Complete Hausa Novels

Kaddarar Rayuwa Complete Hausa Novel

Reading file: _KADDARAR_RAYUWA_cmplt.txt

Chapter 12 of 24

*Page 12*
Sai gashi umma itake rarrashin y'an gidan lokaci guda kome ya k'wauɓe a cikin gidan biki, Alhaji Hammayo kuka, yake tsakaninshi da Allah inda yayita k'washewa Aunty Amarya albarka, har kofar ɗakinta yaje yana tsine mata, karshe dai ya haɗa mata har da saki,

            Karin tashin hankali, umma ta tubure masa da ya dawo da ita kan y'ay'anta ko tafita tabar masa, gidanshi.
Zubawa Umma idanun yayi yana rike da kirjinsa, dakyar yaje sauke numfashi durkusawa yayi cikin tashin hankali ya faÉ—i,kasa yana tari jini yana fita daga bakinsa, haÉ—i da yawun me yauki.

           Nan akayi kanshi cikin tashin hankali, akayi ni'ima dashi.
         _Saurin fushi yana kawo danasani,yanke hukunci cikin fushi, yana kawo nadama mara amfani._

        ***
Kaltingo,kaman yanda corpru bala yayi mata k'watance haka, kuwa tasame Shkurah. Cikin mawuyacin hali, cikin gaggawa aka É—auketa zuwa, gidanta da yake cikin kaltingo, takira likitan da yake cirewa y'an matan da suke É—auke da ciki, a cikin yaranta da suke harkan zaman kansu.

         Duba shkurah yayi sosai, sannan yace mata,
"A gaskiya lady wannan yarinyar, zamanta a cikinku akwai hatsari, dan ki dubi zanin jikinta da É—an kunnen kunnenta, haÉ—i da, kidubeta da kyau y'ar manya ce, ba yar kananun mutane, bane kisan yanda zakiyi da ita."

          Murmushi tayi sosai, sannann ta gyara zamanta tace.
"Idan na turata kaduna gurin, kawata Umaima, ina ganin kaman babu matsala, ko?"

          "Eh duk yanda kikayi,dai-daine, zamanta a nan,me dai akwai damuwa." yace tare da hada kayan aikinshi yafiya.

             Cirewa shkurah kaya tayi, sannan tasake mata wasu,kiran drivent tayi tace.
"Ga yarinya nan, zaka kaimin ita, kaduna, na yarda da aikinka, katabbatar, kun isa lafiya yanzun, zankira Umaima, a waya."

     Yana tsaye takira,umaima ringing biyu ta ɗauka, lady tace.
"Ga kaya nan zuwa, wannan darajarta yafi É—aya da rabi, dan nima sai na biya, wanda ya kawo min ita.Sannan nima nacire iya abinda zan bawa driven zai kawo miki, ki kula dan akwai damuwa a tattare da kayan. katse kiran tayi, tana murmushi,

          A bayan mota suka. Sakata, sai Kaduna.

***
Cikin ikon Mashkur ya farka, nan likittoti suka rufa akanshi, inda suka cire duk wani naura dake jikinshi,
          A hankali abinda ya faru yashiga dawowa, brain ɗinshi siraran hawaye kebin gefen fuskanshi.
         Dr Lakshman ya kalle dr Ajay yace " maybe is love problem,"
   ɗaga kafaɗa, yayi alamun  haka, ne cigaba  da aikinsu sukayi suna gamawa suka juya wajen Mommah suka ce mata.

"Congregation mah, É—anki ya tashi mungodewa Allah dan shi yabamu ikon haka,"

       Haɗa hanunsu sukayi guri guda, kaman yanda saka saba al'adarsu.

       Murmushi tayi sannan itama ta haɗa hanunta tace.
"tabbas Ubangijine ya bashi lafiÆ´a, ta sanadinku ina muku, godiya akan namijin kokarin da kukayi akanshi Allah yabaku sa'a akan aikinku mungode"

          Murmushi sukayi sannan suka fita suna girmama karfin tauhid mommah.
     Ba dole ba,yar borno ce idan bata, san tauhidi ba ai a tambayeta.

     Kwananshi biyu, ya warware, magani nurse take bashi tunda yasha ya kafe mommah da ido, cikin sanyin murya yace,
"mommah don sonki da ubangiji, ki maidani, gida ina son sanin halin, da Shkurah take ciki."

           Shi tayi tana nazarin maganarshi, tasowa tayi tazo har inda yake,

        shafa kanshi tayi, tace.
"Insha Allah, jibi zamu koma gida,kaji kuma, muna komawa za'a nima maka auronta, kaji ko My son"

       Kwantar da kanshi yayi a jikinta, zafin kirjinshi yake masa, amma baya son yasake ɗaga mata hankali, dan yana faɗa zata iya ɗaga tafiyar. idan ya tuna Maina, ji yake kaman ya ɗauki Ak47 ya juye masa, duk bullet ɗin ciki, ak'ok'on kanshi, haɗi  wani yawu me matukar ɗaci yayi.Yana kisima yanda idan yaga Maina zai masa, dukan kisa,

          A cikin kwanaki biyu, su mommah, suka tarkato sai gida bayan Drs ɗin sunce duk bayan wata uku, yazo ana dubashi.

      ***
  A ɓangarensu Alhaji hammayo toh, akwai alamun nasara, sai dai, lokaci guda yasame mutuwar, ɓarin jiki, wato paralyze amma kome da sauki, wheel chair aka bashi.

  Rayuwa kenan.

      A ranar da shkurah keda kwana biyar da rasuwa, (inji mutane) a rana aka sallamo alhaji hammayo, suna zuwa ko minti goma basuyi ba, Mashkur da tawagar Sarki da suka je tarɓanshi, suka tawo gidansu shkurah.

         A hankali ya fito daga motar sauran mutane suma haka, Mommah da Nana, suma suka fito, shi yayi musu jagora zuwa cikin gidan, tare da sallama.

      Suka shiga bilal da yake, ɗakinsu shi ya fara fitowa, sabida jin muryan mashkur yasa ya fito ya gani ko karya kunnenshi yake masa.

  Yana ganinshi ya isa gurin tare da musu barka da zuwa, falon Baba aka kaisu. nan yake ya faɗawa Umma ɗakin Alhaji Hammayo, ya shiga ya ɗauko shi a kekenshi sannan yafito da shi.

       Su umma ne suka shigo da abubuwan drinks, nan aka shiga gaisawa, mashkur kan da bakinshi yayi masa nauyi sunkuyar da kanshi yayi ya gaisu,

        Baba galadima shi yafara, gabatarda sarki hussain da dalilin zuwansu yace, mun zo gidan nan ne  niman auron y'arku wa ɗanmu ne, da fatan bamu shiga wani niman ba."

        Shiru falon ya ɗauka, duk suka sunkuyar da kansu, sai umma ce kawai tayi karfin halin magana,amma taki yarda ta kalle inda mashkur yake dan karya mata, zuciya yake,
           tace.
"Ayya,sai dai kunyi hakuri dan, shkurah kan,"
    zaburowa, mashi yayi, yazo gabanta, yace.
"Don Allah, karkuce zaku hanani Abinda raina yake so, kuyi hakuri, na haÉ—aku da Allah kubani shkurah itace cikon rayuwata, sannan yankin rayuwatace, don Allah Umma, indai rashin zuwana na wani lokacine umma ku yafe min, amma kubani shkurah."

        Juyawa yayi ya koma. Wajen Mommah yace.
"Mommah kisa baki mana, don Allah karna rasata, nima rasa tawa rayuwar zanyi,"

     komawa wajen sarki hussain yayi ya rike kafarshi, yace.
"Abba bantaɓa saɓa umarninka ba, ni mai biyayyane, sannan zan iya kome dan farin cikinka, Abba don sonka da Ubangiji, kace subani, shkurah wallahi sai na maida ita macen da babu wata irinta, Abba kasa baki don Allah."

      kaf ilahin falon kuka, suke kansu a sunkuye mikewa umma tayi,zata bar falon mommah tace.
"Habiba Abubakar Waziri yola."

     cak ta tsaya, a hankali tasake juyowa, hawayen da bata son su zubo suka kuwa ɓalle kaman an buɗe famfo.
       Umma tace.
"Kausar  Muhmud Elkanami"

    girgiza kai umma ta sake cewa.
"ɗauke shi kutafi shkurah babu ita dan wanda ya bamu ya karɓeta, yayi hakuri, kowani rayuwa akwai jarabawa Allah yabamu ikon cinyeta"

       tana gama faɗan haka ta juya tayi tafiyarta cikin gida yana kuka, sai yau tasan shkurah ta mutu.

     Baki ɗaya network ɗin mashkur ya ɗauke......

Yaseen nima wata ta É—auke,
Allah sarki mashkuri😔
       
3/4/21, 9:46 AM - Ummi Tandama: *🙆QADDARAN RAYUWATA🙆*
_SHUKRAH_
Mai_Dambu

*Tabbas na yarda da maganan da ake cewa,kayi me kyau zakaga me kyau,Alhamdulillah, tsakanina daku sai godiya reader Allah yau bani da niyyar typing sabida uzurin gabana, Amma sai gashi, sabida ku dan farin cikinku, na sadaukar da lokacina dan na kyautata muku,Allah yasaka da alkhairin*

_Wannan shafin sadaukarwace ga Mahaifiya, ina nufin Uwa tawa taku, Uwayenmu dukkansu, Musamman Mahaifiyata Ubangiji ya gafarta miki, da sauran musulmin baki ɗaya_Allahumma Amin👏👏👏

     '''Swry duk wacce ta min magana taga banyi reply ba,tayi hakuri Saurayin kakata Fatima ne ya rikeni tun jiya Wato network sannan zaku ce toh fa'''😹😹😹

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.