Complete Hausa Novels

Basan Raina Bace Complete Hausa Novel

Reading file: Basan Raina Bace Complete Hausa Novel.txt

Chapter 7 of 17

Anyi sallar magrib basam yana masallaci yanata laximi har aka kira sallar isha sannan yafito yadan gaggaisa da mutane sukuma sunata tuttudowa dan sugaisa dashi juyawa yayi yakoma gida da sallama yashigo falon,'

Bakowa afalon kaitsaye yawuce shashen Momy tareda sallama,' tanakan sallaya tanajan carbi yashigo tareda zama atattausan kafet din dakin nata,'

Saidata gamajan carbinta tayi adda'a suka shafa tare tajuyo tace,'. ____"katashi Ashe natura kausar tatasheka taga bakanan sainace to katafi masallaci,"

____"eh Momy ainatafi masallaci yanzu shigowata shine nazo akan maganar dakikace zamuyi ina sauraranki,' BASAM yayi tsai yana kallon mom dinshi yaji mezatace,'

____"gaskia ne BASAM to dama bawani Abu bane akwai wata Yarinya wato damuka hadu kwanakin baya da'ita akofar makarantarsu sannan danasake fita nasake ganinta yarinyar ta kwantamun araina sosai nayaba da kamalarta da shigar mutuncinta hakanne yasa harna dauketa amota zuwa islamiyya wlh bakaji kalaman bakintaba cikin biyayya gasu masu Dadi,' sainatura abakar yaganomun gidansu kuma mukayi nasara yagano naje Gidan iyayanta Yan mutunci masu San mutane an karramani agidan sosai BASAM sunan yarinyar *MEENAL*",

Yayima Momy murmushi yace ___"Allah sarki mekikeso to aimusu suna bukatar taimakone?,'

___"eh to kusan hakan domun natura kawunanka wajan iyayanta antsaida magana yanzuma haka da baikonka akanta kaimuke jira dama kadawo sai agama komai,'

Dasauri yadago yayinda yaji wani razanannen faduwar gaba kanshi yawani saramai bakinshi yana rawa yace,'. _____"mom banganeba mekikeso kicemunne bangane hausarkiba,'

______"uhm BASAM ina nufin meenal itace matarda Na zabama kuma kawunanka sukaje nemamaka auranta kuma anbaka dan har'ankai akwatin Nagani inaso anyi baiko,'

Rassss rasss yagabanshi yasake yankewa yazube yayinda yaji kanshi yanata wani Sarawa yadafe kanshi tareda sauke idanunshi kasa zuface tashiga ketomai takota ina dukda sanyin a c din dakin wani dacine yasoma keto mashi daga kirjinshi zuwa bakinshi gawani jiri dayake kwasarshi idanunshi sukayi jajir suka cicciko da kwalla yamarasa mezaice,'

___"inkaganta zaka yaba sosai sannan kasandai bazan zabarma abunda zai cutar dakaiba amatsayina na mahaifiyarka banida burin daya wuce inga kasamu macce tagari wacce zata tsarema mutuncinka da darajar iyayanka Na tabbata meenal duk zatayi abubbuwan Dana lissafo dinnan,'

Idanunshi sunzama tamkar garwashin wuta yayinda fuskarshi tazama jajir yace,'. ____"to Momy bakomai nagode dskulawarki agareni tunda tayimiki shikenan Ai,' amma meyasa ba'ayi shawara daniba kuka yanke hukuncin........

____"aa BASAM meenal itace wacce tadace tazama matarka
Domun annabi (s a w) yace ana auran mace sabida Abu hudu,
Nafarko zaka iya auran macce sabida dukiyarta
Nabiyu zaka iya auran macce dan kyawunta
Na uku ka auri macce domun danginta wato nasabarta
Sannan Na hudu ka auri macce dan addininta
Sannan daga karshe Annabi (s a w) yabamu shawara ka auri macce ma'abociyar addini hannunka ta yalwata ma'ana iyalanka zasu tarbiyya irinta addinin musulunci
Dan haka na kwadaitama auran meenal BASAM inkanaso raina yayi fari to ka auri meenal,'

Kanshi yadafe dayake kokarin tarwatsemai wai kamarshi za'a zabama macce baza'a barshi yazabi San ranshiba yace,'. ____"shikenan Momy Na amince da auran tundahar takwanta miki aranki,"

Murmushi tayi mai,'. ___"alhamdullah naji dadin wannan zancan Allah ya tabbatar da alkairinshi sannan gobe kashirya da yamma zanmuje gidansu meenal din ,'

Aranshi yace,' ___"ninema zanje gidansu bayan ko Bby girl dina bantaba zuwa gidansuba saidai muhadu a park wainine zanje wajan wata dasunan zance tarainanima kenan hartadauka ta'isane ina bazai yuyuba gaskia,' afili yace,'. ____"gobe inada mitting dazan attending da misalin karfe uku kuma bansan yaushe zamu fitoba kibari musaka wata rana,' mikewa yayi tsaye cikin kunan xuchiya da bacin rai yace,'. ___"nizantafi mukwana lfy,'

Tace ___"to tunda kanada mitting da yamma maje da rana sabida nariga nasanar dasu goben zamuzo so yakamata muje,'

Baice komaiba yafice adakin bayako iya kallon gabanshi haka yakarasa dakinshi tareda fadawa Gado yana dafeda kanshi wanda yakeji kamar zai dagargaje yace,'. _____"why Momy meyasa zakisa baki acikin rayuwata meyasazaki zabamun Matar aure bayan inada wacce nakeso why why???,'

Yanaushi pillow dake kusa dashi tareda mikewa yazabura tace,'. ____"ina bazai yuyuba baxan auretaba domun *BASAN RAINA BACE,'* inada wacce nabama zuchiyata I'm so sorry Momy bazan iyaba,' bude kofar yayi tareda fita yanufi dakin Ummu yasameta tana zaune tanashan maganinta Na hawan jini yasamu waje yazauna babu annuri Sam a idanunshi,'

Ummu tace,'. ____"megida takobin yaki yanaga ranka abace kazomun ayanayinda bansaba ganinkaba lafiya incedai bawani Abun bane yafaruba ko?,'

Yadago idanunshi dasukayi jajir dasu yace,'. ____"magana nazo muyi domunni nasan kezaki taimakamun dan bazakiso abunda zai zamemun matsalaba arayuwata ba .'
Tasowa yayi tareda tsugunnawa agabanta aguiwowinshi biyu yakamo hannunta yace,'. ___"kitaimaka kisa baki kifadama Momy inada wacce nakeso wacce zuchiyata tazama mallakinta dan nariga nabata amanar zuchiyata Momy tazomun dawani batu wanda kwakwalwata takasa dauka balle zuchiyata plz kisaka baki tajanye furucinta,'

*love u oll*

πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“πŸ“πŸ“
πŸ“

*BASANπŸ“*
*RAINA BACE*

*BY__________________*
*_Badiat Ibrahim_*

*________________61to65✍🏻*

__"wlh banasanta,'

Ummu tazame hannunta acikin Na BASAM tareda matsawa gefe .'. ____"kasani duk wacce kakeso bazatakai nagartar meenal ba nima nakwadaitama auran meenal domun meenal salahace BASAM matan yanzu basuda tabbas ta'iya yuyuwa wacce kake ikirarin kabata amanar zuchiyarka ita awajanta bahaka bane ta'iya yuyuwa tanasankane dan wani Abu daka mallaka amma meenal ta amince da auranka batareda tasankaba balle tasan kokai waye tanayima mahaifiyayyar ka biyayya tareda kyautata mata danima kaina,' zama tayi akusa dashi takamo hannunshi tace. __"inasan kayima mahaifiyarka biyayya kaso abunda takeso karkaki bin umarninta akaronta nafarko data bukaci wani abu daga gareka kuma kanada halin yimata abun sannan Kai mijin macce hudune kana iya auran waccan bayan ka auri meenal,'

Hawayanshi dayaketa kokarin tarewane suka biyo kumatunshi zurrrr zurr yamike tsaye tareda juyama Ummu baya,'. ____"naji zan aureka tundakema kin amince in aureta din amma kisani *BASAN RAINA BACE* ummu I'm so much love Basma she's the love of my life yazanyi in tunkareta da zancannan ta'ina zanfara ni atsarina babu auran mata biyu kuma bazanyiba dan bazan iyaba yazanyi da Bby girl dina?,: yasauke kanshi yayinda zuchiyarshi tashiga tafasa

___"saika bata hakuri aitasan iyaye tasan mahimmancin iyaye indai da gaske tanasanka zata tayaka kayima Salma biyayya tayi hakuri tasamu wani mijin ta aura aidama ance Matar mutum kabarinshi in kaddara ta lissafota acikin matanka dole ka aureta inkuma dama ba matarka bace bazaku tabayin aureba,'. Babana kayi hakuri ka yadda zaka faranta ran Salma dani kakarka?,'

Yadago kanshi ya kalli Ummu yaga duktabi tadamu kanta gashi yana bala'in San kakarshi yadaure tareda karasowa gareta yace,'. ___"Na amince shikenan bawani Abu Ummu kiyi murmushi plz karkiyi fishi da mijinki kuma karki fadama Momy munyi wannan maganar.'

Murmushi taimasa tareda kamo hannayansa tace,'. ____"Allah yaima albarka kuma bazan sanar da'itaba aini takace kokaifa.'

Sukayi daria dukkansu yaimata sallama yafita,'

Daki yakoma yakasama yin komai yana kwance rigingine yanata tunane tunanen yadda zaiyi zuchiyarsa tanawani tafasa tunkamun yaga wacece meenal yaji duk duniya babu wanda yatsana kamarta idanunshi sunkada sunyi jajir dukyashiga firgici,'.

Yashiga tunanin Basma dinshi wanda yaimata alkawari zasu hadu yau yanada tabbacin takira wayarshi yafi sau Dari zataji akashe,' yalumshe idanunshi yayinda yabude yakurama wani zabgegen hotonshi dake jikin bango idanu shi ba hoton yake kalloba amma kai inkashigo zakaga hoton yakurama idanu tunaninshi yayi zurfi,' yabude bakinshi yace,'

Chapter Navigation

Use this section to move to any chapter without going back to the top.