taji motarta ta bugi motar dake gabanta,
kana motarta ta d'anyi baya sannan ta kumayi gaba ta k'ara bugar motar dake gabantan,
cikin tsananin firgici da razani ta taka birki da k'arfi ji kakeyi, k'uuuuh, ta caki motar ta tsaya.
Sautin bugun da tayiwa motarnan da kuma sautin taka birki da tayi shiya jawo hankalin mutanen dake wurin gaba d'aya.
Kai mutane suka rirrik'e tare da cewa.
"Innalillahi".
sabida motar ta kasa sarrafuwa har saida ta kuma bugan jikin motarnan a karo na uku,
sannan ta samu ta tsaya, gaba d'aya jikinta rawa yakeyi sabida tsananin tsoro da razani,
yayinda duk mutanen dake sashin wurin suka zuba musu ido tare da sassauk'e numfashi da furta.
"Alhamdulillahi."
duk sautin nan da bugun motar ta Saifuddeen dake bakin kemis d'in nan shi baima juyoba, duk da hatta ma'aikatan cikin kemis d'in saida suka fiffito,
idonshi ya zubawa bakin d'aya daga cikin maikatan kemis d'in yana ganin yadda lip's inshi ke motsawa hakan yasa ya gane abinda yake fad'i inda shi saurayin yake cewa.
"Innalillahi wannan wacce ce tsautsayi ya rubtawa rayuwarta ta bugi motar Dalla shi kenan zai illata rayuwarta gashi macece ya samu abinda zayita bibiyar rayuwarta."
d'aya dake gefenshi ne yayi saurin cewa.
"Kai subahallahi *Zaleeha M. B.S. Dukku ce.
da sauri Saifuddeen
ya juyo ya kalli inda yaga mutanen wurin gaba d'aya suna kallo,
dai-dai lokacin kuma wanda aka kira da Dalla ya bud'e marfin motarshi gaba d'aya fuskarshi tayi jazir sabida tsananin bala'i fuskarnan tasa tamkar tayi aman jini,
wani irin taku yakeyi wanda yafi kama dana azzalumai,
gaban motarta ya nufa gadan-gadan. Yayinda ita kuwa Zaleeha ta zazzaro ido tare da kame jikinta tanajin hanjin cikinta na bada sautin k'ululuku sabida tsananin tsoro da firgici.

Shi kuwa yana isa gaban motarta cikin rumtse ido ya wore tafin hannnshi kana ya mari glass d'in gaban motarta a take ya tarwatse yayi cikin motar,
jin sautin tarwatsewan glass d'in yasa gaba d'aya mutane sukayi cirko-cirko domin duk cikin fad'in gombe ansan waye Dalla domin yayi k'aurin suna,
akan izaya da d'agawa da zalumcin Mace koda aurenta ko ba aure in dai ya ganta kuma ta mishi tofa zaisa yaranshi su d'auko mishi ita ya biya buk'atarshi da ita so yana cin karensa babu babbaka tunda yana ganin yanada manya gashi cikekken É—an kalare mai girman daba.
Bata dawo daga firgincin daya sataba taji ya bud'e marfin motar tata kana yasa hannunshi ya damk'i hannunta da azaban k'arfi wonda saida ta saki k'ara,
fincikota yayi woje ya tsaidata gabanshi sannan ya ware tafin hanunshi ya yarfa mata wani gigitaccen mari mai azabar tsiya wanda saida taga taurari na gilmawa kana taji kunnenta yayi dummmm.
A take sai ga jini ta hancinta,
shi kuwa Dalla ba tare da yace mata komaiba ya juya ya shiga motarshi, dan ya sawa ranshi wannan jan kunne kawai ya mata yanke hukunci kuma na nan tafe a kanta haka yasa ya juya
don fitilar bada hannu ta basu damar wucewa.

Shi kuwa Saifuddee ganin abinda Dalla yayi mata tun fasa mata glass da yayi ya nufo kansu da gudu so kasancewar akwai 'yar tazara tsakaninsu gashi sai ya ratsa gaban babura da keke napeps da motocin da suka cika titin yasa kafinma ya isa tuni Dalla ya shiga motarshi,
kana babura da napep da motoci duk sun fara shirin wucewa wonda dole suke ratsawa ta gefen motarta. Itako tunda ya mareta zafin marin da gigita yasa ta fad'in gaban motar tata ta kifu samanshi.
Cikin gudu da sassarfa ya isa gareta, yana zuwa yasa hannunshi duka biyu ya kamo kafad'unta, kana ya d'agota ya tsaidata suna fuskantar juna yadda in tayi mgna zai iya ganewa,
idonshi ya rumtse da k'arfi ganin jini na bin hancinta kana tuni fuskarta tayi jazir hatta shatin yatsunshi sun taso a fuskarta,
ga wasu zafafan hawaye dake kwaranya a idanunta sabida rad'ad'in marin da k'unar zuciya kan cimata zarafi da tozartata da akayi a tsakiyar gari.
shi kuwa Saifuddeen tuni fuskarshi ta sauya launi daga fara ta koma jazir kana idanunshi tamkar su amayar da wuta tuni jijiyoyin kanshi suka taso,
yayinda jijiyar kan goshinsa tayi ziwat har kan tsinin karan hancinsa a fili zaka gane zallan b'acin rai, gaba d'aya jikinshi tsuma yakeyi,
ido ya zubawa fuskarta kana itama ido ta zuba mishi cikin rauni da muryar kuka tace.
"Wlh ban saniba bada gaggan na buga mishi motarshi ba hankalina ya tafi wurin kallon wani ne."
lips enshi na k'asa ya taune da k'arfi tamkar zai hudashi,
kana ya kama hannunta tare da yi mata nuni data shiga motarta,
cikin rawan jiki ta nufi gefen direban,
hannunta ya kamo da sauri, juyowa tayi tana kallonshi itama kai ya jujjuya mata alamar a a kana ya nuna mata gefen mai zaman banza,
ba musu ta zagaya ta shiga ta zauna.
Shi kuwa gefen driving sit ya shiga ya zauna,
sit bell yaja ya sank'ala jikinshi,
kana ya juyo ya kalleta tare da yi mata alamu da idonshi tasa nata sit bell d'in.
ba musu ta saka,
sai ta kuma d'ago kanta da sauri jin ya dannawa motar Key kana ya figi motar a guje,
ido ta zazzaro ganin yadda yake tsula gudu tamkar zai tashi sama,
gudu yakeyi da tsanani amman cikin bin k'a'ida da dokar tuk'i cikin abinda bai gaza 5 minutes ba ya cimma motocin su Dalla, yayinda su kuwa tuni sun mik'a hanyar data ratsa bakin kasuwa zata kuma wuce zata bi ta kaisu fantami daga nan su ratsa bayan gidan goje,
binsu yakeyi kib da kib haka yasa suka gane binsu akeyi,
tuni kuma an fara kiraye-kirayen sallan mangrib,
murmushin mugunta Dalla yayi kana ya juya akalar motarshi ya shiga cikin sitadiyon ,
shima binsu yayi a baya kusan a tare sukayi parking.
cikin azama da zafin nama ya bud'e ya fito kana ya zagoyo inda take ya bud'e mata tare da kamo hannunta ya juyo ya nufi inda motar Dalla take,
shima Dalla wurinsu ya nufa,
a tsakiyar sitadiyon d'in sukayi kicibus,
cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa Saifuddeen yayiwa Dalla alama da hannu akan ya bata hak'uri.
cikin izaya da tak'ama Dalla ya gyara tsayuwanshi tare da cewa.
"Baka da bakine ko iskanci ne zaka zo kana min mgnar kurame?."
cikin tsuke fuska Saifuddeen ya kuma yimishi alamu daya bata hak'uri, ganin haka Dalla ya kuma motsotsu kana yace.
"OK kyautarta ka kawo min kenan?, baka san waye Dalla bako? shiyasa ka biyoni da mace kana nufin in bata hak'uri ne ko?."
cikin sauri da jin dad'in Dalla ya fahimci abinda yake nufi ya tsare fuska kana ya gyad'a mishi kai alamar eh ka bata hak'uri.
wani fatsik'in murmushi Dalla yayi tare da lashe manyan lip's enshi yace.
"Hmmm aini Dalla bana bada hak'uri sai dai in bata ciki tunda ka biyoni da ita, gata kuma zata iya kashe kishin dake addabata wunin yau gaba d'aya ban hutaba kaga yanzu na samu wurin hutawa gashi tanada lafiyayyun kayan marmari a jikinta, yanzu zan mata inkiyata Dalla-dalla da budurcinta zan rab'i jikinta."
Ya k'arishe mgnar tare da kai hannunshi kan k'irjinta.
Wani irin wawan ihu da kururuwa Dalla ya kurma jin wani irin damk'a da Saifuddeen yayiwa hannunshi ba tare da ya samu ya isar da hannun nashi kan k'irjintan ba,
ihu Dalla ya kuma kurmawa jin Saifuddeen ya kuma murd'a mishi hannunshi har saida ya bada sautin b'as alamun ya k'arya mishi hannun, ihun daya sane yasa tarin zugan matasan dake cikin sauran motoci hud'un nan duk suka fito,
wando gaba d'ayansu 'yan kalarene domin duk kansu da makamai a hannunsu wasu da sanduna wasu da kataki wasuma da wuk'ak'e.
A guje suka nufin inda suke, shi kuwa Saifuddeen ko kad'an bai karaya da ganinsu ba,
asalima zagewa yayi ya fara dukan Dalla tamkar Allah ne ya aikoshi,
kunsan fad'an kurma babu sauk'i shiyasa basa tsokana basa tada husuma sabida sun san zuk'atansu basa iya jurar suga ana raini ko zalumci bare fajirci.
sam Dalla ya gaza bawa kanshi kariya,
shiko Saifuddeen dukan ƙaton gargadi yakewa Dalla tare da dandatseshi ta yadda bazai sake sha'awar wata d'iya maceba a duniyar nan har gaban abadan, ita kuwa Zaleeha ganin yadda suka nufo kansu haik'an k'adaran ne yasata sakin ihu tare da bubuga tsalle tanayi tana yarfa hannu tana cewa.
"Zomu gudu zasuyi maka illa zasu kasheka fa,
kazoo mugudu karsu isomu zasu illata ka."
ganin sam bai sararawa Dallanba yasa tayi sauri ta shiga tsakanin su kana ta rik'o hannayenshi tare da kallon fuskarshi tace.
"Mu gudu zafa su kashemu."
ido ya d'ago ya kalleta yadda jikinta ke rawa tamkar mazari tsoro da firgici k'arara a idanunta da ka ganta kasan cikekkiyar matsoraciya mai lasisi ce, haka yasa ya kamo hannunta kana ya juya da ita inda motarta take,
su kuwa zugan 'yan kalaren nan kansu suka nufo a guje ganin hakane yasa,
yajata da k'arfi sannan ya bud'emata motartata wurin zaman direba ya ajiyeta kana ya meda marfin ya rufe sannan ya sunkuyo kanta tare da kad'a mata yatsunshi biyu kana yayi mata alama dataja motar ta gudu, gane abinda yake nufine yasa ta jujjuya kai tare da zubda hawaye cikin haki tace.
"Mutafi zasu kasheka fa 'yan kalarene fa yaranshi ne."
ganin zata b'ata lokaci har suzo su sameta suyi mata illane yasashi buga marfin motar da k'arfi tare dayi mata gurnani irin nasu na kurame wanda in bawai ka saniba sai kayi zaton tsawa ya buga mata hakance ta kasance ga Zaleeha dan jin sautinshi tayi a sama haka yasa ta figi motarta a guje, tana jan motar suna isowa inda yake, yayinda shi kuwa yake kallonta so yake yaga fitanta a wurin, su kuwa suna isa inda yake ba tare da ya juyoba don shi dai kurmane bazaiji sautin takun k'afafunsu ba,
suna isa d'aya daga cikinsu ya narka mishi k'aton katakon dake hannunshi a tsakiyar gadon bayanshi kafin, yayi wani yunk'urinma
d'aya daga cikinsune ya dab'a mishi wuk'a a tsakiyar bayanshi kana ya zaro wuk'ar wanda tuni sun farka mishi rigarshi
wani irin razanennen ihu Zaleeha tasaka tare da zubawa bayanshi ido sabida tana ganinshi ras dan hasken motoci dake haska wurin da hasken fitulun dake zagaye da farfajiyar wurin
cikin tsananin tsoro da firgici taja motarta ta bar sitadiyon d'in,
tana fita kai tsaye gombe division ta nufa.

Shi kuwa Saifuddin tuni sun mishi illa sun daddatsa mishi kataki a tsakiyan bayanshi.
yayinda duk da haka bai bar kare kanshiba sai dai ance sarkin yawa yafi sarkin k'arfi gashi sun zomishi ta bayanshi kuma sunzo tare da makamai yayinda shi kuwa babu ko allura a jikinshi,
haka yasa sukayi mishi illah mafi muni a jikin d'an adam, haka suka rink'a hankad'ashi kan k'arafun wurin suna buga bayanshi a kai
saida sukaga yabar motsi kana suka dauki uban gidansu da Saifuddeen ya daddaga mishi jelershi sukaja motocinsu suka tafi,
yayinda tuni mazauna wurin kuwa sun watse don kowa yasan rashin mutuncin Dalla.

Shiru cikin sitadiyon d'in ba ko tsuntsu sai Saifuddin dake yashe tamkar mamaci,.

Ita kuwa Zaleeha bayan ta sanarwa hukuma, ganin ita macece kuma sananniya kana yar babban Malamin da akeji dashi a fad'in jihar dama k'asar bak'i d'aya yasa aka had'ata da police officer d'aya ya rakata gidansu dake New G.R.A...

A haka police officers na station d'in gombe division suka iso,
yayinda aka had'a da sosojin Anty kalare,
kana
suna isowa ganin halin da yake ciki ne yasa suka d'aukeshi,
kai tsaye general hospital Gombe suka nufa dashi, kai tsaye aka wuce dashi o,p,d. suna isa ma aikatan wannan sashin suka turo irin yan wannan gadaje na d'aukar marasa lfy,
tare dasa hannun hukuma aka karb'eshi bayan an duddubashi ganin aikin babbane ya kuma ji rauni sosai ne sai aka basu takarda wacce zata sadasu da babban likitan dake Medical Center.

Kan hanyarsu ta zuwa Medical Center d'inne d'aya daga cikin police d'in yayi saurin zaro woyar dake al'jihun wondon Saifuddin
ganin tanata kawo haske alamun shigowar sak'o,
text ne aka turo kamar haka.
```"Babana Saifuddin Kana ina? ka dawo kayi bud'a baki mana, ka sani duk muna jiranka kasan hankali na bazai kontaba in baka ci abinci ba."```
shiru police d'in yayi yana jujjuya kalaman, a ranshi yake cewa.
"Bawan Allah azumi ma yakeyi kenan."
sai kuma ga wani sak'on da yaga suna no daya turo text d'in Hayatuddin inda yake cewa.
```"Slm Hamma Saifuddeen ka dawo gida muyi dinner yunwa nakeji kuma kasan bazamu iya cin abinci ba in baka nan please ka dawo da wurin shalelen Ummi kaga ta k'i kula kowa sai cekiyarka takeyi kamar kaine autanta."```
haka nan yaji tausayin ahlin wannan bawan Allah ya kamashi,
dai-dai lokacin suka shiga harabar Medical Center Gombe,
kasan cewar da jami'an tsarone lokaci d'aya aka karb'eshi, aka fara bashi taimakon gaggawa
d'aya daga cikin doctors da sukayi kanshi ne domin bashi taimakon gaggawa don ceto rayuqarshi yayi saurin matsoshi ido ya zazzaro woje Cikin tsananin kad'uwa da tarin tsoro da tausayawa yace.
"Saifuddeen!."
sai kuma yayi maza ya fara had'a na'urar dai-daita nufashi wato oksijin kana yayiwa sauran doctors guda biyun alama dasu fara aikinsu,
mazuk'in numfashin suka manna mishi,
kana suka kunna wani wuta mai tsananin haske sannan suka matso da dukkan abin buk'atan aikin suka fara, duddubashi ciki da woje sam babu wani yanka ko karta a sauran sashin jikinshi sai na bayan nashi kawai, sai kuma alamun duka da katako dake tsakiyar k'ugunshi da bayanshi.
Kana sai suka koma duba kwokwon kanshi inda suka samu buguwar guda uku, amman iya karsu woje basu shiga ciki yadda zasu shafi hankalinshi da tunaninshi ba.

Sosai suka duk'ufa dan ganin numfashi sa ya dai-dai ta,
amman abin yaci tura,
sosai suke aikinsu cikin iyawa da gwarewa da sanin makaman aikinsu,
shiru kakeji ba motsi sai body language da sukeyi a tsakanin su.
Tsawon awa biyu sukayi a kanshi kafin suka samu nasarar dai-dai tuwar numfashi sa,
canza mishi gado sukayi kana Doctor Adnan ya turo gadon da kanshi ya nufi I, C U inda nos guda biyu suke biye dasu,
bayan ya dai-dai ta mishi komai sai ya fito kai tsaye office nashi ya nufa.
Yana shiga ya zame bisa kujerar dake mazauninshi, idanunshi ya rumtse da azabar k'arfi yana jin wasu hawaye masu azabar zafi suna tsatsafo mishi cikin jijiyoyin idanunshi,
sai ya kuma mik'ewa da sauri kanshi ya kifa da jikin bongon office enshin yana mai zubda hawayen.
cikin rauni da tausayawa murya na rawa yake cewa.
"Astagfurillah Allah na tuna ya Allah nasan ka fini sanin waye Saifuddeen ya Allah nasan kafi ahlinshi sonshi, ya Allah ka sauk'ak'awa Ummi wannan jarrabawa dake shirin sauk'a gareta ya rabbil izzati ka duba larurar Saifuddeen ka yaye mishi ka bashi lfy."
sai ya kuma koma ya zauna kan kujerar kana ya kifa kanshi bisa babbn table dake gabanshi,
dai-dai lokacin Doctor Arabi ya shigo tare da police officer biyu,
da sauri ya matso wurin abokin aikin nashi ganin yana kuka cur-cur tamkar yaro,
cikin kad'uwa yace.
"Doctor Adnan meke faruwa?."
kai ya jijjiga jikin son tsaida hawayenshi yace.
"Dr Arabi wannan da aka kawofa k'anin abokina Nuruddeen ne."
cikin firgici Arabi yace.
"Innalillahi Saifuddeen! to kuma me yayi musu meya tsare musu, meyasa zasu cutar da bawan Allah shida baya mgna meyasa suke son sa ahlinshi a rana Allah sarki Ummi da Rahma wayyo Hayatuddeen wayyo Raliyya da Raihana."
cikin kad'uwa police d'in yace.
"Alhamdulillahi abu yazo da sauk'i tunda kun sanshi."
cikin rauni Arabi yace.
"officer kun kama wad'an da sukayi mishi dukan ne su waye ne ina suke me ya musu?."
cikin kauda kai officer d'in yace.
"Ina bamu kamasu ba asalima bamu san su waye bane,
domin kafin mujema shi kad'ai muka samu a wurin babu ko mutun d'aya,
itama wacce ta sanar damu cewa tayi wucewa tazoyi ta gefen sitadiyon d'in ne so sai taji ihu shiyasa ta kawo rahoto,
to ganin a firgice take yasa muka had'ata da d'aya daga cikinmu ya rakata gida don ta gaza yin draving dan tace itama sun biyota ne ganin ta d'an tsaya shiyasa har suka samu daman fasa mata glass d'in gaban mota, so kunga bamu da hanyar samun wata shaida, abu mafi sauk'i a bashi taimakon gaggawa kana ga woyarshi ku nemi yan uwanahi ku sanar dasu."
cikin rauni Dr Adnan ya rink'a jujjuya kai tare da cewa.
"Innalillahiwainna'ilaihirajiun wayyo ni Adnan ta yaya zan tinkari ahlin Saifuddeen da wannan mummunan lbri da wanne baki zancewa Ummi Saifuddeen d'inta na asibiti cikin d'ayan biyu mutuwa ko rayuwa taya zan sanarwa Rahma halinda k'aninta ke ciki?."
ganin haka Dr Arabi yayi saurin cewa.
"Please officer ga adireshin gidansu kuje ku sanar dasu kana ku d'aukosu ku kawosu nan d'in."
da wannan shawarar police d'in suka nufi federal lowcost
babu wuya ya gane kwatancen da Dr Adnan yayi mishi,
a k'ofar wani babban gida sukayi hon minti uku tsakani mai gadin ya lek'o, ganin motar jami'an tsarone ya sashi bud'e k'aramar k'ofar ya fito cikin hausarsa ta buzaye yace.
"Sannunku lfy kuwa?."
cikin saisaita fuska mai jan motar yace.
"Wurin masu gidan mukazo bud'e mana gate."
cikin sanyin jiki da d'an tsoro ya bud'e gate d'in kana ya rab'a gefe suka shigo,
bayan sunyi parking ne biyu daga ciki suka fito,
hannu suka bashi bayan sunyi musabaha ne police d'in yace.
"Kayi mana sallama da Hayatuddeen."
to yace jiki a mace har ya juya zai nufi cikin asalin gidan sai ya kuma juyowa tare da cewa.
"Dan Allah ku gaya min lfy dai ko?."
ganin alamun rashin gamsuwa a gareshi ya sasu ce mishi,
"Saifuddeen ne tsautsayi ya ritsa dashi so ana neman danginshi."
cikin tsananin firgici da tsoro buzun nan ya kama kai tare da cewa.
"Innalillahi! Saifuddeen meya sameshi ina yake?."
cikin mmkin waye Saifuddeen menene nagartarshi shi wayene da Doctors ma suke kuka kan cutarshi kana kalli yadda ma'aikatan gidansu ma suka firgita jin yana cikin matsala, jiki a mace yace.
"Kaga yi maza ka mana sallama da k'aninshi."
cikin rawan jiki ya kusa kai cikin gidan nan mai azabar kyau.
A cikin gidan kuwa Hayatuddeen ne da Ummi suke sauk'owa daga benen ,
cikin shek'iyanci Hayatuddeen ya zame ya zauna kan last step kana ya manna kanshi da k'afafun Ummi dake tsaye a gefenshi cikin shogwab'a ya kalli Raliyya kana yace.
"Yaseen yau a bedroom d'in Hamma Saifuddeen zan kwana, nine auta amman anfiji dashi, komai nashi na dabanne Ummi da kantafa take gyara mishi side nashi, ni kuma nawa ko oho."
cikin wasa sukayi mishi dariya, Ummi ce ta shafa kanshi tare da cewa.
"Yoh kaida kake cewa ka fini sonshi ni uwar data haifeshi ma."
ido ya lumshe tare da cewa. "In banso Hamma Saifunaba to waye zanso a duniyarnan?, amman dai duk da haka nima ina son a gyara min d'akina yayi ta shek'i da zuba k'amshi koda rabin na Hamma na ne."
dariya Raliya tayi tare da cewa..
"Hayatuddeen waya isa ya medaka irin Hamma Saifuddeen ko Allah ma bai halicceku iri d'aya ba Hamma Saifuddeee mutun ne mai tsabta, kaikuma irin kune ake cewa kai dai kaga gaye a titi karkaga ma koncinsa, kaida inda ka tub'e wondonka nan kake tsallakeshi."
dariya sukayi baki d'aya dan shima yasan halinshi kenan.
Raihana kuwa cikin dariya tace.
"Karka damu autan Ummi shalelen Hamma Saifuddeen daga yau zan rink'a share maka side d'inka."
Dariya yayi cikin jin dadi kana yayiwa Raliya gwalo,
cikin raha tace.
"Au nanda yaushe zata koma ka dawo kana min k'aramar murya."
dariya sukayi baki d'ayansu banda Ummi da zuciyarta ke yawan tsinkewa yana fad'uwa ras-ras.

Shi kuwa buzun nan
wata k'ofa ya bud'e tare da kusa kai cikin wannan corridor d'in, wucewa yayi ba tare daya tsayaba cikin wannan had'ed'd'en parlour mai azabar kyau ya kuma baiyana wanda yakeda tsananin girma da fad'i kana ga steps d'in da zai sadaka da sama, sallama yayi tare da duk'awa gefen Ummi kekkyawar mace wacce zata iya kai 49 years to 50 kekyawace wacce yawan shekarunta bai samu nasarar b'oye kyantaba, Ummi kenan sai wannan d'an matashi autan nata da banzai wuce 17 years da yan watanni ba, Hayatuddeen,
Raliyya matashiya yar duma-duma wacce zata iya kai 23 years.
Sai kuma Raihana da zata iya kai 26 year da d'anta Affan wanda bazai wuce shekara biyu ba.

Cikin maida hankali kan buzun Ummi ta juyo cikin wani yanayi da takeji tun da yammacin yau d'in tace.
"Baba ila ya akayi ne?."
cikin sanyin jiki yace.
"Wasune ke sallama da Hayatuddeen."
mik'ewa Hayatuddeen yayi tare da cewa.
"Muje wata k'il Zakariya ne."
kai ya jujjuya mishi cikin sanyi yace.
"A a bashi bane folisawa ne, sunce Saituddeeen ne ya samu d'an hatsari yana asibiti shine akeson yan uwanshi suje."
wata iriyar zabura Ummi tayi kana ta rumtse idonta da azaban k'arfi sabida wani irin duhu da jirin da ya rufe mata ido a take,
wani irin rawa jikinta ya fara har cikin hanjinta takeji suna hautsinewa zuciyarta kuwa tamkar zata faso k'irjinta ta fito fili sabida tsananin razana da kad'uwa lokaci d'aya wata zazzafar zufa ta yanko mata
hakama Raliyya da Raihana shi kuwa Hayatuddeen gaba d'aya idanunshi ya zazzaro woje.
kusan gaba d'aya a tare suka fito Ummi kam duk jikinta rawa yakeyi tamkar mazari.

Hayatuddin ne yayi saurin isa garesu kana cikin tsananin kad'uwa da firgici yace.
"Ina Hamma Saifuddee ina yake meya sameshi ku kaimu wurinshi waya bugeshi?."
Raihana kuwa kuka takeyi mai cike da fargaba,
ita kuwa Raliyya direbansu taketa rabkawa kira cikin firgici da d'aga murya take cewa.
"Sule taho mu tafi wurin Hamma Saifuddee."
a hamzarce Sule direban ya taso wanda yayi ta bai jima da dawowa ba dan shi yana ƙofan Baba bello lokacin da abin ya faru kuma yayi ta kiran Saifudddeen alamun yana nemanshi baiga amsaba, to sai yayo zaton ko yayi wani wurin ne shiyasa ya dawo shi ɗaya,
Motarnda ke harabar gidan ya bud'e ya shiga tare da jawota zuwa gabansu,
dai-dai lokacin kuma police officer d'in yake cewa Hayatuddeen .
"Shiga mota muje yana asibitin Medical Center ne."
firgici da kad'uwan Ummi ya tsananta jin k'irjinta takeyi yana buguwa da azaban k'arfi wata fargaba da razani ya rufeta,
jiki na rawa ta shiga motar da Sule ya kowa gabanta sam ta kasa furta ko k'ala domin harshenta ya mata nauyi jiki na tsuma ta shiga motar, wonda tuni Raliyya da Raihana sun shiga
shi kuwa Hayatuddeen cikin kaifin basira da zurfin tunani irin nasu na maza yace.
"Ummi kuje, bari in d'auko kud'i zan taho a U.D. d'ina."
jin haka yasa Sule jan motar yabi bayan motar police d'in kana suka fita suka nufi Medical Center Gombe.

Shi kuwa Hayatuddeen , a guje ya koma cikin gida sam bai lura da Affan ba d'an Raihana wacce itama Raihana ta mance da d'an nata sabida firgincin halin da d'an uwanta ke ciki,
to bare kuma Hayatuddeen da Ummi,
cikin sassarfa ya haura matakalan benen har yana take steps bibbiyu,
direct d'akin Hamman nashi ya shiga bayan wasu yan mituna sai gashi ya fito,
yana gyara zaman kud'i a cikin al'jihunshi still bai kula da Affan ba ya wuce yana fitowa harabar gidan ya figi mashin nashi cikin azama ya nufi asibitin.

Su Ummi kuwa bisa jagoran jami'an tsaron suka isa k'ofar d'akin da Saifuddeen yake,
sai dai ba damar shiga kanshi.
suna isowa bakin k'ofar Ummi ta rumtse idonta da k'arfi cikin tsananin hargitsin rayuwa tace.
"B.......

Hmmmmmmm. Wasa farin girgi karfa ku manta na gaya muku labarin sashi-sashine, littafin yana tafe da ababe masu tarin yawa,
Salon Saifuddeenfa salone da zai sanyaku shauƙi bage farfaɗo da tsohuwar soyayya hmmmmmm dafa sauran rina a kaba, ku dai ku biyoni a baya.

By
*GARKUWAR FULANI*
8/18/20, 7:52 PM - Ummi Tandama: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*NAKASA BA KASAWA BACE*

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.