Complete Hausa Novels

Basan Raina Bace Complete Hausa Novel

Reading file: Basan Raina Bace Complete Hausa Novel.txt

Chapter 8 of 17

___"I'm so so sorry my Basma duk duniya bawacce nakeso sama dake kuma nayimiki alkawari bazanso wataba never,'

Haka yaki bude wayarshi danyasan yana budewa zata kirashi shikuma baisan mezaice mataba dankuma yasan yana daga wayarta zatasamai kuka yarasa mekiyimai Dadi a duniyarshi gashi yakasa koda runtsawa ga yunwa yanaji but bazai iyasa komai abakinshi,'

Meenal tana kwance itama sai tunane tunane taketayi yayinda zuchiyarta tacika dam da fargaban gobe badan komaiba saidai tana tsoron ganin waye BASAM tareda fargabar karyaganta yace tafasa auranta inkuwa hakan yafaru batasan yazayi da rarraunar zuchiyarta mecikeda miki meyawan gaske

Basma tana tsaye tareda wayarta ahannu tanata Kiran layukan BASAM amma abun mamaki harzuwa lokacin akashe idanunta dasuke jike da ruwan hawaye tadago ta zubama agogo idanu karfe 2:30am nadare tafada gadanta sharab tareda sakin kuka,'. ____"why heart beat why do u do this to me baka taba sabamun alkawariba saiyau why kasan ina mutuwar sanka gashi wayoyinka duk akashe narasa yadda zanyi,'

Tasake ballewa da kuka tareda jifa da wayarta,'

Daga BASAM zuwa meenal zuwa Basma bawanda yaruntsa acikinsu yadda sukaga rana haka sukaga dare har garin Allah yawaye,'

*love u oll*

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“

*BASANπŸ“*
*RAINA BACE*

*BY__________________*
*_Badiat Ibrahim*_

*_________________71to75✍🏻*

Cikin sallama tashiga Gidan khadija da mama suka amsa mata yayinda aka gaggaisa Meenal tafito kanta asunkuye tagaida Momy da fara'a ta amsa sannan tamike takoma ciki gabanta yanata faduwa,'

__"amm Khadija kifita kishigoda BASAM yana cikin Mota,'

__"to mama,' amsarda tabayar kenan tazari hijabinta tafita atsanake takarasa wajan motar tareda kwankwasawa,'

Ahankali yazage glass din suka hada idanu da khadija zare idanunta tayi tareda rufe bakinta acikin ranta tace,'

___'lahhhh wanake gani ido da ido kamar BB dama shine wanda Anty meenal zata aure?,' inkuwa shine to wlh tamore da hadadden miji kuma jaruminda duniya tasanshi ta hanyar jarumtarshi,'

__"hellow lfy malama yahaka?,'.

"Firgigit tadawo daga zancan zuchinta tace,'. __"dama cewa akayi inyima jagora zuwa ciki sunana Khadija ina murnar ganinka sosai bismillah kashigo,'

Yadanja wani karamin tsaki Mara sauti kana yafito ahankali akyamace yaketaka kasar Layin yabiyo bayan khadija itakuma tanata mamakin ganinshi da sallamarshi yashiga Gidan dukkansu suka amsa mama tasha mayafi yatsugunna agabanta,'

___"ina wuni mama ya gida munsameku lfy,?:

___"lfy lau yahanya kadawo lfy ko?,'

___"ahh lafiya lau mama"

__"to madallah sannu Allah yayi albarka Allah ya tabbatar da aikairi' khadija kaishi falo yazauna mana,'

Khadija tamike yabiyo bayanta taimasa iso har falon sannan dasauri tasomakai abincin dakin shidai yana zaune tagama tsab tace,'. ___"yaya BASAM bara inkira Anty meenal din kaci abinci gashinan,'

Yabita da kallo kawai ranshi yayi mummunan baci sosai,'

Dagudu khadija tashiga dakinsu hartana tuntube

_"ke lfy meye haka dagudu?,'

___'uhm bazaki ganeba ina wannan shahararren dan kwallon dokinnan da kwanaki akayi hira dashi a NTA dinnan BASAM B salees wanda akabi Sani da BB ?.'

__"eh natuna wani abunne yasaneshi kome?,"

___"aa shine mijinki shine yakawo sadakinki shine yaron Momy shine BASAM dinki gashican afalo keyake jira,'.

Jadabaya meenal tasomayi tareda tariyo fuskar gayanda akayi hira dashi a Gidan TV __"BASAM shine dama yaron Momy turkashi nasanma bazai yadda ya aureniba shida yasaba Hulda da kasar turawa ina,'

___"karkice haka karkifa manta akwai sadakinshi agidannan harda baikonshi akanki aure yarage kawai kuma dama Momy tace shikawai ake jira bakiganshiba yahadu yafi Kyau afili wlh farine sosai fa,'

Meenal dai gabaki daya guiwowinta sunsage khadija tabata mayafinda tace dakanta tayafa mata kana asanyaye tafito tanufi kofar falon jikinta yanata rawa ga faduwar gaba dataketayi,' da sallama tashiga,'

Harsaida tashiga ta zauna sannan ya'iya amsawa a dakile baiko kalletaba yadaura kafarshi daya kan daya yana karkadawa,'

___"ina wuni kazo lafia ya hanya?,'

Saidayakusan minty biyar yadaure yace ___"lfy sannu '

Kanta yana kasane yayinda shikuma baiko kalletaba dakin yadauki shiru inbanda takaici daya rurnikeshi tareda wani zugi da zuchiyarshi takeyi babu abunda yakeji dataji shirun yaimata yawa tace,'

___"bakaci komaiba koruwa baka shaba?,'.

___"hmmmm ke nalura kinajin dadin kulani ko to kisani ninafi karfinki nesa bakusaba sannan kar kanki yabuga cewarni natako kafata nazo wajanki never kinyi kadan nazone sabida Momy kuma umarninta nabi kingane ko dan haka kikama kanki bansan kauyanci,'

Maganganunshi suka huda dodon kunnenta tareda ratsa duk illahirin jijiyoyin jikinta hawayene ya gangaro a kumatunta yayinda tatsuke bakinta tayi shiru kanta yana kasa yana digar hawaye

Mikewa yayi tareda wani kallamata uwar harara yaja tsaki haryakai kofar fita yatsaya tareda Ciro bandirdin kudi dubu Dari yajefa mata cinyarta yafice abunshi,'

Mama tana hangoshi tasoma murmushi. __"kafito kenan abincinfa kaci kuwa?,'

Yadan Sosa kanshi,'. ___"am banciba akoshe nake a office ne akaikirana ana nemanmu shiyasa tafito da wuri,' yasaka hannu a ajjihu yaciro dubu Dari ya ajjiye,'. Nizan koma,'

___"to madallah Allah yasaka da alkhari sauka lafiya,'

__"mom ina jiranki amota,' yasaka kanshi yafita jiyakeyi kamar yamutu yahuta da rayuwarshi,'

___"to mama saikusoma gaiyatar Yan Uwa nanda sati biyu za'a daura aure sannan ta bangaran kayan dakin amarya wannan kibarmun komai duk abunda Uwa takema diyarta nizanma meenal kudai diya muka nema awajanku ita zakubamu insha Allah bayan meenal bama bukatar komai sannan abincin daza'aci zansa akawo muku komai.'

Kuka mama tasaka tanata godiya meenal tana tsaye abakin kofar falo tana jiyosu kukanta yasake tsananta tareda tsantsar tausayin kanta saidataji tashin motarsu tafito tashare hawayanta ta daddaure bataso tabatama mama rai tabata wannan kudin tahada danawajanta daki tasoma tazauna Tarasa abunda keyimata Dadi aduniya tanaso tayi kuka kozataji sanyi amma badama,'

Basma v
Ce amota itada kawarta manan suna tafe danzuwa gidansu BASAM suduvashi sujiko lafiya sunkaraso kofar Gidan yayinda megadi ya tambayesu sukace wajan BASAM sukazo yabude musu suka shigo taredayin parking motarsu a harabar Gidan,'

Ummu tace,'. ____"leka kigani megidane suka dawo?,

Dasauri kausar taleka tahansu Basma tace '. ____"basubane inaga baki Momy tayi yan matane su biyu gasunanma shigowa,'

Da sallama suka shigo tareda zama akujera suka gaisheda Ummu kausar tamike takawo musu abunsha sunadai zaune sunacin dambun kifi Basma tadauki remote tacanja chanal TAKAI inda takeao ta kalla Ummu tajuyo tace,'

___"bamufa ganekuba wajan wakukazone?,'

Manan tace ___"sunana manan wannan kawatace Basma munzo wajan BASAM ne Basma budurwarshice munkawomai ziyarane,'

Basma tace,' ___"eh hajia nice batsman shi dama munzone muganshi yana cikine?,'

Mamakine yakashe Ummu da kausar kamun suce wani Abu motar BASAM tashigo Gidan ',

*love u oll*

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“

*BASANπŸ“*
*RAINA BACE*.

*BY_________________*
_*Badiat Ibrahim*_

*___________________76to80✍🏻*

"Momy cetariga shigowa cikin sallama daukeda farin ciki a fuskarta ganinsu Basma yasata karaso,'

____"sannunku ahh baki mukayine kausar kawayankine?,'

Manan tace,'. ___"amm sannu Momy ina wuni?,'

___"lfy lau Yan mata daga ina?,'

___"dama munzo wajan BASAM ne ,'

Mamakine yacika Momy tace,'. ___"BASAM kuma?.

Da sallama yashigo falon yana ambatan ,'. ____"Matas matas bazakizo kizo kimun tarbaba ko?,: carab suka hada idanu da Basma gabanshi saidaya fadi yayi kasake awajan yana kallonsu cikin tuhuma,'

Ummu tamike tace,'. ___"saika karaso ga bakinka nan suna jiranka.' Tajuya tawuce kausar tabiyo bayanta suka wuce ,'

Momy takuramai idanu yayinda Basma takurama BASAM idanu juyawa tayi tawuce daki falon yarage dagashi saisu,'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.