Complete Hausa Novels

Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel

Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt

Chapter 21 of 24

*Page 22*

"Na'im zan baka shawara a matsayina na abokinka, idan zaka iya kahakura da shkurah Allah ba matarka bace, ka dubi Æ´anda ya bada rayuwarshi dan nata, kai koni akace nayi wannan kasadar Allah ba zanyi ba, dan akwai mata da yawa a duniya karewa ma ba ahaifi uwar watq ba shawara kayi hkr ka bar mishi ita." inji faruq kenan abokin na'im,

      Shiru na'im yayi, yana nazarin maganar Faruq, ɗago kai yayi cikin karfin hali yace.
"A'a ni bazan barmashi ita ba har sai naji daga bakin shkurah shin meye ya shiga tsakaninsu haka da taki aurenshi."

       Dariya faruq yayi, kafin yace.
"My guy karka wahalar da kanka, ka janye kawai shine gaskiya, amma tunda kace haka ina jiranka, malam majun."

      Sun daɗe suna tattaunawa, akan abinda ya faru.

        Shkurah kan dakyar aka cire mata bullet ɗin, dan ji jiki sosai sai kusan asuba ta farka tana rarra raba idanunta, a ɗakin da take Aisha ce ta matso kusa da ita tace.
"Sannun ya jikin ina ke miki, ciwo."

"Adda ina mashkur yake?"

      tana kokarin mikewa daga kwanciyar datake, shiru Aisha tayi kafin tace.
"MeÆ´e matsalarki dashi, tunda hankalinki ya kwanta sabida ke, ya rasa..."

         "Isa!!! haka barni da ciwon dake damuna, karki kara min wani akai..." tana gama faɗan haka tajuyar da kanta gefe ta fashe da kuka, mara sauti ita kaɗai tasan halin da take ciki,
    har gari ya waye, bata daina kuka ba, shigowan Na'im ta haɗiye kukanta kallonta yayi cikin nutsuwa yace.

"Preety kukan me kike? ko kinji wani abu yasame mashkur ne, da kike kuka."

       D'ago idanunta tayi takalle shi, sannan ta aro dariyar dole akan fuskarta tace.
"Haba ina, ruwana da wani can, kawai hannuna ne ya dameni da zafi yasa nake kuka, amma babu kukan da nayiwa wani kato."

    Kallon cikin idanunta yayi, abinda bakinta yake faɗa daban, wanda idanunta suke faɗa dabam, murmushin yake yayi kafin yace.
"Ai kuwa, naji labari mara daɗi akan ciwon da yaji,dan likitoti sunce yasame matsala akanshi brain ɗinshi ya taɓu bazai wani jima zai mutu, kuma hankalina zai kwanta dan bani da wanda zai damar min mata a tunani."

A tsorace ta É—ago kanta, bakinta na rawa kansan wanda akace kuwa, mashkur ko maina, waye ya same matsala a brain É—inshi."

        "Ooo maina nake nufi ba mashkur ba, kinsan sunan sune kusan iri ɗayane amma ya naga kin damu daga maganar mashkur, ko kina sonshine na janye."

        Tsareta yayi da idanun, ɓata rai tayi cike da borin kunya tace.
"Ban gane ba, mana zargina ne idan da ina sonshi da tuntuni ina gidanshi, bana son haka karka manta É—an uwanane, da kake wannan maganar."

"Kenan kina sonshi? kike kokarin ɓoye emotion ɗinki akanshi Shkurah ki fada min me ya rabaki da shi, yanzun kuma NA hango sonshi a cikin idanunki ni mutum ne meson adalci idan kika min wallahi ashirye nake namiki, common fada min"

       D'ago kanta tayi duk kokarinta da taboye hawayenta amma ta gaza hanasu saukowa, a hankali tashiga bashi labarinsu.

         Har izuwa yanzun, jinjina kai yayi kafin yace.
"Hmm, Allah yasa mu dace zan tafi, kinsan gobe za'a É—aura auren anso É—agawa nace ayi haka muje ki karasa jinyarki agidana, da fatan banyi garaje ba."

     Girgiza masa kai tayi alamun a'a, yana fita ta fashe da kuka, tarasa meke damunta sai zuciyarta babu daɗi.

*........*
Ta bangaren Mashkur da jikinshi da sauki sosai dan har ya tashi kuma, umma ce a wajenshi ya É—an sake kaÉ—an sunyi hira jefe jeje,

  Can umma ta kalle shi, cikin nutsuwa tace.
"Ka faÉ—awa Kausar kuwa, baka da lafiya, naga matarka ma batazo ba ko tana can azare ne,"

dariya yayi yace.
"Umma kina son mommah ta birkice kenan kawai a barta idan nasamd sauki, zan faÉ—a mata."

         "Toh shi kenan, Allah yabaka lafiya."

*.......*
Washi gari.......
A can gida shirin É—aurin aure ake, amma asibiti ba haka abun yake ba dan daga shkurah har mashkur, babu wanda ya runtsa kowa da nashi fargaban.

        Abubakarne yazo ya canza umma, dan ta koma gida, yana zaune sai surutu yake, mashkur ya sunkuyar da kanshi baya uhh baya hmm,  karfe sha ɗaya dai rabi aka ɗaura auren, kiran Abubakar umma tayi ta faɗa mashi, ajiyar zuciya yasauke tare da cewa.
"Ubangiji ya basu zaman lafiya, da zuri'a É—ayyiba,Allah yasa karshen wahalarsu kenan"

      addu'a sosai yayi sannan ya katse kiran ya kalle mashkur, wanda ake wayar agabanshi, tsare abubakar yayi da idanun alamun tamvaya, dariya abubakar yayi, yace.
"An É—aura aurensu shkurah ne"

          lumshe idanunshi yayi, kafin yace.
"Allah ya bada zaman lafiya," daga haka be sake magana ba, sai ma rufe idanunshi da yayi, dan zuciyarshi ta mashi nauyi, tankar a É—aura masa dutsen warinji.

  *........*

Hankalin mommah a kashe har gida biu,ga jama'a da suka cika gidan, ga kuma rashin ganin mashkur, É—aurewa take amma ta gama sarewa da zuwanshi..

      Mika mata waya, Zuhra tayi tace.
"Gashi Umman bauchi take kiranki,"

          Karɓa tayi cike da damuwa, tace.
"Habiba, ya naku jama'a da fatan an É—aura cikin kwanciyar hankali,"

"Alhamadulillah, da fatan kuma haka, daman nakirakine na faÉ—a miki an É—aura auren autarki da yarona, don Allag karki hanasu cikar muradin yaronane don Allah ki samusu albarka,"

dariya mommah tayi kafin tace.
"Allah yayi musu albarka amna idan yan kawo amarya sunzo ki haÉ—asu, akawo min ita bari na sanar da cikin gida."

     kashe wayar tayi, ta aika cikin gidan wato fada, nan akaje aka faɗawa sarki hussain yayi murna sosai, sannan ya tura cikin gida aka faɗa,

      Lokacin da zubaida taji maganar auren mashkur haukane batayi ba dan gigicewa tayi tana kuka da ihu.

*.......*
  A bauchi kuwa abinda, ya faru shine. Bayan na'im ya bar asibiti yaje yasame faruq ya faɗa masa yanda sukayi da Shkurah kwarin gwiwa faruq ya bashi da ya hakura da ita,

       Shine da akazo ɗaurin aure kawunshi da kanin babanshi, suka nimawa mashkur auren shkurah a madadin Na'im abin ya bawa kowa mamaki,  ansa aure da kai an ɗaura da wani mutane da yawa sun saka mashi albarka, da yashiga gurin umma kuwa gaza ɓoye kukanta tayi sai da hawayenta ya zuba, tayi masa godiya sosai.

Asibiti ya tawo, shi da faruq suka shiga gaisawa sukayi, sannan ya zauna a bakin gadon yana kallon mashkur, gani yayi ya ɓata rai yayi ciki-ciki da fuska, dariyar da na'im yake dannewa ne yafito,

        dafa kafaɗar mashkur yayi, yace.
"Kalmar ina sonki ko nace (I love you) word ne masu sauki faɗawa, amma ayukarsu ba kowa yake iyawa ba, sai zaɓaɓe, naga finafinai na karanta novel da hikayoyi akan So, amma banga wanda yayiwa so Bauta kaman kai, ka sadaukar da rayƴuwarka dan Soyayyarka, ko laila majnun, da romeo da julient kashe kansu sukayi, akan so kai kuma, soyayyar kabawa rayuwarka bazan ɓoye maka ba, ko a wasa bazanyi abinda kayi balle a zahirance, kai masoyine na haka kika, dan haka nabar maka lailarka majnun, dan dakai tadace ba dani ba, sai kasake fiskarka dan tunda nashigo kake, hararata, sai kayi hakuri da rayuwa nadai bar maka matarka, indan mutum baeyi dagaske ba, tabbas zaka iya kai mashi nauhi...."

        Dariya suka saka, dukkansu, ɗago kai mashkur yayi, ya ma rasa tacewa  sunkuyar da kanshi yayi.

💋💋💋💋 Nima narasa abin cewa dan wannan irin Sadaukarwa haka.....
3/4/21, 9:48 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*

  '''LOVE AND TOUCHING HEART'''

MAI DAMBU CE

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.