Complete Hausa Novels

Basan Raina Bace Complete Hausa Novel

Reading file: Basan Raina Bace Complete Hausa Novel.txt

Chapter 5 of 17

___"I have too go know idan Ummu tatashi kisanar da'ita natafi plz Auta karkifa tasheta abacci kinji magani tasha,'

Kausar tamike tareda mannama mom dinta kiss a kumatu,'. ____"saikindawo Momy bazan tashetaba nima sama zankoma indan kwanta.'

Sukayi sallama Momy tawuce kausar ma takoma sama abunta,'

Meenal tana tsugunne tana wankema mama kayanta yayinda khadija kuma take wanke wanken kwanuka mama tana zaune takurama meenal idanu tana nazari akanta,'

Meenal kuwa tashagala wajan tunanin Anas tareda abubbuwan dasuka faru take zuchiyarta ta jagule har idanunta suka cika tab daruwan hawaye,"

Sallama suka tsinkayo Na macce mama ce ta amsa tareda cewa,'. ___"bismillah shigo mana,'

Momy tashigo dasauri meenal tadago suka hada idanu da Momy dasauri tamike tsaye,'

___"Momy sannu dazuwa shigo momy gawaje kizauna,"

Mama cikin fara'a tace,'. ___"sannu dazuwa gawajan zama zauna bismillah,'

Momy taji dadin tarbar da akaimata zama tayi tana murmushi,'

Khadija tamike tareda debo ruwa akofin silver me murfi tatsugunna ta gaida Momy cikin fara'a ta amsa tareda tambayar sunanta,'.

Meenal ta tsugunna,'. ___"Momy ina wuni kinkoma gida rannan lafiya? Nagode sosai Momy,' tajuyoda kallonta ga mama tace,'. "Mama wannan itace wacce nake baki labari sunkaini makaranta rannan,'

Cikin fara'a mama tace,'. ___"ayya mungode sosai hajia da taimakonki Allah yasaka da alkhairi,'

Meenal tatashi tabasu waje,'

___"a haba haba wlh bakomai meenal Ai diyatace nayabada hankalinta Dari bisa Dari musamman danazo naga irin tarbar dakukaimun kun amsheni hannu bibbiyu batareda kunsanniba naji Dadi a gaskia,'. Hakanne yasake bani karfin guiwa kan musabbabin abunda yakawoni gareku,'

Mama tace,'. __"to Allah yasa muji alkhairi hajia,'

____"insha Allah aikhairine wato hajia tunranda nasaka meenal araina nayi matukar yabawa da kamalarta tareda shigarta da mutunci dakuma nadauketa amota zuwa makaranta yanayin yadda ta girmamani yamun Dadi abunda yafi burgeni da meenal nadauko kudi nabata taki amsa taburgeni sosai inbazaku damuba inkuma ba'a rigamuba ina nemama Dana auran meenal,'

Mama tadago da Sauri tana kallon Momy cikin mamaki tace,'. ___"dankifa kikace kike namama auran meenal?,'

___"eh Dana ko akwai wata damuwane kokuma meenal takusa aurene?,'

Ajjiyar xuchiya mama tasauke tace,' ____"aa bata kusa aureba hajia nadaiji mamakine dakikace kinzo nemama danki auran meenal,'

____"insha Allah nayi muku alkawari meenal bazatayi kukaba insha Allah dandauki amanar meenal tareda bata farin ciki kwarkwadon iyawata zanbaku lokaci kuyi tunani sannan ki tambayi meenal inta amince to zandawo jibi zanji Duk hukuncin dakuka yanke,' amma kisani harcikin zuchiyata inasan meenal nayaba da tarbiyyar dakika bata sosai,' nizan koma.'

Kudi ta ajjiyema mama bandir guda

___"aa wlh hajia kibar kudinki mungode sannan insha Allah zan tattauna da meenal duk abunda tace zakiji insha Allah,'

___"babu Kyau mayarda hannun kyauta baya kinada ilmi nasan kinsan hakan to Allah yasa muji alkhairi Allah ya tabbatar mana,'

__"Ameen hajia mungode sosai, meenal! Meenak!!! Kifito hajia zata tafi,'

Dasauri meenal tafito tareda raka Momy har Mota tace,'. ____"Momy nagode sosai naji dadin ziyararda kika kawomana Allah yabada lada,'

___"Ameen meenal zakibani number ki yanzu saimudinga gaisawa meenal zakiji sako awajan momynki dan Allah karki bani kunya karkisani inji badadi plz ina rokonki meenal,'

Dasauri meenal tadago tace,'. ___"plz Momy kidena rokona zakisa inji kunya insha Allah bazansa kiji badadiba niyimiki alkawarinnan Momy.'

Murmushi tayi tareda godema meenal tabata number ta itama tabata nata meenal tana wajan har saida motarsu Momy tabarwajan sannan tasauke ajjiyar xuchiya tajuya zuwa cikin gida,'

Mama tace,'. ___"meenal karaso nan muyi magana,'

Atsorace meenal takaraso tareda zama kanta yana kasa,'

Mama takwashe duk yadda sukayi da Momy tasanar da'ita babu abunda tarage Mata,'

Hawayene yagama wanke fuskar mrenal zuchiyarta dukta jagule tarasa yazatayi nezatace,'

Khadija takaraso gaban meenal tana share mata hawayanta dagowa meenal tayi suka hada idanu da khadija rungume junansu sukayi Suna kuka dukkansu

Mama tayi shiru tana kallon yaranta wadanda suka bata tausayi,'

Meenal tace,'. ___"aa mama kicemata tayi hakuri mama basan sake bari zuchiyata takarye akaro Na ukuba domun nasani za'a fada musu komai zasukuma gujeni mama inyi yaya da zuchiyata mikin zaimun yawa wlh bakiji yadda xuchiya takemun daciba yanzu haka bazan iyaba mama,'

Khadija tace,'. ___"zaki iya Anty meenal kibashi dama domun baduka bane akazama dayaba sannan dan Yusuf ya gujeki Anas yagujeki bashi bane hujjar kindena yadda dakowaba kibama zuchiyarki hakuri insha Allah bazata sake samun mikiba awannan karon kiyi tunani kamun kiyanke hukunci,' domun nayabada kirkin Momy sosai tanada sakin fuska taredasan mutane dan Allah kizauna kiyi tunani kamun kiyanke hukunci,'

Mama tasauke ajjiyar xuchiya tace,'. ___"maganarda khadija tafada gaskia ne meenal Dole zakiyi aure tunda bazaki zauna hakaba Dole kimanta da baya mufuskanci gaba meenal kiyi tunani tareda dogon nazari kamun kiyanke hukunci zanbaki lokaci kiyi kokarin tausar zuchiyarki,'

Haka meenal wunin ranar tayishi basukuni dukta takura kanta tanata tunane tunane
Kashe wayarta tayi dib haka meenal takwanta da tunani fal ranta,'

Yayinda Momy takoma gida tanata murna tareda zaiyanama Ummu duk yanda sukayi takuma baiyana mata karamcin gidansu meenal tareda yanayin nagaartar Gidan sukaita tattaunawa suna farin ciki,'

*love u oll*

🏓🏓🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓🏓
🏓🏓🏓
🏓

*BASAN*🏓
*RAINA BACE*

*BY_______________*
*_Badiat Ibrahim_*
*________________41to45✍*

_BASAM_ yatashi daga bacci kaitsaye yafada toilet yayo wanka tareda dauro alwala yafito yayi sallah kana yashirya tsab cikin farin wando da Riga farin takalmi farar pesincap farin agogo kamai najikinshi farine dan *BASAM* yanasan fararan kaya dan kusan dukka kayanshi farare sunfi yawa laptop dinshi yabude yasoma aiki gabaki daya yamaida hankalinshi kan laptop dinshi wayarshi tasoma kara yadago idanunshi yana ganin mekiran nashi yasaki tattausan murmushi tareda saurin daga wayar,'.

___"my hot milk yaya akayi to kinganni ina zaune inadan aiki a laptop anjima munada kwallo dazamu buga dawasu club din saikimun adda'a ko?

___"insha allah heart beat club dinkune zasuyi nasarar cinye wannan kwallo aina yadda da aikinka domun mekyaune kamarka yes heart beat,'

___"uhm kina yabona sabida ninakine ko Bby girl dama muna tare Dana sumbaci lips dinki naji dadin yabonda kikamun hakan zai sake karfafamun guiwa sosai '

"Saikuma tashagwabe mishi tanamai shagwaba tanadan kukannan nawasa '

Lumshe idanunshi yayi tareda dafe kanshi yace,'. ___"come on Bby girl relax relax menene fadamun mana aisaiki tayarmunda hankalina kinsan banasan abunda zai tabaki so tell me I'm listing to u,'

____"heart beat I missed u so much sannan yakamata muyi maganar aure sabida ina bukatarka akusa dani u have to do something plz plz

Kuka tasakamai awaya,'

Rarrashinta yashigayi dukyabi yarude,' listing Bby girl relax mana inbakyaso raina yabaci kiyi shiru yazaki dingamun westing mun hawayanki yana zuba abanza listing to me Bby girl I promised u ina dawowa zanfadama mom komai saita sanar dasu uncle's dina saisumu Dad dinki ayi magana ,'. So are u happy nw? 🙄

___"yea I'm very very happy heart beat love u so much tasakamai ihu akunne yadan kashe idanunshi daya yana daria kasa kasa

___"any way Bby girl lokaci yakusa so I have to go nw,' but promise me bazaki sakemun kukaba plz Bby banaso kinsani Ai,'

__"come on heart beat nashare hawayena Ai basauran kuka I promised u I will never do it again,'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.