Complete Hausa Novels

Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel

Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt

Chapter 13 of 24

*Page 13*
Ga baki ɗaya yaji, kome ya tsaya masa cak,  mikewa yayi ya ɗago idanunshi wanda sun kaɗa jajuri kaman gaushi, jijjiyar kanshi, sun tashi raɗa-raɗa, sauke idanunshi yayi akan Salmah da take kuka, a rakuɓe a guje tashigo, tana zuwa gabanshi ta ɗauke shi da mari, tasake ɗauke shi da mari durkusa kasa tana kuka me cin rai,
cikin muryan kuka tace, " daman ba sonta kake ba. shi yasa ka zalunceta, anya kai mutune kuwa, kasan zunubin da kayi, kuwa, wallahi koda Bestie tana raye, nasan bazata taɓa yafe maka ba, koda zata yafe maka, sai na hanata, kaman yanda kasasu kuka, kaima sai ansaka, kafita, kabar gidan nan,"

       Inji Aisha Abbas kenan babbar kawar Shkurah. salmah ce tazo ta ɗagata tana kuka, itama ko kallonshi basu sake ba.,

       Baba galadima shi yayi gyaran murya yace.
"Meke faruwa, ne? sannan kunsamu a duhu kifitar damu haske."

         Ashe kuka rahama ce, dan mashkur ya nemi kukanshi ya rasa, kallon baba galadima yayi sannan yace.
"Me kuke son kusani, Maina ya rabani da kome, ada ina kallon kaina kaman ba maraya ba, amma daga ranar da maina, ya ruguza mana, farin ciki nake jin kaman narasa kome na, Idan nace Allah ya wulakanta maina, kaman zunubi nakara yi, Amma mun barshi da Allah, Wallahi ina jin bugun zuciyarta tana raye bata, mutu ba duk inda take zan nimota, zan kawota amma don Allah karku sake cewa ta mutu.."

      Haka yayi ta sambatu kaman mahaukaci, komawa jikin mommah yayi yana ajiyar zuciya, dan babu kuka, babu hawaye sun kafe zuciyarce kawai take.Nata kukan.

                Sarki hussain da aboksn tafiyarsa suka, lallaɓa sikayi musu, sallama dan izuwa yanxun jikin Abba yayi sanyi yasan maina kuma zai iya kome dan ba imanine da shi ba balle tsoron Allah,

     Mommah ta kalle sarki hussain tace.
"Abbansu kaje da shi, ni zan gana da mahaifiyar shkurah Classmater É—ina ce, tun muna, Fggc yola zuwa gobe sai na tawo."

            "Ba kome kausar, kije kawai,amma zan tafi da Son Asibiti dan naga kaman, har yanzun da sauransa." inji sarki hussain.

        Komawa ciki, tayi ta kalle Mama tace.
"Kaini wajen Habiba,"
          part ɗin Umma aka kaita, duk yaranta sun kewayeta, suna zubda k'walla da sallama mommah tashiga cikinsu, tana kallonsu, fuska a sake tace.
"Kimanin shekaru talatin da huÉ—u kunsan wacece ita," ta É—ago tana kallonsu sannan ta maida idanunta kan Umma tacigaba da cewa.
"Me yasa kika ɓoye musu Asalinki, Habiba me yasa kika baki faɗa musu, girman darajarki ba, kin zauna shiru, idan baki manta ba ranar da muka gama makaranta na faɗa miki babu kyau bijirewa Iyaye, ko baɗe ko bijima, zaki zubda hawaye, Mahaifinki yaga ke marainiya tasa ya bada aurenki ga ɗan ɗan uwanshi Aliyu sarki yola na yanzun,  Mahaifinki yayi miki tanadi. na musaman yaso kicigajiyar zama cikin gidan sarauta amma so ya buɗe miki ido kika k'i, Yau kimanin shekaru talatin da huɗu, bakiyi kuka ba sai yau, a ranar da na miki magana habiba marina kikayi, sabida na faɗa miki gaskiya..."

      Kukane yaci karfin Mommah inda tasa hanunta ta rufe fuskanta, haɗiye kukanta tayi sannan ta kallesu Abubakar tace.
"Kaman yanda kuka sani, sunanta Habiba Abubakar yola, yanzun haka babban yayanta shine wazirin yola na yanzun, kasancewa ita É—aya ce mace, a cikin maza tara, a cikin gidansu yasa Babanta ya É—auki son duniya, ya É—aura mata karkuyi mamakin haka,Ni da Habiba yan uwane, Mahaifiyar Habiba, kanwar Babanane, kuma itama itace , auta agunsu Babana,"

      Jan numfashi tayi, sannan tacigaba da cewa,
Mahaifin habiba abokin babana ne, dan tare sukayi karatu a Oxford university dake birnin london, dansu huÉ—une, da sarkin katagum na da Da sarkin yola na da,
        Bayan sun gama suka komu kasarsu inda kowa ya dawo jaharsa. Mahaifina tun kafin ya tafi karatu aka ɗaura masa aure da Mahaifiyana kuma, ya tafi ya barta da karamin cikin Bakura, Sarkin yanzun kenan dan haka yana dawowa ya fara aiki a lagos,

      lokaci ya tafi, dake mahaifiyata ba me yawan haihuwa bace, shi yasa muka kasance mu shida, sai sauran ɗakin, Aunty Habiba wacce ake kira da  Yana, tazo wajen babana hutu a lagos, sai akayi dace, Mahaifin  habiba shima yazo, har gidanmu wajen babana, ana yaga habiba yace yana so.
       Aikuwa sanin halinsa Babana be yanke nime shawara ba ya yanke hukunci inda, a cikin satin yabi jirgin kasa sai maiduguri, nan yaje yasamu kakanmu da batundan har yayiwa Abubakar alkawarin ya bashi ya ture magabatanshi, dan lokacin Yana tagama makaranta, kakanmu jin haka, yace ba damuwa,

       Sati na kewayowa sai ga baki daga yola, nan aka basu auren Yana, ganin sutafi su sake dawowa aka ɗaura aure aka kwanakin tarewa, wata biyu.

       Cikin ikon Allah wata biyi ya cika suka kawo kome na bukata, daga nan aka basu ita,
       Yana tana da hakuri sosai, dan haka koda aka kaita cikin manyan mata bata taɓa samun matsala dasu ba,   wata da ta shiga a wata aka sami cikin Habiba, lokacin nima mahaiyata yana ɗauke da tsohon cikina,
         Cikin yana matukar bata wahala Allah sarki ashe ta sanadin Cikin zata rasu, koda cikin yashiga watan haihuwarsa sai ya kasance bata iya barci abun cikin yana zuwa ya tokareta, a haka , har ta shiga kwanankin haihuwarta,
        Ranar da ta haife habiba ko kallon abinda ta haifa batayi ba, ta koma ga mahaliccinta, Abubakar ya shiga wani hali,

         Tsiran tskanina da Habiba kwana uku, dan har Mamata tazo, jijjigar mota yasa nakuɗa yatashi mata, daman Habiba taki karɓan madara, tana haihuwana tace.
"Don Allah ku bani, ita na shayar,"

       ganin haka, suka bata dan har lokacin, Abubakar baidaina zubda hawaye ba,

             Kwanansu Mamata goma, suka dawo lagos inda tacigaba da rainonmu har muka kai yaye, aka ciremu a nono,

       Muna da shekara huɗu, aka samu a makrant, cikin kulawa muka,gaba primary, anan Abbanta yace a maidamun arewa muyi karatun sakandiri.

            Cikin ikon Allah muka, fara bamu taba samun matsala ba har muka isa aji shida anan ne aka turo Hammayo bautar kasa, yola, ana turasu makarnt sai aka turoshi makarantarmu, tunda ya gabatar da kanshi, da kuma yanda Allah yayi masa baiwar kyau yan mata suka mace, akanshi.

        Daga cikinsu kuwa, har da habiba, kaman ba jinin sarauta ba, gashi zuwana lagos Mamata take faɗa min ai amana miji, ni ɗan sarkin katagum ita kuma, ɗan sarkin yola,  ban damu ba dan nasan gidan da nafito, haka ma Habiba, sai dai kashhh, zuwan wannan malamin ya dagula kome,habiba tayi nisa naso ta gane amma taki,  haka na zuba mata, ido dake wani lokacin bama zuwa, lagos hutu, a yola ko maiduguri muke hutunmu,

      Soyayya me karfi yashiga tsakaninsu, nayi nayi ta bari taki,
      Ranar da muka gama karatu ni maiduguri aka tafi dani, ita kuma tana yola bansan me ya faru ba, sai dab bikina nazo wajenta dake za'a riga yin nata, naji wai ta auri ɗan bautar kasa ya tafi da ita bauchi, nayi kuka kaman, idanuna zasu cire.
Ita ta É—aura muku, abinda ya faru,."

           Juyawa mommah tayi tana kallon Umma wacce take kuka, kaman me, sannan ta haɗiya kuka amma idanunta basu bar zubda kwalla ba, tace.
"Lokacin da muke haÉ—a kaya, kika ce narabu da Hammayo, har naji haushi na mareki, wallahi na ji zafin marin ke kike kuka amma ni nake zubda hawayen dan nasan gaskiya kika faÉ—a min, amma so ya rufe min idanun. bayan tafiyarki nima akazo É—aukana, ana nakewa hammayo kwatancen gidanmu, yace zai zo amma sai na kwana biyu.
        
    Tunda nadawo nake son faɗawa Baba, amma ina tsoronshi, ana cikin haka, sai gashi, Aliyu yazo dan mu fahimci juna, tashi ɗaya na faɗa masa ra'ayina ina da wanda nakeso.

    Cikin ikon Allah aliyu ya fahimce ni, sosai daga nan ya tafi gida ys sanar da mahaifinsa yanda mukayi, koda babana yaje fada, sarki ya nuna masa alfanun ya bani wanda nakeso dan kar ashiga hakkina, a lokacin Uwar gidan Baba hajiya zainabu, muna kiranta ya goggo, ita mahaifina ya kira ya faɗa mata, abinda nayi yayi masa zafi, sai aka ɗauki kanwata Zaituna, wacce take aji ukun sakandiru, aka bawa aliyu, ni kuwa aka sani na nemo hammayo, ran baba ya baci sosai washe gari ya bada sadakata""

     kukane ya kwace mata har takifa kanta akan cinyoyinta sai da tayi ya isheta sannan tacigaba da bada labarinta.
"Aikuwa a cikin abinda befi awa huɗu ba baba ya haɗa min kayana " yace kije nagode Habiba, amma duk abinda yaameki karki tako min nan, kinji ko"   haka babana ya korone.

     Dan kuɗin da hammayo yake rikewa na abinci dashi yayi mana, kuɗin mota har bauchi daga bauchi muka, wucce misau.
nazata zan same kyakyawan tarɓa sai nasame akasin haka,
      dan koda hammayo ya labarta musu abindaya faru, Innarshi da Babanshi nan suka tasashi a gaba da faɗa inda suke shiga banan suke fita ba, nayi kuka,nayi danasani mara amfani dan haka na haɗiye kukana, aka bamu ɗakin da ke gefen gidan.

     Da farko zaman ba laifi sai da hammayo ya kuma yola, nashiga cikin azaba nice sarfe, inayi daka sai gari yayi laushi, nice wanke wanke, ashe jin haushinsu da biyune akwai wacce sukeso su bashi ya auroni. shine suka shiga azabta dani, nasha bakar wahala, a hanun Mahaifiyar Hammayo da yan uwanshi da matan yayunsa,
koda ya dawo, na É—auka wahalarmu xata kare, a'a wani muka sake shin dan ya nemi aiki babu, sai dai kwadigo. Shi yatafi gonar mutane aiki, nikuma nayi sarfe da daka,sai kace ba yar gata ba,. Ina ganin wulakanci iri iri, ga gori, na rashin haihuwa,

       Shekaranmu ɗaya da rabi, na haifi, sadeeq sunan mahaifins yasa min, watan sadeeq goma sha huɗu nasame cikin fatima, kuka kan nayi har nagodewa Allah, dan lokacin kome ya dagule min, ga Hammayo, yana shirin juya min baya. cikin ikon Allah na haifi fatima, kayan sadeeq nake saka mata dan ko suna ba'ayi ba,"

         Kukanta ya tsananta amma haka tacigaba.
"Fatima tana, da wata goma, nasame cikin hamdiya,, naga tashin hankali da gori, har Allah ya sauke ni lafiya, kafin suna na tattara kuÉ—aÉ—en da na tara, na haÉ—a, sannan ta rubuta, wasika, zuwa ga sarkin yola, inda naje har gidan sarkin misau na nime agaji, akaiwa sarkin yola akawo min, agaji ina cikin gararin rayuwa,

      Sarkin misau ya tambaye matsala nace masa babu ni dai akaiwa Sarkin yola,

   Allah sarki. a cikin satin aka kai sakona dan ko hammayo bai sani ba,

     da sakona ya isa, sarki yasa Aliyu, ya karanta masa sai da suka zubda hawaye sabida halim da nake ciki."

     ɗago kai tayi tana kallonsu, wani murmushin yake tayi sannan tace.
"Kuma sabida ku, na sadaukar da farin cikin mahaifina dan rabonkune yasa na bijire masa, akan idanunku ake dukan Shkurah babu wanda ya ci ayi hakuri sai da nace zan tafi sannan shine kuke cewa ai.hmmm.!
    
   Aliyu aka tura yakira babana, bayansun gaisane ya mika masa wasika ya karanta shiru yayi jikinshi a sanyaye sarki yace,.
"Kaji halin da take, ciki idan zata ci abinci sai tayi daka da sarfe, yarka ka maida ita baiwa, suturan da zata saka sai ta É—inka da zare da allura, haba Abubakar kayiwa Ibrahim adalci kuwa, idan yaji kayi watse da yar kanwarshi, dan haka nake shawartaka da kaje kaga halin da take ci,"

       Haka kuwa, ranar da akayi suna washe gari sai ga babana lokacin na fito ina daka, naji dirin mota, ta danga na leka sau naga babana a hankali nafita ina kuka, ina zuwa gabanshi na zube ina rokonsa da ya yafe min ɗaga ni yayi yana, kallon yanda na koma, kaman sabuwar halitta duk na tsofe, alkyaban jikinsa yacire yasame yana kallona idanunshi yana zubda hawaye.
Yace"
Habiba kece haka."

        Sai ga mahaifin hammayo, yayiwa Babana iso cikin gida, nan aka shiga hidima dashi be cikome ba daga garesu sai kallonsu yake dake ana tashigowa gaidashi. har inna kallon kayan jikinsu yayi da na yaransu, sai yaji hankalinshi ya tashi kallon  baban hammayo yasakeyi, sannan yace,
"Malam bilal, nayi mamakin ganin Habiba, haka sai kace mahaukaciya,, dubi suturan jikin ta da na sauran mutane, kasan inda tafito kuwa, kasan wazata aura ɗanka ya hure mata kunne, da tabi zaɓina da bazatayi kuka haka ba, kai a cikin yaranka mata, akwai wacce take surfe kafin taci abinci, amma ba kome ita tajowa kanta,"

      Sai lokacin, Hammayo ya shigo, ya kalle cikin nutsuwa, sannan ya kalle Baban hammayo yace.
"Sabida ya aurota, dai dai niman aiki idan yaje kai kake hana , a É—auke shi, ko sabida kar yazo ya ciyar da ita, bayan auren da kayi masa toh kasani Akwai Allah,"
    sannan ya maida kanshi zuwa ga hammayo yace.
"Akwai gida a bauchi, a gwallaga, zaku iya komawa can sai ka fara aiki a can, sannan ga amanar y'ata duk abinda kayi matukar na zalimcine Allah ba zai barka ba. muje ni yanzun zan koma,"

           Fita sukayi har da ni ya saka aka sauke kayan da ya kawo min ɗaukar yarana yayi yana saka musu albarka, sannan ya cire wasu takardu ya mika min, yace.
"Akwai check na banki, akwai takardun filaye nasaya miki jiya sai kuma wasu shaguna  har guda shida, akwai tsabar kuɗi masu matukar yawa kafara kasuwanci sannan nasama maka, aiki, ka rike min y'ata ka rike min yata ga amanar yata, mika min Hamdiya yayi, sannan ya tafi yana me zubda kwalla, kwashe kayana nayi nasaka a cikin ɗan ɗakina nashiga tsabga gaba, sai a lokacin kunya ya kama Babanshi ya har bakin kofa yana bani hakuri,

      Har da matan gidan masu kirana da me farar kafa, duk suka ji kunya,

        satinmu ɗaya muka dawo bauchi da ni dashi da Mama, daga nan kome ya fara zuwa mana, cikin kwanciyar hankali, ina da cikin Aisha ya auro Ummi , wacce itama muna tare,    bayan a hankali na koma karatu dan babana ya roke shi, lokaci da akayi jarabawar sharan fagen shiga jami'a har dani a ciki, kuma nasamu point, nan na ɗauki Psychology, a cikin shekara hudu na gaba, ina shirin ajiye karatu nasame labarin mutuwar babana, inda naje, yan uwana suka min koran kare,dan haka ina dawowa, na koma degree na biyu, ina da shekara guda na sake haihuwan inda na haife shkurah Mama ta yafi salma Amarya ta haifi rafi'a,

         koda nagama ban sake komawa makaranta ba,
 
     Duk lokacin da natuna rayuwar da nayi, akanku nakan sake godewa ubangiji, laifina na bijirewa iyayena yasa shkurah ta fuskanci Rayuwa,"

       Duk ɗakin kuka ake, sabida tausayin umma taga rayuwa sake kallon Mommah tayi  tace.
"Wallahi ranar da nafara ganin mashkur naji,ina kaunarshi da shkurah,ashe jinina ne shi,sai dai kashh koda shkurah tana raye haÉ—i ba zai yuba, sabida wani dalilin."

"Menene dalilin da haÉ—in ba zaiyu ba," inji mommah.

            Nan Umma ta faɗa mata, abinda ya faru, jikin mommah har rawa take kiran Ubaidatu tayi ta tambayeta ina Maina, shiru tayi sannan tace.
"Mommah baya kasan, dan kusan wata uku kenan da barin kasan,"

      " Amma, kinsan abinda yayiwa ɗan uwanki kuwa" inji mommah,

"Eh nasani, mommah nima dan kar na É—aga miki hankaline amma ya jima sa sakeni kuma, kowa yasani keda Yayane baku sani ba, don Girman Ubangiji karki sa shi ya rabu da, Zubaida yaya yana niman wacce zata kwantar masa da hankali kuma , tayi iya don Allah kiyi hakuri"

      Dan dole mommah ta kashe wayar umma ce ra shiga bata hakuri da karta shiga tsakanin mashkur da Zubaida.

****
Sun isa kd da, tsakiyar dare idan hajiya umaima yayi parking É—in motar nan yafito da ita, yashiga da ita, sake fito da ita sukayi inda suka nufi asibiti da ita, prvtne asibitin am basu kulawa, na musaman.

Sai da tayi wata huɗu me kyau sannan ta farka lokacin cikinta yakai wata bakwai sai dai likita ya tabbatar musu, ta manta kome, nata, dan haka yanzun kome nata sai an koya mata, Umaima taso a zubda cikin amma likita yaki kuma koda yay, yunkurin haka, sai ya ɓuge da barci shi yasa ya hakura.

  Cikin na shiga wata tara, aka cire itakam bata sam meke saka cikin girma ba, gidan marayu Umaima takai Yarinyar me kama da Ubanta, kaman an tsaga kara (Boss maina kenan mutane U.S)

    Umaima taci buri akan Shkurah wace tasaka mata Preety, da kanta tayi jinyarta har ta warke, tunda ta koma normal, nan tashiga tsara yanda zata ci kuɗin akanta kayan mata tashiga loda mata, hardasu dilke,  kafin wani lokaci shkurah ta goge, ga shigan banzan da ake koya mata rashin kunya da futsira Mutumin, na farkon da ya fara ɗaukar Shikurah gaskiya, shkura ta zama irin yan gayun nan, ga kyau ga class, dan yanzun haka, tafiya suke wani yauki take da jan hankali duk ya susuce dakyar suka isa hotel ɗin tundaga bakin, kofa, ya fara matseta, suna shiga kuwa suka zube akan gadon, nan ya shiga rabata da kayanta, yana arba da kirjinta ya kaikanshi wani, mugun barcine yayi gaba dashi, tashi tayi ta faɗa ban ɗaki ta sake ruwa, haka kawai ta tsinci kanta da kuka, yaune ta fara fita, amma ta tsani abin kuja take tsakaninta da Allah, fitowa tayi ta saka kayanta tafita, tana kuka, haka ta isa gida babu wanda san ta dawo

        Bayan shekara huɗu, shkurah wani irin gogewa takara girma, dukda gogewarta tsakaninta da yan iska shafe shafe idan suka matsa toh karshe barci sukeyi, Hajiya Umaima tayi kuɗi a jikin shkurah dan manyan mutane suke fita da ita, amma tsakaninsu😹😹😹

        ****
Sannun a hankali lokaci yaja sosai cikin shekara hudu kome ya faru, Mashkur ne zaune a ofis É—inshi yana ta aiki, a computer, ya jima sannan ya mike ya haÉ—a kayanshi sai gida fuskan nan ba yabo ba fallasa.

   Gidanshi ya koma, tundaga bakin kofa yake jin zazzakar muryanta tana ihu da kiran Daddy Daddy, da sauri ya shiga ya sameta tayi kuka idanunta sunyi jajur yar mashkur yarinya me kimanin shekara uku, ɗaukarta  yayi yace.
"Shkurah me ya faru kike haka ke dawaye"

    turo baki tayi, gaba tace.
"Nida Mahne ta hanani shan bobo, wai batason wanca aunty me sunana" tayi point É—in babban Hoton shkurah wanda aka É—auketa ranar saukarsu,

     murmushi, yayi sannan yace.
"Manta da ita, mukan muna sonta ko," sauke ta yayi ya taka har wajen  yana kallon hoton fuskasa ɗauke da murmushi kaman yanda take murmushi yace.
"Kina ina, ne nasan kina raye, yaushe zaki dawo gareni, oo, okni nazo kenan"

   tsaki Zubaida tayi, tace.
"Romeo sai muje kacire kaya, kazo wajen gunkinka ne, karka damu ta jima a kasa dan tsutsa sun gama wantadarta"

Shiru yayi, yana kallonta.

****
U.S.A
Kanal muh'd Hussain Muh'd a gaban ogansu, yace.
"Muh'd zamu turaku siriya, kuma muna son aiki me kyau, bamu son wasa, katabbatar ankai harin wuta tasama da takasa zaka iya tafiya."

      sarawa oganshi yayi, yafita wani murmushi, ogan yayi, sannan yace.
"Nasan yanzun, kakusan mutuwa, saura kaÉ—an zan gama da kai very soon"

        Fita yayi zuciyarshi ba daɗi, kusan sati biyu kenan, yake fama da wani mugun mafarki, gashi yana ganin iyayensu suna gudunshi sai, watsar da mafarki yayi ya shiga mota.

****
Zaune suke, a wani gurin cin abinci, kana ganinsu kasan wayayyune, suna gama cin abinci suka tashi ita tabiya kuÉ—in, zasu fita kanta a sunkuye tana, saka wallet É—inta, A cikin jaka, sukayi karo da juna, zata faÉ—i yayi maza ya tareta,

          Kallonshi tayi sannan ta mike tafita, shima binta yayi da idanun tayi masa bakarya,

 
         Tun daga ranar ya shiga bin shkurah tuɓ bata kulashi har suka zama abokai.

 

        Agajiye ta zube a falo tana maida numfashi kallon hajiya umaima tayi, sannan tace.
"Hajiya, na gaji don Allah yau karki haÉ—ani da kowa ina son zanyi barcine"

      "Toh preety ba damuwa" inji hajiya umaima,

   ****
Zaune take akan sallaya bayan tayi, mafarkin shkurah tana ihu, ga wasu mugayen halittu suna kawo mata sura, gudu take sosai a cikin Dawa, wani bakin kurane yazo ya kai mata mangari ta zuɓe kasa yaje zai kai mata cafka, Mashkur ya tureshi, rike hanunta yayi suka fara gudu sai da suka same wani dutse suka hawa, nan kuma shkurah da mashkur suka rabu yana kuka.

   A firgice ta tashi tayi addu'a san ta shige ban ɗaki ta ɗauro alola ra fara sallar nafiya.

      Wannan mafarkin ya tsayawa Umma a zuciya duk da shkurah, tasan shkurah, Addu'ar niman tsari tayi indan tana raye, Allah ya kareta, daga fitinar zamani idan ta mutu Allah ya jikanta.

   ****
Tagume yayi,cike da takaici, kuma bawani abu bane yaja haka, sai turashi kaduna da akayi ranshi ya gama ɓaci, mikewa yayi, yana nazarin yaushe zai sake farin ciki, tunda Shkurah ta tafi har ynz be sake samun farin ciki ba,

    komawa, gida yayi yana shiga ya zuɓe a kujeran falon, yana rike dan kanshi da yake masa barazar fashewa.

Cikin gidan ya koma, ya ɗakinshi sukayi kiciɓe da Zubaida, tana haɗa masa ruwan wanka dan taji shigowar taimaka masa tayi ya cire kaya ya ɗaura towel zuba masa idanun tayi tace,
"Bansan meke damunka ba, amma kayi, hakuri"

       tausayi tabashi, iya kokarin tanayi, amma sai ya shafe sama da wata uku, basu kwantawa waje guda ba, ba zai manta, ba rabon shkurah yasa ya fara, kula al'amarinta dan sai da suka shekara da rasuwan shkura, ranar yana cikin wani hali, yaje mata, dukda ya sameta full, amma be hana shi kiran shkurag ba dan itace a ranshi.

*Ina yinku*💋
Gaskiya comments da Voting ya yayi😥
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: 🙆🏻‍♀ *QADDARAR RAYUWATA* 🙆🏻‍♀

mai dambu

*KISHIYATA JIHADI NA*
*YARO MA NAMIJI NE*
*NI DA YAYA MOH'D*
*WANI JINKIRI.*

'''Kuyi hakuri jiyan abubuwa da abebeɗe suka sha kaina, kuma akwai matsalar idanun shi yasa na ɗaga kafa😎

kar wata ta juya min maganata dan nima ya bani dariya oll de best👎'''😹😹😹😂

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.