Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel
Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt
Chapter 18 of 24
*Page 18*
A haukace, ya bangaje likitan dan ba gama jin ɓaɓɓatunsa ba yayi kanta, a guje yana zuwa bakin gadon ya zuba, gwiwarsa a kasa, ya rike hanunta yana kallon, fuskarta, cike da tashin hankali cIkin raunaniyar murya yace,
" Shkurah!!!, me yasa kaddaranmu, yake yawo damune haka,shin ban chachanci zama dake bane, hmm Shkurah ina miki so har cikin zuciyata nasan samu da rashi duk na Allah ne, amma shkurah idan kika tafi meye amfanin sauran rayuwata don Allah ki tashi, ina jin a jikina ke É—in tawace."
     Kukane ya kwace masa, yanayi yana, sumbatu mikewa yayi ya kifa kanshi, a goshinta hawayensa masu ɗumi, suna sauka akan fuskarta, bae daina, kiranta ba kuma bai dai sumbatu ba.
   Kusan mintuna 40 yana, zaune, a wajen kuma bai fasa kuka ba, mika masa wasu takardu akayi ya cika na ɗaukar gawa,
  wani mika tayi tare da, jan dogon numfashi, me karfi a firgice yace.
"Dr!!!"
     A guje suka shigo, dan na'uran da aka saka mata, sun fara, kara, dan basu cire ba,
    ****
Cikin shashekar kuka ta É—ago red eyes É—inta tace.
"Mommah, watanshi uku kenan babu kira babu text, ai kome nayi masa ban chanchanci wannan irin hukumci ba, da karuwa fa ya bar k'asar nan meye yake bukata,da bani da shi a jikina, da zai fita niman wata karya a waje, mommah don Allah mommah kice wani abu, zan iya mutu idan na rashinshi."
 Takarshe maganarta cikin,kuka tana me rike, kanta.
    Shiru mommah tayi tana kallonta, cike da takaici da ban haushi dan tasan irin zaman da suke da mashkur, Ubaidatu ce ta gyara zamanta dan ta gama cika fam kiriss take jira ta amaiyar da abinda ke cikinta, kuma ga dama tasameta, cikin ko inkula tafara magana, dacew.
"Yanzun banda abinki, ke har zaki ba laifi Yaya dan ya fita da wata, kasar da wata, ehtoh koda yayi haka ai renon Maina ne,hmm ki tashi salim halim, ki koma gidanki, idan ba haka ba wallahi zan kira Abba na faÉ—a mishi, banda abin kunya Sirrin aurenki, ma bazaki rike ba, har sai kinzo wajen Mahaifiyar mijinki,"
      dakatar da ita, Zubaida tayi, rai aɓace tace.
"Daman kice, kina bakin ciki da auren yayanki dana kikeyi, ai da nasan da haka, da nace ya aureki, ya share miki hawayenki na rashin mijin da kike fama da, shi idan na ban iya rike sirrin aurena ba, aike kin iya tunda har yanzun a gidan mijinki kike, kuma dan nazo wajen Mahaifiyar Mashkur, dan ina ganin ta isa dashine, amma tunda kin nuna min, bata isa da kuba, ba damuwa, idan kika sake ganina a gidan da niman alfarma, kiyi min abinda kika gadama, banziya wacce taki aurowa,"
   suran jakarta tayi tabar gidan, daga mommah har Ubaidatu jikinsu yayi, bala'in sanyi da mamaki, kallon juna suke,
   Ajiyar zuciya, mommah ta sauke ranta a ɓace,tana girgiza kanta,
      batayi, magana ba matukar tace wani abu kome zai iya dagulewa.
   ****
Tun bayan dawowarsu,Umma daga jinyar, Alh hammayo, duk lokacin da ta zauna tunanin Shkurah yake damunta, har ta rasa inda zata cusa kanta, dan ko barci take, abu É—aya, take gani.
Haka kawai ta fara, wasi-wasi, a ranta dan har addu'a tayi, sosai amma bata fasa jin shkurah, a ranta ba, duk abin duniya ya dameta, tun mutane gida basu gane halin da take, ciki ba, har sai  da ranar ta, yanki jiki ta faɗi,
     A guje akayi asibiti,da ita, cikin tashin hankali dan babu wanda yasan me ya kawo haka.
         Likitar mace ce, akanta, bayan ta gama, saka mata ruwa ta fita, gurinsu Abubarka da bilal, dan sune suka kawota sai Ummi, kallonsu matar tayi, cikin fara tace.
"Alhamdulillah, jikinta da sauki jinintane ya hau, amma insha Allah, zuwa anjima zata farka amma don Allah a kiyayye abinda zai É—aga mata, hankali."
  Miqa masu, takardan magani tai, sannan tayi tafiyarta,
     kwanakin Umma biyar aka sallameta, jiki da sauki ba laifi sai dai bata fiya son magana bane, sai da shkurah karama, ita kaɗai ce ke tayata hira.
   ****
A hankali take, buɗe idanunta da suka mata dishi-dishi, yunkurin mikewa tayi, amma tajita gam a jikin abu sake rufe idanunta tayi, da karfi zuciyarta na bugawa, wanda ba kome ya kawo, haka ba, sai jin numfashinsa da kamshin turaren da bazata iya mantawa dashi ba, a rayuwarta juyawa tayi daidai inda yake, ta kalle fuskarsa, zuba masa idanun tayi, a hankali ranta yake ɓaci wanda bata san dalilin haka ba, kokarin mikewa take, ayya yana barcinsa cikin nutsuwa haɗa karfinta tayi waje guda, ta hankaɗeshi.
Abinda yasa ya farka kenan, cikin firgici tare da zaro idanunsa waje yana.
   Cikin farin ciki, ya isa gareta, yace,
"My dear har kin farka, sannun bari na nima miki brush ki wanke bakinki Alhamdulillah."
   Watsa masa, wani malalacin kallon tayi me ciki da tsantsan kiyayya, tace.
"Kaga malam ina ne nan, ka kawoni wato ku abin kunya a jininku yake, shi yacutar dani, kai kuma ka, É—aukoni nan ka maidani gurin iyayena kafin na tara maka mutane, na tsani ganinka bana kaunar ganinka, kafita min, a É—aki idan kuma dan jikina kake bibiyata zo gashi, ai ba wani abin kunya bane a gurinku."
Lumshe idanunsa yayi, ba karya,magaggunta sun masa zafi, ji yake kaman ta fashashen ruwan dalma ake, watsa masa murmushi ya sake mata, sannan yace.
"Eh baki san, nima abinda nafara bakenan, ai daga zuwanmu nan, ai na É—anaki yafi sau goma, gaskiya, kina da garÉ—i tashinki nan ma, da kika ganni amakale dake nagama, danakine gaskiya ina jin kunyarki fa,"
    rufe fuskarsa ya shiga yi, bakin ciki da ɓacin raine ya baiyana, karara a face ɗinta, hawayen da take dannewa suka, kuwa ɓalle daga idanunta, bata san lokacinda ta fashe da kuka ba, me ɗaga hankali take ya ruɗe, yazo gurinta ya rike hanunta yana bata hakuri tare da rantse mata wasa yake, kuma ba zai kuma ba, tayi hakuri tureshi tayi, cikin masifa, tace.
"Ka maidani gidanmu, nace bana son, ganinka inba haka ba, wallahi zan gudu,"
   ɗago kai yayi, yana kallonta mamaki ya rufe shi, yace.
"Ok, bari nakira dr ɗin su dubaki Insha Allah, gobe zamu bar nan zuwa gida kinji."
    Ko kallon inda yake batayi ba, tace.
"Better"
     mamaki fal, ranshi yafita, sai gashi tare da likitotin da suka mata, aiki nan aka shiga dubata, bayan sun gamane, sukace.
"Babu, wani matsala zasu same sallama amma sai next wee.."
    Ai baikai karshen maganarsa ba, tajefa masa wata uwar harara, wanda ya hana shi karasa harafin karshe, takalleshi ta kalle sunanshi da yake jikin rigarsa tace.
"Yau!!!! zan bar asibitin nan, idan kuwa kuka, ki zan gudu kuma idan nafita nace, satone kayi akawoni nan dan ka"
     tass ya ɗauketa da mari, ciken zafin rai yace.
"Duk abinda zakiyi, ya kare akaina banda kowa, badan nasan wacce tabaki tarbiya ba danace baki dashi, na lura ke zuma ce sai an shaki da wuta,kuma sallama sai next wk kiyi abinda zakiyi."
   Aikuwa ɓare baki, tayi ta hau kurma musu ihu, abinda ya ruɗar da drs ɗin kenan take suka, sallamesu hotel ɗin da suka, sauka ya maidasu ɗaki ɗayane, ya kama a madadin biyu,
  Tun asibiti take kuka, har suka iso hotel ɗin banza yayi da ita, sannan ya shiga ban ɗaki yayi wanka da alola yafito ɗaure da towel, ɗagowa tayi suka, haɗa idanun runtsa idanunta tayi, ta soka kanta tsakiyar cinyarta tana kuka, kayansa ya ɗauka ya koma banɗakin yasaka sannan yafita, inda yabada oda akawo mata abinci.
Kuyi hkr, da wannan kusan typing ba sauki......💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆
MAI DAMBU CE*
Afuwa.......ðŸ‘
*Page 19*
Yanda aka, kawo abinci haka ya dawo yasamu, har ita ɗin, mamakine, ya turnike shi taɓe baki yayi sannan ya shiga bandaki yayo alola, sannan yafito yayi sallah,
        ya jima,akan abin sallar kafin ya tashi inda take yaje ya zauna yana kare mata kallo, lumshe idanunsa yayi, sabida kukan da take yana taɓa zuciyarsa a hankali yakira sunanta, amma ko taɗago kanta asalima sake cusa kanta tayi, ta cigaba da kukanta.
   Shiru yayi yacigaba da kallonta, dan ya rasa me zai ce mata, tunda ya lura tana bukatar kukane shi yasa takeyi,
      Janyota yayi, a hankali ya rungumeta, sosai tureshi take tana kara kukanta, bakinsa yakai kunnenta yana mata ynda akewa kananun yara idan suna, kuka "seeeeee......"
     A hankali yake bubuga bayanta, har tayi shiru cikin nutsuwa, yace mata.
"Kinyi sallah kuwa,"
   shirun da yaji tayi yasa, ya leka fuskarta idanunta yagani, a rufe taɓata, yayi yace.
"Kinyi sallah kuwa? idan bakiyi ba tashi kiyi kar lokaci yatafi."
     Mikewa tayi, daga jikinshi ta shiga banɗaki, kafin ta fito ya shimfiɗa mata, abin sallah tana fitowa salla ta gabata, tana idarwa ta kwanta a gurin ko minti biyar batayi ba barci yayi, gaba da ita.
    Zama yayi, yasata a gaba yana kallonta cikin nutsuwa, shi kaɗai yasan yanda sonta yake ɗawainiya da shi,
......
       Karfe uku, saura kwata na dare ya tasheta dan hudu da rabi zasu bar chicago, har yagama haɗa musu kayansu, mika mata brush yayi taje tawanke bakinta mika masa tayi, karɓa yayi sake mika mata wata doguwar riga yayi, da gyalenta,
     A gurguje tasaka, dan taga sai, kallon agogon hanunsa yake, yana kallonta yana son mata magana, amma yasan ba lallai bane ta amsa masa,
      jakarsu yafito musu, sannan ya juya, yace.
"Bamu da lokaci, in dan ne ki shirya a nutse, zan iya jiranki har iya karshen rayuwata, ba xan gaji ba, kuma bazan damu ba, kuma zanji daÉ—in haka pls ba dan ni ba, ko dan sonki da kowa gida, ki hanzarta."
        Fitowa tayi, bayan t ɗaura gyalenta ɗaukar handbag ɗinta tayi, tafito dan tabashi haushi tashiga tafiya kaman me jin tausayin k'asa, tafiya yayi wajen lifter ya buɗe ganin da gaske tafiya, zaiyi yabarta yasa ta haɗa da gudunta,
    tana zuwa, dab dashi yashi itama tabi bayanshi, tunda kofar ta rufekanta, ta koma gefe, ta takure kanta, haɗi da kame jikinta, waje guda ganin haka, yasa yayi banza da ita har suka sauko kasa,
    fita sukayi daga, otel ɗin suna waje me taxi tana jiransu, har airport ya kawosu.
     Sun jima kafin jirginsu, ya tashi, sai da suka biya ta Ethopoeia, hutun awa biyu sukayi sannan suka sake ɗauko hanya,
      ****
Karfe goma, nasafe suka sauka a garin kano, wani jirgin ya biya musu, zuwa bauchi, sun iso sha biyu, saura kwata.
    Suna isowa, ya kira yaronshi yazo ya ɗaukesu, kallon yaro yayi yace.
" Ka kaimu,gwallaga"
    tunda suka, iso take share kwalla dake taruwa, a idanunta gashi jikinta yayi mugun sanyi, a haka suka iso unguwarsu har kofar gidansu tunda motar ta tsaya, ta rike hanunsa, cikin kuka tace.
"Toh ynz me zance musu, idan nashiga ciki, ina jin tsoron Baba kar yasake korata, don Allah ka kaini wani waje, ina jin tsoro."
     Zuba mata idanun yayi, cikin damuwa, dan sai yanzun yayi danasanin tafiya da ita har na tsawon wata uku, batare da sanin iyayensa da matarsa ba, toh idan ya kaita, ciki me zai cewa umma idan ta gansu tare,kar tayi tunanin daman yasan inda take, ya ɓoye mata hura iskar bakinsa yayi, sannan ya cire hanunta, daga rikon da tayi masa,
      share mata, kwallar dake fuskarta yayi sannan yace.
"Ki nutsu, mu shiga babu abinda zasu miki, kinji ko asalima kullum dake suke kwana dake suke tashi. Idan zan iya faÉ—a miki kiyarda shine basu san kina, raye ba amma muje kiji da kunnenki."
       Tare suka, fito daga motar a hankali ya zagayo, wajenta a hankali ya riko hanunta suka haɗa, hanunwarsu suka sarkafe da juna, kusan atare suka kalli juna.
     Shi yake, gaba ita kuma tana baya da sallama suka isa, cikin gidan duk suna tsakar gidan, zare hanunta tayi daga nashi ta koma bayanshi tare da rike rigarsa, shiga cikin gidan yayi,su Ummi da Mama, da Fauziyya, matar Abubakar sai leka bayanshi suke dan cike suke da mamaki kaman, shkurah suka, gani a tare da shi.
    Basu tabbatar ba, sai da ya gaishe dasu ummi, inda ya durkusa, nan duk suka mike a tare,
     suna salati, fauziya kuwa, ta cikawa bujenta isa, dan ta gama razana,
    Umma ce tayi karfin halin cewa,
"Shkurah, kece ? ko watace me kama, dake ?"
    jijjiga kanta tayi, cikin kuka, matsawa tayi, gurin Ummi rike hanunta mama tayi suka shiga da ita, har falon Alhaji Hammayo, dan umma tana gurinshi.
       Har gaban Alhaji hammayo ta kaita,
Â
   mikewa umma tayi, cikin tashin hankali, durkusawa shkurah tayi jikinta har yana rawa,
    cikin kuka, tace.
"Babana kayi, hakuri karka sake korana, idan na tafi, bansan inda zan sake faÉ—awa, ba ku yafe min wallahi ba laifina bane, kaddarace ta faÉ—o min don Allah kayi hakuri"
     A hankali umma ta zuba, gwaiwarta a kasa tayi, sujidar godiya kirari takewa, ubangiji kafin tasake kuka, me sauti inda ta tashi tarungume, shkurah Alhaji Hammayo, kuwa shima kuka yake,
     ganin haka, mashkur ya juya yayi tafiyarsa zuciyarsa cike take da farin ciki.
    Ko da ya isa, gida yasame gidan a hargitse wuccewa ciki yayi, ya rage kanyan jikinshi sannan ya faɗa banɗaki yayo wanka, sannan ya sake kaya marasa, nauyi kwanciya yayi, dan ya gaji sosai.
    Hmm, Zubaida nacan ɗaki tana, barcin asara duk ta rame tafita hayacinta,
    tun karfe goma take, barci har ynx da yunwan cikinta yasa ta juya, sannun a hankali ta farka, wanke bakinta tayi a banɗaki.
    Fita tayi, daga ɗakin kicin tashiga taje nimawa kanta abinda zataci.
       Taliya, da manja da yaji, tayi, taci sannan tafito kallon falon tayi, duk yayi kura tsaki tayi, dan tasan laifintane, saunawa ana kawo mata yan aiki,amma suna guduwa, ga aiki amma babu abinci dan dole suke guduwa, bandan ransu nakin aikinba,
ga kishin jaraba, dan yar aiki bata isa ganin mashkur ba koda yazo fita koranta ɗaki ake dan karta ganshi😜
     Shi yasa yaran basu zama ga tsangwama da hantara.
      Sai karfe biyu mashkur ya farka,
   dogowar riga, yasaka sanan yatafi masalaci.
     Aikan yaronshi, yayi yaje ya sayo masa, abincin dan yasan ba samu zayi ba.
    ****
A can gwallaga kuwa, kafin wani lokaci, gidan yacika da yan uwan da abokan arziki ana barka da dawowanta,
       Abinci ma umma ce ta bata a baki, tsakaninta da mutane sai kuka, dan bata taɓa kawowa a ranta iyayenta zasu neminta haka, ba gashi kowa bata labarin abinda ya faru bayan tafiyarta ake,
......
   Bayan kwana, biyu mutane sunyi sauki nan, umma take tambayarta, yanda suka haɗu da mashkur iya abinda tasani ta faɗa mata, suna zaune sai ga kiran Na'im ya shigo nan,
  yake mata mita kashe wayar da tayi, na tsawon lokaci, dariya tayi sannan ta faɗa masa ai wayar ce ta ɓata, idan ba haka ba sai suta rigima sun jima sosai faɗa masa, tayi tana bauchi nan, murna ya rufeshi yace mata.
"Ina nan zuwa, kuma idan nazo zan nime izinin niman aurenki."
    Zuciyarta fess, ta tace.
"Haba, dai ai ba yanzun ba sai na kwana biyu dan nayi. kewar gida sosai,"
   dariya, yayi sannan yace.
"Allah baki isa ba, nida nake so nan da wata gudu, muna tare Wallahi ina zuwa, zan gabatar da kaina"
    Sun jima, suna musayar yawun kafin sukayi sallama,
  Murmushi Umma tayi, tace.
"
Auta mashkurne, naji kuna musayan kalamai dashi."
Kallon umma dan ta manta da shi, a shafinsa ma girgiza kai tayi, tace.
"Wani ne, a kaduna, Na'im sunanshi, shine zaizo niman izinin a wajenku."
"Me kike nufi, Auta mashkur É—in fa, "
"Umma ni bana, sonshi wallahi kuma ai taimako yayi, dane naso shi, amma yanzun ina son na'im yayi hakuri kawai ya nemi wata, da mata da yawa a garin bauchi bani É—aya bace mace..."
     "Shkurah, anya kinsan me ake nufi da hallaci kuwa, kinsan abinda kike shirin aikatawa, kuwa, wannan shine Batulci, baki san me ake kira da adalci ba."
  Allah sarki duk wannan maganar dasuke yana kofar shiga falon duk abinda suke faɗa akan kunnenshi be taɓa jin ciwon ace ba'a sonshi ba, sai yau kalmar bana sonshi da take yayi, masa zafi jin sabom tsanar Maina yayi a ranshi juyawa yayi, ya bar gidan.
Ran umma ba karamin ɓaci yayi,ba dan haka shiru tayi, tana kallon shkurah, cikin sigar lallashi tace.
"Uwata, kinga mashkur É—an yar uwatace, don Allah karki min haka ki amince ki aureshi zaki so shi sosai kinji, ki tayani rufa min asirinki ki amince da soyayyarsa."
      Kallon umma tayi, cikin nutsuwa tace.
"Umma kigane mana, nifa bana sonsh...."
    Ayi hakuri Dearie's💋
3/4/21, 9:47 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_Husna Kamshi, ga wannan shafin kyautane nabawa yan grp É—inki, bana bukatar godiyarsu Soyayyar dasukewa buk É—in ma ya wadatar dani ina musu fatan alkhairi_💕ðŸ’
*Phatima zahra, na grp ɗin farida sweery ina jin daɗin comments ɗinki keda sauran yan grp gsky jiya naji daɗin comments ɗinku nagode sosai*💋
Chapter Navigation
Use this section to move to any chapter without going back to the top.