Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel
Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt
Chapter 3 of 24
*page 3*
Yana kwashe kayanshi daga É—akin yana kawowa falo sai da ya gama k'washewa tsab sannan yasa kai zai fita Maina yace
"Malam idan zaka kayi hakuri kayi, idan kuma kak'i wallahi xan bika har gidanka ni babu abinda ya dame ni kai kaji gurin"
 Wai akace shiru ma, magana yanda kayan falon baza suyi magana haka ma Mashkur yaki kula maina har ya kwashe kayanshi ya har zai fita sai ya tsaya daga bakin kofar shiga falon yace
"Wannan matsalarka ce ba tawa ba sai dai kayi a hankali da fushin Iyaye, kuma bazan ɓoye maka Wallahi haɗa ka da za'ayi da Ubaedatu shine abu mafi muni dan har ga Allah bana son aurenka da Ubaedatu, dan nasan a dalilin niman matan banxa karka je ka ɗauko bala'i kashafawa yarinyar da ta tsare kanta kuma ta kame kanta, don Allah ya haramta mata saɓa masa"
Yana gama faÉ—in haka yafita yabar gidan baki É—aya, duk da maina yaji zafin maganar,
       mikewa yayi yafito yaga dagske ne Mashkur tafiya zayi ya barshi ai ko ba,syn kome yana tunatar dashi Allah,
   ajiya zuciya yayi  cike da jin haushin abinda ya aikata amma wani shashi na zuciyarshi tana bashi shawara yabi mashkur wani gefe na hanashi yayi da, shaiɗan yake masa huɗubar banza, dan ji yake yanzun yake da daman kawo mata cikin gidan any time abinshi,
   Mashkur yana barin unguwar ya nufi new g.r.a wani ɗan karamin quarts na haya me ɗauke da gidaje ashirin da yan kai, a gida nagoma sha biu yake inda ya kama gidan baki ɗaya sama da kasane dan haka sai ya kama duk sabida yaranshi kuma idan yayi aure matarshi zata xauna a sama, ajiyqr zuciya yayi wank sanyi ji da kewar maina dan wannan shine karon farko a rayuwarsu na rabuwa amma idan yayi dubi da abinda maina, ke aikatawa sai yaji ranshi ya kara ɓaci kuma nan da y'an kwanaki kanwarshi Ubaedatu xata shigo cikin kazamin,  rayuwar maina, tsaki yasake yana me hura iskan dake bakinshi waje abin ya karawa fuskanshi kyau kuma one eleven dake kwance akan fuskar tayi, masifar mashi kyau take yafito bagudiren asali,
    Tunda yashiga sallah ne yafitar dashi dake akwai masalaci a cikin quarts ɗin tunda yayi sallar isha be sake fita.
    ***
Washi gari kowa yashirya cikin unifoam farin riga da bak'in wando sai farin himar da bak'in takalmin haka duk suka saka amma banda Shkurah wacce tasaka siket iyakarshi k'wanji da sai farin riga me dogon hanun wanda kana hango farin vest da brz ɗinta sai karamin himar ɗinta wanda ta manna bajin ɗinta duk suna motar da yake kaisu wato sai horn ake mata amma tak'i fitowa tana zaune ita sai lokaci take karyawa kaman zasuyi kuka dan saura minti ashirin arufe gater ɗin schl ɗin
    Fitowa Aisha tai tasame tana wasa da abinci ɗaukar abincin tai takai mota sannan ta dawo tace
"zaki fitane ko sai nayi waje dake marar kunya kawai fita ki bani, guri kafin na k'waÉ—a miki mari"
   fita tai suka gamu da Ya bilal ya kuwa ya zuba mata rank'washi sai a kan idanun Abba dake akwai abu abakinta garin ihu tak'ware shiɗewa tai zata faɗi yayi maza ya riketa yana ce mata "sannun kinji bansan da abu a bakinki ba," bata iya magana ba sai hawayen da yake zuba mata,
   "saketa bilal wallahi shkurah idan na kamaki zan karyaki kiwuce mota kafin nazo wajen kai Alhamdulillah da samunki nazo wajen nasameki, Allah yashirya min ke tafarki madaidaicciya." inji umma kenan,
     tafiya take kaman wacce k'wai ya fashe mata a ciki sai zubda kwalla take tana sharewa da hanunta,
     shkurah kenan ita dai akan makarantar boko toh sai dai akasheta dan ta ranta baya kaunar karatun boko ba wai bata ganewa bane ita tashin safe ke damunta, zata raba dare tana shigar da hadda da duba wasu buks ɗin bokonta bazata kwanta ba sai karfe sha biu da rabi take kwanciya da asuba kuma tariga kowa tashi shi yasa bata da ishashen lokaci,
     Koda tashiga mota bata kula kowa ba sai Abdullahi sabida shi Aisha tabawa abincinta ya rike mata dan sunfi shiri sosai
     kallonta yayi cikin tsoron karta rufe shi da masifa yace
"Adda shkurah ga breakfast É—inki kar yayi sanyi kinji"
   yana maganar amma fuskarshi cike da tsoronta dan har muryarshi rawa yake kallonshi tai da jajayen idanunta ta amshi tace
"Nagode Abdul zanci"
     ajiyar zuciya yan cikin motan har da sa'ointa suka sauke karɓa tai taci kaɗai ta juya ta ajiye sauran a bayan mota
  Suna isa cikin makarantar ana rufe gater kowa kama gabanshi yayi inda shukrah da rafi'a suka wucce ss³a salmah ta wucce ss³b,
    ***
Sauri yake dan har yaso makara agurguje yafito daga ɗakinshi dan yau suna da exercise na Jirgin kuma shine shugaba a wannan shashin kuma 8 yadace afara aikin ko karyawa beyi ba yabar gidan yaransa naganinsa duk suka k'ame suka sara masa da "good morning sir"
   ɗaga musu hanun yayi sannan ya shiga motar sai ofis,
        yana isa aka fara exercise ɗin basu suka bari ba sai wajen sha biyun rana yana sauka daga jirgi aka shaida masa ga Maina yazo yana jiranshi a ofis yana shiga ya mika masa hanun suka gaisa daga nan suka tsinke da hira kaman wasu kanari,
      sai one pm maina yabar ofis ɗin ya koma nashi ofis ɗin yana tsaka da aiki kira yashigo masa tun daga sauti ya soma murmushi yana kaɗa kai sai da kiran ya kusan tsinkewa ya ɗauka ya kara a kunne da cewa, "Assalamun Alaikumun momma na imiss you dole next week nashigo azare ma "
     dariya akai a ɗaya gefen sannan tace
"toh son Allah ya nuna mana, kuma kazo da shirin ganin dota in-law zubaida dan Abbanku ya faɗa min nan da sati biyu za'ayi bikinku amma son nasan, zubaida ba zaɓinka bane hakuri zan baka, kayi biyayya Allah zai baka wacce kakeso kaji,"
   murmushi yayi sannan yace
"momma karki damu insha Allah zanyi biyayya, anjima zan kiraki ina son nashiga da wasu document ne"
  Kashe wayar yayi sannan yacigaba da aikin gabanshi yana hararo auren Ubaida da Maina sam haɗin be masa ba ina laifin a haɗata da Baffa sai wannan tantirin,
      kauda tunanin maina yayi sannan ya shiga tunanin tasa matsalar shi, a fili yace
"ko sai yaushe nima zan same sarauniyarta" murmushi ya sake ciki da jin daÉ—i, ranshi yake ayana abubuwa da zayi idan yasame wacce ya faÉ—a sonta, toh tabbas zaiyiwa so bauta kuma zai rayasonta fiye dakanshi,
     lokacin salla nayi yafita ƴaje yayi sannan yafita break be dawo basai uku saura nan ya koma bakin aikinshi harsai wajen biyar ya gama la'asar yayi dan yau ya makara beyita akan lokaci ba yana idarwa ya nufi wajen motarshi sai gida
      ***
Karfe biyar da rabi suka fito daga schl dukkansu a gajiye daq'ar suke É—aga kafa nan aka buÉ—e shafin hiran karatun da wasu na tambayar wasu me suka fahimta daga cikin waÉ—an da ake tambaya har da shkurah a ciki, duk da ta gaji amma amsa take basu dai dai yanda aka musu har da karin haske bayan sun gama ne aka shiga hiran jami'a dariya tai sannan tace
"tab wallahi ina son rayuwar bodin amma haka Umma ta hanani, kuma da alamun koda nagama ba zanyi bodin ba sai day, haba ace mutum ya gama day ya cigaba aday da sake wallahi saura wata huɗu zuwa uku, fa zamu gama Insha Allah.
       Dariya Maryam Umar Jama'are tayi cike da zolaya sannan tace
" Kin haɗu mukuwa bodin zamu ke kam sai dai zaman gida fa Allah sarki zamu ji daɗi kuma za'a kiramu da big girls, ko bebes" ta kalle ɗaya abokiyar tafiyarsu tana dariya,
   "Eh mana Muj mun girma ana ganin mu ansan ba yara bane mu sai dae akiramu da manya yara su oo sai dai gida karki damu idan muka waye zamu zo mu wayar dake fa dan babu mugunta" inji bebes,
    duk yan wajen maza da mata suka fashe da dariya abinda ya kular da shkurah kenan ta kaiwa bebes duka kauce ita kuma ta faɗa titi lokacin kuma mashkur yana sharan gudu ya kusan isa gida saura kiris badan ya taka burki ba ai kuwa runtse idanunta tai ta ɗaura hanunta akai ta ɗan d'uka kasa saura ɗaliban ihu suka saka tsoro da fargaba ne ya kama dukkanninsu ba yaran ba har shi kansa mashkur ɗin ai kuwa yaranshi suka sauko daga mota zasu rufeta da duka da bulalarsu wani mahaukacin horn yayi dan dole suka fasa fitowa yayi, daga motar ya karasa wajenta har wannan lokacin idanunta a rufe bata buɗe ba dan bata san,me zata gani ba ratsasu yayi ya harɗe hanunwanshi a kirji yana kallonta daga sama har ƙasa abinda yafi jan hankalinshi tulin gashinkanta wanda ya ɗaga daga baya zaka rantse acuci mazane gyaran murya yayi cikin sanyi rai, yace
"buÉ—e idanunki babu abinda ya faru dake kinji amma nan gaba don Allah kudaina wasan banza yanzun badon Allah ya takaita min ba wallahi bansan me zan cewa iyayenki, ba wucce kije suna jiranki"
A hankali ta buɗe idanunta ɗago kanta sai a fuskanshi kallonshi ta tsaya yi cike da tsoro raɓa gefenshi tai ta wucce bata iya magana ba sabida tsoranshi,
      Juyawa yayi yana kallon yanda take tafiya tsintar kanshi yayi da binta da kallo,
    itama tana tafiya amma zuciyarta na uzura mata da ta juyo dan haka batai wani tunani ba ta juyo aikuwa suka haɗa ido tsorone yasake rufeta, tana ganin napep ta tsara musu suka shiga jikinta har rawa yake,
  yana ganin tafiyarsu ya sauke ajiyar zuciya shaf ya manta a tsakiyar hanya yake mutane sai raɓa gefenshi suke suna jin haushin yanda ya tsare musu hanya shiga mota yayi yabar titin tuki yake amma zuciyarshi yana shirin hanashi sakat fuskar shukrah ne yake masa yawo a cikin idanun dakyar ya isa gida kayanshi ma yaransa ne suka k'waso masa a gajiye yashige.
   Â
Inayinku💋
3/4/21, 9:44 AM - Ummi Tandama: *QADDARAN RAYUWATA*
_SHUKRAH_
  Huwallahu lazi Al'illa ha illahuwa
  AR-RAHAMAN AR-RAHIM AL-MALIK AL-QUDDUSðŸ‘ðŸ‘ðŸ‘
_Tsokaci akan wannan buk ɗin tun farko ya dace na faɗa amma ban faɗa ba labarin zai nuna mana karfin Addu'ar Iyaye akan Y'ay'ansu da kuma Addu'ar wannan aka zalumunta,Sai Addu'ar matafiyi, Wanda yazo a cikin hadisan manzon Allah (S.A.W) yace Ubangiji yayi Alkawarin amsar Addu'ar mutane uku" cikin ɗauki sahabansa suka ce "Ya Annabin Allah suwaye mutanen ukun" yana kishingiɗe sai yatashi ya zauna yace " Addu'ar Iyaye, Addu'ar wanda aka zalunta sai Addu'ar matafiyi" yace kusani Allah baya taɓa juyawa Addu'arsu baya idan sukayi kafin rana tafaɗi yake amsarta idan kuma cikin dare ne kafin gari ya waye yake amsarta"_
    '''Allah ka kara masa son Annabi''' Amin Yarabb
_Fans ɗin wattpad kuna bani kala fa dan haka wannan shafin na kune ga voting jina nake kaman nafi kowa sa'a Ina godiya da fatan Alkhairi_💕💘
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.