Complete Hausa Novels

Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel

Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt

Chapter 6 of 24

*Page 6*

Sai da ya shafe about awa É—aya yana, abu É—aya yana, abin tausayi duk tafita hayacinta dakyar take ajiyar zuciya, kifa kanshi yayi akan fuskanta yana lashe ruwan hawayen da yake zuba daga idanunta, tabbas yau yasame nutsuwa fiye da tunaninshi,
so yake yajanye daga jikinta, amma yanayinta ya hanashi, sabida itace mace ta farko da yayi mu'amala da ita babu condom, janyewa yana ya koma gefenta ya kwanta yana maida numfashi, a gajiye rufe idanunshi yayi yana tuna irin matan da yayi lalata dasu, so yake ya haÉ—asu da ita ko, zai gane akwai bambanci,."Hmm Ubaidata tafisu nesa bakusa ba,"yace.

Matsawa yayi, gurinta ya rungumeta,sosai yake jin tausayinta ya shiga zuba mata albarka dan yaji kome daga gareta, kaman yanda yace zatayi citta me yaji kuwa dan musaman aka sakata aÉ—aki na tsawon sati biyu ana mata dilke, tashi yayi ya sauka a gadon banÉ—akin yaje ya haÉ—a musu ruwa, zuwa yayi ya É—auketa cak, ya kaita banÉ—aki ya taimaka mata ta gasa kanta yanda ya dace, sannan sukayi wankan tsarki suka fito,

wani rigar barci Æ´a É—auko mata, tasa sai binta da ido yake, dan ta shayar da shi mamaki sosai,
k'wanciya sukayi yana manne da ita,

***
A ɓangaren maahkur kuwa, tunda ya ajiye mata laida yashige ɗakinshi, cire kayan jikinshi yaƴi, sannan ya shiga bandaki ya watsa ruwa, da alawala yafito, sallar shafa'i da wutiri, yayi sannan yayi addu'a ya shafa ya kwanta,

Washi gari....
Tunda Mashkur ya dawo sallar asuba, be kwanta ba ya shiga banÉ—aki yayi wanka, ya shirya cikin É—anyen boyal me masifar tsada, skyblue, takalminshi fari yasaka sai hularshi itakuma skya blue ce yayi kyau turare ya fesa , kallon kanshi yayi a mirro sannan yasaka, agogonshi silver, yayi kyau ba laifi.

Yana fita falo ya nufi É—akin Zubaida, knocking yayi ba'a buÉ—e ba dan haka ya kama handle É—in kofar ya murÉ—a yashiga dai-dai tafito kenan daga wanka, goge gashin kanta takeyi dan haka hankalinta yana kan abinda take,

Hankalin shi yana kan wani abu ya dauka yana, dubawa kuma y juya mata baya dan haka be san yadda take ba, gyara murya tayi sannan tace,
"Ina kwana Ya mashkur,"
juyowa yayi yana amsawa, ganin yanda take, daga ita sai towel, yayi saurin kauda kanshi yace,
"Lafiya lau, ya kika tashi ya bakunta, zanfita zuwa gida daga nan zan isa Fada, dan nasan yau gidan nan baza'a rasa masu zuwa ba, kin gane ko,"

gyaÉ—a masa kai tayi, cikin nutsuwa, be sake kallonta ba yafita sai da ya isa bakin kofa yace "sister sai anjima"

mamakine ya rufeta, shi kuma wani irin mutum ne, haka girgiza kai tayi sannan tacigaba da gyara jikinta,

.....
Ubaidatu tariga Maina farkawa wajen karfe shida da rabi, dakyar ta mike tashiga ban É—aki, ta sakw haÉ—a ruwan zafi, tashiga a gurguje sannan tafita a rawan ta É—auro alola, tafito sallah ta gabarta sannan ta koma inda Maina yake ta tasheshi, a sanyaye tace,
"Yaya maina katashi, munrasa sallar asuba, ynz kuma shida da arbain ne kar rana tafito bakayi sallah, ba babu kyau."

Ta karshe maganar tana kallon fuskanshi, buÉ—e ido yayi a hankali ya zubasu akanta, murmushi yayi mata sannan ya mike ya fita daga É—akin. ya koma É—akinshi.

A can yayi sallarshi, sannan ya shiga banɗaki yayi wanka, shima ya shirya cikin farin shadda, ya fito ɗakinta ya kome yasamu ta gyara ko ina tsab har tayi wanka, murmushi ya sakar mata sannan yaje har inda take shafa mai yakarɓi robon man ya latsa a hanunshi ya shiga goga mata, cikin wani irin yanayi a nan suka lalace,

Koda mashkur ya isa gidan Momma, yasamu yan maiduguri, wasu zasu je gidan shi dan sun kunsan tafiya gaishesu yayi sannan ya wucce É—akin, Momma inda suke zaune da wasu daga cikin kannenta da matan Yayunta,
Hira suke irin na zumunci, da sallama ya shiga durkusawa yayi ya gaishesu, cike da jin kunya,

Zuciyar momma fari tass, haka take jinta ba kome ya kawo haka ba, sai dan samun nagartaccen É—a, kuma me ladabi da biyayya, girgiza kai tayi a ranta tace,
"Ya Allah ka albarkaci rayuwar Mashkur da na yan uwanshi baki É—aya,"

Zuba mata ido yayi cikin nutsuwa da shagwaɓa dan mashkur indai a gaban Momma ne kullum komawa yaro karame yake yace,
"Momma yunwa."
Duk mutane É—akin suka zuba masa ido, yanda yayi maganar ko Zuhra bazatayi ba, kuma, koda ya faÉ—i haka tsuke fuska yayi yana kallon wayarshi,
"jeka zan sa Zuhra takawo maka, amma ai na aika muku da abinci, kashigo." tace mashi,

"Ok" yace sannan yafita daga É—akin,

Abinci tayi mashi mara nauyi sannan ta haÉ—a mashi da farfesun kaza, tabawa zuhra takai mashi.

Satinsu biyu suka kai matansu makaranta,shi da Maina wanda ya É—an same kintsi, a cikin sati buyi, dan tunda Ubaidatu ta gane irin mijinta ta cire raki da ta mike tsaye dan ta rikeshi da hanun bibiyu.

Suna kaisu suka juyo, zuwa bauchi, basu shigo ba sai kusan hudu na dare dan haka gidan maina da yake kusa nan suka yada zango,

Washi gari monday sukayi sallama kowa ya wucce wajen aikinshi.

Farin cikine fal zuciyar mashkur dan tunda a can zuciyarshi yake kaiwa da kawowa, dan cike yake da son yin tozali da ita, uwa uba kewarta da ya cika zuciyarshi,

Da wuri ya taso aiki a gurguje ya sake kayanshi, sannan yafito dai-dai hanyar wuccewarsu da motarshi ya pake a wajen ya hawu, samar motar ya xauna yana kallon hanyar da zata ɓulo,

dukda hira suke da zubaida a wasup amma be bata hankalinshi kaman yanda yazubawa hanyar da Shkurah zata fito,

Can yashiga jin muryan É—alibai, kashe datar wayar yayi yana me raraba idanunshi.
Hangota yayi rataye da jaka,a kafaÉ—arta riga da sekit É—in unifoam É—in ya É—auketa cak,
zuciyarshi ce tacigaba da bugawa a hankali har suka iso gurinshi, zasu wuce shima binsu yayi suna tafiyan dashi,

hiran da suke duk suka daina, yana tafiya amma yana satar kallonta, duk sai taji ta atakure dan haka tare napep suka shiga yi amma sukak'i sabida É—aurowan hadiri lokaci guda, karshe shi ya tsida musu napep kuma yabiya kuÉ—in, kallonta yayi sannan yace,
"Shkurah, "

É—agowa tayi suka haÉ—a ido,da saurin ta saukar da kanta tayi tana k'amk'ame jakarta. sai murza hanun jakar take, taki sake É—ago kai, ga ruwan da ya sauko kaman da bakin k'warya.

Me keken ne yace,
"Bawan Allah zamu tafi, kaga ruwan ya sauko da karfi"

gyara tsayiwarshi yayi sannan yace,
"Nima tsayi dani tayi, kace ta min magana sai na barku kutafi,"

mamakine ya rufe su maryam,
me nape da ya k'agu ya tafi yajuya, yace
"don Allah kisallame shi, mana mutafi,"

"Kyaleta malam kuje ga kuÉ—inkan" ya mika masa kuÉ—in, shi har ya juya,zai tafi ya tsinkayo muryarta tana cewa,
"malam maida mashi kuÉ—inshi, muma iyayenmu sun bamu kuÉ—in komawa gida, bana son haka, duk kabi ka uzura min"

murmushi yayi, sannan yabar wajen zuciyarshi cike da nisha, amma kuma ya yanke hukunci kauracewa hanyar har na tsawon kwanaki, yana cikin wannam tunanin ne, aka kirashi yashirya zasu wani aiki a lagos,

Bayan me napep yaja, sun fara tafiya, Salmah ce ta gaza hakuri tace,
"Wallahu baki da kirki, wannan mutumin yana da mutunci, tun daga ranar da ya kusan bugeki yake bibiyarki, zakiyi mamakin yanda muka saka miki ido dukkanmu nan muna musan dalilinki yasa yake zuwa nan ya tsaya kuma ke da kanki ranar kika ce badan shi ba da wasu yan iska sun miki rashin mutunci, masa kallon mutumin kirki beyi kama da na banza ba, kuma Allah kowa yaga yanda yake miki yasan sonki yake, dubeshi mana, kafin asame irinshi sai kin sha bakar wahala, my dear ki fahimce ni"

"Wallahi ni dai banga aibunshi, ba asalima, kun dace, a cikin kusan wata guda, ya faÉ—a kogin sonki don Allah karkiyi wasa da damarki" inji bebes,

Dariya maryam tayi, tace "yarinya kinyi, ba mamaki da zafinshi yake, kuma yanda nake ganinshi, kaman ma'aikacin tsorone, kawai baby, inda yazo da tayinshi karki mana bakin cikin shiga wancar motar"😜

Shiru tayi bata san me zata iÆ´a ce musu, ba amma kuma bazata iya son mutumin da suka haÉ—u a hanya ba, toh taya ma haka zai fari God forbid,

......
Bayan sun isa gida me napep ya ya basu canji taki karɓa tace,
" jeka kaima Allah yaci da rabonkane,"

godiya yayita zuba musu maryam da bebes suka nufi gidansu ita da salmah da rafi'a suka shiga gida, duk wannan hiran da akeyi tana ji kulle abin tayi a ranta,

Suna shiga cikin gida, kowa ya nufi wajensu ganin Babansu yasa rafi'a sake murmushi tace,
"Baba nikan makaranta katuramune ko tsayiwa da samaruka, amma ka tambayi sallama sune yan bada shawara."

Tana gama faÉ—an haka tashige part É—insu a guje, dan tasan shkurah bazata kyaleta ba,

tsaresu yayi yana kallonsu jikinsune ya É—auki rawa,
"Bangane me take nufi, ba ku min bayani yanda zan gane inba haka ba zan zaneku,"

A nutse salmah tayi mashi bayani yanda ya fahimta, tana gama faÉ—a mashi Aisha da take kicin itama ta faÉ—a mashi yanda yayi musu hidima a haÉ—uwansu,

mai da kallonshi yayi kanta sunkuyar da kanta tayi kasa, murmushi, yayi sannan yace,
"Me yasa kike, masa haka kuma har hidima yake miki baki iya ce mashi kingode, me yasa"

Muryanta na rawa ta É—ago kai takalle Alhaji Hammayo, tace
"kai kace karatu, katuramu ba shashanci ba." shiru tayi idanunta na zubda kwalla ta cigaba da cewa.
"Baba ban wulakantashi ba amma kuma ai nimace ce, kuma na fito gidan mutunci da kima, akan hanya zan tsaya ina kulashi, nasan nayi kuskure rashin masa godiya, amma banyi haka da manufa ba,"

"Jeki É—akinku" yace mata,

tana shiga falo, jikin Umma tazube tacigaba da kukanta,shafa mata kai umma tayi, hankali ta É—ago kai tace,
"Ummana laifene abinda nayi, kuskure na aikata, don Allah umma koda zanyi kuskure a rayuwata ki É—auka Qaddaratace tasame ni, don Allah karki juya min baya"

rashe mata hawaye Umma tayi sannan tace,
"Wa yace miki, uwa tana iya juyawa y'ay'anta baya, koda sunayi ni bazan juya miki ba auta, dan nasan kowani bawa da yanda Allah yake jarabta shi, karki sake faÉ—an haka."

Tashi tayi tana dariya tashiga É—akinsu,

Tun daga ranar bata sake ganinshi ba, tun abin be damunta har yakai idan suka biyo hanyar ta dunga raba idanunta kenansu Bebes suna lura da ita,

sannun a hankali tashiga musu maganarshi takance,
" Kunga wannan sarkin nacin yanzun ya daina zuwa, daman yan amore ne, hmm"

Idan sukaji haka shareta suke suyi banza da ita.

A cikin satin na biyu da ta ganshi Bebes da Maryam da Salmah suka haÉ—u a masalaci, salmah tace.
"Shkurah fa tadamu da, rashin ganin mutumin nan dan ko jiya da muka dawo , sai da tasake min maganarshi, ina ganin kaman sonshi take,"

"Kina ganin dagsk sonshi take, " inji maryam,

"Eh mana idan baso ba meye, zaisa takoma wata silent, kuma haka kawai zaki ga ta zauna tana rubutun abinda ya faru, na haÉ—uwansu am think that ta faÉ—ane" inji Bebes.

"Toh idan muna tamtama, idan tazo mana da maganarshi mu dizgata mana muga yanda zatayi." inji salmah.

duk sai sukayi na'am da shawaranta, aikuwa ana tashi, sun zo inda yake zaman jiranta kallon wajen tayi fuskanta É—auke da murmushi tace,
"Ai kunga inda yake tsayawa, yayita binmi Allah sarki"

"Mtsew ina ruwanmu, da inda yake tsayaewa ince damuka miki magana banza damu kikayi sai ynx da kika ga babu sarki sai Allah shine zaki addabemu, nan zayita binmu amma ko kallon arziki baya samu daga gareki sai ynxne zaki damemu da maganarshi dalla malama karki sake takura mana."

Allah sarki shkurah sarki faÉ—a yau itace ake muzanta mata akan abinda zuciyarta take azalzalarta da ta amayar dashi, kwalla ne masu zafi take zubdawa inda kuka yaci karfinta tsayawa sukayi suna kallon ikon Allah,

Durkusawa tayi a wajen tafashe da wani irin kuka me cin rai da taɓa zuciya suma sai suka biye mata suna kukan, sun zagayeta har da Rafi'a itama kuka take sosai.

Daga can ya hangosu dawowarshi kenan daga tafiya karkata kan motar yayi inda yayiwa yaranshi hanun da sutafi.

Wajensu yazo yayi parking sannan ya sauko, a hankali yake takawa dan ya gama gajiya ganin kaman itace a durkushe yasa ya kara saurin tafiyarshi, juyawa salmah tayi ta ganshi zatayi magana yasa hanunshi a bakinshi dan yaji tana magana ne,

haka ma sauran hanasu magana yayi ya durkusa, gabanta inda take cewa,
"Allah shine shaidana dan kaina bazan damu, da maganarshi ba zuciyata ke ingixani da nayi magana akanshi, toh meye laifina da zaku min masifa,"

duk cikin kuka take wannan maganar, tausayi da sontane suka cika zuciyarshi,
"lallai yau zaku sha, dukka shine kuka samin ita kuka, maza kubata hakuri." kaman daga sama take jin maganarshi dan haka da sauri ta É—ago kai shine kuwa,

Share hawayenta tayi ta mike ta ɓala mashi harara tare da murguɗa mashi baki, take kuka ya kare.

Murmushin nasara yayi dan haka tana gaba shi yana baya rike da jakarta da ya rigata É—auka, su maryam kuwa suna bayanshi.
A gaban murmushi take, shima haka,

sun jima kafin dai daga karshe shi ya kaisu gida,

***
Har ynx ya gaza buÉ—e mata zuciyarshi, dan so yake, ta gama skull, tunda yasan gidansu jifa jifa yana zuwa,

Lokaci yatafi dan har sun kunsan fara jarabawa fita saura wata biyu.

*Muguwar Gamo*
Yau tun karfe uku ake sheka ruwa, har kusan sutashi sannan ruwan ya tsagaita, aikuwa tashesu da sauri suka fito abinda basu hawa mashin dan haka duk mutum biyu sukayi ta hawa, saura ita gashi ruwan ya dawo,

busu jakarta tayi suka tafi dashi.

Mashkur wanda be jima da dawowa ba ya tambayi wanda yasa tsaron shukrah ko suntashi yace mashi eh sauran sun tafi saura ita amma zaibi bayanta har tasame abin hawa.

Kashe kiran yayi ya É—auki lema da rigar ruwa yafito kiran maina ne yashigo masa yace gashi a hanyar gidanshi nan zuwa,

be saurari me zaice ba ya kashe kiran,

tafito dai-dai jibrin Aminu model school shi kuma maina ya tawo kenan ya hangota, yanda kayanta ya kwanta a jikinta, riga da wandone a jikinta duk sun kwanta sabida ruwan da ya bugeta,

sai da yasame guri yayi parking yana kare mata kallo tsaye take a gurin tana jiran mashin ko nape ai wani mugun sha'awartane ya make shi, duk da yayi aure be fasa bin matan layi ba, shaiÉ—an ne yayi mashi huÉ—ubar tsiya yafito daga motar ya tunkareta, kuwa da rigar ruwa yana zuwa wajenta ya warware zai kai hanunshi, wai zai saka mata ja da baya tayi tace,
"karka taɓa ni malam"

dake yasaba da hidimar mata ganin kowacce ma haka take aikuwa kaman an aikeshi yakai hanunshi kugunta,
a razane ta É—ago ta kifeshi da mari wanda sai da yaga wasu stars

dai dai isowar Mashkur kenan tun daga nesa yake hango dramarsu ai kuwa fashewa yayi da mugun dariya ya fashe har yana dukan sitiyeri fita yayi fuskanshi É—auke da murmushi ya isa wajen mika mata rigar ruwa yayi sannan ya kalle maina a yake rike da kunci yace,
"Bro ya dae karike fuska"

kallon mamaki shukrah tayi masa tace,
"daman kasanshi ne, rashin hankali ya nime yi min ni kuwa na kwaÉ—a mashi mari muje kakaini gida hankalin Ummana yana tashe."

Ko takan maina be biba, ya juya suka tafi, a mota ya kalleta yace,
"Don Allah karki sake fita haka idan ana ruwa kinji ko"

É—aga mashi kaitayi, har gida ya kawo ta, sannan ya mata sallama fuskansu É—auke da murmushi,

Tunawa yayi da maina da sauri yaje inda yabashi aikuwa yana wajen rike da fuska, da sauri ya fita daga mota yaje gurinshi yace.
"Maina me yasa, ka tsaya a ruwa idan mura ya kamaka fa,"

"Kana ganin, ta cimun mutunci, ta keta min duk wani jinkaina, kace na tafi ita wacece a gurinka meye haÉ—inka da ita, a iya sanina baka niman mata meye ke tsakaninku"

duk wannan maganar,a faɗa yake tambayar Mashkur, shima tsawa ya daka mashi wanda be taɓawa wani ba yace,
"Tambaya kake, toh ita nake so, kuma da ita zan rayuwa wallahi lokacin da kakai hanunka da niyar taɓata da ina kusa da kai sai na harbaka, don Matata ce, Ina sonta da duk xuciyata, da kuma ta iya kare kanta tabiyani, Wallahi tallahi maina koda wasa ka sake yunkurin kai idanunka kanta, sai na nak'asaka, ido kawai ina kuma ka kai hanunka hmmmm zaka sha mamaki wallahi."

yana faÉ—an haka yabar wajen zuciyarshi tana tafasa.

Sabida bakin ciki da maina yake ciki naushin glass din motarshi yayi idanunshi yayi jajur yaÉ—a murya yayi yace.

"Wallahi sai na sata kuka sai na wulakantata sai naketa alfarmanta, sai na jefata wata duniyar bakin cikin da damuwa, sai tarasa tundun dafawa, Mashkur idan na barka da ita cikin farin ciki, ba jinin sarauta nake ba,

yana gama faÉ—an haka yashiga motarshi yabar gurin.

Shima mashkur haka,

*Hmmm kusan six read more, nayi muku, ga ciwon idanun da nake fama da shi be hanani nayi muku typing ba, kuyiwa Marubuta adalci dan suma suna iya bakin kokarisu wajen nishaÉ—arta daku, amma abin haushi dakyar zamu sami sanun ko madalla, Allah yaga zuciyata idan kasaka min tnx bana bukata ko Hrt rike kayanka dan idansume nima zan iya jinjinawa kaina,kuyi hkr iya gskyna na faÉ—a*

_Toh fa me maina yake shirin aikatawane sai naji daga bakinku, Yawan comments É—inku yawan read more É—inki_

*Ina yinku_💋

#Mashkra💘
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

Al-Musawwiru Al-Gaffar Al-Wahaab Al-Qahhar👏

     '''Allah sarki Maina ashe haka kayi bakin jinin, H'ello makaranta, Sunan Buk ɗin zaku duba Qaadaran Rayuwartace zaizo mata a kai-kaice dan haka, ku biyoni a sannun muji wani irin kaddara ce haka Fatan Alkhairi nake muku'''🌹💋💕

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.